KIBIYAR AJALI 8-9

Advertisement

 I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

PG: 8&9

BOOK 2. 

BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻

____*Sai* da ya shiga ya zauna sannan dogaran sa suke rufe shi sauran yan zaman fada suka fara shiga, Kowanne sai an masa kirari, Tukun sannan ya zube ya kwashi gaisuwa wajen Sarki.. 

Advertisements

Shi dai Salman yana zaune ne kawai, Gangar jikin sace anan, Amman gaba d’aya zuciar sa na ga tunanin acting din Khadija.. 

 “Unbelievable…”

Ya furta batare da yasan ya fada ba. 

“Allah ya k’arawa sarki lapia, Magana kayi..?”

Shiru yai ya cigabada sauraran bayanin shamaki. Gaba d’aya zaman fadar ranar cikin walwala yayi ta, Tacikin rawani yake murmusawa a duk lokacin da ya tuno kalaman Khadijaa…

Bayan an tashi daga fada manyan yan majalisar sarki suka nemi ganin sarki, Ya basu dama bayan ya tashi daga inda yake ya koma parlorn sirri. Daga shi sai waziri daya musu iso..

Advertisements

Har cikin babban parlorn sirrin sa dake cikin fadar sa suka shiga bayan an musu iso, Salman na daga kishingide kansa a sama. Da alamun har yanzu ya lula duniyar tunanin Khadijaa.

 “Ranka ya dad’e, Allah ya kara wa sarki lapia, Ga su wambai, Galadima da Chiroma za’a yi magana da kai..” Cewar Waziri. 

Salmaan na daga kishingid’e ya mike zaune yana gyara zaman glasses d’in fuskar sa.

 “Gurin ka muka zo… Tunanin me kake yi haka?  ba haifa kayi ba balle ace hayaniyar yara ce ke chake maka kai…” wambai ya fada yana daria.

“Kaji wambai da wata magana, Mutumin da bai da kwan halittar haihuwa? Ta ina zai same su.” Galadima ya bashi amsa yana murmushi shima. 

“Me ake cewa namijin da baya haihuwa ne? Mace dai juya ake cewa ko? Namiji kuma sai dai ace masa baho.” Cewar chiroma dake gefe. 

Suka sheke da da dariya baki d’aya, Banda Salmaan da waziri, Waziri ya hade rai tamau yana muzurai, Cikin tsananin bacin rai ya dube su. 

 “Menene haka ne dan Allah? Wannan wane irin wulakanci ne da tsawagaran shirme? Ya zaku zo kan sarkin mu kuna wasu maganganu..? Da nasan shirme zaku zo kuyi da bazan yi muku iso bama.”

“Yo waziri banda abunka ai shigowa sashen sarki ko an mana iso ko ba’ai ba dole mu shigo.. Su waye suka dora sarkin akan kujera idan bamu ba? Karka kauce hanya yanzu ba sai anjima ba sai mu nemo sauran yan majalisa a sauya ka da wani.. Daman kai shisshiginka ya yi yawa a gurin yaron nan” Cewar galadima, Yana magana ne cikin izza. 

Waziri yai shiru ransa a mugun bace, sai dai bai kara cewa komai ba, Salman dai yana zaune yayi shiru kawai yana sauraron sa.

 “To kai Salman wajen ka muka zo, Kuma gaskia magana ba zata yiwu agaban waziri ba, dan besan ma maganar da muka zo yi ba..”

“Saboda me ba za’ayi agaba na ba dan ban san abin da zaku tattauna ba? Ban isa bane ko ban kai ba?..” Waziri ya tambayi chiroma cikin tsantsar mamaki.

“Baka isan ba..Kuma baka kai din ba, Saboda haka ka tashi ka bamu waje, kai ma bama shigowa idan kuna tare.”

“Babu inda zanje, Ku baku isa ku bani umarni ba wallahi.. Nan wajen gaba d’aya maganar mutum d’aya zanji kawai, wato Sarki Salman! Bayan shi babu mahalukin daya isa. Na taba hana ku shigowa idan muna tare dashi? Me zai sanya ni kebewa dashi kamar wani marar gaskiya?”

Su Galadima suka harzuka suka fara magana sama-sama, Sarki Salman ya cije leben sa na kasa yana d’aga musu hannu a hankali.

“Enough please! Waziri zaka iya tafiya, Kayi hak’uri.” Waziri ya zube a kasa yana d’aga hannuwa,

“Tuba nake ranka ya dad’e.. Amman me suke nufi da ina kebewa da kai? Kenan zargi na suke yi da yin wani abun? Wallahi ba zan cutar da kai ba ranka ya dade, kai amana ce a guri na, a rai na ma banji zan iya cutar da kai ba bare har na aikata. Amman Allah ya kara maka lafiya da kwarjini, Zan fita yanzu. A huta lapia.”

Ficewa yai bayan ya zabgawa su Galadima harara don yana da yakikin zuwa sukai su yi masa wani abun na tilas. Wani dogon tarihi suka fara dakkowa Salman, Wannan ya saki wani ya kama, Haka suka yi tayi. Duk Salman ya gaji sai lumshe idanu yake a hankali. Wambai ya kar’kare da,

 “Yanzu dai abunda mukeso kuma muka yanke shawara, Kamar yadda kaka da kakanni suka yi, Har hakan ya zama al’ada ya zama wajibi akan kowane sarki, Kaga kuwa akan ka ba za’a soke ba..” Chiroma ya cigaba daga inda wambai ya tsaya,

 “Bayan bula mana kasa da kayi a idanun mu ka auro bare, Wacce ba jinin sarauta ba, Bata cikin rakunun sahun masu mulki ko sarauta, Ka jajibo mana yar talakan talak marar usuli, Wanda kakan ta na goma bana tunanin yayi arziki. Amma saboda tsabar ka rainamu shine har sai za’ai daurin auren ka sanar mana.. Shin yaushe ka fara d’aukar Kan ka kai sarki ne? Nace yaushe.”

Salman dake gefe yai shiru kawai yana kallon gefe, Galadima yaja tsaki yana ture flower vase din dake gefen kujerar da yake, Wanda har sai da hakan ya zamto sanadiyar fashewar ta,

 “Ana magana kana shiru ko? Wannan dan iskan halin awajen uwar ka ka samu, Itace duk ta koya muku girman kai, Kuna jin Kan ku, Yo ai barewa batayi gudu danta yai rarrafe ba. Baban ka ma haka ya rakito mana mahaifiyar ka yar dogari, Me yafi wannan kaskanci? To ka bude kunnen ka dakyau kaji, Kodai ka karo auren mata biyu yan cikin dangin sarautar mu, Ko kuma ka sauka daga karagar mulki wanda ya dace ya hau… Ina fatan ka fahimci maganata?”

Salman yai shiru kawai yana binsu da kallo, Sai da Galadima ya sake maimaiatawa tukun sannan da k’yar ya cire idanun sa saqale da glass ya kalle su,

 “Yanzu bana jin dadi.. Kuma a gani na tara matan aure a gare ni bashi da wani amfani tunda ba haihuwa nake yi ba, idan har na tara su a haka na zalince su. Shaheedah taji ta gani tace zata zauna dani a haka, wannan ma akwai dalilin auran mu kuma….” 

Be karasa ba Galadima ya katse shi da sauri yana cewa. 

“Zancen banza kawai, toh yadda wadannan suka yadda zasu zauna da kai ba tare da sun haihu ba. Suma wadanda zaka kara aurowa zasu zauna me ye a ciki?” 

“Shikenan Amman zanyi shawara!”

 “Shawara da wa? Waziri ko? Hohoho yaro baisan wuta ba sai ya taka.. Lalle daga kai har wazirin kuna gab da yin murabus kuwa.. Kasan an ce sarkin yawa yafi sarkin karfi, Bama wannan ba yanzu ace wancen ginin da kasa aka narka dukiya sama da kasa daman na shegiyar amaryar da kayo ne? Dama bana Wambai bane? Shine gidan sa ke yoyo idan anyi ruwa? Ko abdulqadeer da zaiyo aure kwanan nan.. Tukun nama wa, Wanne munafikin kabawa kwangilar yin ginin? Har akai nisa ba wanda yakeda masaniya sai gab da gamawar sa? Toh zancen komawar matar ka ta biyu babu shi, Sai dai gimbiya Shaheedah ta koma, Ko wambai ko abdulqadeer yai aure ya zauna aciki…”

Chiroma ya karb’i zancen da, 

 “A zahirin gaskia dai Salman baka kyauta ba, Ya za’ai har ka aiwatar da aiki ba tare da masaniyar mu ba? Shin me ka dauki kanka? Sarki?..”

Wambai ya kece da dariya yana bubbuga hannun kujerar da yake kai, 

 “Wato kila yanda mutanen gari suke masa kirarin sarki shine yasa yafara jin kansa shi sarki ne ko? Har yake ganin masarautar nan tasa ce ya yanki fili yayi gini.. Dukkanin mu nan tsatson sarautar nanne, Don haka kowanne acikin mu yana da gadon wannan gidan daka gina.. Kowanne yanada ikon zama acikin sa..”

Salman yai shiru kawai yana jujjuya zoben azurfar hannun sa. 

“Ku tashi mu tafi, Duk abunda ya biyo baya ka kuka da kan ka..”

Ficewa su kai baki dayan su, Ransu a matuk’ar b’ace, Waziri ya shigo, Kallo d’aya yaiwa Salman yasan yana cikin tashin hankali. Kwantar masa da hankali ya shiga yi, Yana karfafa masa gwiwa. Sai daya tabbatar zuciar Salman ta d’anyi sanyi sannan yai masa sallama ya tafi.. Yana fita Salman ya mike ya shiga bandakin cikin parlorn yayo alwala ya fito, Zai tada sallah wayar sa tafara haske, Shaheedah ce ke kiran sa, Kashe wayar yai gaba d’aya. Ya tada iqama yafara sallar nafilar sa, zuciar sa na kara nutsuwa, Yai sujjada yana mai rokon Allah zabin alkhairi acikin rayuwar sa…

*GIMBIYA KHADIJAA*

Ina koma bangaren Ammi na zube a kujera ina haki, Ni kaina mamakin kai na nake, Lalle nayi kokari sosai, Na kuma ballowa kai na ruwa. Ammi na sama, Hakan ya bani daman kiran Addah Maryamah a waya na sanar mata komai, Ta yabamin hade da sake bani shawarwari, Tace kuma gatanan tafe. 

Ba jimawa kuwa tazo, Na rakata saman Ammi, Anan ta sanarwa Ammin kancewar zan koma sabon ginin da akai a sashen sarki Salman, Ba karamin dadi Ammi taji ba. Domin yadda fuskar ta ta kara fadada da murmushin farin ciki zaka gane taji dadin komawar da zanyi can. 

Addah Maryama ce da masu aikin su guda biyu suka nufi sabon shafin nawa don ganin yadda za’a kwaso tsofaffin kayana azuba acan. Suna zuwa suka tarar sama da kasan an zuba furnitures, Komai Italian royal ne, Saboda haka kayan sawa na kawai suka dauka suka jeramin acan, Aka yayyafa ruwan magani da turaren habbatussaudah da tazargade. Da sauran magunguna da malam ya harhada ciki harda na tsari aka rataye a kofar shigowa. 

Ta WhatsApp addah maryama taita turomin hotunan koina ina nunawa Ammi, Zuciata sai hasaso shaheedah take, Shin ko awani yanayi take yanzu? Oho. Kai bama ita kadai ba harda su gimbiya Jaleelah. Duk na gano bakin su d’aya, Amma kowannen su yanada wani boyayyen quduri a zuciar sa game da Salman da karagar mulkin basannabas.

Ranar gaba d’aya Addah maryama da masu aikin su a masarauta suka kwana, A sashe na, Ammi taimin adduar tarewa lapia hade da fatan alkhairi. Amma bata rakani sabon sashe na ba, Saboda gudun abinda zaije ya dawo dongane da Salman dinma anan yake. 

Tabbas nera tayi kuka agidan nan, Kaya wanda suka amsa sunan kayan gida su ne acikin sa. Kai harya dustbin k’irar Royal ne, Murmushi nai tunowa da nid’in ba tabbata zanyi aciki ba, Nan da lokaci kalilan da komai ya tabbata zan karb’i takardar saki na na kara gaba.. 

Munsha hira sosai da Addah maryama tana kara dorani akan network, Sai da muka raba dare muna hira tukun sannan bacci mai nauyi ya dauke mu..

 *GIMBIYA SHAHEEDAH!*

Sashenta ta shiga tana kuka, Dama akwai lapiar zagi, Haka taita lailayowa tana durawa hadimanta, Kayan babban parlorn ta kuwa haka taita farfasasu tana kuka, Tamkar idan tayi hakan magani zasuyi mata. 

Ranar dai mutum uku ta targada daga cikin hadimanta. Dak’yar ta iya janyo waya ta kira mahaifiyar ta ta sheda mata komai, Ta bata hak’uri da doriyar ta kwantar da hankalin ta, Khadija yasar ta za’ai a fitar da ita daga masarautar nan ko da rai ko babu. Sai a sannan Shaheeda ta danji sanyi sanyi a ranta,

 “Shikenan Hajjaju… Na hakura, Amman kamar yadda kikace wallahi ba zan bari su samu sukuni ba, Tunda ta shiga gonata sai na nuna mata ita kaskantacciya ce…. Ki sanarwa wannan banzan bokan aikin sa baici ba dan haka kaza ta ubansa…”

Tana gamawa ta katse kiran ta kuma jefar da wayar ji kake tartsssss.. Ta fashe. Tashi tai ta shige da’ki wani kullum magani ta dakko ta zuba a ruwan wankanta ta shjga wanka, Tanayi tana tsinewa Khadija albarka…

<><>••.   <><>••.   <><>••. 

   Komawata sabon sashe na yau sati d’aya kenan cif, Tunda na koma ban kara shiga sashen Salman ba, Saboda daga kofata idan na saka maganin yana ruskar sashen sa, Gashi karatun AlQur’an nake so nake na sauke hizb sittin. Shiysa kullum ina daki ban cika fita ba, Ko gayda Ammi sai bayan kwana bi biyu nake zuwa yanzu na dukufa sosai ina addu’oin neman kariya.. Ta window na ina kallon shige da ficen da shaheeda keyi kullum, Sai zarya take safe rana dare. Ta d’auka ina wajen sa. Ni abunma dariya yake bani. Ba ita kadai ba, Su wambai ma kusan kullum sai na jiyo hargagiyar su, Suzo saitin kofata suyita yada magana.. Na kanyi murmushi a duk sanda suka yi haka, Ni wallahi gaba d’aya yanzu basa damuna. Kuma lokaci kawai muke jira da zai bayyana gaskiyar komai. Yanzu kam Alhamdulillah muna samun cigaba sosai a bangaren Abdullah domin har ya zana SSCE successfully. 

____Turare masu sanyin kamshi na shafa, Na nufi sashen Ammi. Har a raina nake jin ta. Shi yasa bana iya kara kwana biyu ban lek’a mata ba, Musanman da magungunan temakon su yake hannu na. Wadaraccen mayafi na na yafa akan doguwar rigar jikina ta lace. A hanyar da zata fitar dani daga sabon sashe na na had’u dasu gimbiya jaleelah, Gaishe su nayi suka amsa babu yabo ba fallasa,

 “Sai ina kuma amarya..?”

Gimbiya Najwa ta tambaye ni tana karewa kayan jiki na kallo..

Takaici ya isheni, Su din ina zasu je da daddaren nan? Na yatsina fuska ina bin farcen hannu na da yasha lalle da kallo. Can cikeda k’asaita nace,

 “Zan kai gaisuwa ne… Daga unguwa kuke ne?”

Suma yatsina fuskar suka yi, A dakile gimbiya Jaleela taban amsa,

 “Uhm… Munje zagaye ne.”

 “Okayy! Sai da safen ku. Allah ya tashe mu lapia.”

Gaba sukai basu amsa ni ba, Nima na wuce ban sake bi ta kansu ba. Ta baya na zagaya na shiga sashen Ammi, Suna zaune da Abdullah kunnen sa saqale da earpiece,

 “Ammi..! Barka da dare.”

“Barkan mu dai Khadijaa.”

Ammi ta ansani ni cikin fara’a 

 “Abdullah ya gari..? Me ake jine?”

Turo baki yai gaba yana yatsina fuska,

 “Wani abune..”

“Okay! Kaci abinci? Ko a soya maka favorite dinka a hada da tea dinnan me dadi?”

Saurin kada kai yayi yana murmushi, Nima murmushin nayi, Shi dai yanasan wainar fulawa da ruwan shayi marar madara. Shiysa na dage nake masa saboda shayin nake zuba maganin da Malam ya bayar, Kuma Alhamdulillah anata samun ci gaba. Domin Abdullah sosai ya rage yawan daren da yakeyi, Kuma baya shaye shayen abubuwa kamar sanda na dawo masarautar. Sai dai kawai yayi shiru yana jin waka baya shiga harkar kowa. Wakar ma so nake ahankali na koya masa ‘kinta, Ta yadda komai zai dai-daita. 

 “Kede bakya gajia Khadija? Ki bari su Na’imah suyi mana?”

 “A’ah! Bakomi Ammi, Bara nayi sauri na kammala.”

Kitchen na shige, cikin k’ank’anin lokaci na gama hada kayan wainar fulawa na fara soyawa ina zuba masa acikin food flask. Ban d’au lokaci ba na kammala soyawa, Na hada masa tea din na zuba duk abunda malam yace kamar koyaushe na kai masa na ajiye,

 “Sakko kaci Abdullah…!”

Lumshe idanu yai ya bude yana murmushi,

 “Na…Nagode Kh..”

 “Uhm uhm dai bana hana sunan na ba..” Cewar Ammi tana gyara masa.

 “Thanks Aunt Kay.”

Murmushi nai, Kaina har girma yake Idan naji yana cemin Aunty Kay dinnan, Sufa yan gayu komai nasu na dabanne. Gashi mun fara sabawa dashi, Ammi ba kadan ba takejin dadin hakan. Sai dana tabbatar ya cinye komai sannan na musu sallama na koma bangare na..

Ina cikin tafiya tamkar ance juya kawai na hango shaheeda sai zuba sauri take yi, Ko kallo na batayi ba ta shige ciki wajen Salman, Murmushi nai kawai na shige sashe na, Turaruka nima na bulbula na *yerwaincense&more* Sannan na cokala dauri na ya koma ture kaga tsiya, Wadataccen gashin kai na ya bayyana.. 

Lemon iced drink na dauka, Ina tafe ina taunar strawberry chewing gum a baki na, A haka na shiga wajen Salman baki na dauke da sallama. Suna zaune shi da ita, Ya tallafe habarsa yana kallon cup din gaban sa data zuba masa tea. Ina shiga ta dago ta zabgamin harara, Nayi murmushi ina danne dariyar data tahomin,

 “My Whole world… Barka da dare.”

Da sauri ya dago ya kalle ni na kashe masa ido d’aya ganin tana kallo na, Batasan da biyu nayi hakan ba.

 “Yaya… Yaya barka da dare.”

Daga shi har ita tsayawa sukai suna kallo na, Na sake maimatawa ina dashare mata hak’ora, Mik’ewa tai tana fiffita da kasan mayafinta duk kuwa da na’urar sanyaya parlor dake sanyaya mu,

 “Yaya…. ?Ke banason munafurci, a gidan uwar uban ki na zama yayar ki? Salman ka shiga tsakani na da yarinyar nan wallahi, Dan yanzu sai mu debi yan kallo.”

Nayi murmushi kawai ina sosa tulin packing din gashi na, Can na cire dankwalin na ajiye a gefe, Ina kallon irin mayen kallon da Salman kebin gashi na dashi. 

 “Yaya Allah ya huci zuciar ki…. Ni na kai matsayin mu debi yan kallo dake? Haba wane mutum.”

Komawa tayi ta zauna tana huci, Na matsa daf da kafafuwan Salman na zauna, A hankali nasa hannu na zaro kafafun sa dake cikin takalmi half covered. Na shiga matsa masa k’afafuwan ina murmushi,

 “Sannu da hutawa.. Kasha zaman fada, Kaga yadda suka kumbura kuwa.? My Whole world Allah dai ya baka ladan mulki.. Ya biya bukatu na alkhairi.”

Lumshe idanu yai ya bude su a kai na, Shaheeda tacika tayi fam, 

 “Salman magana muke, Ka tashi mu karasa maganar sai mu dawo..”

Ahankali yasa hannun sa ya dafe goshin sa dashi,

 “Shaheeda.. pls let me be…”

 “Toh ai kuwa zan dawo nan sashen naka da zama wallahi. Gwara ka zabi d’aya.”

Shiru yai bai tanka taba, Na guntse dariar data tahomin, Can na tuna da lemon iced drink din dake gaba na, Dauka nayi na dora masa akan hannun sa,

 “Sha kasamu coolness your majesty.. Kamata yai a barka ka huta wallahi..”

Ai bansan na janyo ruwa ba, Shaheeda ta shjga surfa min zagi tana neman janye ni daga kusa dashi,

 “Allah ya huci zuciyar Yaya… Nifa ba dake nake ba, Idan dake nake ai da kai na nake kenan, Ni dake ne awajen fa Ko kin manta…? Ina maganar jama’a na waje.”

Na karasa fada ina turo bakin shagwaba, Gaba d’aya ina magana ne ina kallon Salman, Yayin da ita kuma tana tsaye kamar muciya tana surfa kwakwazo. Nan kuwa da ita nake.. “

“Washh Allah na… Kai na kwana biyu yaita kaikayi, My whole world tun ranar daka wankemin shi dinnan a bandakin kasa? Bai sake yi ba sai dazu ya dawo. Dan sosamin tsakiyar gashin plss.. Kaji nawan.”

Tamkar soko haka ya zama, Na samu kai na da kwantar da kai na akan cinyar sa duk kuwa da tulin fargabar dake zucia ta. Hannu yasa ahankali ya shiga sosamin kan, Na tsiri lumshe idanu ina mai magana ahankali cike da jan hankali… 

 “Wasssh Allah na dadi .. Gaskia My whole world zaka zama personal hair stylist dina, Ni da zaka iya dakamin kalabar nan guda biyu irin ta last week..”

Wani dogon saki shaheeda ta saki tana tafa hannuwa, “Lalle Salman shekaru nawa da auren mu kitson kai nama baka kalla amma ace dagayin auren ka har mace kake wankewa kai, kitso da wani susa kamar dan daudu..”

Zaiyi magana nai saurin cewa,

 “Nan haka baka sosawa, Kawo hannun kaga cikin nan..”

Ai ban karasa ba, Shaheeda ta janyo hannun sa ya tashi,

 “Na rantse da Allah ba Za’a dinga bariki agabana ba, Kawai kace yar tasha ka debo mana. Salman mai zan gani? Sarki ne fa kai, shugaban al’umma.”

Daria ce ta kufcemin nace,

 “Haba Yaya.. Dan sarki ne shikenan sai ace cikin matan nasa ma sarauta zai yi? Haba Yaya dan Allah, Ni last week gashi ki tambaye shi haka kawai ya tsiri shiga kitchen ya soyamin kwai..”

Salman ya gwalalo idanu nai masa gwalo ganin ta juya, Ganin karna kasheta da ranta, Na mike na dauki dankwali na ina rausaya..

 “Na manta kwanan ki ne ko….? Kar na shiga hakki, Yaya a huta lapia. My whole world ka kulamin da kanka… Sai da safe..”

Peck nayi masa a kumatu na fuce da sauri, Ban jira cewar wanin su ba. Dak’yar na koma sashe na Ina tafe Ina dariya haka na dinga hada stairs, Tun a bene na kira Addah maryama tafara bacci ma na bata labari. Ina jiyo sautin takalman shaheedah fuuu ta fice ta koma sashenta, Ranta a matuk’ar tashe, Ina sane nayi hakan, Insha Allah kuma haka zanta mata har sai ta yi dana sanin auren sa… Alkawari ne wannan na daukawa Gwaggo.. Zan shige gaba a nema musu lapiar su daga shirin sihirin da ake jefa su.. Da komai ya gyaru kuma zan karbi takardata na kara gaba…

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…

KIBIYAR AJALI 27

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…