KIBIYAR AJALI BOOK 2 PAGE 3

Advertisement

 I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

BOOK:2 

PG:3

    

     _____

Advertisements

Tun a cikin mota hankali na yake a tashe ina tunanin ta yadda zan shiga masarautar nan mai cike da makirci kala daban daban. Babban abin da yake sake bani tsoro da masarautar shine, yanayin makircin matan gidan da kuma masu rike da mukamai, wanda ko wannen su yake son mulkin ya koma tsatson sa. Lissafi na gabaki d’aya ya kwance sai tsantsar addu’a da nake ta faman yi cikin zuciyata.

Gwaggo ta Fada ce ta yi min magana cewa na ciro mukulli na saboda tana so kafin na shiga sashe na Adda Maryama ta shiga ta yayyafa ruwan maganin da muka taho dasu. Jiki na a sanyaye haka na bude jakar na dakko dan tun ranar da tasa aka karbo shi nasa cikin jaka ban kuma bi ta kanshi ba, sai yanzu da tace na ciro shi.

Sai da muka fara ajiye Adda Maryama a sashe na sannan Gwaggo ta sanar da shi inda zai kai mu. Abin da ya daure min kai shine wani sashe muka shiga, wanda ko ranar da aka kawo ni na zazzaga ba’a kai ni ba. Shiru banyi magana ba duk kuwa da tarin dimbin tambayoyin da nake son yi mata.

Tunda muka fito daga cikin mota hadimai suka fara yi mana kirari tare da barka da zuwa har muka shige cikin sashen da gwaggo tasa driver ya yi peeking. Tun daga babban parlor zaka gane inda ka shigo saboda wani katafaran hoto dake sakale jikin bango yana kallon kofar shigowa. Gabana ya yi mukun bugawa lokacin da nai ido biyu da hoton, sai dai karfin da addu’ar baki na ta yi shine ya hanani shiga cikin wani yanayin na daban.

Babu kowa a cikin parlorn, Gwaggo ta nuna min kujera na zauna, tana shirin zuwa wani daki sai ga Abdullah ya fito yana faman hade rai, alamar wani abu ya hado shi da mahaifiyar tashi. Har zai wuce be gaida Gwaggo ba, sai kuma ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba ya shiga mika gaisuwa. Itama kin amsawa ta yi sai binshi shi da kallon sama zuwa kasa tana tabe baki tace.

“Ashe ka dawo?”

Advertisements

“Eh na dawo, ya gida?”

“Yana inda kasan shi. Kai yanzu Abdullah duk tsahon lokutan nan ina kake tafiya baka zuwa ko hutu? Ko ka manta har yanzu mahaifiyarka tana nan a raye? Baka koda sha’awar zuwa ka ganta sai lokacin da ka fa dama kamar haka ko?”

Ya yi shiru ba tare da yasan abinda zai iya furtawa ba. Kada kai kawai ta yi ba ta kuma cewa dashi komai ba ta shiga cikin dakin, ya yin da shi kuma ya turo baki ya fara tafiya ya ganni zaune ban masa magana ba shima kuma be yi min ba, sai dai ya tsaya cak yana bina da ido tamkar ya sanni. Na dago ido muka hada dana juna sai duk muka sauke a kusan tare, yana kama da Salman, sai dai Salman ya fishi cikar zati, sannan shi yana da matukar haske, amman daka gansu kasan cewar tsatso d’aya ne ya haife su.

“Uhmm….Ke kuma fa?”

Na samu kai na cikin izza ta yadda naki koda nuna cewa dani yake, sai da ya kuma yin magana sannan na kalleshi a yatsine.

“Kai ma waye?” 

Ni ma na tambaye shi ta irin sigar da ya yi min tambayar, na kuma dauke kai na zuwa kallon gefe.

“Kut…! Kin san ko waye ni kuwa? Toh idan baki sanni ba baki san matsayi na ba ki tambayi ta fada zata gaya miki. Mtseww.”

Ya karasa yana jan tsaki duk da cewa na yi masa kwarji duba da ko ido baya son mu hada. Saboda kar ya yi tunanin wani abun hakan yasa na dan daga murya yadda zai jiyo ni sosai nace.

“Na ce maka ina son sanin ko kai waye ne? Bana bukata dan haka kar kai tsammanin zan tambayi Gwaggo.”

Abdullah ya juyo a fusace yaga alamar nima bani da mutunci yadda yake magana nake mayar masa a matsayinsa na yarima dan marigayi sarkin Basannabas kuma kani gurin sarki mai mulki a wannan lokacin. Sai da yazo dai dai inda nake sannan ya tsaya yana kuma kare min kallo, ganin ko motsawa banyi ba yasa shi dan matsawa baya kadan yana cewa.

“Da me kike takama ne?” 

Kai tsaye nace dashi.

“Allah… Da shi nake takama a duk cikin lamari na.”

“Ba wannan nake nufi ba. Nayi zaton ko kina takama ne da mulki ko sarauta.”

“Kai a zaton ka sune kawai abin takama a cikin duniyar nan? Akwai yan kasuwar da sunfi masu mulki da sarauta komai na rayuwa. Akwai kuma masu takama da ilimi kaga kenan abubuwan tin kaho suna da yawa.”

“Ke d’in a wane rukuni kike? Ina son naji.”

“Kaje ka tambayi duk wanda kake so a cikin masarautar nan, zaka samu amsar ka yadda ya kamata. Sannan bana son wata tambayar, ina bukatar hutu yanzu.”

Kamar daurin baki ya kasa cewa dani komai haka ya juya ya fita yana huci kamar wani tafasasshen ruwan zafi. Ni kuma na saki murmushi cikin rai na ina jin babu wanda zan bari ya rai na min hankali a cikin kannansa, dan naga alamar suna da jiji da kai irin na yaran masu farcen susa.

Cikin daki kuwa da Gwaggo ta shiga, tarar da Gimbiya Sa’adatu tayi tana faman girgiza kai alamar wani abun Abdullah ya yi mata. Sai da Gwaggo tayi sallama kusan hudu sannan ne Ammie taji tayi saurin amsawa tana kallon bakin kofar.

“Kina na kin ci gaba da sanya matsalar yaran nan cikin ranki ko?”

“Ba haka bane Gwaggo, sannu da zuwa shigo ciki.”

“Na shigo ciki kuwa, saboda tare nake da yarinya a can parlorn.”

“Au to bari ni na taso muje can d’in, ko Maryama ce?”

“Ba ita bace ba ma. Bari ina so muyi magana dake kafin muje parlorn.”

Jin haka yasa Ammie komawa ta zauna, itama Gwaggo guri ta samu ta zauna tana sauke numfashi.

“Zahiri da badini kowa yasan kina cikin damuwa Sa’adatu, an shiga hakkin ki sosai. Amma ki kai ta hakuri, kuma yanzu ma shi zan ce ki ci gaba da yi saboda shine kawai zai fitar dake da taimakon Allah.”

Tayi murmushin karfin hali saboda ta nunawa Gwaggo cewa babu komai, sai dai ta makara dan tuni Gwaggo ta Fada tasan cewa duk abinda zai fito daga bakin ta dauriya ne kawai da iya yadda da kaddara a duk yadda tazo.

“Gwaggo ai babu wani abu, kamar yadda kika fada ne komai yana da ranar karshe. Fatana kawai shine Allah ya kara min karfin gwiwa, na ci gaba da yadda cewa komai daga gare sa yazo min. Na gode da kulawarka akan duk wani lamari na, Allah ya ji kan iyaye da kakannin mu.”

“Amin… Amin Sa’adatu, daman bakuwa ce kuma yar gida na kawo miki ita dan na hada ku kusan juna. Idan har ba haka na yi ba toh ban san lokacin da za’a nunawa kowanne a cikin ku matsayin juna ba. Amaryar Salman ce kawo miki ita dan tace ran da tazo ba’a kawo ta gurin ki ba har na sauke ta.”

Kirjin Ammi ya buga, a farkon auran da taji labari ta yi murna sosai. Amman ganin har tsahon wannan lokacin na yau bamu hadu ba yasa ta karaya tayi zaton ko nima haka nake kamar su Shaheedah masu jiji da kai.. Muryar Gwaggo ta Fada ce ta katse tunanin ta, inda take cewa. 

“Baki da matsala da yarinyar nan yar mutunci ce, tana da nutsuwa da hankali dan gaskiya Salman ya yi dacen mata. Kuma insha Allahu alkairi ne a tsakanin su damu baki daya.”

Jin haka yasa Ammi yin murmushi saboda babu abinda take bukata a cikin rayuwarta irin taga wanda zai so su tsakani da Allah babu wani tuggu a ciki. Ta dinga kallon kofar shigowa dakin da alama ta kagu ta ganni, hakan da Gwaggo ta gani ne yasa tai dariya tare da cewa.

“Zaki iya zuwa parlorn ne?” 

Cikin sauri Ammie ta ce.

“Eh zan iya.”

“Toh muje ku gaisa, daga nan dakin ta zan mai da ita.”

Jin ta ambaci daki yasa ta tunawa da tijarar da Abdullah yazo ya yi mata yanzu, na cewa wallahi sai an bashi sashen shi babu inda zai koma. Gashi wadda aka bawa gurin ta dawo bata san yadda zata yi masa bama yanzu, dan koda ta lallaba shi da cewar ya bari za tai magana kin yadda ya yi, har da cewa waye zai ji maganar ta a masarautar bayan duk sun rai na ta.

Da wannan tunanin ta mike da kyar ta gyara hijab din jikinta ta bi bayan Gwaggo ta Fada. Lokacin da suka fito bacci ya fara dauka ta a zaune, har sai da Gwaggo tai min magana sannan na farka cikin sauri ina murza ido. Na sakko kasa ganin sun fito da wata wacce nake da yakinin cewa mahaifiyar Salman ce, na kasa kallon ta sosai bare na gane da ita yake kamanni ko kuwa da mahaifinsu.

Har suka samu gurin zama ban dago ba, haka kawai naji nauyin dago kai na. Ina shirin gaida ita sai naji muryar Gwaggo tana cewa.

“Khadija ga mahaifiyar mijinki Salman ku gaisa.”

Kamar jira nake a bani dama, cikin ladabi da sunkuyar da kai na gaishe da ita, ta amsa cike da fara’a kamar daman ta sanni yadda naji tana ta murna. Daga nan kuma hira ta barke ni dai murmushi ne kawai nawa bana iya cewa komai saboda yadda suke min kwarjini duk kan su, har Adda Maryama ta shigo itama ta zauna aka dora da ita, Ammie tasa mai yi mata hidima ta kawo mana abubuwan motsa baki, duk muka ci a tare bisa umarni Gwaggo, kuma da alama Ammie taji dadi dan ta ware sai hira take cikin jin dadi wanda ta manta rabon da taji makamancinsa.

“Ga magani nan mun taho dasu, akwai wanda naki ne sai nasu Abdullah. Ku fara yin amfani dashi muga yadda zai kasance, insha Allahu komai zai tafi azo aga kamar ba a yi wata rayuwar ba makamanciyar wannan da ake ciki.”

Ammie ta karba tana godiya tare da sake jin kaunar Gwaggo ta Fada dan ita ce kawai mai jin ciwon duk abubuwan da ake yi mata a cikin masarautar Basannabas. Daga nan muka yi mata sallama su Gwaggo da Adda Maryama suka yi min rakiya zuwa sashe na bayan anyi yayyafin ruwan ganyen magarya a duk inda zan taka, baki na kuma cike da addu’o’i har muka shiga parlor na wanda tuni aka canza kujerun, na karamin parlorn aka dawo dasu babba, na babban kuma aka mai dasu karamin parlorn.

 

Zaman mu ba dadewa sai ga Jakadiya ta shigo cikin rawar jiki, ganin ta yasa Gwaggo ta Fada tsuke fuska dan tasan irin bakin munafuncin dake cikin Jakadiya, shi yasa ta tsane ta fiye da abin da baki zai furta.

“Ya akai Jakadiya?”

“Lafiya lau wallahi Gwaggon mu, ji nai ance amaryar mu ta dawo, shine nazo na yi sannu da zuwa. Allah ya taimake ki ya kara miki lafiya da nisan kwana.”

Ta karasa magana tana sunkuyar da kai kamar wata mutuniyar arziki. Gwaggo ta Fada sai faman hade rai ta ke, ta tsani Jakadiya tafi san sauran da aka dakatar kuma tasan duk makircin wannan ne da iya munafunci.

“Oho! Toh d’an bamu guri dan Allah zamu karasa tattaunawa.”

“Allahu Akubar, toh Gwaggon mu Allah ya ja da ranki uwar kowa.”

Bata kula ta ba har ta fita, sannan ta mai da hankali waje na tana kuma yi min gargadi da jan kunne.

“Sai kin kula sosai da masu shigowa gurin ki Khadija. Mutane basu da gaskiya musamman na cikin masarautar nan, karki yarda da kowa bare har ki bude baki ki fadi wani sirri naki. Kome nene ki nemi Maryama ko ni ki sanar damu zamu yi miki shi da ikon Allah.”

“Insha Allahu Gwaggo zan yi yadda kika ce, na gode Allah ya kara girma da daukaka. Allah ya ji kan iyaye ya rabaku da sharrin masu sharri.”

“Amin ya rabbil alamin, bari mu zo mu tafi kafin a fara yada zancen mun zo gurin ki mun zauna. Allah ya bada sa’a. Sai kin dage sannan zaki iya taimakawa Salman Khadija, yana bukatar taimako sosai musamman daga gareki tunda ke din matarsa ce ta sunnah.”

Na jin jina kai cike da jin kwarin guiwar zan taimaka musu iya karfi na, zan daure duk da tsanar da nake ji ta Salman naji zan taimaka mishi saboda girma da darajar Gwaggo ta Fada, wacce ta yi min komai a lokacin da nake bukatar taimako. Daga haka suka mike bayan munyi sallama ina jin kamar na bisu saboda mun sabo sosai a dan zaman da nayi dasu. Bayan sun tafi na koma daki na zauna ina saka ta inda zan fara gabatar da aikin maganin wannan ran rainin hankalin da be damu da ni ba bare ya martaba matsayi na na matar sa da ya auro.

<<<<<<<>>>>>>

Jakadiya ce a gurfane gaban Gimbiya Shaheedah kamar zatai mata sujjada saboda tsantsar biyayya, ta gama sanar da ita cewar na dawo. Kishingiɗe take ana faman yi mata fifita, jin cewar na dawo ta mike zaune tana ware ido, da alama dawowar tawa ta mugun bata mamaki. Tsam ta mike tare da daukar wayar ta da sauri ta shiga daki tare da rufewa da karfi, jiki na kyarma ta kirawo mahaifiyar ta, bugu d’aya ta dauka ba ko gaisuwa ta shiga magana.

“Anya wannan yarinyar ba shaidaniya bace? Ta ya ya boka zai ce mana tabar masarautar nan kenan koda marmari ba zata kuma shigowa, amman yau gashi ta shigo har ma ta shiga sashen ta lafiya kalau. Na shiga uku ni dai idan har wannan matar tana kusantar Salman.”

Sosai ta razana da dawowa ta, kuma ita kadai tasan tsoran menene dan yadda ta firgice, musamman da taji cewar Gwaggo ta Fada ce ta dawo dani, tasan tabbas sai an bani kariya, dan Gwaggo kowa yasan cewa itama ba a kwance take ba akan lamarin masarautar Basannabas.

“Kuma kin yi aikin kamar yadda na sanar da ke?”

“Nayi wallahi, na yi yadda kika fada. Kawai ni dai ban yadda da bokan nan ba, sake wani zan yi bana san shirme da shiririta a cikin lamarina.”

“Ki dena damun kanki kar ki janyowa kanki wata matsalar. Zanje wajan shugaban yan bori, zan sa ya turo aljannun da zasu hanata ganin Salman d’in, ita d’in wa bare wata ta fada. Kin san ni dai bana wasa da duk lamarin ku bare kuma naki shalele na.”

“Shikenan har zuwa yaushe zan ji karin bayani?”

“Zuwa anjima ma zanje.”

“Ina jiran ki.”

Ta maganar tamkar tana yi da bayin ta ko wata kaskantacciya, dan ba zaka yi tunanin da mahaifiyarta take wannan wayar ba. Guri ta samu ta zauna tana maida numfashi, lallai akwai matsala, ba ta nan ma Salman yana ambato sunanta ina ga yanzu ta dawo zata kuma je gare sa tunda matar shi ce, ba ta cikin masarautar ma tazo ganin shi ina ga yanzu da ta dawo kacokam? Dole ta tashi tsaye dan ko ta kan sauran matan gidan da suke yin wasu surkullen tare ba zata bi ba.

Mikewa tsaye ta yi tana son ganin Salman a wannan lokacin kafin naje. Ta shirya tsab tare da dora alkyabba, Jakadiya na gurin da ta barta, suka fito tare tana ta yi mata fadanci, bayi kuma suna biye kamar wasu jeluna. Gabanta ne ya buga hango Gwaggo ta Fada na fitowa daga sashen Sarki Salman, tunani barkatai suka dinga yawo a ranta har suka hadu ta gaishe da Gwaggon a tsaitsaye ba wani girmamawa bare mutunci, haka ta wuce tana tsine mata. Gwaggo kuwa girgiza kai tai taja hannun Adda Maryama suka wuce mota.

Mamaki ne ya kamata ganin Sarki Salman akan sallaya, alamar sallah ya yi. Rabon da ta ga ya yi tun lokacin da ya kwanta wannan ciwon, sai dai ya yi a kwance ko a zaune, yau kam akan kafafuwansa yake yi cikin nutsuwa kamar ba shi ba. Guri ta samu ta zauna tana karewa bedroom d’in kallo, so take ta gano abinda su Gwaggo suka ajiye ko su ka aiwatar amman duk jarabarta ba ta ga komai ba. Taga ya daga hannu sama yana addu’a, tasan be saba yi a fili ba, amman yau kamar wanda aka budewa makogwaro haka taji yana zuba addu’a wacce tasa ta tsarguwa, inda yake cewa.

“Allah duk wani mai nufi na da sharri ban yi masa komai ba, ka mayar dashi kansa. Allah kasan abin da yake zuciyar duk wani abin halitta, kasan masu yi min makirci, ka hana su jin dadi kamar yadda suka gana min….”

Baki bude ta ke kallansa saboda mamakin yadda ya yi wannan doguwar maganar, nan da nan ta rude ta mike tare da nufar inda yake. Yasa hannu ya riko nata tare da kallon cikin idanunta, abinda be taba yi ba tsawon zaman su. Sai dai kallon yana tattare da abubuwa wanda kwakwalwarta ba zata iya bayyana mata ko menene ba. Ya matse hannunta tare da cewa. 

“Duk abin da zan ce kice amin Shaheedah.” 

Kirjin ta ya kuma bugawa, tana ganin tamkar ita yake tuhuma. 

“Allah ka bani lafiya Shaheedah.” Ta ce,

“Amin honey.”

“Idan yadda nake ji a jiki na, wani ne ya yi min makirci Allah ya yi min maganinsa fiye da abin da aka yi min.”

Bakin ta ya shiga rawa ta kasa amsawa kai tsaye, ganin asirin ta yana shirin tuno wa sai ta fada jikin sa tare da sakin wani marayan kuka tana cewa……

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 32

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 22

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI…..!_…

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…