KIBIYAR AJALI 26

Advertisement

 

*2__6*

 

Tun da aka yi salla asuba ya dauki motarsa yabar masarautar Basannabas shi kadai ba tare da ya dauki d’an rakiya ba dan baya bukatar hakan, daman haka yake yi idan yaga duk sun kasa ai watar da komai

akan sarki Salman. Shi kuma duk duniya babu wanda ya tsana sama da yaron nan, ko baban shi ba ya ja musu rai kamar yadda yake yi musu sai kace wani yayan su.

  

Tafiya kawai yake yi yana jin zuciyar shi tana suya saboda ya yi mamaki kwarai da gaske da yaga Salman ya yi aure ba tare da sanin zai yi ba sai a ranar. Saboda haushi da kuncin da yake ciki besan lokacin da ya tuge rawanin dake kan shi ba, ya wurga kujerar gefen shi. Sai da ya kusa barin cikin kwaryar birni sannan ya yanki wani daji wanda ba a taba halatta mishi kwalta ba. Nan ma ya yi tafiya sosai kafin ya yi parking ya fito, ya fara tafiya a kafa kasan cewar mota bata shiga gurin sai dai kaje a kafarka.

 

Da kyar yake iya takawa saboda ya gaji amman da yake zuciyar shi a kekeshi take sam be ji ya karaya ba har sai da ya dangana da wata yar karamar bukka dake jikin wani katon dutse. Wani hayaki ya fara fitowa daga cikin ta, yana tsaye har hayakin ya dena fitowa sai yaji ana yi masa iso cewar ya shiga. Yana shiga bokan ya kalle shi wanda shi din ma ya manyanta alamar ya dade a cikin harkar bokanci ta bayyana a jikin shi, ya dakko wani farin ruwa karkar dashi a cikin kwarya ya ajiye a tsakiyar su tare da sanya d’an yatsa a ciki, hotan sarki Salman ya bayyana a ciki shida Dije suna kallon juna. Bokan ya sake kallon shi tare da cewa.

Advertisements

 

“Daman nasan dole zaka zo, tabbas aljani kurt ya yi gaskiya da yace min kana cikin bacin rai.”

 

Yaja dogon numfashi tare da shafar kanshi yace.

 

“Yaron ne ya shammace mu, tabbas ya matukar bani mamaki saboda na yi tunanin duk wani sirri nashi a tafin hannu na yake ashe ba haka bane. Tabbas ni da su muna cikin damuwa boka.”

 

Boka ya kankantar da idanuwa yana kallon cikin ruwan yace.

 

“Kayi kyan kai da kazo tun da wuri, ina tabbatar maka da ka bari sai anjima to babu abin da zan iya yi maka. Yanzu me kake so a aiwatar maka?”

 

Sai da ya kuma jan wani numfashin sannan ya gyara zama yana cewa.

Advertisements

 

“Kamar kullum dai, ina son a cire masa son mulkin Basannabas. Sannan yaji ya tsani komai dake cikin duniyar nan, a kawar da hankalinsa daka kan komai har sai abin da muka zartar masa.”

 

“Kenan kai baka da matsala da wannan yarinyar da ya auro ko?”

 

“Bana jin zata iya hanani aiwatar da duk abin da naga dama, shi yasa banji ta dameni ba kamar shi da ya yi mana wannan kitumurmurar.”

 

Boka ya buga kasar dake gefen shi, sai ga wuta ta fito ta tsakiyar tana ta ci. Sannan ya kalleshi yace.

 

“Kayi zaton wuta zata fito daga cikin nan?”

 

“A a boko ban yi zaton zata fito ba, kawai ganinta nayi.”

 

“Toh idan kayi wasa haka yarinyar nan zata zame muku. Kana daukar ta karamar alhaki, ita kuma za ta yi amfani da damar ta na matsayin matarshi ta tarwatsa ku gabaki d’aya.”

 

Mamaki ya kama shi, nan da nan kuwa yace yana son ayi aikin har akan ta. Taji ta tsani mijin nata, kuma bata son ganin shi ko jin muryar shi.

 

“Shikenan zamu fara yin aikin ka yau bayan rana ta fadi. Karka damu kanka kayi bacci mai dadi kasa a ranka anyi komai an gama.”

 

Jijjiga kai ya yi sannan ya ajiye masa wata bakar jaka wacce da alama muhimmin abu ne a ciki, daga nan suka yi sallama ya tafi shi ma boka yaci gaba da aikin sa. Sai da ya shiga mota sannan ya dauki rawanin sa ya mayar kasan cewar ya dan fara jin sassauci akan kuncin da zuciyar shi keyi. Ya koma Basannabas yana jin wata iska tana shigarsa ta ko’ina.

 

*KOFAR KUDU*

(SASHEN GIMBIYA KHADIJAA)

 

Ina zaune na rafka uban tagumi ina kallon tv, Yanzu bataliyar yayan uncles dina suka tafi, Kowanne zai dauki iyalin sa su kuma garin su. Duk cimar da aka kakkawomin ne nide na tarkata na babbasu, Na harhada da wasu kayaiyakin na cikin lefe na. Sai tsaki nake jerawa saboda zaman kadaici…

 

Bahijja d’aya daga cikin hadimai dake tayani zama ta shigo kanta a kasa tana murza hannaye,

 

 “Uwar daki na.. Allah yakara miki lapia gimbiyar mu. Ummah Hansatu tace na mata iso zata shigo an aikota..”

 

Cike da farin cikin zan sake ganin mutane atattare dani na daga kai da sauri ina nuna mata da hannu alamun nabata dama. Facemask dina na zare ina sake baje kofofin hanci na.. Tabbas warin nan yana nan, To ko dai wani abunne ya shigo ya mutu? Ko bera ne? Na tuno idan jaba ta mutu a dakin da nake kwana a k’auyen mu haka wurin yake tashi .

 

Ina sanye cikin atamfar super wax, Amber color, Tasha surfani da stonework. Santsin da gashi na yake shi yasa ban daura dankwali ba, Na yafa mayafi a kai na. Bahijja ce ta rako matar da ta kira da ‘Ummah Hansatu..’ Dattijuwar mata ce amma bata manyanta can ba. Wasu yammata ne abayanta kowacce tana janye da akwatuna, Har guda 5 da baskets baskets. Da kumbuna suma cike da kaya. Yammatan suka futa, Ita kuma ta zube a gaba na tana kwasar gaisuwa. Ta kark’are da,

 

 “Ga kaya nan… Inji mai babban daki..”

 

‘Mai babban daki….? Bayan kayayyakin da suka babbayar?’ Tamkar tasan maganar da nake a zuciata. Tace,

 

 “Mai babban ‘daki itace mahaifiyar sarki Salman.”

 

 “Okay! D’aya daga cikin wanda naje na gaisar jiya..?”

 

 “A’ah! Anya kuwa? Ranki ya dade. Jiya gaba d’aya ba wanda ya shiga sashen mu. Amman dai ga sako tace akawo miki..!”

 

Kai na ya k’ulle. Kwarai matuk’a na kasa gano wacece mai babban daki.. Tunda dai har su uku naje na gaisar, To wacece acikin su.

 

“Sunana Hansatu. Amma yara da tsirarrun mutanen masarautar nan na kira na da Umma Hansatu. Nice babba a hadiman me babban daki, Kiyi min afuwa tun jia naso kawo kayan nan. Amman ban gama hada su ba…”

 

 “Toh nagode sosai Umma Hansatu. Ayiwa mai babban daki godia, Da yardar Allah zan shigo Na gaishe ta.”

 

 “A’ah ki kara hutawa ranki ya dade. Allah ya huta gajia, Na barki lapia.”

 

Ficewa tayi bayanta rissina ta kwashi gaisuwar ban kwana, Ta fice kanta a kasa. Naja tagumi na zanga shi ina taune lebe na.

 

 ‘Shin wacece mai babban dakin to? Ita kanta Ummu Hansatun bata wayar min da kai ba.. Kila ba’acikin masarautar take ba, Wata zuciar tabani amsa. Na sauke ajiyar zuciya ina kallon tilin kayan da suka kusa shanye rabin royal center carpet din dake malale a tsakiyar parlor na. Ni gaba d’aya abubuwan su sun fara bani tsoro, Haka ake kyauta kamar ba’ason kudin? Kowa idan ya tashi sai yayi bajinta? Shiyasa naga Kawu daddy kenan su Mami nata gulmar wai kayan garar da yasa akamin wai Ko na yar shugaban kasa albarka. Ashe yasan irin gidan da zan shiga? Mikewa nai daga kan kujerar da nake na koma daki, Bandaki na shiga na canza pad. Jinin sai kwarara yake tamkar dai sabon period. Dama kwanaki uku nake, Gashi jiya ya dawo min idan na hada da na yau kwana har 5 kenan. Kila circle din nawa ne ya canza, Wata zuciar tacemin. Sabuwar waya ta na kunna da Kawu daddy ya bani. Dake sabon sim ne du babu contacts dina na da aciki. Siririn tsaki na saki, Na rasa mai zanyiwa zucia ta taji dadi.

 

                  CYPRUS

        (HOTEL——NICOSIA)

 

Bluetooth ne a kunnen sa ya hada hannuwan sa waje d’aya yana dan bubbuga su. Magana yake a hankali cikin nutsuwa,

 

 “Okay! Nagane.. No no issokay. Go ahead! Wai dole seda yadda na.. ? Huh! Toh approved!…Waziri na baka wuk’a da nama.. Yauwa! Jia nayi mafarkin mun kusa haduwa dashi fa…Ah’ah I.. Ah..”

 

Kasa furta sunan yayi. Gashi yanajin sunan a zuciar sa, Amman labban sa sun gaza furtawa. Yayi yayi ya kasa, Kawai ya katse wayar yana mai dafe kansa, Ji yayi wani irin yanayi na neman kamashi. Alhassan ya kira a waya ringing biyu ya dauka,

 

 “Yauwa Alhassan.. Nace a fara ginin nan. Zanen farkon nan yayi. Su fara. Ba tsayawa please.” Kit ya katsa kiran.

 

Gallery din ipad dinsa ya shiga, Zanen wani gidan bene ya shiga kalla yana murmushi. Ginin benen za’a fara yin sa ne. A gefen sashen sa daga baya. Gida ne wanda ya barwa kansa da Alhassan amanar yin sa. Sai angama shi tas. Sannan zai sa a maida Khadija cikin sa. Murmushi yai yana tuno sanda yafara ganin ta a wajen sauka. Bai sake mata gani na biyu ba har yanzu da take a matsayin matar sa. So yake yaji koda muryar tane amma izzar sarauta ta hanashi. Ya tsotsi kasan leben sa yana hasaso Kyakkyawan fuskar ta. Jingina yai a jikin kujerar sofa da yake. A hankali yake furta,

 

 “Cute! Brave little lioness..”

 

 “Your majesty… Itz time! Your majesty! Your majesty..! Your majesty.!”

 

Firgigit ya tashi daga duniyar tunanin Khadija daya tafi. Kallon baturen yayi, Wanda escort dinsa ne na wajen taron da za’a tafi.

 

 “Pardon…!” Cewar sarki Salman yana sake hade rai tamkar ba shi ne ya lula duniyar tunanin mace ba.

 

 “I said.. Itz time, Thrice!”

 

 “My bad.. Lead d way!”

 

Ficewa sukai, Suna gaba yana biye dasu baya. Cikin kayan sarauta da rawanin sa mai kunne biyu. Designer shades din dake idanun sa ya sake amsar kayan jikin sa. Tafiya yake cikin k’asaita , Matashin sarki mai jini a jika. Mai madaukakin kwarjini da hasken annuri. Har kujerar da zai zauna sai da suka Kai shi, Dogaran sa guda biyu na gaban sa. Kujerar tasama wadda zai zauna ta alfarma ce mai dauke da tambarin …’His royal highness ‘Emir of Basannabas. Salman Aliyu Salmanu. (SAS), Kowa sai da ya rissina masa, Guri ya dau shiru na yan mintinan girmamawa. Wani zama yai na sarauta. Ya mike kafafun sa akan table din gaban sa.. Ta cikin rawani kuwa jan leben sa yake. Kunnen sa d’aya da bluetooth yana sauraron voice-notes din da Galadima ya turo masa kan lalle abunda zai ce kenan idan jawabi yazo kansa…

 

 *MASARAUTAR ‘BULLO…*

(FADAR MAI MARTABA SARKI IBRAHIM HASHIMU)

 

“Shin fulani da sanin mai gidan ki kikazo nan…”

 

Cewar sarki Ibrahim mahaifin gimbiya Shaheeda.

 

 “Bappah na kira shi sau ba adadi bata shiga, Nagaji da wulakancin da yake min. Bappah ace zaiyi aure amma bansani ba?” Gimbiya Shaheeda ta karasa fada tana kecewa da kukan makirci.

 

“Ya isa! Bar kuka.. Ni nasan Salman bai isa ya tsallaka karan dasu Galadima suka ajiye ba. Sai dai idan wata kullalliyar aka shirya..”

 

 “Bappah suma wai acewar su Gimbiya Najwa diyar sa tace ko shi galadiman bai sani ba, Sannan ko ciroma bai sani ba shima. A tak’aice dai Bappah bawanda yasan da auren da yayo.. Sai dai idan Sa’adatu ce (mahaifiyar SAS)”

 

“Itan da ko kallo bata isheshi ba? Kai akwai kullalliya dai..”

 

 “Ko ni Bappah ca nai sai dai idan ita yarinyar ce tayi asiri. Domin Salman ko kallo mutane basu isheshi ba.. Kuma Bappah yar rik’o ce fa. Ashe ba shine mahaifin ta ba.”

 

“Eh haka naji labari da nasa akamin bincike. Kiyi hak’uri. Mu dai burin mu baya w…”

 

Kasa karasawa yai sakamon yadda matar sa ta shigo tana baza kamshi sai rausaya take, An girma ba’asan an girma ba.

 

 “Yar baffan ta ashe kina nan…?” Cewar Gimbiya Asma’u (Matar Sarki Ibrahim ta farko. Mahaifiyar su gimbiya shaheeda.)

 

“Ina nan Hajia…”

 

 “Ranka ya dade. Afuwan zan dau fulani na yan wasu mintina. Akwai masu jira awaje, Su magatakarda, Da shamaki, Da. dokaje.. Naga jakadiya Yaruwaiyya sai tare-tare, Nasan dai badan ta tsare ka da surutu ba aida kana tare dasu.. Fulani tashi muje, Allah yakara maka lapia, Bari muje.”

 

Bakin sarki Ibrahim a hangame suka fice, Sai murmushi yake kaman sabon tabi.

 

    *SASHEN TORO BABBA*

(GIMBIYA ASMA’U)

 

Suna komawa gimbiya shaheeda ta zube a kujera tana yatsina fuska,

 

 “Shikenan na zama kaskantacciya kenan Hajia? Shikenan na zama bani da gata kenan? Hajia kuna raye har Salman ya kara aure? Bayan alkawarin da kika yimin na dagani ba ‘kari? Kwata kwata shekara nawa da auren namu? Amma harya kara aure.”

 

“Ya isa haka Fulani.. Kibi komai a sannu, Ta karkashin kasa zamu bi. Yadda ta shigo haka Zata fita. Da gundumemin sharri ma kuwa, Bazata koma gidan su ba sai da tabo. Malam na gangare ya tabbatar min da hakan. Ba zaki koma ba sai da boma boman harka..”

 

 “A hayye.. Hajjaju tawa..”

 

Karaf suka tafa suna shewa..

 

 “Kince plan 1 dinku yayi har kin ganta da mask ko?”

 

 “Eh hajjaju. Amma fa kyawunta ya tsorata ni, shegiyar akwai yalwar gashi da jiki mai kyau. Too bad yar talakawa ce. Dana rena kai na..”

 

 “Haba wa ai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, Uta din banza? Yadda ta shigo da tsunmomaran kayanta da jikin ta haka Zata fita dashi da dankwalelen tabo ma kuwa..”

 

 “Hajjaju na.. Shiyasa kike sake shiga can cikin zucia ta. Ta gaban goshin Bappah, An buga dake an barki ya zasuyi dake..?.”

 

“Farin wata…”

 

 “Sai kallo Hajjaju na.. Ki da’de kiyi karko.”

 

“Kome zasu kitsa miki, Ki bar su a haka..Kuyita tafiya a haka. Muga gudun ruwan su.”

 

 “Ai dama bana nuna komai, Kome suka ce yi nake.”

 

 “Yauwa sai da kwantar da kai… Ina Sa’adatun kuma?”

 

 “Oho mata wallahi… Tana sashenta a yashe..”

 

Dariya suka shiga babbakawa a tare, Tamkar masu tabin hankali…. Suna yi Suna shirya surkullen da Shaheeda Zata tafi dasu Masarautar Basannabas. Wanda gaba d’aya duk na kauce hanya ne. Haka bokan nasu yazo, Shima da tulin layoyi kowace laya da allura ajikin ta guda 99. Da barkono tsidugu guda 7 an rubuta sunayen Khadija akai. Ta kona kowanne guda d’aya sau bakwai. Kowanne da ranar sa, Da sauran abubuwan kauce hanyar da bazasu lissafu ba……..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 31-32

Advertisement  _*KIBIYAR AJALI…..!!!!*_ _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_            🏹👑👩‍❤️‍👨💝 *MALLAKAR:- NANA…

KIBIYAR AJALI 11

Advertisement                  *11*         *Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin…