KIBIYAR AJALI BOOK 2 PAGE 1

Advertisement

 I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

_*KIBIYAR AJALI…..!!!!*_

_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_

           🏹👑👩‍❤️‍👨💝

Advertisements

_MALLAKAR:- NANA HAFSAT 🧕🏼*_

   _*(MISS XOXO)*_

_*©️®️ZAFAFA 5: 2021*_

     _(PAID NOVELS)_

_Wattpad:missxoxo00_

 *_BOOK 2_*

Advertisements

_PAGE: 1_

_Barka da sallah lovelies! Allah yasa munyi ibada karbabbiya, Aamin! Allah ya amshi ibadun mu ya karba mana.🤲🏻 Kamar yadda kuka sani, Kafin azumi mun kammala KIBIYAR AJALI na d’aya (book 1)! Yanzu da yardar Allah zamu dora a book 2. Daga inda muka tsaya a baya.😅🥰 Asha karatu lapia🤗💖_

_MASARAUTAR BASANNABAS_

Ya riko Kasan rigar jiki na, Yana mai rintsa idanun sa. A hankali cikin wata irin kasalalliyar murya yake cewa,

 “Sha..shaheeda! Kizo gare ni please.”

Takaici, Bakin ciki da bansan na meye ba ya tsaya min a wuya. Na wulkita idanu na na zabga masa harara. Banda tsabar renin hankali dama dik abubuwan nan ya dauka itace? Kwafa nayi na dube shi shakeke,

 “Ba ita bace…”

“No… Nooo! Shaheeda, Kizo gare ni plsss.”

Naja siririn tsaki a hankali, Da ace bayamin kwarjini bane dana ja masa Allah ya isa wallahi. Cike da takaici na mike na koma can karshen d’akin kan wata royal sofa. Na zubawa screen din wayata idanu ina jiran shigowar kiran Adda Maryama, Domin tace idan lokacin tafiya yayi zata kira ni. 

Cikin zaman kuramen da muke na zabga tagumi ina kallan gefen kujerar da na ke. Shin yana sane yai min haka ko kuwa duk cikin ciwo ne? Wata zuciar tace yana sane, Rabu da maza halin su sai su. So yake ya kunsa miki bakin ciki. 

Na sake jan wani tsakin a karo na ba adadi. Dai dai lokacin kunnuwa na da hanci na suka jiyo mini sauti da wani arnen turare mai tsananin kamshi. 

Gimbiya Shaheeda ce ta shigo bayan jakadiya ta sanar da isowar ta. Kan ta tsaye tayi wajen Sarki Salman tamkar batasan ina zaune ba. 

“… Shaheeda…. Come to me.”

Na dan kalle su ta kasan idanu na ina zubawa sarautar Allah idanu,

 “Sssh! Love! Ni ce.. Gani nazo ai. Sannu kaji, Sannu..”

Tana magana ahankali tana shafa kwantacciyar sumar kansa. Mik’ewa nai na fuce bayan na d’auki laffaya ta na barsu lokacin da naga tana kokarin cire mayafin jikin ta. 

Cikin sauri na fice ina harde tafiya. Gaba d’aya ji nayi bazan iya sake kara koda second d’aya bane a masarautar nan. Jiki na sai rawa yake, wasu irin surutai na rika ji a cikin kunne na. Nasa ka hannu akai ina rintse idanu na. Baki na ya gaza furta tulin addu’oin da nake ji dankare a kirji na.

Wani irin dishi dishi na fara gani, Sama-sama nake jiyo sautin muryar Addah Maryama,  Ni dai sulalewa nai awajen ban sake sanin inda kai na yake ba.

  Koda muka koma gidah, Addah Maryama ta taimakamin na shiga band’aki nayo wanka da alwala. Ji nayi gaba d’aya yanayin da na tsinci kai na a cikin masarauta dazu yanzu bana ji. Sai kadan kadan. Sallah na mike nayi na shiga addu’oin kariya da neman zab’in Allah. Na kasa manta wulak’ancin da Salman yayi min yau. Koda bama son juna bai kamata ace ya cimin fuska haka ba. Cikin haka sai ga Addah Maryama ta dawo da filet a hannun ta dauke da funkaso da miyar ganye data sha tantakwashi. 

 “Sakko kici gimbiya…”

Bamu su na sakko nayi bismillah na fara ci saboda yunwa nake ji matuk’a. Sai da naci na gyatse sannan na wanko baki na da hannu na,

 “Gimbiya.. Ya aka kare da yallabai? Fatan dai abu yayi kyau.!?”

 “Addah Maryama baki ga a yadda kika same ni ba?”

 “Wai awajen kofar sashen sa? Na dauka kawai irin yanayin nan ne kin gane ai..”

Nayi murmushin takaici kawai ina mai girgiza kai na, Idanuwana suka kawo ruwa, Naja gefen zani na na goge hawayen,

 “Addah Maryama.. Salman yamin wulakanci… Ko kinsan duk abubuwan da kike ce nayi nayi..Wai anma tsabar cin fuska se kira na yake da Shaheeda. Duk abubuwan nan ya dauka ita ce….”

Addah Maryama zatai magana na sake katse ta ina jan wata ajiyar zuciya,

 “Can sai ga matar sa. Bansan ta ya akai tasan da zuwa na ba.. Kinga wulakanci.? Agaban idona suke…”

Kasa karasawa nayi na fashe da wani irin marayan kuka, Addah Maryama ta janyo ni jikan ta tana bubbuga bayana alamar ban hak’uri.

“Sssh! Ya isa! Bar kuka gimbiyar mu, Nagane abunda yasa ki jiri dazu. Kiyi hak’uri. Inaso kisan ba lefin Salman ba. An rigada an juyar masa da hankali. Mutumin da sam mahaifiyar sa bata gaban sa. Kai harta yan uwan sa da suke ciki d’aya gaba d’aya baya ta tasu. Banda aikin tsibbu aina ake haka..? Inaso ki san ba lefin sa bane wallahi. Sihiri gaskia ne. Addu’a kawai zamu cigaba da yi. Kuma mu tashi a tsaye muma mu nemi na kariya.. Kina jina?”

Daga kai na nayi sama alamun Eh! Na cigaba da share hawayen fuska ta ahankali.. Hankali na tacigaba da kwantar wa ta hanyar bani labarai masu ban dariya. Ni kuwa gaba d’aya daren ranar ban runtsa ba, Tunani kawai na cigaba da yi, Shikenan ni kuma haka tawa rayuwar zata k’are a wahala? Haka zan ta bautawa wasu ni ina disashe tawa rayuwar? Na rafka salati ina mai cigaba da juyi a makekiyar katifar dake kan gadon da nake. Bansan sanda bacci barawo ya sace ni ba…

*MASARAUTAR BASANNABAS*

 *SASHEN SARKI ALIYU SALMAN ALIYU (SAS)*

Zufa ce kawai ke kwarara a jikin sa. Sai rawar sanyi yake yana mai sake takurewa a karshen makeken gado dakin sa. Shaheeda tayi rau-rau da idanu, Gaba d’aya duk daukarta nata bomaboman aikin ne suka masa yawa shi yasa yake haka. Ta cire idanu ta maida kallon ta ga kujerar da Khadija ta tashi akai. Wani tsaki taja mai cike da takaici. 

 “Yanzu Salmaan har ganin banzar matar can kake a boye? Why Salman? Me nayi da har zaka ci amana ta haka? Uhm..”

Shi kuwa Salman sam bai masan inda kansa yake ba. Taita maganganu ita kadai tamkar zaucacciya. Can tabi robobin ruwan tofin da aka shanye da kallo. Tamkar sabuwar tabi haka ta mike jiki na bari ta kunce mad’aurin zanin jikin ta ta ciro wani kullin magani. Ta zuba a roba ta karkada shi sannan ta durawa Salman a baki. Yana kwance ba Uhm bare uhm uhm, Sai kakkarwar ciwo da yake faman yi. Tana gamawa ta sulale ta koma sashen ta hankalin ta a matukar tashe ganin yadda ta samu Khadijaa bayan duk ta aiwatar da abubuwan da malam yace tayi zasu rabu da Salman.

*GIMBIYA SHAHEEDAH*

Zagaye ta shiga yi a dakin ta, kafofinta kunnen ta rike suke da na’urar Bluetooth ta amsa waya. Maganata ake haukace tana daga hannaye. Don dama idan tana cikin tsananin tashin hankali to hakan ne yake faruwa da ita. Tayi ta yin abubuwa tamkar na marasa hankali,

 “Hajjaju… Ni de ki kara tambayar sa. Domin Salman fa bashi da lapia sosai. Kuma tinda na binne layar nanne aka sanar min bai san inda kansa yake ba. Anya kuwa malamin nan da kika rakita yasan abunda yake yi?Gaskia bazan lamunta ba Hajjaju. Ko dai bai san kan aikin bane? Ina gaya miki Salman is out of his senses. Ya zama kamar soko.. Ko Kinsan da tsinanniyar nan na ganshi.. Hajjaju ki kara ‘kaimi dan Allah, Zata wargaza min sirri matar nan.”

Tana magana cikin tsananin fushi, 

Hannun ta d’aya tana dukan bango dashi. Mahaifiyar tata sai neman kwantar mata da hankali take amma sam tak’i yadda,

 “Kawai ki je ki same shi, Idan ba zai iya bane mu nemi wani malamin, Domin wannan yana neman ‘ballo mana da ruwa.. Okay! Seda safe.”

Kit ta katse wayar ta koma ta zauna tana cizan leben ta na ‘kasa, Magana take ita kadai tamkar da wani a kusa da ita,

 “Ya zaai ace ni da miji na amma sede ni na nemi shi ba dai shi ya neme ni ba? Ya za’ai ace mu’amalar aure kullum sai baya cikin hayyacin sa yake tunkarata? Dole na nemi mafita.. Tun kafin komai ya bayyana.” 

Tayi mita tayi tsaki haka ta kusan raba dare tana abu d’aya…

*SAS*

Kunsan yadda zance yake yaduwa a masarauta.. Kan kace kanzil! Magana ta yanyana har cikin gari da wajen sa.. Cewar Sarki bai da lapia baya fita ko’ina, Zaman fada ma yanzu waziri ne yake zama. Atakaice dai sarautar ta dawo tamkar babu sarki. Babu irin ciwon da mutane basu kwakwulo sun jajiba shi akan sarki Salman ba. Kowa tofa albarkace bakin sa yake. 

Sarki Salman na kishingid’e akan wani lallausan carpet dinsa dake malale a makeken parlorn sa. Tufa ce agaban sa. B’angaren sa na dama kuma waziri ne kansa a kasa. Sarki Salman kallo d’aya zakai masa kasan tabbas bayajin dadi. Gaba d’aya ya zabge sai dai ya kara haske. Manyan idanun sa sun sake manyanta tubarkAllah! Kwarjini ya kara lullube shi, Idanun sa saqale da gilashi. iPad ce a gaban sa yana nunawa waziri wasu abubuwa.. Waziri ya kara k’asa da kansa alamun girmamawa da tausasa harshe yace, 

 “Ran sarki ya dade yayi karko. Ko dai zaka kokarta ka leka fadar ne?”

Sarki Salman yai hanzarin girgiza kansa yana jan leben sa ta kasa. 

 “Ba zan iya ba waziri, Jiri ne ke kwasa ta idan har na mike. Na kuma gaya maka har yanzu kirjina nauyi yake min, Tamkar an dora duwarwatsu…”

 “Assha! Sannu ranka ya dade! Allah ya kara maka lapia.. Da yardar Allah zan kara karb’o maka turaren miyagunnan. Idan kayi kana jin dadi ko?”

Daga kai kawai Sarki Salman yayi ya maida kansa kan wani pillow ya kwanta. Bai kara cira kai ya dubi waziri, Kambun mulkin nasa sun motsa. Haka waziri ya karaci zaman sa ya mike yai masa sallama ya tafi. Ya bar sarki salman kwance yana tunanin da shi kansa bai san na menene ba.

<<<<>>>>>>    <<<<<>>>>>>

Kwance yake akan wani katafaran gado, a kalla zai iya daukar mutum bakwai ba tare da sun matse juna ba wajan bacci. Amman shi kadai ne a kai ya yi ruf da ciki kafafuwansa a wale yana ta sakin munshari. Idan ka karewa bedroom d’in kallo zaka tabbatar da cewa jiya ya sha bidirinsa, saboda kayan da ya cire duk gasu nan a kasa ya yi wurgi da su. Dogon wandon yana gefe, T.shirt din ma na wani gurin daman, p.cap din sa ma haka.

A tsakiyar center carpet kuwa, kwalaban barasa ne da ya sha kusan guda hudu. Akan bedside d’in sa ma wasu guda biyu ne an shanye daya an rage wata a cikin kwalbar. Idan ka kare masa kallo tsab kuwa a yadda yake ta shakar bacci, ba zaka taba zato ko tsammanin yana da wata tawaya a cikin rayuwarsa ba, saboda wani irin sihirtaccen kyau da Allah buwayi gagara misali ya yi masa. Wani kyakkyawan abin hannu ne a tsintsiyar hannunsa, tsakiyar an rubuta A.A.S. Wato Abdullah Aliyu Salman.

Cikin tsakanin firgicewa ya tashi yana waige waige tamkar me neman wani abun. Idanunsa ya kai kan agogon dake ajiye akan bedside ya duba lokaci, take ya kuma zabura ya mike yana furta.

“Subahanallah….”

Bathroom ya shiga nan da nan ya sakarwa jikinshi shower, ko cikakken minute biyu beyi ba sai gashi ya fito daure da towel. Da sauri ya bude drower ya ciro suit dark blue, ko mai be tsaya shafawa ba haka ya zura kayan tare da karasawa wajan madubi ya kalli fuskarsa. Duk da cewar be yi wani abu ba, amman ya yi matukar kyau, idan Allah ya baka cikar zati tofa ka godewa Allah koya a wane yanayi kake, kai d’in mai kyau ne. Cikin sauri ya fesa turaruka kusan kala biyar sannan ya dauki jakarsa ya fito yana ta faman buge mutane.

Yau ya yi alkawarin zuwa gidan su shi yasa ko tsayawa yin wasu kakale-kakale beyi ba, kasan cewar ya kusa makara ko da wane lokaci jirgin da zai bi zai iya tashi a lokacin. Yana zuwa kuwa ya tarar passengers duk sun shiga har ana shirin rufe kofa, aka jira shima ya shiga, nan da nan kuwa suka tashi sai jahar shi ta gado, wacce ba zai iya tuna rabon shi da zuwa cikin ta ba. A Abuja suka sauka, amman a ranar ya taho Kano duk da cewa akwai guraran da zai kwana amman sam hankalinsa yana kano yafi son yaje can kai tsaye.

*SASHEN MAI BABBAN DAKI*

       (GIMBIYA SA’ADATUH)

Carbi ne a hannunta, Lazumi take yi ganin yadda labbanta ke motsawa ahankali. Hawaye d’aya na bin d’aya a kyakkyawar fuskar ta. Taja ajiyar zuciya ta sauke tana mai goge hawayen da kasan jilbab din jikin ta. Cikin haka Yareemah Abdullahi autan ta ya shigo yana harhada hanya,

 “Ammi…….!”

“Na’am Abdul..” 

Kasancewar sunata mahaifin yaci. Hakan yasa bata iya karasa furta sunan nasa duka. Da sauri ta karasa goge hawayen fuskar tata gudun karya gani. 

Girgiza kansa yayi saboda yadda yake jin kansa a duniyar sama, 

 “Ya makaranta..?!”

Pcap din kansa ya zare ya wullar a gefe, Zubewa yai akan kujera saboda tangadin da yake yi. Duk da acikin maye yake, Bai gama sakin saba, hakan bai hana shi dafe kansa da hannun sa na dama ba ya runtse idanun sa dakyar yace,

 “Ammi…! Barka da rana.”

“Barkan mu Abdul.. An dawo lapia? Maza tashi jekai wanka kaji? Kafin ka fito za’a shirya maka abinci..”

Mik’ewa yai dakyar yana tangadi yayi hanyar fita kenan ta katse shi,

 “Ina zaka Abdul?.”

 “Waww..Wan.. Wankan zanyi.”

 “Au..  Shiga bandakin kasa na cikin dakin nan kayi. B’angaren ka sai dai kayi hak’uri, Yayan ku ya kara aure amaryar can take.”

Wani ashar ya lailayo ya dura yana rike cikin sa,

 “Amma bashida mutinci. Bara na fito sai nayi ‘kasa kasa dashi.”

Yana magana yana tafiya har ya shige cikin dakin, Kansa ne ya shiga juyawa ya zube akan gado ya fara jan munshari take baccin maye yai awun gaba dashi.

Gurfane Ammi tayi tana girgiza kai, Matsalar ta duk duniya akan yaranta ne. Dan autan ta da zata kalla taji dadi shima an gurbata tasa rayuwar. Kullum cikin shaye shaye, Ba’a makaranta ba ba’a gidan ba. Makarantar kwana suke suna babbar sakandire. Kullum idan sunyi hutu shi sai ya jima kafin ya dawo hakan ce take kasancewa dashi, Yaita shaye shaye yana debo mata magana.. Gashi dik cikin sauran yaran shi kadai ne meyi..

Sabon shafin kuka sosai Ammi ta bude tana yin sa ba kakkautawa.. Tarasa madafa, Tarasa farin cikin ta, Hannu ta daga sama tana rokon Allah daya kawo karshen wannan kaddarar rayuwa da take gani itada ahalin ta kala kala…

*GIDAN GWAGGO TA FADA*

Band’aki na shiga na canza pad din jiki na, Wannan jini na rasa ranar da zai dena kwarara, Ya ragu sosai ba kamar da ba. Amman har yanzun yana fitowa. Wani lokacin harda guda guda.

Kaya na zura marar nauyi na fesa turare mai sanyin kamshi marar karfi. Haka kawai na tsinci kai na da kallon kai na ta mudubi. Shin ni din menene laifi na da mutane basa so na? Se bina da sharri da mugayen alkaba’i? ‘O ni dije Allah ka jikan iyaye na da rahama, Wasu abubuwan da akeyi min don rashin babu idanun su ne. Tabbas iyaye katanga ce mahallakar makiya. Nayi kewar ku Ummah Da Baffanah. Allah yasa aljannatul frdwas ta zama makoma agare ku da dik musulmai baki d’aya.’

Siraren hawayen da suka zubomin na goge da tafin hannu na, A haka addah maryama ta shigo ta same ni. 

 “Ah’ah! Gimbiyar gimbiyoyi, Takawar ki lapia sarauniyar zuciyar sarkin garin mu adali me son mu, Dan Allah ki dena zubar da hawayen ki, Inajin ciwon hakan har cikin zuciya tah… Kinji?!”

Murmushi nai kawai hade da kada kai na. Ta tako har gabana tana mai rufe murfin Kullaccam din dana gama shafawa,

 “Gwaggo na neman ki..Tana babban parlor ki sako mayafi ko hijabi domin itada bako ne.”

Sake kada mata kai nayi, Domin labbana sunyi nauyin furta kalamai. Ficewa tayi bayan ta ciro min wani gogaggen hijabinta a drawer, Na dan jima a Zaune ina sakawa da warwara kafin na mike na nufi babban parlorn Gwaggo ta fada wanda ya kasance na masaukin baki. Baki na dauke da sallama na shiga ciki, Suna zaune su uku. Gwaggo, Addah, Sai wani dattijo gemun sa ya zama furfura gaba d’aya. Ya rufe kansa da hirami. Gaishe su nayi baki d’aya, Gwaggo ta nuna min kusa da ita na zauna.

 “Itace wannan Hajia.?”

Ya tambaya yana mai kallon Gwaggo ta fada. Gwaggo ta jinjina kai. Ya sauke numfashi yana girgiza kai. Na kalli Gwaggo kallon karin bayani. Gwaggo tace,

 “Khadija wannan da kike gani babban malami ne na sunnah, Yanada makarantu na tsangaya dama Islamiyya. Kuma ya kasance kamar dan uwa ne agare mu. Domin duk abunda ya sha mana kai ma’ana ya zarce karfin sanin mu.. Toh awajen sa muke neman karin haske. Sunan sa Malam Mujaheed Na Soro, Na gaya masa matsalar da kike ciki tunda dama yasan Salmanu ya kara aure, Tofin nan da kika yiyyi amfani dashi dana wajen Salmanu duk almajiran sa yasa suka yiyyi, To dana gaya masa ba wani canji dai shine yace zai kara bincike akai duk yadda ake ciki zai zo da kansa…”

 “Toh Gwaggo.. Allah yasa adace.”

 “Aamin Yaa Rabbi… Malam! Bismillah!”Cewar Gwaggo Ta Fada.

Gyaran murya Malam yayi, Ya sosa gefen kunnen sa kafin ya fara cewa,

“Wato azahirin gaskia Hajia wannan babban makaru aka yi musu jifa daga ita har shi sarkin.”

“SubhanAllah..!” Addah Maryama tafad’a tana mai girgiza kai cike da tausayawa. 

“Ai Malama Maryama akwai mutane marasa imani a duniya, Wanda digon tausayi wallahi basu dashi a zukatan su. Ahar kullum su dakushe farin cikin mutum yai ta zama a lalace shi suke so. Da zakuga yadda zukatan su suke bakikkirin idan farin ciki yasamu wanda suka tsana zakuyi dimbin mamakin yadda suke shiga mawuyacin hali, Sai sun bi ta kowacce hanya sun kauce sunyi shirka sannan suke jin dadi. Wallahi duk yadda zasuyi sai sunyi wajen ganin sun dakushe mutum, Kai Allah ya mana katangar k’arfe da makiyan mu..”

 “Aamin Aamin!” Muka hada baki wajen amsa addu’ar malam…

Masu tambayan if yerwas truly a scented product.?…Well yess😅 Yerwa incense and more as the name implies dagaske kamfanin turare ne na turaren wutan kanem empire (bornu) Turaren Kaya, gidah, khumrah’s, kulaccams, turaren ruwa na larabawa dana fesawa, English perfumes, kabbasas, burners, steaming chairs, Kai komai da komai dai na turare Muna dashi.. You can check us on ig @yerwaincense_and_more, Muna tura kayanmu ko’ina a fadin najeriya kai harda nahiyar ketare ta dhl👏🏻Muna bada kayanmu akan farashin sari da saya dai-dai… so please do follow our Instagram page above👏🏻

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…

KIBIYAR AJALI 33

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…

KIBIYAR AJALI 21

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR…