Advertisement
*ZAFAFA BIYAR (2021) NA KUDI NE !(PAID STORIES) KAMAR YADDA KUKA SANI, LITTATTAFAN NA ZUWA MUKU NE GUDA BIYAR CHAS. DUKA BIYAR DIN AKAN FARASHI MAI RAHUSA NERA DARI BAKWAI (700 NAIRA ONLY). *
*KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR. DAN ALLAH KI SIYA KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUKI YAR’UWA, AKWAI KARUWA SOSAI ACIKIN BOOKS DINNAN. MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.. DOMIN MALLAKAR NAKI BIYAR DIN, KI TUNTUBE MU A PAYMENT DETAILS DINMU DAKE ‘KASA*
*30….*
Advertisements
_*KIBIYAR AJALI…..!_*
_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_
🏹🥰😍
_*MASARAUTAR ‘BULLO_*
👑
Alokacin baya. Masarautar ‘Bullo ta kafu ne lokacin da yan yankin wani gari da ake kira ‘Margu’ suke kai wa yankin yamma hari. Wanda idan suka tashi bullowa ta gabas suke bullo musu su far musu. A duk sanda maharan suka zo, Yan yankin suna tafiya a guje zuwa garin Basannabas dan su taimaka musu da mayaka. ‘Sun ‘bullo ta gabas..’ Shine kalmar da yan yankin yamman ke fada a kodaya yaushe. Ma’ana maharan da suke karkashe su suna b’ullowa ta gabas. Al’ummar yankin yamma da taimakon Basannabas suka kewaye kansu, yadda mahara ba za su shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ginuwar garin Bullo, kuma wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen. Yankin ya tashi daga yan yankin yamma zuwa garin ‘Bullo’. Garin Basannabas da garin ‘Bullo sun zama aminan juna, Duk kuwa dai da garin Basannabas shi ya raini garin Bullo. Akwai aminta sosai tsakanin su tun zamani shekaru aru aru na baya har ya zuwa sanda garin ya tumbatsa ya tsaya da k’afar sa, Sai ya zamto akwai masarauta a karkashin ta. Wanda kaf nijeriya bayan masarautar Basannabas, To masarautar Bullo itace ta biyu a tsarin mulkin gargajiya.
A tarihin sarautar ’Bullo dai ance marigayi sarki Lukaro ne ya fara mulkarta bayan ya samu nasarar mamaye garin ‘Bullo, Sai kuma ya himmatu wajen samar da tsarin sarauta mai karfi domin tabbatar da ikon sa. Don haka ne ya samar da tsari mai kyau wanda masarautar ta ginu har ya zamto idan ka cire masarautar Basannabas, Sauran masarautu na kwaiwayar ta. Toh bayan sarki Lukaru da shekaru masu tarin yawa, Sai sarauta ta koma hannun tsatson sa, Wato jikokin ‘yayan’ ‘yayan sune ke karbar karagar mulki. Har dai sarauta ta dawo kan Sarki Ibrahim Hashimu. Kuma duk sarakunan dake hawa karagar mulkin ‘Bullo ko wannen su sai zumunci tsakanin sa ya sake kulluwa mai karfi da masarautar Basannabas. Akwai aminta sosai a tsakanin su, Kusan idan aka zurfafa bincike ma sun hada yan uwantaka. Toh bayan hawan marigayi sarki Hashimu Idrisu kafin rasuwar sa aminin marigayi sarki Salmanu ne mahaifin sarki marigayi sarki Aliyu. Kafin rasuwar su dai. Sarki Hashimu ya dauki sarki Aliyu tamkar dan da ya haifa. Saboda aminan juna ne shi da marigayi sarki Salmanu. Ance wani lokacin har canzan zaman fada suke yi domin su gano ta yadda zasu warware matsalolin al’ummar karkashin su. Hakan ya Kara dankon zumunta sosai tsakanin su, Har zumuntar ta taso akan ‘yayan su wato sarki Aliyu Salmanu da sarki Ibrahim Hashimu. Sun taso sosai cikin karfin zumunci tun yarinta har manyan takar su. Toh Bayan rasuwar mahaifan su sai ya zamto sun sake shakuwa, Sun kasance suna baiwa junan su shawarwari gwanin sha’awa. Hakan yasanya lokacin da ruguntsumi ya tashi akai kokarin hana sarki Aliyu sarautar Basannabas. Sai shi sarki Ibrahim Hashimu ne yatsaya tsayin daka wajen ganin sarki Aliyu ya hau karagar mulki, Dake sarki Ibrahim Hashimu shi ya dade da yin aure bai yi zurfi a karatu ba. Hakan yasa yayan sa na farko duk manya ne. Yarsa ta farko itace matar shugaban kasar lokacin. Sarki Ibrahim Hashimu ya tsayawa sarki Aliyu ya hau sarauta saboda amintar su da kuma wani abu daya boye a zuciar sa, Bai bayyana hakan ba sai bayan sarki Aliyu yahau kujerar mulki. Har ya samu albarkar haihuwar Salmanu alokacin da yazo yiwa sarki Aliyu murnar samun karuwar da yayi, Masana sun bayyana cewa a ranar sarki Ibrahim ya bayyanawa sarki Aliyu abinda ke cikin zuciar sa. Amma sarki Aliyu baiso hakan ba saboda yasan sarki Ibrahim yayi hakanne saboda ragamar mulkin Basannabas ya koma hannun masarautar Bullo. Ashe yar cikin sa ta karshe wadda aka haifeta bayan an haifi Salmanu da shekara d’aya da rabi ita yake son ya hada auren su. Babu yadda sarki Aliyu ya iya a lokacin. Ya dubi tsayuwar da yai masa akan sa, Halacci d’aya zai masa ya hada ‘yayan nasu aure idan rai yake. Hakan kuwa akayi karshen wasiyyar sarki Aliyu shine Salmanu ya auri yar sarki Ibrahim ko bayan ransa, Koda kuwa hakan zai janyo matsala ga karagar mulkin Basannabas. Bayan rasuwar sa ba jimawa aka dakko Salmanu daga kasa mai tsarki inda yake karatun sa a jami’ar King Saud university (Saudi Arabia) inda ya k’arashe matakin digiri na biyu a fannin Islamic law & Shariah. Anan aka nad’a sarki Salmanu Aliyu Salmanu a karagar mulkin Basannabas , Husuma da tarzoma hade da tsantsar makirci da hassada Kai harda tuggu babu wanda ba’ai kalar sa ba, Don hana Salman karbar mulkin Basannabas. Duk wani bangare na masarautar sun soke hakan, Amma dake Allah qadirun ne ala manyasha’u sai yai fatali da duk abubuwan da suke yi yasa Salman shine magajin mahaifin sa wato marigayi sarki Aliyu Salmanu.
Advertisements
Girgiza kai nayi lokacin da na ji bangaren masarautar ‘Bullo, Ashe auren had’i ne ko ince auren dole ne tsakanin SAS da Gimbiya Shaheeda bana nagani inaso ba ne? Tabe baki nayi. Kunnuwana suka jiyo min muryar Gwaggo Hajara na bani labarin ranar da aka dora sarki Salman Aliyu Salmanu (SAS/junior) akan mulki wato miji na a yanzu.
*RANAR NAD’IN SABON SARKI MAI MARTABA SARKI SALMAN ALIYU SALMANU: (SAS)*
Da dakan kade-kaden gargajiya da algaita aka rako sabon Sarkin Basannabas, Salman Aliyu Salmanu (SAS) zuwa fada, kamar yadda ake rako mafiya yawan Sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya.
Fadawa ne da sauran ‘yan fadarsa ke biye da shi inda suke sanya masa lema domin kare shi daga zafin rana. A shekaru fiye da hamsin din da ta shafe ba a taba samun matashin sabon sarki mai cikar ido da zatin halitta da haiba irin na sarkin yanzu Salman ba, Sabon sarki mai cike da sabon takun kasaitar karagar mulki, Gaba d’aya kowa ya sanya kansa a kasa, Babu wanda ya cire ido ya kalli sarki Salman saboda cikar kwarjinin sa ma ba zai taba sa ku had’a idanu ba. A yadda yan uwa da al’ummar gari ke fada, Babu wanda yasan ya kalar kwayar idanun Sarki Salman take koda kuwa matarsa Shaheedah, Tun yana kankanin sa baya shiga cikin yara suyi wasa, Yana da wata irin madaukakiyar ‘kasaita wadda tafi girman bayyana miki ita. Yakan tsame kansa a duk harkar da zata sada shi da jama’a, Ko lokacin da yayi karatun sa a waje, Kullum idanun sa na saqale da gilashi baki. Baya taba cire idanu ya kalli mutane, Haka zatin halittar sa take, Indai kasaita ce to akan Sarki Salman Aliyu Salman ta ‘kare.
Cincirindon al’umma kuwa sunyiwa alkalami yawan da bazasu kirgu ba, Ko’ina bil adama ne sai hada-hada ake, Duk wani mai mukami a nijeriya ya halacci wannan babban taron nadin sarautar. Gabaki dayan wannan shekaru, Masarautar Basannabas na daga cikin wadanda suke taka rawar gani wajen tabbatar da dorewar al’amura a kasar nan, Duk da cewar sarakunan gargajiya ba su da wani cikakken iko sosai a kundin tsarin mulkin k’asar nan, amma babu wani dan siyasa da zai nemi mukami ba tare da neman albarkarsu ba. Kafin samun ‘yancin kai, sarakuna kan yi mulki da cikakken iko a Arewacin Najeriya. Domin ko bayan zuwan turawan Burtaniya, sarakunan sun ci gaba da kasancewa masu fada a ji a harkokin mulki.
Walima sosai aka yi, amarya gimbiya Shaheeda ta tare a cikin gidan ta dake sashen sarki Salman. Zaure d’aya ne ya raba su da sashen mahaifiyar sa wato sashen ‘Mai babban daki’ (Gimbiya/Haj Sa’adatu) daga sashen ta kuma gaba kadan sai na kishiyoyin ta wasu sashen su Haj Jaleelah, gaba d’aya matan marigayi sarki Aliyu suna cikin masarautar basu canza waje ba. Kowacce tana wajen ta, sabon sarki Salman yace suyi zaman su kada kowa ya tashi. Tun shekaru aru-aru gaba d’ayan su tsatson Jirgau Basannabas a waje d’aya muke. Sai dai Idan sabon sarki ya hau zamani ya canza sai a sake gine gine a rurrushe wasu wajajen a sake kawata masarautar (renovating).
Koda zai aure ki anyi mamaki dan bai sanar da kowa ba sai ranar da za’a daura muku aure. Kowa ya yi mamakin wannan al’amari, wanda nafi tunanin ya yi hakan ne saboda yan bakin ciki ko a kawo masa cikas wajan auranki. Kiyi hakuri Khadija ki zauna da Salman kodan ya samu farin ciki a rayuwarsa, karki ce zaki guje shi duk kuwa da kema kina cikin matsananciyar taimako. Kiyi tunani Khadija idan Salman ya mutu baya magana da mahaifiyar sa, bashi da wata walwala sai yadda aka yi dashi. Salman yana sonki duk da cewar be fito fili ya bayyanawa kowa sirrin zuciyar sa ba
Naja wani dogon numfashi ina tuno rana ta farko dana fara yin tozali da sarki Salman, Fuskar sa sanye cikin rawani. Kwantaccen gashin girar sa ya leko ta saman bakin gilashin dake zagaye da idanuwan sa. A hankali na furzar da iskar baki na ina mai furta,
“Salman Aliyu Salman… (SAS)”
Na furta sunan nashi a zahiri amman ba yadda gwaggo zata iya jiyowa ba. Lokacin ne Adda Maryama ta dawo tare da yaran ta da ta biya school ta dakko su.
“Gimbiya kin ganni sai yanzu ko?”
Nace,
“Ai kuwa muna ta jiranki ba.”
“Afuwan Gimbiya, amman ai nasan kila gwaggo ta taya ki hirar.”
Dariya kawai na yi bance komai ba, ta shiga daki nima na bi bayan ta dan nafi sakewa tare da ita. Haka na rayu a gidan gwaggo ta Fada, babu mai nema na daga can gidan kawu daddy, Dama shi Kawu daddy sanda akai daurin aure na da kwanaki biyu ya tafi Riyadh yin wani kasuwanci. Can masarautar ma ba me cigiya ta bare na sanya ran akwai wanda ya damu dani. Sai da na dauki kusan sati biyu ana ta bani magani da hayaki da sauran abubuwan kariya, na fara jin dadi har ma ban so naji ance zan koma masarautar Basannabas saboda rikicinta.
Ina zaune Adda Maryama tana min oiling a kai na naji tayi dariya kasa-kasa tace.
“Gimbiyar mu anya kina son shi kuwa?”
Da mamaki na ce da ita.
“Waye kuma?”
Ta kuma murmusawa.
“Ina nufin mai martaba.”
Naja numfashi kasan cewar na yarda da ita yasa nace mata.
“Ba wai haka bane, kawai naga matsayi na da nashi ba d’aya bane ba. Kuma sh… Shima fa ba so na yake yi ba.”
“Kai! Wannan duk hasashe ne ranki ya dade. Shi ne fa ya auro ki, kuma auran ma dan kar a kawo masa suka a hana shi.”
“Uhmm Adda Maryama k….”
“Ranki ya dade kiyi hakuri, koma me yake cikin zuciyarki akan mai martaba dan Allah dan annabi ki taimaka kece a yanzu mafi kusanci dashi, wacce zamu taimakawa ta dawo dashi cikin hayyacin sa. Gimbiya Shaheedah babu yadda bamu yi da ita ba akan mu’amalar mai martaba da mahaifiyar shi, wallahi tasa kafa tayi fatali da zancen shi yasa duk muka kyaleta tunda babu yadda zamu yi.”
Jikina ya yi matukar yin sanyi, amman na kasa yadda cewa ba wai haka halinsa yake ba na izza da wulakanci tunda gashi ya yi min, baya kula ni tun da aka kai ni masarautar….
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma’ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
GIPHY App Key not set. Please check settings