KIBIYAR AJALI 24

Advertisement

 

 

*24*

 

 

Sanda aka bude min mota wai na fito, sai naji wani dummm…. A cikin kunne na kamar an cire min duk wani sauti, sai magana kawai da nake ji kai tsaye daga bakunan mutane kamar suna dariya. Da kyar na sakko da kafafuwana ina rike da Aisha gam sai kace ance guduwa za ta yi ta barni. Kai tsaye sashe na

aka nufa da ni kasan cewar su Ciroma sun ce ba sai an kai ni wajan kowa ba,Naji dadi kuwa dan ni dama ba so nake yi na ga ahalin shi ba nasan raina baci zai kara yi tunda ba kaunar su nake yi ba nima.

 

“Shiga da kafar ki ta dama Dije, kiyi addu’a ki shiga Allah yasa mutuwa ce zata raba ku keda mijin ki.”

Advertisements

 

Matar kawu Hashim ta fada tana daga gefe na wajen hagu, Aisha kuma tana bangaran dama na rike ta sosai. Bismillah kawai na yi a zuciya ta nasa kafata ta dama kawai na shiga, sauran suka biyo baya na suna guda kasa-kasa dan su kansu sun gane cewar akwai abin da yake faruwa a cikin masarautar. Babu abin da ya burgeni a cikin parlorn da muka shiga, sai ma wani irin wari da nake ji ya cika min hanci na. Nayi saurin janyo mayafi na tare da toshewa amman still kara karuwa warin yake, Na saci kallon mutane naga babu wadda ta rufe hancin ta sai ni, na fara tunanin su basu ji bane? Abu kamar zai bata maka ciki ko ma nace zai lalata kwakwalwa.

 

Suka dinga jana har cikin bedroom din wanda ya gaji da tsaruwa. Allah sarki kawu daddy, hakika ya yi min abin da ko a mafarki ban taba zaton zan same shi ba. Komai royal ya yi min wanda ko su Ya Shukrah iya abin da zai yi musu kenan. Aisha ta zaunar dani a gefen gado, Na zauna sai naji tamkar an cake ni da kusa saboda wani zafi da naji a hq dina kafin na yi wani yinkurin kawai naji wani abu yana fitowa daga gurin kamar an kunna famfo.

 

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.” Na furta da d’an karfi.

 

“Me ne ne Khadija?”

 

Na janyo ta ina dafe kai nace.

 

“Period ne ina jin ya dawo min, kuma fa ban dade da yin wankan tsarki ba.”

Advertisements

 

“Subhan’Allah, Amma ai ba abin damuwa bane tunda daman yana yin haka. Kedai kici gaba da kirga kwanakin.”

 

Sai raba idanu nake yi. Ta cikin laffayar jiki na nake hango komai. Kaya kala kala sai kawo su ake yi a baskets da gift boxes dana cikin paper bags. Wasu kayayyakin aka kawo cikin wasu irin basket da aka yi da kaloli masu kyau, kowanne kaya ne acikin sa fal. Baskets din zasu yi kala goma. A gaban Mami wasu mata suka ajiye, Tamkar ba zasu yi magana ba, da kyar wata daga cikin su tace,

 

 “Ga kaya inji fulani…. Wato Gimbiya kuma Sarauniya sannan uwargidan Sarki Salman, Gimbiya Shaheedah diyar Sarki Ibrahim Hashimu da ke masarautar ‘Bullo.. Tace a shaida gaisuwar ta, Kafin taga amarya.”

 

Gaba na ya yanke ya fadi. Oh ni Dije! Wai kishiya ce da wannan aiki haka? Babu karamin kaya a cikin kayan da ta bayar a kawo. Turamen atamfa da shaddodi kuwa harda na iyaye duk an sako. Sai wulkita idanu nake.

 

Sannu ahankali kowannen su sai an bayyana mana na gurin Gimbiya wance ne. Da alamun na matan baban sa ne. Saboda yadda ko wacce take nuna bajinta, Tana bani waje na fiki komai. Kowa cikin shigar alfarma da dandatsa dandatsan kayayyaki, Wai ashe budar kai aka yi.

 

Matar kawu Kabiru ta rakani wani band’aki dake cikin sashe na tasa nayo wanka. Na fito tsab dani bayan na saka pad a jiki na. Cikin wasu hadaddun lace ta shirya ni. Aka doramin alkyabba wacce tafi wadda na cire da safe kyau da tsari, Waziri da kansa ya shigo da wasu mata yan mata su wajen biyar yace ga masu tayani hidima nan. Duk abunda nakeso na sanar musu. Akwai zagi kuma da duk aiken da zanyi fada shi zan tura. Sannan yace za a yi min rakiya sashen mutanan masarautar.

 

Sannu ahankali sauran yan uwa da suka rako ni suka sani agaba aka fara rarrakani gaishe da matan gidan. Banda sashen d’aya daga cikin matan marigayi sarki da aka ce mana bacci take yi. Amma sauran matan da bangama sanin su waye suba duk an kaini sashen su. Kowanne ya karb’e ni babu yabo babu fallasa..

 

  “Ni wacece me babban dakin ne acikin su…?”

 

Hairah diyar Kawu kabeeru ta tambaya tana mai daukar hoto na awayarta.

 

“Kila acikin wa’ennan guda 3 take.” Cewar Ya Shukrah!

 

 “Yo acikin sune mana.. Ai da ba acikin su bane zasu sheda. Tunda su suka sa akayiyyi mana rakiyar. Tab a hayye! Dije zaki ci kan kaza ta ubanki a masarautar nan. Yo uwar mijin ma ba sanki take ba.. Kina ganin ko nuna kanta batayi ba. Banda barbadadden aure ma irin wannan ace ranar auren ka babu angon ka? Daren farko ace ba ango. Makira abinda kike so kenan dama.”

 

Mami ta shiga fada min a kusa da kunne na, Matar kawu Kabiru dake gefe na ita kadai ce ke juyo Mami, Na matsa gefe ta sake danko hannu na da karfi,

 

 “Ba dai kin wargaza duk wani farin cikin gida na ba Dije? Kin hada ni da miji na ko..? Farin cikin ki kenan ko? Toh masarautar nan sai ta zamo ajalin ki..”

 

 “Assha! Haba Hajia? Ba girman ki bane wannan maganar wallahi.”

 

Cewar Matar kawu Kabiru. Sauran mutane na gefe ba susan wainar da ake toyawa ba. Mami ta jefawa Matar kawu Kabiru harara, Taja dogon tsaki kafin ta cigaba da cewa,

 

 “Uhum! Ke kuma asuwa? Me zaki nuna min?”

 

 “Hajia munanan kalaman ki sunyi tsauri wallahi, Sannan furucin ki na karshe bai yi dadi ba sam bai dace ba.”

 

 “Dan nace sai ya zamo ajalin ta? Zaki gani ai. Muna daga gefe zamu ji labari.”

 

 “Hajjaju tunda dije ta tsallake siradin azabar Gajiyalle ai ko’ina zata iya jurewa, Tata kalar jarabawar kenan, Sannan muna fatan anzo karshen wahalhalun da tasha. Jin dadinta ne yazo yanzu. Ai mai hankali ne zai iya ganewa amma wannan yarinyar Khadija kafin Allah ce, Ta riga ta zamarwa makiya da mahassadan ta *KIBIYAR AJALI*, wadda sulke bai isa ya tsare ta ba sai ta wuce. Ba boka ba Malam.”

 

 “Iyeeee…. wa kike gayawa wadannan kalaman?”

 

 “Haba hajjaju ni na isa nace da ke nake? kukan kurciya ai jawabi ne, Me hankali shike ganewa. Zo muje Gimbiya Khadija… Takawar ki lapia, Taka a sannu yau ranar taki ce..”

 

Matar kawu Kabiru ta karasa magana tana mai janyo hannu na, Muka wuce sashe na muka bar Mami a daskare tana cizan yatsa. Sannu ahankali da dai-dai da dai dai yan uwa da abokan arzuka suka yayye suka barni daga ni sai hali na sai hadiman da akace su taya ni zama.

 

Ina tsakure akan kujera na ma rasa abinda ke min dadi, Tunda suka tafi nake ji na a takure, An kawoni inda bansan kowa ba. Ba wanda ya sanni. Shi kansa wanda ya auronin ba gama sanin wacece ni yayi ba.

 

 “Oh ni dije… Tawa samfurin kalolin kaddarar kenan?”

 

 “Allah ya kara miki lapia.. Magana ki ke?”

 

Na hadiye kakkauran miyau jin wani sabon lamari, Sai kace a mafarki? Ko irin fina finan nan? Na kakaro murmushi ina kallon su su biyar a jere reras kowaccen su kanta a kasa,

 

 “Ba.. ba magana nake ba.”

 

Yasin ni nama manta dasu, Wayar intercom dake gefe ce tafara kara. Wata acikin su ta mike ta rissina min,

 

 “Ran gimbiya ya dade… Zan dau wayar salular da ake kira. Zan iya dagawa.? An ban dama?”

 

Kada kai nayi kawai, Ina kallon sabon al’ajabin dake wakana a gaba na, Dauka tayi tana amsawa kafin ta sake maida kanta kasa,

 

 “Sarkin kofar kudu ne yake neman iso, Yace wai dogarin yamma ne ya aiko shi.. Sako ne daga falaki Shima daga hannun dangaladiman waziri ne, Hannu da hannu daga ma’aji babba. Ance idan babu takura za’a aiko.”

 

Gaba d’aya bansan me take nufi ba, Ko sunayen menene ta jero haka oho? Ni dai na jiyo k’arshen za’a aiko, Dan haka na daga kai kawai. Domin za’ai tata’burza kuwa. Ba abunda nasani dangane da irin rayuwar su. Gaskiyar Mami.. Inaga gidan ajali na nazo. Na sake sauke ajiyar zuciya. Ban gama tunanin ba. Na fara hangen manyan farantai shake da kayan alatu da cima kala kala, Gaba d’aya wajen ya hautsine da kamshin abinci, Su dai basa gajiya dazu fa aka kawo wani sai tafiya su Mami sukai dashi.

 

 “Bara mu baki waje Gimbiya…”

 

 “Dan Allah ku zauna..”

 

 “Allah ya kara miki lapia ki dade kiyi kargo. Muna waje zamu jira.”

 

K’ada Kai kawayi nayi badon naso ba, Domin ni banason zaman kad’aici wallahi. Dan ba yadda zanyi ne. Gashi ciki na acike yake, Dan haka na mike mai shigewa ta wani d’aki dake dauke da kayan ciki komai purple. Na shiga rusar kuka ina tunanin baudaddiyar rayuwar da zanyi a masarautar Basannabas. Wai nan ni matar aure ce, Gidan aure na ne, Daren farko kuma.. amma bansan waye angon ba, bantab’a ganin sa ba. Wanne Irin cakwakiyar zama zamu yi!? Ni banmasan baya kasar ba sai da wasu acikin matan dazu ke fada.. Ban’daki na fada nayo wanka hade da alwala. Kasan cewar na saba ko ina cikin rashin tsarki ina yin alwala na zauna da ita ina mai rokon Allah da kada ya barni da iyawata ya shiga lamurana a ko da Yaushe…

 

 

                     *CYPRUS *

           (HILTON-NICOSIA)

 

  Zaune yake a balcony din dake parlorn babban masaukin sa dake 5 star hotel Nicosia, Sanye cikin bathrobe, kanannadadden gashin kansa ya kwanta luf a kwanyar kansa. Tea ne agaban sa. Tun yana da zafin sa bai sha ba har ya huce, Hannun sa na dama yasa ya shiga bubbuga goshin sa,

 

So yake ya kira falaki a waya yaji lapiar Khadija amma izzar sarauta ta hana shi. Yaja dogon tsaki yana kallon screen din wayoyin sa guda biyu dake kan table din gaban sa, Abubuwa ne da dama yake ji a game da farar wayar dake gefen sa. Bazai iya tina musababbin ajiyarta agare shi ba. Amman ya san dai iya shekarun nan tana hannun sa. Sannan Lokaci zuwa lokaci yakan kunnata ya kashe ta. Har yau ya kasa gano mafita.

 

  “Yaa Salaam!”

 

Furzar da iskar bakin sa yayi, Ya kamo kasan leben sa yana ciza wanda yai jajawur, Saboda tsabar yadda yake ciza. sometimes ya shiga tsotsa kamar alawa. Abune da ya zamar masa dole.

 

 ‘Wazirin Basannabas..’

 

Shine sunan dake bayyana a screen din wayar sa baka. Wani abu dake saqale a kunnen sa ya latsa, Yana sauraron wazirin. Tamkar bazai yi magana ba, Tsawon lokaci tukun sannan yace,

 

 “Ok fine! Ta…Ta, Tayi bacci..?”

 

Lumshe idanu yai ya jingina da kujerar da yake kai, Yana sauraron waziri, Da alamun labarta masa yadda akai yau yake.

 

 “Ok Kha..Khadija take care.. oh sorry waziri take care!”Katse wayar yayi. Ganin baran-baramar da yayi, Da waziri dayake jinsa tamkar mahaifin sa.

 

MASARAUTAR BASANNABAS

(SASHEN WAZIRI)

 

Shima wazirin a nasa bangaren murmushin yai kawai ya ajiye wayar agefe yana kambama yadda SAS yakeson sabuwar amaryar sa.. Ransa a matuk’ar bace waziri ya dubi su Galadima dake gaban sa,

 

 “Shin wai me ke tafe daku… Yaro ya riga yayi aure shine kuke son kulla masa wata kitimirmirar? Harda cewa kar a kai amarya sashen kowa? Akan me? Why??”

 

Ciroma ya bude baki zai yi magana, Waziri ya daga masa hannu yana nuna kofa,

 

 “Ku fice min a gida, Bana son sakarci.”

 

Mikewa kowannen su yayi, Jiki na bari suka masa sallama suka fita, Gefe suka koma bayan sun fita suka shiga magana ahankali, Sannan suka tafa kowanne ya kama hanyar sa…….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement   28….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍    …