KIBIYAR AJALI 25

Advertisement

 _Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna _

https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg

_This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing you my latest films, and musical videos at lit more_

_Wannan duk daga bakin shahararriyar jarumar nan ce.. NAFISA👆🏾_

Advertisements

_Shin kunsan sabuwar fucacciyar jarumar nan ta film ta bude YouTube site d’inta? *nafisakabdullahi…*  Tana kan manhajar YouTube. Sabon shafin tane dake kan YouTube inda zata dinga kawo muku sabbin fina finai da bidiyo da sauran abubuwa na amfani…_

_Ina masoya makaranta books na zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora.._

_Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye._

_DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba…_

_Akwai Facebook site dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi_

_Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: _

Advertisements

_08071172003_

_Please show some love… Follow, Subscribe, View, Click on bell.. Stay tuned🥰🧚🏻‍♂️_.

_B2_

_PG:25_

*GIM. SHAHEEDAH*

YINI tayi tana zazza’bi da firgici tun sanda aka tone asirin data bunne, Bayan an dawo da ita daga sashen Mama Huwaila ma haka taita farfasa kayan parlorn ta tana sumbatu kamar sabuwar tab’i. Sai da asubah sannan jikin ya dan lafa. Amma duk da haka a tsorace take ganin yadda ta sake makalewa a karshen gado tana tukwikwiye jikin ta da bargo. Cikin wata irin kasalalliyar murya mai cike da fargaba ta shiga kiran hadimarta. 

“Batula… Batula! Batula.”

Duk hadiman na bakin kofa da sauran masu aikin gidan gudun kar wani abun ya sake faruwa na fashe fashen da take yi.  jikin Batula na ‘bari ta shiga a tsorace.

“Ranki ya dade… Ga ni! Allah ya kara miki lapia da nisan kwana.”

Shaheeda ta yunkura ta mike dakyar tana mai dudduba kusurwoyin d’akin ta, Gaba d’aya a birki ce take kar su kara fitowa.

“Batula… Maganin da muka binne da ke, Kin tabbata yana lapia babu abunda ya same shi?..”

“Ranki ya dade. Yana nan k’alau, Dan ko shekaran jiya dana leka na hango shukar tana yadda muka sata.”

Shaheeda ta girgiza kai tana sosa keyar ta dake mata azababban kai’kayi. 

“K’arya kike makaryaciya… Ki gayamun gaskia ancire ko a’ah?”

Batula ta shiga zare idanuwa, Ita sam bataga alamun ancire ba, Don tana yawan lekawa tana kuma da masu sa su leko mata. 

“Ni nake miki magana kina shiru Batula? Zaki magana ko sai na take kan ki? Baca nai miki duk bayan minti ki dinga dubawa ba? Zaki gaya mun gaskiya ko sai na sharara miki mari?”

Batula tarasa yadda zatai da ranta tunda batada tabbacin ko ancire ko yana nan. 

“Ranki ya dade ki gafarce ni, Ni dai gaskia da idanu na banga alamun ancire ba, Kuma wanda nasa su lura suncemun babu wanda ya zagaya baya wajen shukar…”

Ganin shaheedah ta ki magana hakan yasa Batula sake gyara zama tashiga sharara wata karyar,

“Amman dai ranki ya dade, Ancemin anga y’an uwan su mama Jaleela sun shiga sashen mai martaba washe garin ranar da mu k…”

“Rufemin baki, Kawai kice anbi sahun mu an tone. Haba biri yayi kama da mutum, To tashi ki fita tun kafin na mugun saba miki…”Ta karasa magana hade da lailayo ashariya ta dura mata. Jiki na bari Batula ta mike tafice da sauri.

Wata razananniyar kara ta saki, Cikin hanzari ta jawo wayar ta ta kira mahaifiyarta, Ta sheda mata abunda ya faru. Ta kar’kare da,

“Wallahi Hajjaju an samu wani ya tone abunda muka bunne, Yanzu shegiyar nan… Takece mun wai y’an uwan su Jaleelah taga sunje gidan washegarin ranar da muka binne. Hajjaju abunda yake bani mamaki babu wanda yasan da shirinmu kai har binnewar ma sai da kafa ta dauke…. Eh ina ta furgita hajjaju, Ki samo mafita…”

Cire wayar tayi daga kunnenta tasa a speaker. Hajian su taci gaba da kwantar mata da hankali ,

“Gaskia dai akwai zagon kasa wannan zaman naki da su. Amman karki damu furgicin nan duk zaki dena. Yanzu abunda nakeso dake shine, Kisan yadda zaki ki koma sashen Salman din, Tunda kince ana sanar miki har yanzu basa shiga sabgar juna ko? Koma suna shiga kedai Kiyi maiyiwuwa wajen ganin babu abunda ya ke shiga tsakanin su. Ina fatan kin fahimta?”

“Nagane hajjaju.. Amma fa ki sake jiyowa ba komai idan antone ko? Saboda kar abun ya wuce firgici kuma”

“Kakki damu… Babu abunda zai faru dake sai alkhairi da ganin bayan makiyan ki fulani.”

“Godia nake hajjaju…”

Sallama tayi da mahaifiyar tata, Ta kashe wayar tana sakin nannauyar ajiyar zucia. Ta ina zata fara ne? Sashen nasa zata koma? Ko kuwa zuwa zata dingayi kullum? To idan taga Khadija fa? Wallahi zamu kwashi yan dambe kuwa…. ‘Zuciar ta tabata kwarin gwiwa. Haka taita zance ita kadai tana bawa kanta amsa. Rabin zancen kuwa duk kwashewa dije albarka take.

*GIM. KHADIJAA*

…..Koda gari ya waye, Wanka na sake yi na shirya cikin wata atamfa dinkin bubu, Taje kai na nayi bayan na tsefe kalbar na d’aure da ribbon. Scented hair cream din *yerwaincense&more* na dakko na shafa a cikin gashi na, Ina tuno shi jia yadda yake fadan wai kamshi, Dadi, Laushi…  Na daura d’ankwali na samfurin ture kaga tsiya.. 

Wadataccen babban mayafi na na yafa, Sashen Ammi na fara zuwa da hadimai na guda biyu, Acan na rashe munata hira. Sai bayan magriba na dawo sashe na. Tunawa nayi duk yau banji duriyar Salman ba, 

Sake faffesa turaruka nayi na shiga sashen nasa. Yana dakin sa akan gado a kwance yana danna ipad dinsa. Yana hango ni ya mikomin hannu na riko nasa,

“Zawjatii.. Yanzu nake tunanin ki a rai na..”

“Ranka ya dade.. Kaci abinci ko kuwa a dafa wani.?”

“Ni na isa na tashi gimbiya shiga kitchen duk wannan kamshin da take zubawa?..”

Samun kai na nayi da murmushi kawai nace,

“Ka isa har kayi yawa yallabai.. Ko a hado coffee?”

Mikewa nai na isa wajen tea shelf dinsa, Na dau kofi kenan zan dauraye..

Da gudu ta shigo cikin dakin tamkar wata zakanya ranta a matukar tashe, Allah ya taimake ni na sauka daga kan gadon ina tsaye wajan coffee table Ina hada mishi. Kai na tayo gadan-gadan ta shako min wuya na, coffee d’in da na zuba ya baro min a kan kafa ta, shakar da tai min itace ta hanani yin ihu saboda azaba.

Salman dake kwance akan gado yana kare min kallo, shigowarta dakin yasa shi dan zama, ganin ta shako ni kuma yasa shi saurin sakkowa daga kan gadon ya nufo inda muke. Hannunsa yasa yana son ya kwace ni amman ya kasa saboda ba rikon wasa tayi min ba, gashi idanunta sun rufe so take kawai taga bayana.

“Shaheedah ba magana nake miki ba, ba zaki saketa ba.”

Wallahi taki saki na gashi ko kwakwaran numfashi bana iya yi, bacin rai yasa shi daga hannu ya wanke ta da marin da shi kansa besan ya yi mata Shiba. Toh ya yi Iya yinsa wajan ganin ta barni amman taki, shi yasa ya zuciya tare da daukar wannan danyan hukuncin da yana sauke hannu ta sakar min wuya na koma gefe ina kakarin amai idanuwa a waje saboda rudewa.

Shaheedah kuwa shiru tayi hannunta dafe a gurin, tama rasa daga Ina marin ya taho, kuma ta hana zuciyarta amincewa da yarda akan Salman ne ya yi mata shi. Kallansa tayi cikin tsantsar mamaki tana son taji yayi magana yace bashi bane amman taji shiru alama shi d’in ne yayi mata ba wani ba. Idanunta suka cicciko da kwalla ta dinga girgiza kai baki na rawa tace.

“Salman kai ne kasa hannu ka mare ni? Kai ne ka mare ni akan wannan munafukar yarinyar?”

Tsaye yake ko gurin Dijen ya kasa zuwa ya lallashe ta saboda shi kansa yasha mamakin yadda ya Iya daga hannu ya mari mace, macen ma kuma matarsa ta aure ba wata ba. Sai dai yadda yaji tana aibata Dijen shine ya sa shi kallonta a yatsine yace.

“Ke ta yiwa munafinci bani ba Shaheedah. Amman ke ni kike munafinta nasan duk wani makirci naki wallahi. Kinsan Allah? Kallonki kawai nake yi akwai lokacin da zan baje ki a fai-fai ta yadda zaki san waye munafiki a cikin ku, amman yanzu baki san komai game da kalmar munafunci ba.”

Cikin bacin rai da zafin kalamansa duk kuwa da cewa ta firgita jin yace yasan duk wani abu da take yi masa. Amman da yake ita d’in makira ce kuma tasan yadda zata kawar da maganarsa sai tace.

“Ka mare ni saboda kayi sabon aure ko Salman? Akan wannan bagidajiyar kake neman ka wulakanta ni bayan na rufa maka asiri ina tare da kai ban taba jin cewar zan barka ba saboda baka haihuwa. Shikenan wallahi kayi da yar halak Salman, zaka san kuma ka mare ni wallahi.”

Daga haka ta fice fuuuuu kamar wata iska, shi kuma yaje ya rufe kofar ya dawo gurin da nake durkushe Ina kukan takaici da bakin ciki. Kafata ya kamo yana duddubawa saboda yaga yadda nake ta faman rike ta saboda zugin da take min.

“Sorry my love, bari na dakko kankara na saka miki a gurin.”

Bance masa komai ba dan har lokacin ban gama dawowa daidai ba, ya dauke ni ya dora akan gado sannan yaje ya dakko kankara a cikin fridge yasa a karamin towel yana gasa min gurin.

“Kiyi hakuri dan Allah, ni ban ma san abinda ya shigo da ita cikin dakin nan ba.” 

Muryata na rawa nace.

“Ga abinda ya kawo ta nan kana gani, zuwa kawai tai fa dan ta kashe ni tunda sunyi Iya yinsu sunga ban mutu ba. Wallahi lamarin masarautar nan tsoro yake bani, na rasa me nayi musu suke neman kassarani.”

“Kiyi hakuri, nasan koma menene ni na janyo miki tunda ni na auro ki na kawo ki cikin masarautar, dadin dadawa ma kema ba so kike yi ba. Amman kiyi hakuri, insha Allahu komai zai zama tarihi. Gobe ki shirya muje gidan kawu daddy ya bamu address d’in gidan uncle na Lagos mu kai masa ziyara.”

Ina haka wani farin ciki ya mamaye ni na manta da halin da nake ciki. Wai zanje na gano su Mami wayyo ni Dije dadi kashe ni. Salman ya tsaya yana kallo na ganin yadda na kasa boye farin ciki na, a ranshi kuwa tausayinta ne sosai.  ashe ya dade yana cutar ta be sani ba, yasan tunda ya aure ta bata sake zuwa gida ba sai yanzu da yake yi mata wannan albishir din.

Ya janyo hannuwa na yana son sanya idanunsa cikin nawa amman naki biri, ya tausasa murya bayan ya sumbaci hannu na yace min.

“Nasan kinyi kewar su ko?” 

Na daga kai banyi magana ba.

“Toh kiyi hakuri insha Allahu haka ba zata kuma faruwa ba. Yanzu zanje na sanya Falaki ya shirya mana komai a sirrince, kema idan kinje gida bance ki gayawa kowa cewar tare zamu yi tafiyar ba saboda tsaro.”

“Toh takawa babu wanda zan sanarwa.”

“Wai ke meye wani takawa?”

“Sunanka ne ranka ya dade.”

“Haba dear takawa sai kace wani tsoho. Toh ko zamanin su Ammi wallahi nawan take cewa maimartaba bare kuma ni duka duka da shekara nawa kika girmeni.”

Na zaro ido tare da kama habata Ina cewa.

“Na fika ko ka fini? Ai ka ninka ni.”

“Zo mu gani idan baki fini ba.”

Yayi maganar yana kokarin leka min kirji nayi saurin dafe gaban rigar Ina hararasa, daman ta haka ake gane mutum ya girmi wani banda dai yaso ya raina min hankali. Ya dinga dariya kasa kasa yana sake janyo ni jikinsa, kansa a gefen wuya na ya sargafo shi yace.

“Ya kike ji?”

“Na me?” 

Wuyana ya shafa alamar da nan yake, nace.

“Na dena jin zafin sai dai har yanzu gurin baya min dadin.”

Shafar gurin ya dinga yi a hankali ni kuma ina lumshe ido saboda yadda nake jin dadi, ya tashi daga baya na ya dawo gabana tare da kura min ido. Mamaki ne ya cika ni hakan yasa ni saurin yin magana ina murmushi kasakasa.

“Ya haka ne?”

“Tsoro nake ji Kar sai na kaiki gida ki cewa kawu daddy ba zaki dawo ba, ko ki gaya masa irin kalubalen da kike fuskanta a cikin masarautar nan.” 

Na zabga masa harara Ina cewa.

“An gaya maka ni din yarinya ce.” Murmushi ya yi yana kallona.

“Oops na manta ashe fa an zama manyan mata.”

Yunkurawa nayi zan tashi ya yi saurin mai da ni yana dariya ni kuma nayi kicin-kicin da fuska ya rungume ni yana cewa.

“Sorry har yanzu ke yar babba babba ce kuma yar karama karama tunda sau biyu ne a…”

“Ni ka bar ni na tafi tun kafin waccen matar ta debo min mutanan masarautar nan bana san kananun zance dan zan Iya yi mata dukan tsiya wallahi.”

“Allah my love? Kai zan so naga yadda kike fada wallahi.”

Kamar yana kallo na haka na sakar masa harara kasan cewar ta baya ya janyo ne ya makale ni. Da kyar na samu Salman ya rabu dani na koma sashe na shi kuma ya nufi dakin sirrin sa dan yin bincike. Ina komawa na janyo yar karamar jaka na fara zuba kaya a ciki tare da addu’ar Allah yasa gobe tayi saurin yi dan naje naga su kawu dady.

*GIM. SHAHEEDAH*

Tana baro sashen Salman nata ta nufa Allah ya taimaka bata nuna wani abun ba a hanya da zai janyo mata idanun Mutane, tana shiga ta fara wurgi da kayan dake kan center table, ta ruga dakinta da gudu kamar wacce zaki mayunwaci da ya hango nama ya biyo ta. Kamar mahaukaciya haka ta kuma yin fatali da kayan dake jere kan mirro d’in ta, Sai a lokacin ta saki wani gigitaccen kuka wanda yasa jijiyoyin goshinta suka mimmike.

Kuka take yi sosai ta yake alyabbar jikinta da dankwalin kanta tare da fadawa kan gado tana birgima kamar wata yarinya. Juyi kawai take tana kuka tare da shure-shure da kafafuwa, bakin ta yana rawa take cewa.

“Ni Salman? Ni zaka wulakanta ko? Wayyo Allah Salman karka min haka, karka ce zaka wulakanta ni akan wata ya mace cikin duniyar nan.”

Ta zabura da sauri kamar an tsunkule ta taje ta dauki wayarta, a kunne ta kara bayan ta yi danne-danne a ciki. Bata dena kukan ba har aka daga, babu ko sallama haka ta fara magana a haukace.

“Na shiga uku hajjaju yau Salman ya mare ni, Mari na ya yi akan waccen annamimiyar yarinyar.”

“Kambalasti…. Kina nufin kice wannan maganin da su Falmata suka ce kinyi ya fara aiki a kan su, yanzu kina so kice min karya ne duk a banza?”

“A banza a wofi ma Hajjaju, ni kam na shiga uku na lalace idan har Salman ya kusanci yarinyar nan. Mari na ya yi a gabanta Hajjaju, wallahi wannan yarinyar ban san da uban da take takama ba har yasa aikin da muke yi akanta baya tasiri.”

“KI bari zan yi magana da mahaifinki.”

“Yaushe zaku yi har ku samo min mafita hajjaju?”

“Idan muka kebe zan sanar masa tunda yanzu yana fada.”

“No Hajjaju yau nake son mafitar nan, Ina son a kashe yarinyar can tun kafin asirin mu ya fara tonuwa.”

“Shikenan to bari naje nasa ai min iso da shi, duk yadda mukai Zaki ji.”

Katsewa Shaheedah tayi ta mike tsaye tare da kallon madubi tana faman goge hawayen da suke zubo mata tace.

“Wallahi sai na yi maganinki gobe Dije kike ko wa, na tsakeni na tsani duk wani naki. Yau kin sake Sanya min tsanarki tunda har sanadinki Salman ya mareni, Sai na kashe ki Kowa ma ya huta, Koda kuwa Salman zai hauka ce na rantse da Allah Sai na ga bayan ki muje zuwa zaki San kin shiga gona ta.” Kafa tasa tayi wurgi da kwalbar turaren kusa da kafarta tamkar shine ya yi mata laifin.

*WASHE GARI.*

Daman tun daren Salman yaga abinda Shaheedah tai da irin kudirinta, dan haka gari na wayewa ya kira ni a waya muka gaisa yace na shirya a lokacin Alhassan zai zo ya kai ni gida, kamar nace masa yayi wuri Sai dai nayi shiru na amsa masa da to. Wanka na shiga na fito Ina cikin shafa mai ya kira yace na fito ba Sai na tsaya yin kwalliya ba, abin ya dinga bani mamaki irin wannan gaggawa haka?

Pink shadda ce da akai min doguwar riga dinkin ya zauna a jiki na das. Yar jakar da na zuba kaya na janyo bayan na yafa mayafi wadatacce a jikina, na fito na sanar da hadimaina cewar zan yi tafiya kakata ce bata da lafiya suka dinga yi mata sannu, ban san me yasa na kife su da hakan ba ko dan naji Salman yace baya son kowa yasan da tafiyar?.

Kirana ya sake yi saboda duk yana kallo na ta cikin cctv, yace na tsaya Alhassan zai zo ya karbi jakar tawa, kafin ma ya gama gaya min..Sai gashi ya zo ya karba yace nabi ta kofar kudu nace masa to. Shi kuma Salman yace kafin na fita nayi addu’a, nayi sannan na fita still Ina rike da wayar a jikin kunne na muna magana.

“Zan kira kawu daddy zamu yi magana dashi, abin da nake so dake shine ki kula min da kanki baby na.”

Murmushi kawai nayi bance komai ba saboda rashin abin fad’a. Sai da na shiga mota sannan yace zai gayawa Ammie kome ne ne dan yasan za tayi cigiya idan taji shiru. Da kyar ya ajiye wayar ni dai Ina jin kamar da akwai dalilin da yasa shi cewa na tafi tunda da munyi magana cewar dashi zamu amman yanzu yace na taho. A raina dai nace tafi nono fari naje na sake ma babu nacinsa na kwanaki biyu.

A tsaye a parking lot muka ga kawu daddy da alama yasan da zuwan mu, ya karaso cike da fara’a nai saurin bude murfin na fito, cikin murnar ganinsa naje na rungume shi. Har ga Allah bana raba shi da mahaifina hakan yasa nake manta cewa uncle dina ne ba wai shine Baffa ba.

“Sannunku da isowa Gimbaya.” 

Na dago cike da kunya tare da sunkuyar da kai Ina cewa.

“Daddy harda kai a sunan nan?”

“Eh mana ai Gimbiyar ce. Shiga ciki muyi sallama da malam Alhassan.”

Nace to tare da shiga cikin gida cike da murna. Yaushe rabona da gidan tun randa aka fitar dani zuwa masarauta. Babu Kowa a parloun kasa hakan yasa kai tsaye na nufi dakin su Ya Shukrah, na gansu duk sunyi dai-day akan gado suna ta bacci, na saki murmushi tare da juyowa na nufi dakin Mami, itama tana kwance tana bacci a raina nace ‘kaga yan hutu basu da wata matsala’ a zahiri kuma fitowa nayi na nufi parloun kasa Ina jiran daddy dan ba zan Iya tashin su ba.

Da fara’a ya shigo ya zauna, na gaida shi cike da ladabi ga kunya da nake ji dan gani nake tamkar sun gane duk abinda yake tsakanina da Salman. Kawu daddy ya gyara zama tare da cewa.

“Nasan baki yi breakfast ba dan mijin ki ya sanar min, ki shiga kitchen kisa masu aiki su yi miki abinda kike so kici, gashi wadannan sarakan baccin basu tashi ba tunda suka yi sallah suka koma.”

“Na leka ai naga suna ta bacci shi yasa ban tashe su ba.” 

Yace.

“Eh tashi kije kice suyi miki abin kari dan maimartaba sai nanata min yake baki yi breakfast ba kika taho.”

A rai na nace ‘lallai Salman babu kunya, kawu daddy yake ta shaidawa banci abincin na sai kace ya fishi sona’ A fili kuwa mikewa nayi naje na sanar da masu aiki wadanda ni banma sansu ba da alama sababbi ne, nasan kuma kila ajiye aikin suka yi saboda halin su Shukrah na wulakanci da gadara. Parloun na dawo inda na samu kawu daddy zaune yana duba wata takarda wacce da alama tana da muhimmanci. Kallo na ya yi bayan ya ajiye takardar yace min.

“Kinga kinyi sa’a daman jibi zamu tafi Lagos bikin Fatima. Nan suka aiko da cards dinki, Sunce kunyi magana ko? God so kind kuma mai martaba yace daman kuna da shirin zuwa amman ba zai samu dama ba shi saboda wasu matsaloli da yake son ya yi settling d’in su.” 

Baki na yana rawa nace.

“E! Nasan da bikin, To! Kawu to me yace? Yace dai na biku ko?”

Shiru yayi yana nazari na kafin ya yi dariya yace.

“Yace aje dake kiga gurin idan kun tashi zuwa ba sai kunzo kun nemi address ba.”

Murna ta cika ni na dinga yi daga nan muka ci gaba da hira har zuwa lokacin da aka kammala dafa min indomie da kwai, abinda ya bani mamaki guda biyu ce amman na cinye ta tas harda sude plate abin da nake cin daya da kyar amman yau har biyu da dafaffan kwai uku. Lokacin ne Mami ta fito, tana gani na ta saki baki tama kasa karasowa kasan.

“Hajiya sakko mana.”

“Su Dije na gani yau a gidan, anya ba b’atan hanya tayi ba kuwa.”

“A’a zuwa tayi ta gaishe mu.” 

Cewar daddy dan yasan tsab zata Iya gasa min magana.

“Alhaji kenan, baka san Dije yar dadi miji bace? Ace tunda yarinyar nan tai aure bata sake zuwa gidan nan ba saboda bamu muka haifeta ba.”

“Wallahi Mami ba haka bane ba, Salman d’in ne bashi da lafiya.”

Nayi maganar cike da son ta yarda dani. Karasa sakkowa tayi ta zauna a kusa da kawu daddy tana jan furfurar kansa da ta dan fara yawa, nayi kasa da kai na cike da kunya Ina tuna yadda muke da Salman. Gaida ita nayi ta amsa min tare da tambayar yadda nake da lafiya ta, naji dadi sosai na kuma gaya mata lafiya lau. A nan ne kawu daddy yake ce mata zasu tafi dani Lagos din tunda dama zuwa nayi da niyar yin kwanaki luckily kuma yazo da bikin Ya Fatima.

Fitowar su Ya Hameedah ne yasa ni saurin tashi Ina murmushi, suma dai kamar Mami tsayawa sukai suna kallo na, Sai dai kawu daddy ya taka musu birki tare da ce musu su san yadda zasu dinga yi min magana, wannan dalilin ne yasa duk suka hadiye abinda ya taso musu suka shiga gaida ni. Bayan mun gama gaisawa ne daddy yace mu koma daki muka tashi duk muka koma Ina ta jin dadin ganina cikin Yan uwa.

Jefi Jefi idan Salman ya samu time yana kirana yaji lafiya ta, har zuwa dare. 

Shaheedah kuma sai aikin neman ganin bayan dije take, inda aka tabbatar mata da cewa bata cikin masarautar, Koda ta tambayi Salman cewa yayi shima tashi ya yi yaga bata nan ta Iya yiwuwa guduwa tayi saboda abinda Shaheedahn tayi. Muka cigaba da shirin tafiya Lagos inda Salman ya turo min da kudi masu yawa Wai nayi amfani dasu, gashi kawu daddy ma ya bamu mu da su Shukrah kuma duk kai daya.

*LAGOS*

Tunda muka sauka aka turo driver ya dauke mu nake jin wani irin farin ciki, kasan cewar Ina kusa da window yasa Ina hangen komai akan hanya, wani ya burgeka wani ya baka haushi a haka har muka isa gidan uncle Haysam. Gida ne katon gaske mai kyau da tsari, Sun canza gida, Ba wanda na sani bane zuwa na nafarko, Yara da manya suka fito yi mana maraba suma cikin murna da nishadi.

“Gimbiya Khadija….”

Suka dinga fada kunya kamar ta kashe ni, na samu ni dai da kyar na zauna bayan nasa an kawo min ruwa nasha. Kiran Salmanu

 ne ya shigo, a raina nace shidai baya gajiya da kira kamar wani marar aikin yi sai na kira na. Gajiyar hanya ya yi min tare da sake jaddada min cewar ban da zama da yinwu na amsa masa, hayaniyar da ya dinga jiyowa itace tasa be dade akan wayar ba ya katse. Aka dinga zuwa gani na ai matar sarkin bassannabas ce, wacce tazo kwanakin baya kafin auran cacacaca aka dinga yi.

Munsha biki sosai an kai amarya gidan mijinta ina kallon ta a rai na nace ‘itama fa haka zasu yi da nata angon oh ni Dije’ wallahi abin ne yake bani mamaki idan Ina tunawa da irin yanayin da muke kasancewa da Salman, wani ince Anya ba shi kawai yake irin wannan abun ba? Wani kuma ince Wai ko wace mace haka ake mata ne? Babu amsa saboda ni nake tambayar zuciya ta.

Satin mu daya muka yi shirin dawowa gida, da yake Ina son wasu kaya nace a kaini wani shooping mall d’in zanyi siyayya uncle Haysam ya bani driver muka tafi da yaransa kannan amarya su uku sai Hameedah da tace itama zata yi siyayya. Muna zuwa na zabi abubuwan da nake so itama ta dauka suma suka nuna abubuwan da suke so na siya musu akai mana bill na bayar.

Muna fitowa Ina Kokarin saka wayata a cikin jaka na hango wata mata, sosai tayi min kama da malama Mardiyya ta Durbun. Na sake ware ido dan kamar ta baci duk da cewar wannan ta kuma zama babbar mace amman kamannin suna nan. Kasa wucewa nayi sai da na karasa wajan da suke na gaida su, suna ta bina da kallon rashin sani, nayi murmushi tare da cewa.

“Dan Allah kuyi hakuri tambaya zanyi.”

“Toh Allah yasa mun sani yan mata.” 

Cewar wace nake da tabbacin itace malamar tawa.

“Wallahi gani nayi kina min kama da wata malamar mu mai suna Malama Mardiyya, ta koyar damu a makarantar Durbun nursery, primary and secondary school.”

Baki bude  tana kallona, sai naji jikina ya yi sanyi tare da shaida min bafa ita bace, ina kokarin bata hakuri ashe ita kuma mamaki ne ya kusan kashe ta dan tasan bata koyarwa irin wadannan wayayyun ba a Durbun, muryar ta radau tace dani.

“Kwarai kuwa nice malama Mardiyya ta makarantar Durbun, amman ban gane ki ba gaskiya.”

Ai ban kuma jiran cewar ta ba na rungume ta a jikina cike da murna harda hawaye na, wadanda suke tare da ita suka fara min magana cewar na sake ta na fara yi mata bayani, ga motar mu Hameedah Sai horn take yi min saboda lokacin tafiyar mu airport ya kusa.

“Malama ni ce fa Khadija Basheer.” 

Rufe baki tayi, Hawaye suka fara wanke fuskar ta, Gaba d’aya sai farin ciki kuma ya lullube ta..

“Khadija, Dije, Dijen gala yar Baffa ta Gajiyalle mai yar hakiya. Idan ma baki gane ba mune farkon students a Durbun budurwar malam Auwal mai dan gemu.”

Zabura tayi ta mike kasan cewar da tana zaune ne akan kujera, kallona take tana mamaki ganin yadda na canza gabaki daya na, jin horn din ya yi yawa yasa nace cikin sauri.

“Malama akwai labari sosai amman sai mun hudu. Nayi aure idan kunzo kano a masarauta nake, ki tambayi sashen Gimbiya Khadija zamu hadu.”

Ina kaiwa nan na juya da sauri dan karma muje gida Hameedah tayi min sharrin cewa nice na tsaida mu Mami tayi min masifa. Na shiga Mota Ina kallan ta tare da daga mata hannu itama tana daga min, wani irin dadi yana ratsani, gani nake yi kamar naga uwar da ta kawo ni duniya saboda malama tayi min halacci sosai.

*GIM. KHADIJAA*

Mayafi na cire, Dawowar mu kenan inason nayi bacci call din Salman ya sake shigowa wayata, Na wajen ashirin kenan a iya sakkowar mu daga jirgi zuwa yanzu,

“Ranka ya dade…”

“Na gaya miki babu kwanan da zaki sake yi Zawjatii, Ki tattaro kayan ki ki dawo gida yau.”

“Amma yallabai dare ne fa, Ya za’ai nace zan taho yanzu? Fisabilillahi ka bari zuwa da safe mana…”

“Yanzun ne dare yayi? Yanzu fa muka idar da sallar isha’i, Nide na gaya miki ki dawo gida.”

“Ba fa na jindadi… Na kwaso malaria ne maybe saboda weakness din jiki na.”

“Ki dai zo gida yanzu, Akwai doctors.. Zawjatii..! Kinji zucia ta kuwa? Bazan iya kwana batare da naji dumin jikin ki ba, Zucia tah da gangar jiki na sunyi kewar ki… I love and miss you soo much.”

Ajiyar zucia na sauke, Bacci ne dankare a idanu na, Na lumshe idanu kawai ina sosa kunne na da dan karamun yatsa na,

“Shikenan…”

“Na aiko a dauke ki…?”

“No za’a kawo ni..”

“Allah ya kawomin ke Lapia ya tsare mun ke.”

Ahankali nace ‘Aamin..’ Na maida mayafin dana cire jiki na, Jiki ba kwari na sakko kasa ina d’auke da trolley na,

“Ahh.. Ba dai tafiya ba..?”

“Eh wallahi Mami.. Zan tafi, Wai Ammi ce ke tambaya na.”

Na amsa ahankali rashin karyar da zanyi, Mami ta gyada kai tana murmushi, 

“Ummale!!! Jeki kira driver ya sauketa a gida.”

Jira nai har Kawu Daddy ya dawo daga masallaci sannan na masa sallama, Da Ya shukrah naci karo a kofar karamin parlor zata shiga, Hannun ta ri’ke da tray dauke da lemo, Ruwa da kuma snacks.

“Ya shukky.. Zan tafi.”

Kallo na tayi jikin ta yai sanyi, Lokaci d’aya naga ta burkice, Ko bataso na ce mata Ya Shukky dinbane?

“Meya faru..?”

“Ahh babu komai.. Na dauka kwana zaki sake yi ai.”

“Eh! Da sai da sss…”

Ban karasa ba sakamakon hango Masoud da nayi, Yana tafe yana gyara hular kansa. Kicib’is yai yana kallo na, Nima na shiga kallon sa, Kallon mamaki, Meya kawo shi gidan Kawu daddy? Kuma da alama wajen Ya shukrah yazo. Da sauri na saisaita kai na ina a’uziyya da sharrin shaidan daya sa ni tsayawa,

 “Hajiya Khadijaa.. Ranki ya dade rai kanga rai?”

Kasa k’oda motsi nayi, Jin muryar masoud da nayi cikin kunnuwana, Wanda ko suma nayi na farfad’o zan gane ta, 

“Sannu! Ina yini.?”

“Lapia qalau… Ya mai gidan naki.”

Kasa amsa nayi na koma ciki kawai, Kawu daddy na parlor da Mami da Ya hameeda suka ga na dawo ban tafi ba,

 “Ah dije kin fasa sai da safe ko…”

Mami ce ta tambaye ni tana bina da kallo, Ni kuwa gaba d’aya zucia ta naga su Ya shukrah da tsohon saurayi na Masoud, Wanda na d’au son duniya na dora masa, Shin wannan cin amana ne ko ci baya? Na tambayi kai na ina nisawa.

“Khadija… Menene?”

Kawu daddy ya tambaye ni cikin kulawa, Na sauke ajiyar zucia hade da girgiza kai, 

“Babu komai Kawu daddy.. Ya shukra ce take zance shine na basu waje.”

“Kice tana zance da tsohon saurayin ki dai.. Masoud, Itama shukrah bataji wallahi.”

Mikewa Kawu daddy yayi yana bin ya hameeda datai magana da kallon karin bayani,

“Saurayin Khadija na baya?”

“Eh daddy..”

Ficewa yai wajen Shukrah , Bansan ya akai ba najiyo muryar sa yana wa shukra fada, Can ta shigo kanta a kasa tana kuka. Dawowa yai yana huci,

“Haba wannan wane irin rashin kan gado ne eh? Ko kunya bakya ji? Tsohon saurayin kanwar ki? Kinsan shi sarai ya san ki shine zaku dawo yanzu gotai gotai dake kina kula shi..?”

“Daddy ya girme ni fa…”

Shukra tace cikin kuka.

Kanta yai tamkar zai doketa ta fadi, Ya shiga karkada mata hannu,

“Na hada ki da girman na gwara kan ki. Ni zaki kawowa maganar Shirme? Duk kin kore samarin ki, Dama shine yake hure miki kunne?”

Kuka shaheedah ta fashe dashi tana shessheka, Kawu daddy yaja tsaki,

“Hajia ya akai ake wannan katobarar a gidan nan ba’a sanar dani ba? Ina Shukrah ina tsohon saurayin Khadija?”

“Kayi hak’uri daddyn su. Nima nayi nayi taki yadda, Ni nafi mata sha’awar Sulaiman ma dan gidan Amb Haroun.”

Tsaki yaja yana bubbuga kafafun sa, cikin fada yace,

“To ku saurare ni daga ke har su Hajia, Daga yau idan na sake ganin kafar yaroncan a go….”

“Daddy be dade da accepting feelings dina ba.. Da ya..”

Wani mari ya sauke shukrah dashi seda naji tamkar a fuska ta aka falla shi. 

“Idan na sake ganin kun cigaba da mu’amala dashi ban yafe muku ba gaba d’aya. Sannan ku saurare ni dakyau kuji, Ba zamu cigaba da zama rida rida daku ba kai d’aya agidn nan ba zeyiwu ba, Kuna samu kuna korar su akan me? Wallahi ba Za’a sake ba, Abu na biyu mungama magana da su yan uwana, Ke Hameeda kece babba zamu hada ki aure da Na’eem dan Yaya kabiru dake jos. Ke kuma shukrah Abdul (yaron sa) dai na waje na, Da shi Zan hada ku, Domin na yaba da hankalin sa da nutsuwar sa, Tun ba yau ba nake kwadayin ya sake kusanci dani ta hanyar bashi auren jini na, Da Khadija kafin anemi aurenta shi nayi niyyar hadasu saboda hankalin ta. Na gaya masa tun tuni kuma ya amince yana son ki, Ke shukrah ba magana nake miki ba?”

Kuka wiwi shukra take, Ita kuwa Hameeda batace komai ba, Domin dama Ya Na’eem yana burgeta, Shukrah kuwa burgima tashiga yi tana yakushin kanta,

“Daddy Abdul fa kace?Dan girman Allah kayi hak’uri ka sauya mun wani.”

“Alhaji ka duba zancen shukrah, Haka dinne, Ni dama aciki….”

“Yimin shiru, Ai duk kusan hankalin ku d’aya keda su, Duk Ke kike sasu agaba kina hure musu kunne…”

Wayar Kawu daddy ce tai kara ya dauka ya fice yana amsawa cike da girmamawa, Sai a sannan hankali na ya dawo jiki na,

“Kinji dadi kin shiga tsakanin soyayya..”

Cewar ya shukrah tana harara ta. Daria ma taso bani wallahi, Ni da ita kowa ya shiga tsakanin soyayya oho, Na sauke ajiyar zucia kawai. Agogo na kalla tara saura kwata. Da sauri na dakko wayata a jaka, 30 missed calls  Salman yayimun. Kiran sa nayi najita busy da alama waya yake yi. Sai ga Kawu daddy ya shigo yana murmushi,

“Kawu zan tafi…”

“Ah ai gashi nanma ya taho nan din.. Yace dama yana da niyyar zuwa mu gaisa.”

“Wa…?”

“Mai gidan naki…”

“Sarki Salman?”

Cewar Mami ta tambaya cikin tsantsar mamaki.

“Eh wallahi, Yace ya kikkira wayarta bata dauka, Hankalin sa ya kasa kwanciya shine ya taho da kansa.”

Kunya duk ta kamani, Nasan Salman zai aikata fiye da haka. Zama nai a hannun kujera ina wasa da yatsun hannu na…..

<>

_Afuwan zafafa fans.. Ba zaku samu kibiyar ajali ba na yan wasu kwanaki. Saboda wani uzuri daya taso🤲🏻Dana kammala zan cigaba da posting IN SHAA ALLAH!_

_Yar uwa kinason karanta zafafa amma documents? To zafafa na harhada kayan su. Da an kammala Za’a yi documents dinsu duka akan Naira dubu d’aya da…….._

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…

KIBIYAR AJALI 22

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI…..!_…

KIBIYAR AJALI 19

Advertisement  _ I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…