KIBIYAR AJALI 27

Advertisement

 

*2__7*

 

*MASARAUTAR BASANNABAS*

 

Bayan waziri sun gama waya da sarki Salman, ya tara manyan yan majalisa ya sanar dasu abinda suka tattauna. A take kuma ya dauki wayar ya kira Gimbiya Huwaila cewar ta kira babban d’an ya dawo za’a mishi mukami, ta amsa tare da katsewa har da rawarta a cikin bedroom. Bata wani jira ba ta kirashi

kusan sau biyar sannan ya yi picking , dan kar ma ya tsaya bata lokaci ta sanar dashi sakon waziri, cike da murna kuwa yace gashi nan zuwa.

 

 

Advertisements

*SASHEN GIMBIYA JALEELA.*

 

Gabaki d’aya ta rasa inda zata sanya kanta taji dadi, tunda Gimbiya Huwaila ta sanar da ita sakon Waziri hankalinta yake a mugun tashe, tabbas tasan duk cikin su itace ke cikin siradin rayuwa saboda rashin samun ‘da namiji. Ta juya tare da kallon yaran nata, wani madacin abu ya tokare mata wuya saboda bakin ciki, yanzu duk gidan wani zasu tafi su barta, babu wanda zata yi iko akai sai dai ayi mata iko da su. Ba abin taje ta kai kukan ta wajan mahaifinta ba sam ba zai saurareta ba, yana matukar yi mata kokari wajan ganin ta kwantar da hankalinta, hakan yasa ba ta fiye kai kuka gurin shi ba, gara taje wajan Galadima ko Ciroma ko kuma Wambai.

 

Mtwww ta kuma jan tsaki a karo na ba adadi, ta kwalawa yarta Sabeera wacce tana ji amman ta yi shiru taci gaba cin abincin ta.

 

“Baki ji ina kiranki ba ne Sabeera?”

 

“Haba Mah gani ga ki amman ace ki ta kwalamin wannan uban kiran, gani ai duk abinda zaki fada zan ji ki.”

 

“Kunsan dai komai zan yi akan ku ne, so nake naji wai har yanzu kuna tare da d’an gidan vice- president d’in nan kuwa?”

 

Advertisements

Sabeeera ta yatsina fuska sam bata son yaron nan saboda yaudara gare shi ta masifa, akwai wanda ita take so kuma shi sai wahalar da ita yake yi yana ja mata rai. Ta ture plate din gafe tare da kallon mahaifiyar ta tana cewa.

 

“Wallahi Mah ko maza sun kare ba zan auri Kamal ba, yaran nan mugun dan iska ne.”

 

“Toh ke ina ruwan ki da iskancin shi? A jikin ki zaki yafa ko kuwa? Ni a gani na kuna yin aure zai dena. Yaron nan gaba baban shi ne zai rike mulkin kasar nan, ki zama first lady me ye na cewa ga aibun shi Sabeeera?”

 

“Ni wallahi bana son Kamal Mah, bana son shi I hate….”

 

“Ya isa karki karasa, abin da nake nufi s….”

 

Ganin mahaifiyar ta na nema takura mata sai ta mike ta bar mata gurin. Gimbiya Jaleela ta dafe goshi, ita kuwa ta shiga uku, ba magajin sarki ga yaran nata mata duk sai a hankali, idan ta taro wannan sai waccan tayi can gurin. Dole ta mike ta dauki alkyabbarta ta nufi wajan Gimbiya Sa’adatu ranta a d’an bace. Bayan an yi mata iso ta shiga ta tarar da ita a kishingid’e, ta nuna mata gurin zama amman ta girgiza kai alamar bata bukatar gurin zaman. Sai da ta dade tamkar ba zata yi magana ba sannan tace.

 

“Kina ganin kinyi sa’a a cikin rayuwarki ko? Saboda kin haifi yara maza zaku gaje masarautar Basannabas. Toh wallahi bari kiji, idan har shegen abokin danki ya auri Sabeeera, na rantse da Allah sai kunyi nadama. Nasan duk wani makirci daga gareki ne na sani, toh ko da bokan ki kike yawo na fiku wulakanci da rashin mutunci. Sa’adatu ina son duk wani abu da ya shafeki kar ya kuma rabo ni, idan kuma kin ki uhmmm.”

 

Gimbiya Sa’adatu ta yi kasa da kanta, bata gane abin da duk Jaleela ke magana ba, sannan ba ta san a cikin ya’yan nata wanne take nufi ba, sai kawai ta shiga bata hakuri cikin karya wuya. Jaleela ta kada alkyabbarta ta fita, yayin da Sa’adatu ta girgiza kai tana nemar musu shiriya idan suna da rabo. Sun ki su barta taji da damuwar da take ciki. Da sunyi abubuwan su suka ga babu nasara sai su takura mata cewar ita ce ta yi musu wani abun. Juyawa tayi taci gaba da yin hailalarta tare da neman Allah ya shiga cikin lamarin ta dana yaranta.

 

*BAYAN WASU AWANNI….*

 

   *Kishingide* Gimbiya Sa’adatu take, Lokaci zuwa lokaci hawaye kan kwarara a kyakkyawar fuskarta. Yar dattijuwa ce wadda bata manyanta can ba. Kana kallonta kasan akwai jin dadi a tattare da ita, Amman rashin kwanciyar hankali shi ya mai data ta dan rame ta idanuwan ta manya suka kara furfitowa. Fara ce sol tamkar ita tayi kanta. Kallo d’aya zaka mata kasan tanada manyan kyau. Sai dai ace tubarkAllah kawai. Domin Allah yayi mata zatin halitta.

 

Ahankali tasa hannun ta toshe kunnenta d’aya saboda yadda sautin bushe bushen algaitu ke tashi ta ko’ina a masarautar. Da alamun wani babban taro ko nad’i za’a yi. Amman batada masaniya ko kadan. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Bayan ta bawa hadimarta izinin shigowa,

 

Hadimarta ce ta shigo kanta a kasa. Gurfane tayi awajen bayan ta kwashi gaisuwa,

 

 “Uwar daki na.. Allah yakara miki lapia da nisan kwana..”

 

 “Aamin Khairat!”

 

 “Uwar daki na…. Yarima ne yace na masa iso wajen ki.”

 

 “Ahh! Na baki dama. Hanzarta ki shigo da shi.”

 

Shigowa yayi sanye cikin manyan kaya na sarauta, Kansa yasha rawani me kunnuwa biyu. Kana kallon sa kasan tsatson gimbiya Huwaila ne. Domin kamar su d’aya tamkar dai tayi kaki ta tofar. Sede shi dogo ne sosai ya dakko zubin tsayin marigayi Aliyu Salmanu, Mahaifin su.

 

Yana shigowa gaban ta ya yanke ya fadi. Domin batai zaton Abdulqadeer bane, Ta dauka wani ne daga cikin yaran dai. Gaba d’aya sai jikin ta ya nemi d’aukar rawa, Ta shiga kalle kalle tana duban ta ina zata hango shi..

 

Murmushi yai irin na gefen bakin nan kafin ya shafi kasan rawanin sa inda gemun sa yake.

 

 “Ammi… Ni baki farin cikin gani na bane?”

 

Muryarta na rawa ta girgiza kai da saurin gaske tana mai neman saisai ta zuciar ta dake barazanar fad’owa saboda tashin hankali tace,

 

 “Abdulqadeer! Barka da dawowa!”

 

 “Hmm! Kamar gaske! Barka kadai Ammi, Fatan na same ku lapia?”

 

 “Alh… Alhamdulillahi!”

 

 “Khal ko?… Nasan Khal kike begen gani. Well long story shot, Yace bazai zo ba. Wannan karon ma yace bai da ra’ayi. Ko fa sunan ku na kamo masa ca…”

 

 “Ya isa Abdulqadeer! Ya isa dan Allah.” Tai saurin katse shi tana dartse hakoranta.

 

Wata shegiyar hamma ya saki kafin ya mike yana duba hadadden agogon hannun sa,

 

 “Sarauta za’amin fa.. Tunda wancen juyan baya haihuwa. Kuma idan akace za’a raba shi da kujerar zai iya rasa ransa saboda mayatar so. Anyways yau dai za’amin nadin hakimci. Na manyan yan majalisar sarki, Nasan ba wani sani kikai ba, Tunda ba gada ki kai ba, Well…. Uhmm! Kowacce fada akwai manyan yan majalisar sarki da duk harkar data shafi fada sai an dama dasu, Duk wata sarauta ko wani nadi bayan ta manyan yan majalisar sarki, To suna ne kawai domin sarautar sunan ta ta taka haye bata gado bace.. Kamar irin su shirmen mukaman sarkin kofa haka ko… Kingane?”

 

Murmushi kawai tayi, Saboda tasan zuwa yayi kawai ya tada mata da hankali kuma ya ci mata mutinci. Tunda ya tabo mahaifin ta yanzu( Marigayi Malam Abdullahi( Dogari/Sarkin kofar kudu).

 

 “Nagane.. Kuma nagode.”

 

 “Yauwa…So za’a bani hakimcin waje.. Babban hakimi/Makaman Basannabas.”

 

 “Allah yabada sa’a Abdulqadeer!”

 

Ya sheke da dariya yana kureta da idanu,

 

 “Anya.. Anya har zuci wannan adduar take? Saboda zaki so ace Khal ne keda wannan mukamin ko? Wait ai da yazo kila shima abashi dallatu haka.. Koya kikace Ammin mu ta mutunci?”

 

Shiru tayi tana maida kanta ga shiegegiyar talabijin din dake nuna wani wasan kwaikwayo na india,

 

 “Toh bara na kyale ki haka. Sai gani na biyu.”

 

Mikewa yayi ya fuce yana murmushin mugunta. Yana fita ta bada damar a kulle mata kofar sashen ta. D’akin ta ta koma ta bude shafukan kuka tana jijjiga kanta,

 

 “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yaa Allah! Ka shiga lamuran mu. Astagfirullah! Allah na tuba..”

 

Kuka kawai take na tsantsar tashin hankali, Ace babban d’anta ne sarki, Amma batasan komai na harkar mulkin sa ba? Shi kansa ba tada ikon ganin sa. Sauran yan uwan sa da zata kalla tadanji dadi suma ana neman mata katangar K’arfe tsakanin ta dasu. ? Shin wa zata gayawa damuwarta a duniya taji sassauci. Kirjinta cike yake da damuwa kala-kala. Gashi batada wani dan uwa da zata tunkara da maganar…

 

Ranar gabaki d’aya a daki ta wuni tana kuka, Sannan tayi nafilfili tana mai rok’on Allah daya sassauta mata kangin rayuwar da take ciki da iyalin ta…..

 

<><><><><><> 

 

*KOFAR KUDU…*

(SASHEN GIMBIYA KHADIJAA)

 

Yan kwanakin nan gaba d’aya a hargitse nake, Cikin bacci zan farka na shek’a da gudu nayi wajen kofar parlor, Gaba d’aya ko’ina na sashe na tsoran sa nake. Ji nake tamkar ana kiran sunana.

 

 “Wayyo Allah na! Wayyo Umma na, Wayyo Bappah na… “

 

Na rufe kai na da hannaye na ina hawaye. Gaba d’aya yanayin da nake ciki yana da wuyar fassarawa. So nake na bude kofar na fita, Kashedin Kawu daddy daya min ranar da Za’a kawoni kan cewar Kar naje ko’ina sai da izinin mijina, shine yake hanani tafiya. Tunda nazo bana fita, Sai rakiyar baki zuwa bakin kofa, Gashi yanzu kwata kwata ba’kin ma sundena lekomin tamkar anyi ruwa an dauke.

 

Razana nake yi, Jiki na sai kakkarwa yake. Da dare yayi shikenan bani da sukuni, Sai fargaba. Wallahi na tsani masarautar nan da abunda yake cikin ta. Ni dai gwanda zaman kauyen mu na durbun sau dubu, Da kuma zaman gidan Mami wallahi. Akan masarautar nan. Kwanciyar hankali ? Bacci mai dadi? Ina tuntuni nayi sallama dasu, Na nemi farin ciki na rasa, Saboda tsabar tashin hankali wallahi ko wayata bana dauka, Gashi jinin nan sai zuba yake. Ni na rasa wane irin period nake? Tabbas don ina cikin tashin hankali ne shi yasa bai tsaya ba.

 

Ina tsaye har akai assalatu. Na koma kan kujera na rakube ina jiran gari yayi haske. Ina tsakure a kujera har gari yai haske. Bandaki na shige nayo wanka. A tsorace na zura kaya na fito da gudu daga dakin na koma dayan parlorn,

 

Naja tsaki lokacin da na jiyo kirarin dogarai suna yiwa SAS, Ta sashe na suka wuce lambun sa, Nayi Allah ya isa tafi dubu. Na tsane shi, Na tsani mai kiran sunan sa, Na tsani abunda ya dangance shi. Ni wallahi zaman gidan nan tamkar akan kaya nake. Shima bai damu dani ba, Tunda yai tafiyar sa har ya dawo baitaba nemana ba ko da awaya. Babu ruwan sa dani, Duk yadda akai ya aure ni ne ya tarwatsa farin ciki na ya raba ni da Mas’oud.. Allah ka bimin hakk’i na..

 

Ina zaune na jiyo duriyar dawowar su, Hasken kyalli kyallin lemar sa da ake dagawa har ta window na. Zuciya ta amsa dai dai lokacin da shi da fadawan sa suka wuce..

 

 *SAS*

 

Tun wucewar sa ta farko yake son ya shiga sashen nata, Amma gangar jikin sa ta hane shi, Gaba d’aya tun ana’i washegarin ranar da zai dawo daga cyprus ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali, Haka kawai yaji tamkar an zare masa ita aransa, So yake yayi tunanin ta ya kasance da ita amma tamkar an musu katanga da juna, Tana zaune a masarauta inda yake amma kamar ba matar sa ta sunnah ba? Hawaye ne suka shiga reto ta cikin gilashin sa,

 

‘He badly wants her by his side… Amman yarasa meyasa duk lokacin da zai so ganin ko da fuskar tane sai yaji tamkar an hanashi ya kasa. Gashi ginin da yasa ana mata sai nisa yake yi. An kusa kammala shi abunka da masu nera, Kwana akeyi ana aikin gina shi… Wayar sa yar karama ya janyo a drawer k’irar torchlight, Haka kawai ya tsinci kansa da kiran kanwar kakan sa, Gwaggo Ta fada (Haj Hajara Ibrahim).. Kiran ta yayi.. Sun jima suna magana kafin ya katse kiran yana mai dafe da kansa. Ita ba acikin masarautar take ba, Tana cikin gari gidan ta daban.

 

°°°°°°°     °°°°°°°°

 

Cikin kwanaki kalilan mahaifiyar Shaheedah ta kammala tanadar mata da duk abinda zata tafi dashi, daman tun tuni suka fara aiwatar da wasu abubuwan. Ganin ta gama samun komai yasa ta fara shirin dawowa Basannabas, taji gaba daya ba zata iya yin sati daya da tace ba. Gashi daman taji labarin dawowar Salman. Haka ta biyo jirgi ta dawo, bata bi ta kan sarautar da aka yiwa Abdulqadeer ba burin ta kawai ya zata raba wannan auran na Dije da Salman dan shine kawai tashin hankalinta.

 

Jakadiya tasa aka kirawo mata wato Zainabu Abu, ita kadai ce Jakadiya a cikin Basannabas, sauran guda biyun duk ba’a neman su an jinginar da su basu da wani amfani sakamakon duk tafi su iya kai gulma da hada gwarama tsakanin duk wanda tasan yana neman bayan d’aya. Tsaye ta tarar da ita sai zagaye take a tsakiyar parlorn ta, cikin sauri ta kai guiwarta kasa tana gaisheta cike da kaskantar da kai.

 

“Sannu da dawowa farin cikin sarki Salman, takawarki lafiya Gimbiyar Gimbiyoyi, kowa ya yi kewarki a cikin masarautar nan, sannu da dawowa uwar daki na.”

 

Shaheedah ta lumshe ido tare da dauke kai daga kallon Jakadiyar tana cewa.

 

“So nake kije kiyi min iso wajan mai martaba yanzu.”

 

Jakadiya ta yi jimmm! Saboda a yanzu babu ta yadda zata iya zuwa gurin Salman, kafin ya shiga cikin daki ya shaida mata baya son ganin kowa yau ya gaji yana son ya huta, yace komai ake da bukata a sanarwa Waziri tunda yana cikin fadar shi kam a barshi.

 

“Baki ji abin da nace bane Jakadiya?”

 

Sai ta daburce ta rasa yadda zata yi mata bayani saboda tasan Shaheedah idan ta kwallafa rai akan son ganin Salman, to da kamar wuya taki ganinsa, dan ko da bala’i ne sai sun hadu. Baki na rawa tace mata.

 

“Ranki ya dade mai martaba yace dani karna shiga inda yake, yace koma menene a je a sanarwa Waziri.”

 

“Mtwwww zan cen banza zancen wofi, to ni ba waziri nake son gani ba, shi Salman din shi zan gani bayan ya gama fito da abin da yake boyewa? Meye na cewa babu wanda zai gani saboda rainin hankali.”

 

Ita dai Jakadiya ta kasa magana, ran Shaheedah ya kuma baci tace.

 

“Ki tashi ki bani guri, tunda ke baki san yadda zaki yi naje gurin sa ba.”

 

Jakadiya ta bar sashen tana ta bata hakuri. Aikuwa Shaheedah ta kira mahaifiyar ta cikin tashin hankali ta sanar da ita cewa ta kasa haduwa da Salman yace baya bukatar ganin kowa. Ta shiga kwantar mata da hankali tare da shaida mata cewa ta bari za ta yi wani aiki a kan lamarin. Ai kuwa kafin wani lokaci sai gashi sarki Salman ya kirawo Shaheedah a waya yana shaida mata ya dawo amman zai huta ne zuwa wani dan lokaci, yanayin da taji muryar shi ne yasa taji zata hakura da zuwa inda yake har sai ya huta zata ji zai ma fi gane abin da zata sanar dashi. Ta koma wani daki inda ta ajiye kayayyakin da ta zo dasu, ta dauki wani abu a cikin wata yar tukunya, ta zuba a borner, aikuwa dakin ya dauki hayaki mai kauri, ita kam ko a jikinta. Alamun warin baya damunta sam-sam.

 

Misalin karfe uku na rana ina kwance a kan gado ina bacci cike da jin dadi, kawai naji kamar ana tashi na, na yi juyi kafin na bude ido a hankali. Babu kowa hakan yasa na kuma gyara kwanciya ta naci gaba da yin bacci na harda murmushi saboda tsabar dadi da ya yi min. Sake tashi na naji anyi wannan karan amsawa nayi.

 

“Uhmmm….”

 

Abin mamaki ba a dena tashi na ba sai da na tashi da sauri ina buge hannun da naji yana tashi na akan kafada, a fusace nace.

 

“Wai meye ne?”

 

Na bude ido fuskata da alamun bacin rai, abin da na gani shine ya sani sakin wata gigitacciyar kara tare da sakkowa daga kan gadon na fito da gudu sakamakon wata irin halitta da na gani a kusa da fuskata. Bakikkirin ne gashi d’an guntu, ma’ana wada ne, hakoransa zako-zako, idanuwa jajur kamar wanda aka zubawa barkono. Hadimai na sai taro ni suke yi ina turo su ina faman ihu kamar wata zararriya, koda yake zarewar nayi tunda naga halittar da ban taba gani ba a rayuwa ta. Ganin ina shirin fita daga cikin sashe na yasa duka suka rike ni da karfi suna tambaya ta abin da yake faruwa.

 

“Innalillahi wa’ina ilaihir rajiun, yana daki na wallahi aljani ne. Na ganshi da ido na.”

 

“Subahanallahi ranki ya dade Kodai sharrin mafarki ne? Amman duk muna parlor bamu ga wani abu da ya shigo ba.”

 

“Daman nasan haka zaku ce, na tambaye ku kuna jin wari kunce a’a, a karshe a gabana kuka sake gyara jeran aka goge ko’ina. Still ban dena jin warin nan ba kamar na mutuwa. Yau gashi ina bacci an je an tashe ni naga abin da na gani kunce min babu komai mai koke tunani toh? Zan yi karya ne ko zan yiwa wani sharri?”

 

Duk sai suka yi shiru kansu a kasa, sai da daya daga cikin su tace.

 

“Ranki ya dade kiyi hakuri ki koma ciki kafin mutane su ji a fara surutu. Zamu dudduba mu gani ko meye zamu fito dashi.”

 

Naja gwauron numfashi tare da saukewa a hankali, ta ya zasu gane yadda nake ji a cikin gidan nan? Koda yake kila dan na kasa kwantar da hankali na ne shi yasa bana jin dadi har nake ganin wadannan abubuwan. Da kyar na iya daga kafa na koma ciki amman sai na zauna a parlor, suka shiga suna ta dube-dube ko zasu ga wannan abun da na gani amman babu komai. Na dinga girgiza kai cike da takaici, kamar na ce su nemo min lambar Salman dan ji nake tamkar na zazzage shi, amman sai naji nauyin haka, ace kamar ni bani da lambar shi sai na fito na samu? Kuma idan ya dauka me zance dashi bayan ko muryarshi bana son ji….?!

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement   28….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍    …

KIBIYAR AJALI 29

Advertisement   *29….*      _*KIBIYAR AJALI…..!_* _(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_                  🏹🥰😍   Advertisements…