KIBIYAR AJALI 25

Advertisement

 

 

_*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *_

_*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*_

*2___5*

Advertisements

*SASHEN MAI BABBAN ‘DAKI*

Duk da ta saba jin irin wannan kide-kiden amman na yau yafi karfin tunaninta. Bayan ta idar da sallah ne ta shafa maganin ciwon kafarta tana ta murzawa sai ta kira hadimarta wato Hansatu tace taje ta duba mata hayaniyar me a ke yi a sashen yarima Abdul?Sai da ta mika gaisuwa sannan ta tafi zuwa wajan sauran hadimai tana tambayar su, suka shaida mata da komai wanda suka sani suma. 

A karamin parlorn ta take a hakimce a doguwar kujera mai cin mutane uku. Kafafuwan ta akan center table. Tana zaune ta dora k’afarta d’aya kan d’aya, Cikin haka Hansatu babbar hadimarta ta shigo kanta a kasa,

 “Allah ya kara miki lapia da nisan kwana… Na bincika miki, tabbas mai martaba aure ya kara, Kuma a binciken da nayo ba jinin sarauta bace, diyar wani hamshakin dan kasuwa ne, Ance ba yar cikin sa bace yar kanwar sace mai rasuwa…”

Mamaki da d’in bin al’ajabi suka cika zuciyar ta, amman har cikin ran Gimbiya Sa’adatu taji dadin wannan zance da Hansatu ta sanar mata, Sai dai ba tasan ko itama amaryar acikin hayyacin ta take ba basu juyar mata dashi ba? Taji dadi kwarai da Salman ya kara aure, Tare da yi masa fatan Allah yasa auren nasa ya zamo mafificin alkhairi..

 “Kinfi sanin me yara mata keso yanzu, Kije ki harhada abinda ya kamata ki kai musu b’angaren su.” Gimbiya Sa’adatu ta baiwa Hansatu umarni.

Advertisements

 “Ai ranki ya dade, Mai martaba baya kasar domin na hangi saman tutar dake nuna alamun yana nan, Yanzun an cireta batanan.”

 “Dama ai na ita bakuwar ne.. Ina fatan kin fahimta?”

 “Nagane ranki ya dade. Yanzun zanje na harhada komai da yardar Allah.. Allah ya bamu sa’a! Aamin!”

Kwasar gaisuwa tayi ta fice, Ita kuma gimbiya Sa’adatu taja ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai. Addu’oi take ta kamowa a bakin ta tana mai zubar da hawaye ahankali.

*SASHEN GIMBIYA SHAHEEDA.*

(Uwar-gidan sarki Salman)

Duk da ta bawa Dije gudun mawarta mai tsoka hakan be yi mata ba, Gani take tamkar ba tayi komai ba, tana jin kamar yarinyar zata rai na kayan. Amman wani sashen na zuciyar ta yana kwabarta akan karin da take son yi mata cewar ta kyale ta haka tunda dai kowa yasan ita d’in yar gidan basarake ce, mai gogawa da ita sai ya shirya. Ta fara shirya kayan ta da zata tafi gida gobe dan ba zata dawo ba sai da shirin fitar da Dije, wacce tayi gangancin aurar mata miji mafi soyuwa a zuciyar ta.

“Ke! Tashi kije ki shirya min kayan da zan tafi dasu ‘Bullo.”

“An gama Allah ya taimake ki, kamar kala nawa za’a tanadar miki?”

“Karki ishe ni da surutu dan Allah, kije ki hada min na sati daya kacal.”

“Toh gimbiyar gimbiyoyi, Allah ya kara lafiya da nisan kwana bari naje.”

Mtwww! taja tsaki saboda bacin rai, gabaki d’aya ta kagu gari ya waye ta tafi. Gidan gaba daya ya yi mata zafi, gashi Salman d’in ma baya nan ta kuma kasa samun shi a waya switched-off ake ce mata tun dazu. Lallai tana cikin tashin hankali tunda har Salman ya fara kauda ido akan ta gashi har aure ya fara shigowa tsakanin shi da ita, Shin me ta tsarewa Salman da har yasa karo aure, kuma ma tsabar rashin mutunci ba jinin sarauta ba, a’ah yar riko? Dole ta tashi tsaye wajan ganin ta ruguza auran ya zama ita daya ce tilo a cikin fadar zuciyar shi.

Tayi saurin mikewa tsaye ta nufi bathroom da sauri ta sakarwa kanta ruwan sanyi saboda wani irin gumi da taji tana yi. Bata taba zato ko tsammanin akwai irin wannan rana da lokacin da zasu zo ta shiga wannan halin ba, sai gashi auran Salman yasa ta kasa nutsuwa. Kullum a cikin mutane cewa take mijin ta ba zai iya kara aure ba, saboda dalilai guda uku. Na farko baya haihuwa, na biyu baya kallon mutane bare ya kalli mace bayan ita, na uku sam taga alamun Salman bashi da karfin sha’awa saboda sai ya dade be neme ta ba. Hasalima, Itace me takura masa, Wannan sune dalilin da take alfahari dasu na cewa ita kadai ce a gurin mijin ta. Sai da taji zafin da take ji yaki sakin ta sannan ta fito daga cikin ruwan ta daura bathtub tare da dafo bango ta dawo cikin bedroom ta kwanta kan gado tana sakin kuka.

_“Sai kayi nadama Salman, wallahi sai ka san ni ka wulakanta a cikin masarautar nan. Ko zanyi yawo tsirara sai na ga bayan wannan yarinyar tunda ka tozarta ni akan ta.”_

Haka ta dinga kuka tana fadar maganganu na neman masifa tana dorawa Khadija. A ranar dai kam haka Shaheedah taga rana dan ko rufe ido kasa yi tayi, idan ma ta gwada rufewa to Dije take hangowa tare da Salman rungume da juna kamar dai yadda suke yi. Kawai ta saki wata kara wacce tasa daya daga cikin hadiman ta shigowa da gudu dan ganin ko lafiya.

“Ranki ya dade ki…” Bata bari ta karasa ba tace.

“Fita ki bani guri munafuka kawai.”

Tun kafin ta rufe baki tabar wajen cike da tsoro, daman tazo gani ne ko babu lafiya ta taimaka mata, ashe lafiyar ce ta ishe ta har take yi musu ihu da kururuwa. Gimbiya Shaheedah ta sake sakin wani ihun a karo na ba adadi tana buga kai akan katifa, gashi ta kagu gari ya waye dan ta tafi gidan su.

*WASHE GARI….*

SASHEN GIMBIYA KHADIJA.

Bayan gari ya waye daman ba bacci na yi ba dan cike nake da tsantsar tsoro ina ganin kamar za’a zo a kashe ni, hakan yasa na kasa bacci ko bedroom din ma kasa komawa nayi nace da hadiman da aka kawo min suma duk su kwanta a parlorn. Suka yi ta bacci sabanin ni ina kwance ne kawai akan kujerar, kuma wacce suka shafa mata wannan makircin nasu, wanda nake da yakinin cewa shine yasa na dinga jin sashen nawa yana wani irin mugun doyi kamar an kashe mushe. Koda na farka wanka nayi na sake pad gashi wani irin bleeding nake kamar wata wacce ta haihu, da yawa dan sai na hada pad biyu tukunna nake samun sassauci wajan bata min jiki da jinin yake yi.

Shiryawa nayi tsab cikin riga da zani na lace, bayan na gama shiryawa na zauna ina tunanin nifa amarya ce, wacce ya dace ace ina tare da ango na kusa da ni. Amman har na kwana na tashi ba bu shi ba alamar shi saboda kawai ya auro ni a sadaka. Eh mana sadaka in ba haka ba a aura min shi ba tare da na taba ganin koda kwayar idanunsa ba, dole ya yi min duk abinda yaga dama harda wannan rashin kulanin da ya yi a ranar farko na aure na da ko wace mace take alfahari da shi.

“Assalamu alaikum.”

Naji an yi sallama, sai na tashi tare da janyo mayafi nasa a Jikina. Fita nayi sai naga Bahijja d’aya daga cikin masu yi min hidima da aka kawo min su jiya, kafin na yi magana ta durkusa har kasa tana gaishe ni kamar zata min sujjada.

“Ke tashi menene hakan?”

“Allah ya ja da ranki Galadima ne yace azo a tambayi abin da kike da bukata za’a kawo miki.”

Naja dogon numfashi kafin na sauke nace.

“Allah sarki kice masa bama sai ankowo komai ba, saboda kinga abubuwan da aka zo dashi ga wanda aka kawo wasu suna nan, zan yi amfani dasu kawai.”

“Allah ya taimake ki, al’adar gidan nan be kamata ki ci duk wani abu da ya kwana ba, ki fada kome kike so akwai shi a cikin masarautar nan za’a kawo miki, Allah ya taimake ki.”

Mamaki ya kamani, koda yake bai dace na yi mamakin ba idan na yi duba da su Yaya Shukrah yadda suke yin abubuwa a gidan kawu daddy tamkar ba fita yake yana nemowa ba. Babu yadda na iya dole na yarda nace a bani duk a binda aka dafa zanci. Cikin sauri ta mike ta fita, na bi bayan ta nima na koma parlorn bayan na toshe hanci na da facemask wanda hakan be hana hancina jiyo wannan warin ba.

Ina zaune abin duniya ya yi min yawa kawai sai ga Gimbiya Shaheedah ta shigo sashen nawa, kasan cewar jiya ina cikin alkyabba ban ganta ba sosai. Yanzu da ta shigo sai naji gabana ya yi mummunar bugawa, nayi-nayi dan na janyo koda kalmar Innalillahi ne wallahi naji na kasa, naji ana ta rike min wuya. Babu ko sallama haka ta shigo cikin shiga ta alfarma, kai da ka ganta kasan cewar tasan ta kan mulki ta kuma san yadda ake murza shi. Tsabar na rude ban san lokacin da na diro daga kan kujerar ba na fara yi mata sannu da zuwa.

Da mamaki na sai naga ta yi murmushi idanunta yana bin duk wani sashe dake parlorn har ta gama kare masa kallo sannan ta dora da cewa.

“Haba Amarya, irin wannan ai sai kija a zage ni a gari.”

Na kasa yin magana kai na yana kasa, me zan ce mata bayan ban san matsayin ta ba a masarautar, ba ta zauna ba ta yi taku biyu zuwa tsakiyar parlorn ta tsaya. Alkabbar jikin ta ba karamin kyau ta yi ba, ni kai na sai da ta burgeni saboda tsarin ta.

“Zuwa nayi na baki hakuri a maimakon miji na, ranar da ya kamata ace kina tare da shi a lokacin ne ya tafi wata kasar. Kiyi hakuri kinji? Kin san babbar giwa kika aura dole sai kin yi hakuri kinji kanwata.”

Maganar nan da ta yi shine ya ganar dani cewar itace uwar gidan sarki Salman. Sai tunani na ya canza akan wanda nake yi mata na cewa kila tana da zazzafan kishi, duk na dauka ba zata so ni ba ashe mummunan zato nayi mata. Fargaba da tsoran kar taji yadda sashe na yake wari suka cika ni, duk da na tambayi masu aikin sunce su basu ji wari ba sai kamshi, toh itama naga kamar ba ta ji ba, dan banga ta rufe hancin ta ba. Naji dadi sosai ganin yadda take lallashi na akan rashin ango, duk kuwa da cewar naji dadi kwarai da baya nan, kuma bana jin idan zai shekara be dawo ba zan damu. Ban tashi daga kasan ba, sai dai na gyara zama na yadda zan yi mata magana sosai, nace mata.

“Nagode, kuma babu komai ai tunda ga ku duk muna tare.”

Tayi shiru na tsawon wani lokaci duk na dauka ma ba zata kuma yin magana ba, gashi tana tsaye na kuma cewa.

“Dan Allah ki zauna kya yi ta tsayuwa.”

Nan ma tayi shiru sai nayi tunanin ko ba taji bane? Zan kuma yi mata magana naji ta kalleni tana cewa.

“Noooo! Na gode ni ma tafiya zan yi. Ina dad’a baki hakuri dai, zan kuma yi kokarin takura masa ya dawo tunda yasan an kawo ki.”

Wannan Karon shiru na yi saboda bana son ganin shi bare nace ina son dawowar shi, ita dai da take son shi sai tayi ta jiran shi, haushi yake bani wallahi. Sallama ta yi min na tashi na yi mata rakiya har kofar parlorn sannan na dawo, hadimai na da suke ta gyaran parlor ga turaruka duk an saka amman ni ko kadan banji kamshin ba. Sai kawai na shiga bedroom tare da hayewa gado naja bargo na rufe duka jikin har fuska wai ko Allah zai sanya na dena ji amma ina, warin yana nan…..

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 11

Advertisement                  *11*         *Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin…

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement   28….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍    …

KIBIYAR AJALI 1

Advertisement  *KIBIYAR AJALI…..!!!!* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 29

Advertisement   *29….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍   Advertisements…