KIBIYAR AJALI BOOK 2 PAGE 2

Advertisement

 I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.   

*BOOK 2*

*PG:2 *

      ________

Advertisements

“Sihiri gaskia ne, Kuma kowa zai iya kama shi dik kuwa da yadda kake tsarkake jikin ka, Sai dai kamuwar na wani yafi na wani, Saboda karfin tashi tsaye da kariya. Ranki ya dade ina fatan kina saurara?… ”

Ya karasa fada yana duba na, Na daga kai ina mai cigaba da jinjina kalaman sa na baya akan ma’kiyi. 

“Nayi bincike sosai akan zancen ki da Hajia ta sanar min, Har na sassa yara suka yiyyi addua aka yi miki tofi kuma.. Har yanzu jinin na fita kamar da ko kuwa ya ragu?”

“A’ah! Ya ragu ba kamar da ba.. Nagode Malam!”

“Toh gaskia babban sihiri ne wannan, Kwanaki can baya an kawo min ire iren matsalolin nan. Kuma duk yawanci dai abokiyar zama ce silar ko kuwa wani makiyi na daban.. Shi sihiri gaskia ne domin ya kama annabin Allah ma ballantana mu karan kada miya. Wannan jini da aka sakar miki duk d’aya ne daga sharrin sihiri. Ki cigaba da ibadar ki, Anyi hakane domin wata manufa don kada auratayya ta shiga tsakanin ki da mai martaba. Kuma ta Allah bata suba,

“Sannan duk wannan warin da kikace kina ji na kamar shekararren mushe duk makuru ne wallahi, An miki jifanne don ke kan ki ki kyamaci kan ki, Sannan wani kara da gane gane da kike yi duk razana ce don ki fita ki bar masarautar ne. Sannan an dasa miki tsoro da fargabar cikin ta. Wannan duk sharrace sharracen sihiri ne, Ana kara nisan ta tsakanin ku da juna, Ma’ana ke da mai martaba, Sannan duk wutar kinsa dake sake ruruwa a zuciyar ki duk Sharrin shaidanu ne da akai amfani dasu, Amman In shaa Allahu nan ba da jimawa ba komai zai dai-dai ta da yardar Allah…”

Advertisements

Shiru nayi kawai ina maimata maganganun sa a zuciya tah, Allah na tuba Salman ai ba son hakika yake min ba. Ya aure ni ne dan ya muzguna min. Kawai saboda nayi kokarin ganin ya amsa tambaya a saukar qur’ani da akai. Na sauke nannauyar ajiyar zuciyar da sai da dukkanin su suka dago suka kalle ni,

 “Gimbiyah ya dai…?” Cewar Addah Maryama da kulawa.

Na girgiza kai kawai alamun ba komai, Hade da ka’karo murmushin yak’e. Malam ya cigaba da cewa,

 “Toh abubuwan sammu dai da yawa akai miki gaskia, Wanda duk wani bakon lamari da jikin ki ko zuciyar ki zata kissima miki duk sharrin shaidanu ne la’anannu, Domin da su ake hada kai acuci bil adama. Allah ya saka muku da gaggawa kuma ya yaye muku dukkanin matsalolin da aka jefa rayuwar ku aciki… Sai kin kara jajircewa da addu’oi sosai, Da yawan salloli, Lazimi da karatun qur’ani, Babu dare,  babu rana. Da yawan sadaqah In Shaa Allahu rayuwar ki da tasa zata daidaita da duk wani masoyan ku da ake dakushewa. Muma a namu b’angaren zan sa yara suyita sauke qur’ani, Zan tayaku da adduoi nima, Sannan ga ruwan tofi nan na kawo da akai da zam-zam, Gasu Zaitun nan, Da habbatussaudah da ganyen magarya nan ma, Zan baki ayoyin da zaki karanta.. Kina ji?”

“Inaji Malam.. Nagode!”

“Yauwa shi wannan magani da ake da ganyen magarya ba sai an maka sihiri ba ko an jefe ka, A’ah kowa zai iya yi don tsima jikin sa daga sharrin masharranta, A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai kingan su nan (idan an samu busassu sunfi), sai a nika a zuba cikin ruwan. Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan. Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara). Sai a karanta Suratul A’araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.  Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82. Suratul Kafirun kafa daya Falaki da Nasi kafa uku- uku. Sai a karanta wannan addu’a, 

“Allahumma rabban-nas az’hibil ba’as ashfi wa antash-shafi la shifa’a illa shifa’uk shifa’un la yugadiru sakaman” kafa uku. Sannan za’a iya karawa da wannan addu’a “Bismillahi urkika min kulli shai’in yu’uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika” kafa uku. Insha Allahu ta’ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi. Wala nan kusa wala nan da wani dan lokaci. Allah ya shiga lamuran ku gimbiya, Allah ya kara tsare ku da tsarewar sa, Ya kare ku da kariyar sa. Allah ya kara muku ni’ima daga cikin ni’imomin sa, Allah ya karba mana Allahumma Aamin.. Ga kuma wasu addu’oin na rubuta miki, Ki dingayi kullum, Sannan azkhar ma na safiya da maraice dana kwanciya bacci dan Allah ki rike su karkiyi wasa dasu.”

 “Sannu Malam, Allah ya amsa. Mungode Allah ya saka da alkhairin sa.” Gwaggo Ta fada ta amsa masa fuskar sa dauke da fara’a. Da alama taji dad’in addu’oin da ya babbani. 

 “Babu komai Hajia, Yiwa kai ne, Fatan Mu dai addu’oin mu su karbu Allah ya yaye musu..”

 “Malam Nagode, Allah ya saka da alkhairi..” Nai masa godia ina karanta addu’oin dake cikin paper daya rubuto min. 

Sallama ya mana, Ya mike ya tafi bayan Gwaggo tai masa goma ta arziki, Ya tafi yana mai godia sosai.

Bayan tafiyar Malam muka yi sallah muka sake sabon zama, Gwaggo Ta Fada ta shiga kara kwantar min da hankali, Tana mai sake bani wasu labarun game da masarautar basannabas. Ta kar’kare da,

“Rayuwar sarki Salman abar tausayi ce gaba da baya, Kada ki manta gaba d’aya an juya masa hankali akan mahaifiyar sa, Yana abubuwa tamkar bashi da uwa, Tana raye gida d’aya dashi amman an riga da ancireta cikin zuciar sa, Yan uwan sa da suke uwa d’aya uba d’aya ma an cire su a zuciar sa, Gaba d’aya an cire sanayya, So da shakuwar yan uwan sa na jini da mahaifiyar sa a zuciar sa. Bayaga haka.. Shin ko Kinsan yan uwan nasa da suke uwa d’aya uba d’aya?”

Na girgiza kai, Alamun bansani ba. Gwaggo Ta Fada ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa,

 “Kamar yadda na gaya miki a baya, Su uku ne wajen mahaifiyar su, Salman shine babba, Sai Khaleel (Khal) sai auta Abdullah, Khaleel tun karewar karatun su aka kafe shi acan ya’ki dawowa, Ba ruwan sa da yan uwan sa da mahaifiyar sa shima, Yaki dawowa, Har aika mutane akeyi su gano inda yake an kasa samun sa, Ance dai ya zama babban likita acan din. Shi kuma autan su Abdullah yana ajin karshe a sakandire baya maida hankali ga karatu sai shaye shaye da d’auke dauke, 

“Shima an gurbata tasa rayuwar, Kullum sai neman magana, Gaba d’aya dai gasu nan gasunan ne, Salman a nutse yake kawai dai an juyar masa da hankali ne.. Yan uwan sa da mahaifiyar sa basa gaban sa, Sarki ne a zahiri amma a badini ba shine ke mulkar masarautar basannabas ba, Ba shida ta cewa sai hukuncin da aka zartar akan sa, Ga wancen na ketare (Khaleel) An kafe shi acan, Ga k’aramin cikin su shima, Gaba d’aya abubuwa sunyiwa gimbiya Sa’adatu yawa. Ba wanda zata kalla taji dadi, Har gwara-gwara Abdullah karamin su… Kina jina ko gimbiya?”

Hawayen dake mak’ale a idanuna na share, Tabbas wannan damuwar su ta shanye tawa. Wannan wacce irin musibace? Fisabilillahi duk akan mulki? Ka salwantar da rayuwar mutane? Ka raba su da farin ciki? Akan me? Mulkin da za’a mutu a barshi? Nasa kasan tissue din hannu na nagoge idanuna dake zubar da hawaye,

 “Inaji Gwaggo… “

“Auren ki da Sarki Salman alkhairi ne, Domin In Sha Allahu kece zaki zamto silar warwarar matsalolin ahalin Gimbiya Sa’adatuh da iyalanta, Saboda haka dan Allah ki cire waswasin ba zaki iya zama a masarauta ba, Munata addua, Ana tayamu, Kina yi kema , Da yardar Allah, Allah zai kare ki daga sharrin masu sharri…”

“In shaa Allah Gwaggo..” 

“Yanzu zamu kara zage damtse da addu’oin neman kariya, Maryaama zata kara nunar dake wasu abubuwan, Daga nan sai mu tsaida rana ki koma dakin ki..”

Gaba na yai mugun bugawa, Idanuna suka ciko da hawaye. Baki na na rawa nace,

 “Gwaggo meyasa?”

Gwaggo tayi murmushi irin nasu na manya Kafin tace,

 “Ai dole ne ki koma dakin ki gimbiya, Ko ni badan gudun fitnah ba ai da har yanzu ina cikin masarauta, Amma saboda nuna bangaranci da iko dasu wambai suke, Shiysa na tattara na dawo nan din tun haihuwar babban ‘da na mai rasuwa, Ni kinsan mahaifiyata ni kadai ta haifa ta rasu, Ba mahaifiyar mu d’aya da su Yayan mu ba, Wato kakan sarki salman na yanzu,

 “Amma kanmu mu a hade yake ba zaki taba banbance yan wannan dakin dana wannan ba, Duk inda aka samu rabuwar kayuwa dama daga iyaye mata ne, Saboda kishi. Yanzu dubi zaman doya da manjan da mahaifiyar Salman take ciki da yaranta. Kishiyoyin sun ware ta da ‘yayanta, Dama nan kadai suka tsaya da sauki,  zallar sihiri suke jifan su sun rarraba mata kan ‘yaya.. Kai duniya abun tsoro..”

Bata k’arasa magana ba sakamakon mugun tarin daya sarketa tashiga yi, A sukwane na d’akko ruwa na bata ta balli magani ta sha. Addah Maryamah tashigo alokacin ta min nuni da gwaggo ashe har bacci yafara daukarta ta bingire. Na mike a hankali Na fita, Muka jawo mata k’ofar muka koma d’aki, Nan Addah maryama tashiga karasa min daga onda Gwaggo ta tsaya, Ahmkali take wayarmin kai gameda kowane bil adama dake cikin masarautar, Tun daga kan sunan su, Da mukamin su, Da sashen da suke, Da komai daya kunshi Salman kannen sa da mahaifiyar sa. Kai Harda Matar sa, Da kishiyoyin mahaifiyar sa.

“Duk wani makirci da tsibbu da akeyi ki sani yana futowa ne daga kishiyoyin mahaifiyar sarki Salman, Kai basu kadai ba harda iyayen su, Dama wanda bamu Sani ba a b’oye, Sannan matar sa gimbiya Shaheeda Itama ba’a barta abaya ba wajen bunka masa nata sihirin, Tun fil azal batasan mahaifiyar sa dama.. Lamarin dai Sai addua kawai.”

Naja gwauruwar ajiyar zuciya na sauke, Cikin tsananin tashin hankali nace,

 “Kenan bakin su d’aya dasu?”

 “Eh bakin su d’aya ta wani bangaren, Amman kowanne daga cikin su yana da boyayyen burin sa a zuciya, Ita gimbiya shaheeda ai burinta baya wuce ta haifi magaji.. Sai dai ance dan kuwa ban sani ba, Amma dai an tabbatar cewar wai shi sarki baya haihuwa, Su kuma kishiyoyin mahaifiyar sa wasu daga ciki nason’yayayan su su gaji mulkin Wato a tsige sarki Salman akan karagar mulki a dora nasu, Nasan kuma akwai meson mahaifinta ya gaji sarautar, Tunda kinga duk yan ahali d’aya ne, kowacce tsatsonta zai iya gadon karagar mulki,

 “Kowane rukuni so suke sarauta ta dawo hannun su, amman mutan gari sunfison tsatson ilyasu wato familym sarki salman kenan. Kuma a yanzu gaskia mutanenan gari da ma makotan garuruwa kowa yanason sarki Salman yanada farin jini da kwarjini a idanun su, Duk kuwa da a Zahiri ne yake kamar sarki a badini ba sarki bane.. Gimbiya Salman na bukatar kasancewar ki a kusa dashi.! Domin makiya nason tube shi daga rigar mulki. Ki temaka dan Allah.”

Nayi murmushi ina maimaita maganganun data fada, Baya haihuwa? Tafi nono fari, Domin dama banda ra’ayin samun jini na daga gare shi,Haka kawai na tsinci kai na da ce mata,

 “Gaskia rayuwar su na cikin hatsari, Amman ni yar tahaluka dani ta yaya zan iya gyara rayuwar su? Bayan ni kai na kina ganin yadda aka mayar da ni, Ba don taimakon ku ba ai da Bansan wane hali zan tsinci kai na ba..”

“Tunda dai kikaga har an auroki an shigo dake cikin gidan nan kinsan kedin kainuwa ce dashen Allah, Yadda kika gayamin labarin ki ma tabbas nan gaba Kadan zakici ribar hakuri, Sannan ceto rayuwar sRki Salman da mahaifiyar sa wallahi ba karamin lada zaki samu ba, Gwaggon mu yawan shiga masarauta data yiyyi har wani sharri akaso hada mata, Allah ne kawai ya kareta, Badan Allah yasa gwaggon ta tsaya akan mahaifiyar Salman din ba, Ita ma kuma jajirtacciya ce mahaifiyar sa wallahi da tuni sun kassara ta..So gimbiya hakuri zakiyi a kara shirya ki ki koma dakin ki ki zauna, Ki rike mahaifiyar sa a b’oye, Ta zamto abokiyar amanar ki, 

“Ita kad’aice wadda zaki yadda da ita acikin masarautar nan, Domin ita dinma dake din kawai zata yadda, Batada kowa da zata fuskanta da kukanta, Macece mai gudun zuciya da sanin yakamata, Sannan sai kin iya takun ki, Kin zamto kamar mara wayo kin kwantar da kai sannan zaki zauna Lapia, Domin ko hadiman ki ai na gaya miki kwanaki, Nace miki karki yadda dasu, Abinci ma inda hali dena ci inde tahannun su yake. Za’a iya hada baki dasu a cutar dake, Sai kina takatsantsan. Zama acikin masarautar basannabas sai da iya taku..”

Na had’iye kakkauran abun daya tsayamun a wuya ina tuno wahalhalun danasha na jin wari da fargaba sanda ina cikin ta. Don ma jinin na samu yanzu yana sauki sosai. Haka addah maryama taita wayar mun da kai, Wani na dauka wani kuma naita mamakin yadda zan aiwatar. Haka muka kusan Kwana a zaune muna hirar masarautar bassannabas,

*BAYAN SATI BIYU!*

Yanzu kam Alhamdulillah!! Zama na agidan Gwaggo babu abunda zan iya saka musu da shi, Sai dai na ro’ki Allah, Daya biya musu bukatun su na alkhairi, Yadda suka ceto rayuwata daga kogin halaka, Allah ya saka musu da mafificin alkhairin sa ya kare su da kariyar sa. Domin acikin sati biyu kacal dana kara yi nayi amfani da addu’oin malam, Rass na warke. Jinin gabana ya dena fita, Babu wani abu dake damuna sai dai tsanar Salman da har yanzu bata ragu ba ko mislaka zarratin. Bayaga haka duk wani abu baya damuna, 

Sai dai gaskiya har banson a ambaci komawata gidan Salman, Sam banason komawa. Nafison wajen Gwaggo baabu takurawa bare fargarbar miyagun mutane. Sai dai alk’awarin dana daukawa Gwaggo zan koma masarautar basannabas, Sannan zan aiwatar da duk addu’oin da Malam yace na dingayi ina tofawa a sashen Salman da garin habbatussadah na turarawa. Da sauran abubuwa da dama. Zan kokarta nayi komai dan neman lada da ceto rayuwar su suma. Bayaga haka digon kaunar sa banaji a rai na, kuma naci alwashin duk sanda komai ya daidaita zan nemi yabani takarda ta. Na kara gaba na auri wanda nakeso yake so na… Da wannan tunanin Addah Maryamah tashigo ta karasa shiryani, Driver ya dauke mu, Suka maida ni sashe na a masarautar basannabas a karo na biyu…..

  *MASARAUTAR BASANNABAS*

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 23

Advertisement   __I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…

KIBIYAR AJALI 32

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…