KIBIYAR AJALI 23

Advertisement

 2___3*

 

 

*KHADIJAA*

 

   *Kukan* rabuwa da Mas’oud da nake yi ashe ba komai bane sai da naji ance Sarki Salman shine miji na, A take na yanke jiki na sume ban sake sanin inda kai na yake ba. Haka yake a bangaran Mami, tana

jin wanda aka aura min itama ta yanke jiki ta fadi, ganin mu biyu abun ya faru, sai ba ayi tunanin bakin cikin darajar wanda na aura shine yasa Mami suma ba, aka dinga cewa ai mayya ce ta kama mu, wasu suce jefa aka yi mana ni da ita. Aka dinga bamu taimako har Allah yasa Mami ta dawo cikin hayyacin ta, ta tambaya waye mijin nawa suka tabbatar mata cewar sarkin Basannabas.

 

Advertisements

Amman Alhaji ya Munafince ta da gaske, shi yanzu saboda tsabar rashin tunani ya bar ya’yan cikin sa ya dauki yar kauye wacce iyayenta basu bar mata gadon komai ba ya bawa sarki guda. Anya akwai miji irin nata kuwa marar lissafi idan ba na dukiya ba? Ban da haka ya zai yi wannan shirmin sai kace wanda aka cewa jeka ka gani. Shikenan aikin gama ya riga ya gama tunda har an riga an daura babu yadda za ta yi, Dije tayi sa’a sauran su Shukrah wanda take hango musu matsayin matan shugabanin kasashen waje ko na cikin gida Nijeriya.

 

*SAS*

 

Sarki Salman kuwa ana gama daurawa ya tattara suka tafi, Bai yadda ma sun koma masarauta ba yace a kai shi airport zai jira lokacin tafiyar shi ya yi. Kamar ya sani dan da ya koma da yaga abin da ya ragowa kansa, saboda su Galadima sun sanarwa su Gimbiya Shaheedah zancen auran tana can tana haukan kuke koke da zage-zage tare da cewa sai yasan yaci amanar ta, ya Munafince ta ya yo mata kishiya kuma yar matsiya ta. Labari ya kuma zuwar musu cewar ai ba zai dawo ba ya wuce Cyprus. Koda su ga kai shi guri na musamman aka bashi ya zauna dan jiran lokacin tafiyar, mulkin kuma ya barshi a hannun waziri duk kuwa da yaso su tafi tare amman Salman d’in ya ce aka ya yarda dashi shi yasa yace ya koma ya rike masarautar kafin ya dawo.

 

   Yana zaune ya rasa yadda zai yi saboda Alhaji Isma’il ya tambaye shi a wane muhalli zai ajiye Khadija saboda suna son aje a shirya gurin, yace masa zai kira shi a waya idan ya gama shawara. Da wa zai yi shawarar ma oho masa. Wani tunani yazo masa sai ya kirawo bafadansa da ke yi masa wasu abubuwan masu muhimmanci wanda be son kowa yaji, yana can bakin kofar da yake saboda tare zasu. Ya shiga tare da dukawa har kara ya yi gaisuwa tare da yin shiru yana jiran umarni.

 

“Ka kira mahaifin yarinyar nan kace idan sunje a nuna musu bangaran Abdullah, idan an nuna musu nan zasu kai ta har na dawo.”

 

“Takawarka lafiya sarkin mu mai share hawayen mu. Aiki ya gamu da ikon Allah, gaba salamun baya salamun d’an toron giwa.”

 

Advertisements

Al-hassan bafade ya fada yana mai ficewa daga cikin dakin.

 

Yana fita ya kira lambar Alhaji Isma’il tana ta ringing amman be daga ba, ya yi tunanin kila yana cikin mutane dan shi kansa Al-hassan yaga yadda yan kasuwa suka cika gurin daurin auran, sai da aka dan jima ya sake kira sannan yaji ya dauka, suka gaisa ya sanar dashi sakon sarki Salman. Da farin ciki Alhaji Isma’il ya amsa sannan yaje ya gayawa su Mami cewar azo aje a gyara bangaran da za’a kai Dije. Aikuwa sai ta je itama kodan taga me zai faru, daman kuma ba shiga masarautar ta taba yi ba yau gashi ta sanadin Dije zata shiga son ranta.

 

*KHADIJAA*

 

Ni kuwa sai da ta kai ta kawo an saka min drip, kawu daddy sai addu’a yake Allah yasa na samu sauki a kai ni gida na kamar yadda ya yi alkawari, ba ya san a samu matsala shi yasa da ya fita zai dawo yace ya jikin nawa. Allah sarki Mas’oud abin kauna ta, an raba ni dashi a lokacin da zuciyata ta makance akan shi. Tabbas nasan zan rayu ne cikin kunci da zama da makiyi, ba wai nafi karfin auran sarki Salman ba. A a kawai zuciya ta bashi take so ba, na kuma san akwai wata manufa da ya sanya shi auran ta, ban da haka me yasa lokacin da ta karaci kwanciya a asibiti be taba zuwa ya duba ta ba sai da ta warke sannan ya turo dan munafunci wai a duba ta.

 

Ai kuwa tun kayan da nasa da safe ban cire ba, Babu yadda ba’a yi dani ba akan na canza amman naki dan banga dalilin yin kwalliyar ba. Aisha ma tun tana jin haushin naki canza kaya har ta dawo tana lallashi na akan auran dan ita kanta ta yarda da cewa Mas’oud shine buri na, amman babu yadda zanyi kaddara ta riga fata. Ta kuma yi min murna cewa matarsa daya ni ce ta biyu, amman nasan ai zai karo biyu tunda sarakuna baka raba su da aure-aure. Amman da Mas’oud ne nasan sai mutuwa nida shi babu kishiya.

 

 

      ••<>••.  ••<>••.   

 

  Yan tafiya gidan jere suka tafi kusan mota uku saboda kowa yana son zuwa ya ganewa idanunsa. Na kuma fashewa da kuka tabbas zanje gidan can tunda gashi har an tafi shirya min kaya na a can, wayyo Allah, sai naji har gwara zama wajan Gajiyalle da auran nan da za ayi amfani da ni wajan cin mutunci.

 

 

*MASARAUTAR BASANNABAS..*

 

Lokacin da su Mami suka shiga masarauta daman waziri yasan da zuwan nasu hakan yasa basu sha wahala ba gurin shiga cikin gidan. Nan suka tambayi sashen da za a sanya amarya, waziri yasa aka nuna musu wani waje can kusa da sashen Gimbiya Sa’adatu wato mahaifiyar sarki Salman, wacce ba ta san wainar da ake toyawa ba a masarautar, kasan cewar tana zaune ta tashi da wata irin ciwon kafa (muscle spasm) ta yadda ko tashi ba ta iya yi. Matar kawu Hashim ce ta fara bude kofar tayi bismillah tare da kallon kowa da suka zo tace suma suyi sannan su shiga. Haka suka dinga yi har suka shige cikin sashen masu guda nayi masu hotuna suna yi masu fara shirya-shiryan gurin suma duk sun fara.

 

Gurin ba laifi babba ne, sai dai be kai gurin sauran matayen ba kasan cewar daman an yi shi ne dan yarima Abdul kuma ba a nan yake zaune ba shi yasa aka bawa Dije shi. Suna cikin aiki sai ga gimbiya Jaleela tare da bayin ta masu take mata baya. Babu ko sallama haka ta shigo tana kallon su one by one daga bisani kuma ta tabe baki sai faman hura hanci take yi, su kuma duk sun dauka cewa uwar gidan sarki Salman ce.

 

“Wacece gwaggon amarya?”

 

Aka fara kallon kallo ko wacce jira take ace itace, sai kuma matar kawu Kabiru tace.

 

“Ko wacce a nan akwai matsayin ta, amman ga marikiyarta wacce ta rai ne ta har zuwa yau.”

 

Suka nuna Mami wacce itama saboda mulki wai ita matar babban d’an kasuwa. Gimbiya Jaleela ta kare mata kallo tas, ganin babu abin da zata yi mata gori dashi sai ta rausayar da kai.

 

“Ya yi kyau uwar amarya, muna fatan dai kun shirya mana ita sosai.?”

 

Itama Mami sai da ta sha kamshi tamkar ba zata ce komai ba sai suka ji tace.

 

“Sai ma ta shigo zaku tabbatar da hakan. Shin maman sa ce ke?”

 

Gimbiya Jaleela ta cije lebe ganin da ta yi ba ta da tsoro kenan.

 

“Eh tamkar uwa nake a gareshi, amman dai zaku sani nan gaba.”

 

“Shikenan ranki ya dade, Allah ya nuna mana lokacin.”

 

Juyawa gimbiya Jaleela tayi ta nufi sashen gimbiya Najwa, a can duk ta same su zazzauna sun zabga tagumi da alama ita suke jira daman. Guri ta samu ta zauna itama tare da jan numfashi ta sauke da karfi tana cewa.

 

“Ashe ma yar riko ce, shi kuwa yaron nan a gidan waye ya ganta?”

 

“Yanzu dai kin makala man a jikin wani abun na ta ko kuwa?” Gimbiya Huwaila ta tambaya cike da zakuwa.

 

“Na makale shi a jikin one seater d’in parlorn.”

 

“Good job Jaleela, yanzu sauran na kofar dakin, shi kuma sai da yamma idan Allah ya kai mu. Zanje nasa shi kamar yadda Abba Galadima yace.” Cewar Najwa tana tsuke baki.

 

“Bamu san abin da zai faru ba kenan wallahi, da duk ba zama mu bari ta shigo cikin gidan nan lafiya ba ma. Salman ya ci ka marar mutunci wallahi, ace har kana ta shirye-shiryen aure amman baka sanar da kowa ba sai a ranar dan tsabar wulakanci? Amman babu komai zai gane duk wannan abun nashi babu inda zai kai shi. Shaheeda ki dena kukan nan haka, kinji dai abin da Baba ciroma yace, sai ya gwammace beyi wannan auran munafincin ba.” Najwa ta yi maganar cike da tsantsar takaici.

 

Shaheeda dake zaune kasan carpet kanta yana kan cinyar Gimbiya Huwaila sai faman bubbuga bayan ta take yi alamar lallashi. Cikin kukan bakin ciki ta fara magana tana dafe kirji da alama zuciyar ta tana cikin hargitsi, tace.

 

“Bana tunanin Salman ne yace yana son auran nan, wallahi ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba nasan jan zuciyar shi akai ta hanyar yi masa asiri. Ban da haka ta ya za ai ace wanda ko daga ido ya kalli mutane ba ya iya ya bare har yaga wata banza wacce ba kowan kowa ba yace zai aura? Na rantse da Allah asiri suka yi mishi, kuma wallahi sai ta gwammace ba ta aurar min miji ba. Saboda ni kadai ce tashi babu wacce ta isa ta shigo min bukka dan shiga cikin sheka ta, wallahi sai nai mata abin da zai sanya ta gudu da kafafuwanta yar iska kawai.”

 

Magana take cike da tsantsar bakin ciki wanda idan zaka kashe ta ba zata iya maimaita abubuwan da ta ke furtawa ba, su kuma duk sun zuba mata ido ko wanne da irin abin da yake cikin zuciyar sa. Shaheeda da komai ya fi yi mata zafi saboda abubuwan da take gudun faruwarsu suna da yawa a game da sarki Salman da ita. Waya kuwa ta kira shi yafi sau ashirin amman ba ta shiga, shi tuni ya sauka a birnin Cyprus cike da tunanin abubuwan da ya baro a gida Nijeriya. Mikewa tayi tana sharar hawaye ta kalli su Gimbiya Jaleela wacce ke dafe da goshi tace musu.

 

“Dole zan yi tafiya zuwa gida dan sanar da lamarin nan a gurin iyaye na, duk da na kira wayoyin sa bana samu gobe zan shirya na tafi ku kuma kuci gaba da tsara komai kafin na dawo.”

 

“Baki da damuwa ai Shaheeda, kuma ko baki fada ba kinsan tabbas wannan fadan ba naki bane ke kadai har da mu. Kije lafiya ki dawo lafiya, zaki ci gaba da rayuwarki ke kadai a birnin zuciyar Salman.”

 

Jaleela tayi maganar cike da karfafawa Shaheeda gwiwa.

 

_____Su kuwa can bangaran suna ta shirya sashen amarya, basu gama ba gashi har dare ya yi dole sai dai abar wasu shirin zuwa wayewar gari sai a karasa. Sun kafa gadaje sun sanya kujeru da dining da sauran su, kitchen ne dama ya rage basu kammala ba, gashi ana ta kiran su akan su dawo za’a dauki amarya a kawo ta gidan ta. Haka suka tashi suka harhado komatsan su suka dawo cike da mamakin abin da ya sa aka hana su zuwa wani sashe dake gefe (mahaifiyar sarki Salman) dogarai dake bakin gate din su suka shaida musu cewa wai tace kar wanda ta shiga ba taji dadi ne.

 

Suna dawowa suka tarar na gama kimtswa da taimakon Aisha cikin janyo min ayoyin Allah tana fassarawa har sai da naje na yi wanka nasa kayan da suka fito min dashi sannan ta shafa min mai a kafafuwa saboda cewa na yi babu abin da zan kuma yi bayan sanya kayan. Zata shafa min a fuska wai nayi kwalliya ko hoda ce na sa amman na dage akan cewa ba zan yi ba sai dai idan an kai ni ya koro ni, amman ba zan wani yi masa kwalliya ba dan babu wannan tsarin a cikin zuciyata. Kawu daddy, kawu Kabiru da kawu Hashimu sune suka yi min nashiha, sannan suka saka ni yi musu alkawarin zama da miji na lafiya kamar yadda iyaye na suka yi gashi yau babu su ko daya a cikin su sai labari.

 

Daga nan kuwa suka riko ni ina ta kuka suka sanya a mota, Aisha ta samu ta shigo kusa dani da taimakon matar kawu Kabiru. Sai da aka cika motocin da aka tanada wajan kai ni, sannan aka dauki hanya cike da kide-kide da bushe-nushen abubuwan sarauta har muka je cikin masarautar Basannabas, wacce a baya ina burin naji ance za aje cikin ta naji ina ma dani za a shiga saboda murna, sabanin yanzu da babu masarautar da na tsana irin ta. Kirjina ya dinga bugawa tamkar zai zazzago ya fado, ga wani mugun bacin rai da nake ji a rai na ko addu’a na kasa yi bare naji sassauci, sai ma kara zafi da zuciya take yi 

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 13

Advertisement                   _13//KASBTSTW_     *BRITISH ENG LEARNING CENTRE*   Idanuwa na shiga zarewa a lokacin da…

KIBIYAR AJALI 8

Advertisement   _*BABI NA: 8_*     _*Wattpad:missxoxo00_*                 ***   Advertisements “Hannu malama Mardiyya.”  …