KIBIYAR AJALI 31-32

Advertisement

 _*KIBIYAR AJALI…..!!!!*_

_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_

           🏹👑👩‍❤️‍👨💝

*MALLAKAR:- NANA HAFSAT 🧕🏼*

   *(MISS XOXO)*

Advertisements

*©️®️ZAFAFA 5: 2021*

     (PAID NOVELS)

_Wattpad:missxoxo00_

 *31-32*

*KARSHEN BOOK 1*

(EPI finale (BOOK 1)

Advertisements

*GIDAN GWAGGO TA FADA*

“Mun riga munyi magana da gwaggo akan yadda za’a dinga kai masa wannan tofin, saboda tana da yakinin duk wanda take kaiwa ba’a bashi. Zaki shirya insha Allahu da daddare zamu dinga zuwa tunda ke muharramar shi ce zaki iya yi masa abin da babu wanda zai iya yi.” 

Cikin sauri nace.

“Ah toh ai nima ba zan wuce ka’ida ba kinji ki da wata magana.”

“Haba Gimbiya sai kace ba mace ba, kin san mawaki yana cewa dukan namiji bawan mace ne. Yanzu wani opportunity muka samu da zaki canza mai martaba ya koma cikakken sarki ba kamar yadda ake juya shi ba kamar wani waina.”

Dariya kawai na yi saboda ni kadai nasan matsayin sa a zuciya ta, kuma ba zai canza ba dan na san da manufa mummuna a zuciyar shi. Muka ci gaba da hirar mu cike da nishad’i har ta kammala gyara min kai na tayi parking d’in gashin  a tsakiyar kai na. Wanka na shiga nayi wanda shima na magani ne da turaruka masu kama jiki.

Bayan na fito na shafa mai tare da gyara fuska ta daidai misali. 

Lokacin da Adda Maryama ta tashi tunani na shiga yi ina mai jujjuya tofin rubutun dake hannu na, Kalaman ta na karshe sune suka yi ta min reto a kunne na,

“Kota halin ‘kaka ki bashi ya sha tofin nan, Idan yaki sha sai kiyi amfani da kissar mu ta mata ki bashi, Ba cewa nai kokawa ba, No! Ko ‘yar kyakkyawar runguma kika bashi sai ki hade bakin ki da na shi ki dura masa, Cikin yanga har ya shanye…”

Na murza idanu na ina tunanin ta yadda zanyi hakan, Na tsane shi fa ya tsane ni, Taya har zan hade bakunan mu waje d’aya? Kayan data zabo min wai su zan sa na kalla. Wani lace ne gaban rigar a bude yake. Wai laffaya zan dora akai, Idan naje wajen sa na cire. Na sake tuno yadda ta shiga nanata min cewa,

“Mace karuwa ce a gidan ta Khadija.. Ballanta na ke me kishiya, Sai da ‘yan dabaru. Kuma kinga yanzu so muke mu fara neman yadda zai warke daga mugun sihirin da aka kulla shi da shi… Khadija ke kadai ce KIBIYAR warwarar matsalolin masarautar Basannabas.”

Mikewa nayi jiki ba kwari na shiga bandaki, Na yo wanka hade da alwala, Addu’oin da tofin rubutun da Gwaggo Ta fada ke karbomin sun sa jinin ya rage zuwa da yawa, Yanzun na cigaba da sallah ta saboda jinin ciwo ne bana haila ba. 

Shiryawa nai cikin lace din, Adda ta shigo da wasu turaruka ta shashshafamin su a jiki na, Harda na gashi, Kayana sai kamshin turaren kabbasa suke. Ta nad’a min laffaya, Don har yanzu ban gama iya nadawa ba. Riko hannu na tayi muka fito daga cikin da’ki, Gwaggo ta fada na kan kujera tana jan carbi,

 “Gwaggo! Barka da yamma… “

 

 “Barkan mu Gimbiya.. Har an fito?”

Kai na daga sama ina mai wasa da zoben hannu na, Adda ta tsaya daga tsaye tana rufe murfin robar da tofin ke ciki tace da Gwaggo,

 “Kin sanar masa da zuwan mu ko Gwaggo…?”

 “Na sanar masa da zuwan ki dai, Bance har da ita zakuje ba, Saboda kin san yadda gidan nan namu yake. An sake qulla wani abun domin yadda naji muryar sama a waya kamar baya hayyacin sa… “

 “Babu damuwa..  Zan bawa zagi cin hanci shi da jakadiya. Da yardar Allah da mun gama zamu dawo don kar ma wani ya ganmu ta kofar arewa zamu fito mu dawo gida..”

 “To shikenan… Sai kun dawo! Allah yabada sa’a da nasara..”

 “Aaamin! “

Na amsa a tsorace, Adda ta kamo ni muka fita, Driver yaja mu sai cikin masarauta. 

 *MASARAUTAR BASANNABAS*

Tun daga zaure na farko, Adda ta mikomin wasu alawoyi masu futinannun kamshi a cikin ledar su, Ta kanne min ido tana daria k’asa kasa tace,

“Harkar sai da irin su Gimbiya..”

Nidai nai shiru kawai ina kambama gayu da wayewa irin nata, Tagama fahimtar rayuwa ciki da wajen ta, Qaddara ce kawai ta rabo ta daga gidan mijin ta, Amma na san mijin ta yaji dad’in zama da ita. Kuma idan kuna tare tabbas kai ma zaka kara haske, Domin ‘yan kwanakin da nayi da ita, Na gaggane abubuwa da dama, dan Kullum dora ni take akan sabon network..

Ai kuwa muna zuwa muka tarar da Jakadiya, Adda Maryama ta yi saurin janyo ta gefe suka yi magana ta zaro kudi masu yawa ta bata. Nan da nan kuwa tai min iso Allah ciki ita kuma Adda ta samu guri ta zauna jira ba. Tunda na doshi cikin bedroom d’in nake jin bugun zuciya, baki na dauke da sallama amman shiru, har na yanke shawarar komawa sai kuma na yi tunanin ko ba zai iya amsawa ba shi yasa naji shiru, na bude kofar na shiga idanuwa na suna karakaina wajan neman inda zan hango shi.

Kwance na gano wani balarabe a kan makeken gado, na kuma bude ido still balaraben nan nake gani. Na tafi sannu a hankali har na karasa inda yake a kwance idanunsa a lumshe, gaba na ya yi wani mummunar bugawa saboda yadda halittar bawan Allahn nan ta buge ni.

Kardai ace wannan shine sarki Salman, abin nufi dai wanda ake cewa miji na ne? TubarkAllah. Kamar ana jana zuwa gareshi haka na nufi in da yake baki na bude saboda tsantsar mamaki.

Ji nai kawai an riko min hannu na, da sauri na juya dan ganin waye saboda yadda naji hannun zafi rau kamar wuta, babu kowa sai nabi hannun da kallo. Salman ne idanunsa a kulle bakin sa yana motsi a hankali alamar magana.

“Waziri ka kuma samin ruwa a jiki na zafi nake ji, help me waziri ina jin kamar ana dafa ni kasa min towel please.”

Nan da nan sai na rude gabaki d’aya na rasa ya zanyi na taimaka masa, gashi ya rike ni gam har cikin jikina ina jin rikon. Nayi dabara na cire hannunsa daga nawa na fara dube-dube, kofofin da na gani naje na dinga budewa ina neman bathroom har na gani, na shiga tare da dakko wata roba mai dan fadi na zuba ruwan sanyi, towel na janyo guda daya daga cikin jerin da aka yi musu. Cikin sauri na je kusa dashi tare da warware lafayar jikina na ajiye gefe, bargon da aka lulluba mishi na yaye gabaki d’aya.

Ya Subahanallahi ashe babu riga a jikinsa, gabaki d’aya surar jikin shi ta bayyana. Wani irin abu yarrrr ya ziyarci ilahirin jiki na tun daga kan babban yatsana har tsakiyar kai na. Na bishi da kallo ina mamakin yanayin halittar sa. Ashe haka yake da masifar kyau tamkar shi ya yi kansa? Kodai mahaifiyar sa balarabiya ce? Domin ya yi kama da su a komai da komai. Shi kuma jin iska tana ratsa shi kuma ba irin ta yake da bukatar ji ba yasa shi yin yawo da hannayensa yana neman bargo kawai ya kamo kirjina, hakan da na gani ne yasa ni kamo hannun nasa a daidai lokacin ya bude ido a hankali yana furta.

“Please help me….Can I hold you once??”

Ya ruda ni gaba daya na kasa gane wane irin taimako yake nema, gashi duk da bashi da lafiya yana da d’an karfi ganin da nayi yana ta jana zuwa jikin shi. Ashe shi bargo yake son janyowa ni kuma sai faman kwatar jikina nake yi na kasa. Cikin murya mai cike da tsoro na ce dashi.

“Wai me ye haka?”

Sai naga ya dan tsaya da son jana, ya yi shiru alamar yana nazari. Can kuma sai ya sake bude ido still daman hannaye na suna rike da nashi be saki ba.

Mukai ido hudu dashi, ma’ana yana kallo na ina kallon shi cikin wani irin yanayi mai wahalar fassarawa. A hankali ya fara bin jiki na da kallo, ganin haka yasa na fin cike na dama ina kare kirjina da shi dan naga yafi kallon gurin. Da yaga na yi haka ne sai ya langabar da kai hakan kuma yasa na kuma jin tausayin sa yace.

“Nagode kin ji?”

Maimakon na yi masa banza, sai na samu kai na da jinjina masa kai wato naji. Ya sake rike hannun na da yake rike dashi.

“Ki taimaka ki rufe min, sannan ki samo ruwa kisa min a jiki na. Kin san yadda nake ji ko?”

Ya furta ‘ko’ din kamar karamin yaro. Ba kuma samun kai na da jinjina kai, gaba daya tausayin sa nake ji ya mamaye min ilahirin jiki na. Nace masa.

“Toh saki na yi maka.”

“Nagode sosai.”

Ya fada cikin rauni, gabaki d’aya abinda yake yi irin na yara ne. Sai ya sakar min hannun ya kuma lumshe idanunsa, na sanya towel d’in cikin ruwa na d’an rage ruwan tare sa juyowa na dora masa a goshin. Ya ja wata doguwar ajiyar zuciya yana ta tsotsar lebansa wanda yake kamar yana sanya jan baki pink.

Hawaye naga yana yi ta gefen idonsa abin da ya yi matukar bani mamaki, gaskiya bawan Allahn nan yana jin jiki, dole gwaggo ta Fada tace sai sun tashi tsaye tunda shi ba zai nemi kariyar da kanshi ba. Yana yi ina goge masa na kasa bashi hakuri saboda ban san dalilin zubar su ba, har na gama sa masa towel d’in, na dakko jarkar tofin da nazo da ita. Shi kuma jin shiru na tsaya yasa shi bude ido, yana ganin rubutu ya kawar da kai yana fadin.

“Ba zan sha ba, na cewa waziri a dena kawo min wadannan abubuwan wari suke yi.”

Wannan karon samun kai na nayi da yin sanyin murya, tare da lallashi ina gaya masa ba irin wanda ya saba sha bane. Amma ya dage shi ba zai sha ba, wai duk lokacin da aka bashi ji yake kamar zai mutu dan haka shi ba zai sha ba. Na tuna maganar Adda Maryama,

_“Dan Allah Gimbiya duk yadda zaki ki samu yasha ruwan tofin nan, idan ba haka ba muna ji muna gani zasu samu nasarar kashe shi.”_

Sai na samu karfin gwiwa, uwa uba tausayin shi da nake ji a yanzu, sai na dakko alawa d’aya daga cikin wanda Adda Maryama ta bani da zamu shigo. Barewa nai nasa a baki na ina tunanin ta yadda zan iya bashi, idan har na iya to sai na yi dabara na bashi ruwan. Haka na dinga juyayin ta ina zan fara, daga karshe dai na sunkuya gurin shi tare da kamo fuskarsa ina kallo, kirjina yana bugawa shi kuma ya bude ido, kawai na tafi da borin kunya na sanya baki na a cikin nashi tare da zura masa alawar.

Me zai faru? Na dago na bashi maganin ko? A’a sai lamarin ya citura dan sarki Salman rike ni ya yi gam tare da fara kissing dina cikin fitar hayyaci. Na dinga zaro ido ina kiftawa babu mataimaki sai Allah na kai kaina. Sai na fara,

“Uhmm! Uhmmmuhmmm..! Uhmmm… Uhmmm..!!”

Sai naji ya fara kokarin rabani da kaya na, hakan yasa ni nayi kukan kura tare da fincike jikina nai gefe ina sauke uban numfashi. Shi kuma ya rike kai yana furta.

“Baby I cant… I… I wont…”

Jikina na rawa na sauka daga kan gadon, amman sai nai sauri wajan amfani da wannan damar kafin ya dawo cikin hayyacinsa na zuba ruwan tofin a kofi na zauna gefen shi tare da dago masa da kai nace.

“To kasha wannan ruwan idan yaso sai na… Na.. Baka abin da kake so yanzu.”

Ya bude tare da watsa su cikin nawa, kirjina ya kuma bugawa ganin yadda suka canza sukai wani iri alamar yana cikin wani yanayi na bukata. Da sauri na kai masa cup d’in saitin bakin sa amman bawan Allahn nan ya kawar da kai. A rai na nace. ‘Na shiga uku Adda Maryama ta bani bad shawara’ na daure na kuma kai masa ko zai sha amman yaki.

“Shikenan toh bani sweet d’in.”

Babu musu ya turo ta daga cikin bakin sa nasa hannu na dauke ta tare da ajiyewa a bedside, na kurbi ruwan tare da nufar bakin sa ba musu ya bude na dinga zuba masa a hankali. Uhmmm a haka na dinga bashi yana shi har sai da ya shanye ba tare da mun ankara ba.

“Na gama zan tafi.”

“Please.. No! kiss me dear, with passion …softly soft… kiss me with your desire.. kiss me with a little bite…” 

“What….?!!!”

Furucin ya fito daga baki na, sannan a lokaci guda na mike ya yi saurin kamo……………

_ ASSALAMU ALAIKUM MASU KARATU, MASOYA ZAFAFA.. DUKA_DUKA ANAN NI NANA HAFSATU ZAN TSAIDA ALKALAMI NA, SAI HADUWA TA GABA IDAN MAI DUKA YA KAI MU… ALLAH YASA MU SHIGA WATAN RAMADHAN A SA’A. ALLAH YASA MUNA CIKIN YANTATTUN BAYI. RABBI YA YAFE MANA KURA-KUREN MU… MUNA NEMAN YAFIYAR DUK WANDA MUKA BATAWA, ALLAH YA YAFE MU BAKI DAYA. IN SHAA ALLAH! IDAN MUNA DA RAI DA KOSHIN LPY, BAYAN SALLAH DA YARDAR ALLAH ZAMU DORA DAGA INDA MUKA TSAYA… A CIKIN LITTAFIN KIBIYAR AJALI.. NAGODE SOSAI, A AZUMCI WATAN RAMADHAN LAPIA💋💋SON SO!!!_

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like