KIBIYAR AJALI 23

Advertisement

 

__I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_PG:23_

_BOOK:2_

Advertisements

_Ina masu neman mace mai daukan hoto a kano? Special female photographer wadda ta iya daukan hoto na biki, Suna, taro da sauran su? ZAARAGRAPHY… Zaragraphy tana nan agarin kano.. Tana hotuna nasu photo book, photo album, photo sessions da sauran su… Domin duba ire iren hotunan da takeyi.. Sai a duba shafinta akan Instagram: ZAARAGRAPHY. Kota number wayarta: 08093194306_

___*Ahankali* tamkar mai rada ya sake cemun,

“Ina son na samu lokaci, Na ziyarci dangin ki my love..”

“Dangi na wanne kenan…? Akwai karkarar durbun ainihin tsatso na kenan, Inda yan uwan mahaifina suke da kishiyar uwatah, Sai nan cikin gari akwai yan uwan mahaifiya ta, Da kuma sauran garuruwa inda wasu kawunni na ke da zama…”

“Wasu garuruwan??? Zamuje wannan daga baya idan little princess ko prince yazo lapia.. Yawon arbain ake cewa ko?”

Na tab’e baki kawai ina mamakin sa, Kawai saboda yi d’aya sai ace na samu ciki? Bana wannan fatan, Fatana bai wuce mu kammala game din da yasa lapia ba kowa ya kama gaban sa. 

Advertisements

“Haka ake kar’bar bako ba dan drinks….? Uhm?”

Ya katsemun tunani ta hanyar tambayar daya mun, Mikewa nai ban kula shi ba, Na dakko lemo a fridge da cup na ajiye masa,

“Asha lapia..”

Zan zauna a gefe ya sake janyo ni jikin sa yana kallo na, A hankali ya zare gilashin idanun sa, Shagala nai da kallon kyakyawar fuskar sa mai dauke da annuri, Yana da matsakaicin kyakkyawar kalar fatar jiki, shape din fuskar sa ya dace da dara daran idanun sa masu d’auke da gashin idanu zara zara, Yana da wani irin kwayar idanu wata irin kala, idanun sa farare tas. Gashin girar sa sun kusa hadewa da juna saboda yadda suke gazar gazar a kwance. Bakin sa dan karami tamkar shi ya zana abunsa, Jajaye dasu. Hancin sa dogo ne sosai ya dace da yanayin kyakkyawar fuskar sa. Bansan sanda na saka hannu na akan sumar gashin kan sa ba wadda ta kanannade ta kwanto har sajen fuskar sa. 

Hannun sa ya dora akan nawa hannun da nake yawo dashi, Sai alokacin hankali na ya dawo jiki na, Zan janye kenan ya sake riko hannun yana sumbatar tsakiyar tafin hannu na. Kunya duk ta kama ni.

“Gimbiyar zuciar Salman bn Aliy, Yau ni Salman na fara zuwa zance wajen ki…  Kamar yadda kowane manemi idan yazo wajen nema yake dagewa ya bayyana wanene shi, Yau ni Salman zan bayyana miki komai nawa, Sannan kema ki sanarmun naki, Saboda musan komai na juna.. Yadda game din zai fi tafiya dai dai..”

Yanayin yadda yakemun magana a kofar kunne na ne ya shiga jefa ni cikin wani yanayi, Ahankali na shiga zame jiki na, Ya sassauta rikon da yamun. Yana magana ahankali cikin nutsuwa. 

“Kamar yadda kika sani, Su Gwaggo sun sanar dake, Sunana Salman naci sunan kakana marigayi sarki salmanu Ibrahim. Shekaru na 32 a duniya, Nayi primary da secondary dina anan kasar, Inda na tafi matakin degree na d’aya dana biyu a fannin islamic law and shariah a king saud university dake saudiyya… Na gama kenan ko result ban karb’a ba aka dawo dani nan aka mun sarauta. Khadijaa! Na kasance banason hayaniya da shiga cikin mutane tun ina karami.. Bana iya sakin jiki nai hulda da mutane. Abokai na bazasu wuce uku a duniya ba, Suma duk suna kasar Saudiyya…Na fara amfani da glasses Lokacin ina secondary school, Tun ina using portal har na dawo saka wannan, Banason munafurci, Hassada, Riya da kuma cin amana.. Banason wannan halayen awajen mutum. Abu mafi soyuwa a rai na mahaifi na ne, Ko ince iyaye na, Inason Ammi sosai, Kuma irin yadda nake nuna kaunarta ne yasa aka shiga tsakanin mu. Zawjatiii… Kina sauraro na kuwa?”

Samun kai na nayi da girgiza kai, Ya cigaba da magana hannun sa cikin nawa,

“Sannan inde inason abu, Bana taba tsanar sa, Kuma inde mallaki na ne, To bazan taba sharing da wani ba kin gane? Kina yawan tambayana dalilin dayasa na aure ki, Zawjatiii..! Na aure ki saboda ina kaunar ki, Na aure ki ne saboda tunda na dora idanu na akanki naji kin shiga zucia ta, Kin shiga rai na, Ina jin wani abu game dake, Sannan na aure ki ne saboda rashin tsoron ki, Yadda kika kafeni da idanu kina mun tambayoyi ranar saukar nan I cant lieee, I fall for you. Sautin muryar ki ranar shi ya dinga dawainiya da ilahirin gangar jiki na da ruhina, Tamkar majigi haka nake jinki…. Zawjati, Ina kaunar ki sosai, Nasabar ki, martabar ki, Kimar ki.. Me zance dake? Kinsan godiar da nayiwa Allah kuwa da nine nan na fara sanin Zawjatii na..? Inason komai naki deeeeejaaa na, Muryar ki..”

Yana magana yana shafa lebe na, 

“Gashin ki….”

Nanma ya dawo kan jelar kalbar da nayiwa kai na guda biyu dazu.

“Leben ki…… Da nan, Nan… Komai naki abun ne me soyuwa agare ni, Kuma nasan auren ki alkhairi ne, Saboda yanayin istikhara dana dinga yi akan ki, Kome nawa ke nake gani, Nasan Tabbas ke wani haske ce a rayuwatahh Zawjatiii.. Ina kaunar ki..”

Juyawa gefe naga yayi… Ahankali naga ya zaro tissue yana goge hawaye a idanun sa, Kikkifta idanu na shiga yi ina kambama kokarin sa. Ajiyar zuciya na sauke, inajin wani rauni a kansa na tasiri cikin jinina. Kona fada ko karna fada lallai shidin yanada wata kima da girma da daraja a cikin idanuna. Dan ko Mas’ud bana tunanin yana mini irin wannan makahon son. Shin anya kuwa bana yaudarar kaina kuwa….? Saurin ajiye tunanin nayi kafin nace dashi,

“Sunana Khadijaa Basheer, Wadda akewa laqabi da dije, Sunaye na da yawa anace mun Dijangala, Oganniya yar baffanta.. Ta Gajiyalle mai yar hakiya..”

Dariya naga yanayi ahankali cikeda nutsuwa, Na Murguda baki ina cuno shi gaba, 

“Meye abun dariya..? Naga daka bada naka banyi daria ba.”

“Yi hakuri na daina  gimbiya maman prince & princess dina. Sunayen ne naji su kala kala..”

“Wallahi zan fasa baka to…”

Kamo hannuwana duk biyu yayi cikin nasa yana kallon kwayar idanu na, 

“Ai nace kiyi hakuri Oganniya, Gwiwoyina bisa k’asa gashi na zubesu, Allah ya huci zuciar ki, Ni dadi ma sukamin, Baby Dijee na, Sweetheart Dijangala tahh, Oganniyar Salman….!” ya kare maganar yana danne dariyarsa da kyau.

Murmushi nai kawai da danne tawa dariyar nima na cigaba da cewa,

“Shekaru na 23 a duniya, Nayi primary da secondary dakyar bayan mai gari ya samo mana tallafin karatu, Dan da na tsani karatu, Daga baya bayan baffana ya rasu rik’o na ya dawo hannun Kawu na wanda ka nemi aure na awajen sa, Anan garin nayi university na karanci masscomm. Ni marainiya ce gaba da baya. Dan bantaso da mahaifiyata bama, Sai mahaifi na shima bayan nagama secondary a ranar ya rasu. Ni ba yar kowa bace. Mahaifi na talaka ne, Banida wani gata sai na Allah sai yan uwan mahaifiyatahh…”

“Sai dai ba kamar kai ba, Ni gaskia ina da baki sosai dan ba’a takani, Kaf durbun ciki da waje babu wanda bai sanni ba. Inada surutu da neman fada don har siyan sa nake, Inason mutane kuma ina shiga cikin mutane koina ana damawa da ni sosai.. Inada kawaye a durbun sosai, Wasu sun hayayyafa da yawa, Anan cikin garin nema banda su sosai, Inason dik wani meso na, Ciki harda wata baiwar Allah Malama mardiyya..”

“Yess!!”

Ya fada cikin kashemin ido.

Da mamaki nace, 

“Menene?”

Fuskarsa kumshe da murmushi yace, 

“kince kina son duk mai sonki, kinga kuwa ina ciki kenan dan namafi kowa sonki bayan baffa da mama da Uncle”

Samun kaina nai da kai masa karamin duka a kirji ina dariya. Shima dariyar yayi yana rungumeni a jikinsa. Sai da mukai mai isarmu sannan na tashi zaune ina bashi amsa da cewa,

“Ni dai ban fadaba. Kuma kar ai mun sharri. Ni y’ar kauyen kayau ce, Tashin k’auye girman kauye… Zan iya cewa ma jamia ce kadai nayita anan.. Kasan Durbun..?”

“Akwai wata makaranta da za’ai acan.. Gwamna ya turo zansa hannu, Wai yan garin za’a biya su kudin gidajen su su koma k’auyen gaban su, Nan wajen kuma za’ai makaranta har za’a maida wajen orientation camp ma na bautar kasa… “

“Durbun din…?”

“Easy dearrrr naa, Ai dole yanzu a soketa, Na miki alk’awarin babu abunda Za’a yi musu. Dama wai yankar wani sashe za’ai ayi makarantar..”

Sai naji sanyi a zucia tah, Domin yadda nakeda burin zuwa garin nan ai bana fatan ace yau na bude idanu babu marayatah, Tushe na.. Ina bazaiyiwu ba, Da izinin Allah..

“Zawjatiiii! Bakiji hausawa ma nacewa marar kauye baida asali ba, Ina son ki a duk yadda ki ke, Ki yarda kece mahadin rayuwar Salman bin Aliy. Babu ruwana dake wacece, Babu ruwana da nasabarki, babu ruwana da iliminki, babu ruwana da abinda wani zai fada a kanki. Ke nake so a kan kanki. Tarbiyyarki ta isheni komai…”

“Please ki yarda na nuna miki matsayinki a gareni Khadijah. Ki yarda na nunama duniya ke wacece a gareni. Ki yarda na shelantama masu mulki irina su san cewa ba sai mace tana da irin nasabarsu ko nagartarsu bane ta cancanci zama matarsu…Ki yarda nayi koyi da mahaifina Khadijah. Na gaya miki shima ya auri mahaifiyata da irin matsayin da kike ganin kanki da shi a lokacin da yake matsayin sarki. Wannan shine sanadin girmama kiyayyarta da tamu a cikin masarautar basannabas. Me yasa bazaki amince tarihi ya sake maimaita kansa ba a garemu dan mu sake zama mabudin karya lagon kaifin duk wani jahilin dake tunanin yar mulki sai dan mulki? Talaka sai dan uwansa talaka….Uhm? Zawjatiiii..”

Murmushi nayi kawai kaina a kasa. Dan bansan mezance masaba kuma. 

“Please!”

Ya fada saitin kunnena.

Ajiyar zuciya na sauke tare da kallonsa. murya a sanyaye nace 

“karka damu ALLAH na nan ai, shine zai fidda kowanne dan duma a giransa.”

Murmushi ya saki mai kayatarwa, ya kamo hannuna. cikin nasa ya sumbata, 

“To ALLAH ya fidda wannan dan duman kamar zinarin oganniya ta, dan yanzu kam bata gajiyalle bace ko yaya kikace?”

“Tab kwace zakai mata ma? Ai duk muguntarta inason abuta”

Dariya sosai yaringayi. Ya shafa cikina yana fadin, 

“ina sonki da yawa Khadijah. Shiriritarki na burgeni matuka gaya. ALLAH yayi miki albarka kinji”

“Amin” na fada cike da doki.

Ba karamin dadi nake ji ba idan naji yace yana son tarbiya ta. Lallai ilimi haske ne ga dan Adam, fitilace kuma abin daraja a gurinsa. Da zan Iya kuma da Ina da gwarin guiwa babu abinda zai hanani bashi tukwicin kyakyawar runguma saboda farin cikin da kalamansa suka sanya ni. Iskar bakinsa ya hura min a fusa, da alama ya fahimci na tafi dogon tunani.

“My love ya da tunani haka bayan muna tare.?” Nayi murmushi Ina kawar da fuska nace.

“Tunawa nayi da ace lokacin da ina Dije ta a Durbun, nasan da ba zaka taba kallo na ba saboda…….”

<><>>

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 20

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 22

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI…..!_…

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…