KIBIYAR AJALI BOOK 2 PAGE 4-5

Advertisement

 

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

BOOK:2

PG: *4&5*

LITTAFAN ZAFAFA NA KUDI NE, MALLAKI NAKI TA NAMBOBIN MU DAKE KASA… KI SIYA HAKKIN KI YAFI DA KARANTA WANDA BA’A BAKI BA.. DON GUDUN…..

Instagram handle: @yerwaincense_and_more

Advertisements

—-

“Honey kayi shiru dan Allah please, wannan duk zafin ciwo ne karka rudar da kanka.”

Ta shiga shafarsa tana kuka wiwi ta yadda zata mantar da shi irin wannan manyan addu’o’in da yake yi, wanda tasan tabbas harda ita a cikin wadanda yake yiwa tunda itama ba kyaleshi tai ba. Ai kuwa ya yi shiru, sai dai be fasa yi a cikin zuciyarsa ba, dan ajin da Gwaggo ta Fada tace ya dinga fada kenan. Salman ya d’an dago da ita jin duk ta sakar masa jikinta, ya gyara zama kansa a kasa ya yi shiru kamar wani mai nazari.

“Kaci abinci ne?”

Ya yi shiru kamar ba zai kulata ba, tsawon lokaci har ta fitar da ran zai amsa sai ta ga ya daga mata kai nufin yaci.

“Zaka sha coffee nasa a hado maka?”

Advertisements

Ya kuma girgiza kai alamar a’a ba zai sha ba. Duk sai ta rasa me za ta yi masa, can kuma ta sake kwanciya a jikinsa tana son yi masa zancen da ya kawo ta gurin shi. Tana shafar kirjinsa ta ce.

“Honey kasan Amaryarka ta dawo?”

Wannan karan sai da ya dan kawar da fuskarsa, ya kuma hade rai tamkar an yi masa maganar mutuwarsa, be ce komai ba har ta sake tambayar shi karo na biyu.

“Gwaggo ta Fada bata gaya maka ba?”

Lumshe idonsa ya yi yana daga kai, Shaheedah ta ji wani abu ya ziyarci zuciyarta na bacin rai. Bata haka ba amman ba komai zata san yadda zatai ta ga haduwarmu ta yi wahala. Salman ya mike ya hau kan gado tare da jan bargo yana jin zuciyar shi na yi masa zugi. Ganin ya kwanta kuma tasan ba kulata zai yi ba yasa ta saurin fita daga cikin dakin tana daukar alwashi kala daban daban.

<<<<<>>>>>>

Ni kuwa ina sashe na ina faman tunanin yadda zan tunkari sashen Salman, akwai maganin da za’a bashi da daddaren nan. Juyi kawai nake yi akan gado saboda rashin mafita, dan bana kaunar naje na dinga tarar da Shaheedah a gurinsa, ba ta da kunya sam, tun ran da ta shigo ina ciki na gano hakan. Sai dai kuma wani barin na zuciya ta da yake tunatar da ni cewa idan fa ban daure na cire tsoro da fargaba ba bazan taba cikawa Gwaggo alkawarin da na dauka ba. Dole ne na tashi tsaye na dawo da Dije Oganniya ta kamar yadda nake a baya. Sai na cire komai da zai sanya min shamaki wajan gudanar da kudurin mu akan duk wasu makirai dake cikin wannan masarautar ta Basannabas. 

Kamar an tsunkule ni haka na zabura na tashi, toilet na shiga nai wanka tare da dauro alwala na fito. Sai da na fara yin sallar isha nayi shafa’i dama wuturi sai cikin dare nake yi, kawai na bude wardrobe ina bin kayan ciki da kallo, zuciya ta na gaya min cewa ya kamata na saka kayan da zasu ruda shi. Wata kuma na gaya min idan ma sun ruda shi ai zai dauka Shaheedah ce, zai yi miki abin da ya taba yi kwanaki, kawai kisa hijabi ma yadda ba zai taba ganin wani abun ba bare ya yi sha’awa tunda daman ba san shi kike yi ba. Kar ki sa kuma wanda zai rai naki, kije garin nuna rashin so ya kuma ci miki mutunci tunda dai baki san manufar da tasa shi ya auro ki ba. Naji wata zuciyar itama ta ayyana min hakan.

“Oh God…!”

Na fada ina dafe saman gushi na. Toh ni yanzu ya zan yi? Mene ne mafita a gare ni yanzu? Duk na rasa ya zanyi ina ta tunani kawai sai idanuna suka sauka kan wani lace pink da ratsin milk color a jiki, na zaro shi naga dinkin riga da skirt ne, na sanya shi a jikina ya kuwa zauna yai das dashi. Alkyabba na dakko na sanya sannan na nufi gurin madubi na gyara fuska ta, duk da ba kwalliya nai ba, nayi kyau ba laifi, nasa janbaki shima pink daga nan na fara tunanin ta ya zan je sashen nashi?.

Adda Maryama na kira dan gabaki d’aya na rasa mafita, tace nasa a kirawo Jakadiya tai min iso a gurin shi. Ta kuma cewa.

“Kin san menene Gimbiyar mu?”

“A’a sai kin fada Adda.”

“Yauwa idan tafiya tai tafiya ki samu duk yadda za ai ki dawo da sauran jakadun guda biyu. Dama uku ne toh sai suka sauke biyun, yanzu kisan yadda zaki wajan ganin sauran sun dawo dan basu kai wannan hada makirci ba, kinga idan suka dawo zaki samu saukin yin wani abu koda waccen bata kusa.”

Kamar tana gabana haka na dinga gyada kai, kafin daga bisani nace.

“Toh shikenan Adda zan kokarta, na gode.”

Daga nan muka ajiye wayar, na mike na fito parlor na samu hadimai na suna ta goge-goge, na aiki guda d’aya cewar taje ta nemo min Jakadiya. Ashe tana can gurin su Gimbiya Jaleela ana ta kulle-kulle kamar an ce dasu duniyar ba zata tashi ba, ko kuma sun dauka cewar za’a barsu har su gama cin duniyar su da tsinka. Bayan tazo ne na sanar da ita bukata ta, cikin tsantsar ladabi ta amsa min tare da tashi ta tafi dan yi min iso. Kin bin ta da man nai saboda koda yake a’a bazan ganshi ba, bazan ji kunya ba, akan na bi bayan ta na dawo da borin kunya.

Kamar an jeho ta daga sama haka ta shigo cikin parlorn, ta ce Waziri yace zan iya zuwa. Na tashi bayi ba suka rufa min baya, ina tafiya suna biye daji duk sai naji wani iri, kamar wata marar gaskiya da za’a raka prison. Na tsaya na kallesu cike da kulawa nace su tsaya a nan naje na dawo, dan har ga Allah bana son wannan bibiyar da suke yi mun. Babu yadda suka iya dole suka bi umarni na, ni kuma da Jakadiya muka nufi sashen sarki Salam.

   

Muna zuwa muka tarar da su Waziri da su Shamaki su Galadima sun fito, na duka na gaishe su cike da ladabi, wasu sun amsa ya yin da wasu banji sun bude koda baki ba duk da ban san su ba kuma ban kalle su ba ballantana na gane fuskokin su saboda kai na yana kasa. Sai da suka wuce sannan na mike tsaye tare da juyawa na bisu da kallo har suka fice. Kasan cewar nasan inda yake a kwance yasa na kalli Jakadiya tare da yi mata godiya, na dai nuna mata tsananina da ita iya nan ne bana son ta bini ciki dan naga take-taken ta na son bi na ciki.

Na tsaya a bakin kofar bedroom d’in na zaro jarkar dana boye mai dauke da ruwan magarya, nai addu’a sosai kafin na sanya kafata baki na dauke da sallama. Babu kowa sai shi kadai a kishingiɗe kan gado, be kallo bakin kofar ba bare na saka ran zai amsa min sallamar da nayi. Haushi ya kamani, sai kace wani kurma, a zaune yake ido biyu amman saboda mulki yana ji ana sallama ba zai amsawa mutane ba, naja tsaki a cikin rai na ina karasawa gurin shi cikin taku na isa da kasa ita. Lumshe ido naga ta yi yana dan daga fuskar sa, da alama kamshin turaran wutar da ke jikin kayana yake shaka, duk da cewar be nuna ba.

Kallansa nai na sakar masa harara a zuciya ta nace ‘kaji dashi ni ba bata min rai zakai ba’ kawai ma sai na shiga neman burner bayan na ciro garin maganin da zan yi masa hayaki amman ban samu ba. Shi kuma har lokacin be bude idanunsa ba, nai ta dube-dube har Allah ya taimaka na ganta a can wani guri aka ajiye ta na musamman da ba zaka taba zaton ita bace. Na zuba su garin habbatussauda din nan dakin ya fara canzawa daga kamshin da yake yi ya koma kauri, dalilin da yasa Salman saurin bude ido yana toshe hanci. Na kalle shi naga sai faman yatsina fuska yake da alamar kamshin be yi masa ba.

“Ke! Mene haka?” 

Yayi maganar a dan rude. Na sake zuba garin hayaki ya kuma turnukewa ina cewa.

“Magani ne.”

“Bana so please fitar min dashi.”

Ai kamar ya sake zuga ni sai na kara karawa, ya kuwa shiga yin tari da atishawa ba kakkauwa, still kuma hancin sa yana toshe da tafin hannunsa, na ce.

“Shi magani ai ba dan so ake yin sa ba.”

“Please bana son wannan warin, ki fita da shi nace.”

Nai masa banza, na karasa bedside d’in sa na dauki glass cup na zuba masa ruwan addu’ar nan, na dan matsa kusa dashi tare da mika masa ina cewa.

“Karbi kasha.” 

Kai tsaye yace dani.

“Bana sha.”

“Karka ce haka idan ba haka ba zan je na sanarwa da Ammi.”

Kalmar Ammi da na fada ne yasa shi saurin dagowa ya kalle ni karan farko tun shigowa ta dakin. Bakin sa na rawa yake son yin magana amman ya kasa, cikin ransa kuwa tunani yake a ina ma yasan wannan sunan? Babu shakka ya taba jin wannan sunan har ma yana tunanin ya taba alaka da mai irin sunan amman kuma ya kasa tuna a ina ne, yaushe ne kuma wacece hakan. Gabaki d’aya ya saka hannunsa ya dafe kansa yana wani irin cije baki kamar irin wanda ya ke kukan shiga uku nan.

“Karbi kasha dan Allah.” Na fada ina mika masa kofin. 

Sai kawai ya kalli kofin amman be karba ba ya tsaya kamar wani me tunanin wani abun. Ganin haka yasa na daure na zauna kusa dashi tare da jan munfashi na sauke, hannunsa da ya dora a kansa na janyo tare da kokarin sanya idanuna cikin nasa amman yaki bari hakan ta faru, na ce.

“Ashe haka kake? A waje idan kana yawo tamkar wani sarki mai cikakken iko. Amman a cikin masarautar ka sai ka zama tamkar wani lagwani wanda sai yadda aka sarrafa shi why? Naji tarihin yadda mahaifinka ya gudanar da mulkinsa, cikin isa da iko, amman kai sai yadda akai da kai me yasa?”

“Nima ban sani ba.” Ya fada cikin sauri.

“Naji toh karbi kasha wannan zaka ji dadin jiki da zuciyar ka.”

Na fada tare da kai kofin sai tin bakinsa, amman ya kawar da kai alamar ba zai sha ba. ‘yau na ga taurin kai’ na fada a rai na. Wai duk dan saboda ya sha, sai na sake matsawa kusa dashi har jiki na yana gogar nashi, na kwanto da kansa saman kirji na ina shafa lallausan gashin kansa, murya kasa-kasa na fara masa magana cikin taushin harshe.

“Kayi hakuri komai lokaci ne kuma jarabawa ce daga Ubangiji, daure kasha wannan magani ne da aka yi shi da ayoyin ubangiji na waraka. Kayi bismillahi tare da kyakkyawar niya ka daure kasha kaji sarkin sarakuna…”

Sai ya bude bakin bayan ya rintsa ido na saka mishi ya sha har ya shanye, ya fara kakarin amai na dinga shafa masa bayan shi har Allah ya taimaka be yi aman ba. Ganin yasha yasa na zame jikina na daga nasa, na yalle ni na kawar da kai dan kar ya yi zaton zama nazo yi a gurin shi. Ya yi shiru yana ta tunanin yadda zai tambaye ni wacece Ammin amman bakin sa ya gaza budewa, ya kasa min zan cen har na tashi tsaye na cire alkyabba ta na shiga bathroom ya bini da kallo.

Tsab yake ga wani kamshi da yake tashi mai daɗin gaske, na dakko wani d’an bokiti na fito, yadda na barshi haka na dawo na tarar da shi, sai dai idanunsa yana kan kofin da na gama bashi ruwan maganin nan. Ko me yasa ya kura masa ido oho, ni dai nasan ban yi abin da zai cutar dashi ba, idan na cutar da shi me zai tsinana min? Buri na kawai ya samu lafiya ya gaya min dalilin da yasa shi aure na har ya wofin tar dani tsawon lokaci. Ruwan jarka na dakko tare da nufa inda yake na ce ya taso ya yi alwala ya dena zama babu ita ko a wane irin yanayi yake ciki.

Sam ban yi zaton yana iya mikewa tsaye ba, na dauka yana yin komai a kwance ne ko a zaune. Babu musu kuwa ya dago ina zuba masa yana yi har ya kammala, na dauki ruwan naje na zubar. Bayan na dawo na zo zan dauki alkyabba ta tace daukar ni inda kika ajiye. Na gama kalle-kalle na a dakin ban ganta ba, daga karshe dai na mayar da kai na gare shi sai na ga kamar be san ina ne man abu ba dan ko kula ni be yi ba.

“Ammhh dan Allah riga ta fa, ka ganta ne?”

Da mamaki sai ta kalle ni yana tsuke fuska amin da ban yi zato ba. Kamar ba zai ce komai ba, sai naji yace.

“Ban da ta jikin ki?”

“A’a no ba ita ba, alkyabba ta fa da na cire lokacin da zan shiga bathroom. Ina tsammanim kamar a nan na ajiye ta wallahi.”

Na karasa maganar ina nuna gefen shi dan ina ji a rai na tabbas a nan na ajiye ta. Ya tabe baki ina kallonsa, sai wani tsuke baki yake yi. Lallai mutumin nan wai yana nufin be ga rigar nan ba? Daga ni fa sai shi tsabar wulakanci da rashin mutunci, daman nasan ba wani ganin girma na yake yi ba bare ya bani matsayi na na wacce ya auro. Zuciya ta ce ta dinga ayyana min cewar shi ya dauka ya boye cikin bargon da ya rufe kafafuwansa da shi. Sai da na shammace shi sannan na janye bargon, abin mamaki babu alkyabbar nan sai santala-santalan fararan kafafuwansa da kwantaccen gashi ya lullube fatar, banda sheki babu abin da yake kamar ana yi masa stretching.

Haushi ya dada kamani saboda ina son tafiya dare yana yi, kawai na yanke shawarar gwara na tafi a haka tunda dai an samu aljani ya shigo ya ɗauke rigar. Juyawa nai zan tafi saboda na gama abin da zan yi sai kuma zuwa gobe insha Allahu, har sai da na kai bakin kofa ashe yana lura da abin da nake shirin yi, naji muryarsa yace.

“Ke!”

Kamar ba zan tsaya ba saboda ba suna na bane ke, amman sanin da nai da ni yake kuma yana da ikon ya yi min ko wane irin inkiya ne matsayin sa na miji na. Duk da na tsaya amman ban juya ba cak nayi ina jiran jin abin da zai ce, still ya yi shiru sai na kuma yin taku daya da nufin ci gaba da tafiya, ya sake yin magana.

“A haka zaki fita?”

“Ya zan yi to, rigar da na doro an samu aljani ya shigo ya dauke. Zan zauna anan ne ga dare na yi.” Ya ce.

“Haka zaki bar min daki da wannan kaurin?”

“Toh ai nagani ne.”

“Please bana son warin.”

“Gwaggo ta Fada tace a haka za’a dinga barin ka, saboda ai warin shine maganin.”

Salman ya yi shiru yasan tabbas akwai matsala a barshi cikin wannan hayakin, ko bacci ba zai iya ba, dan haka dole kodai tasa masa turarukan wuta ko kuma ita d’in da zauna a gurin shi ya dinga shakar kamshin jikinta. Amman ba zai bari ta fita a haka ba babu mayafi kuma akwai bayi, fadawa da sauran mutane.

Gashi girman kansa ya hana shi tashi ya hanata tafiya,

 “Dan Allah zan tafi….Kaji..?”

Yadda naja kaji dinnan sai da tsigar jikin sa ta mike, Yayi sakatoto yana kallo na yasa nayi gatsine ina murguda masa baki,

 “Dare yana yi ne please.. Inason na koma nai bacci.” 

Shiru ya min ya koma ya kwanta akan pillow, Ganin irin renin hankalin daya mun hakan yasa nai hanyar ficewa, Taku d’aya biyu ban san ya akai ya sakko daga kan gadon ba, sai naji ya riko ni…Banmasan ya akai ya mike ba. Na bishi da kallon mamaki, ashe yana iya mikewa da sauri ban sani ba? 

 “Are you out of your senses..? Zaki fita a haka.”

Yana magana yana nuna kirji na da hannun sa tsabar iskanci ko ina ruwan sa? 

 “To ya kakeson nayi? Ni bacci nake ji, Kuma ni bazan kwana anan ba saboda akwai abubuwan da nake son aiwatarwa. Ahto!”

“To jeki mu gani..”

Na kuwa juya dan har ga Allah na kagu na koma sashe na. Ganin zan fita dagske ya kamo hannu na da sauri, wani irin shock ya ziyarci kowannen mu na kwace da sauri ina kallon gefe,

 “Meye haka…?” Ina fada ina gatsine. 

“Zo Ki kashe wannan warin… I hate it! It smells awful..”

“Magani ne.. Gwaggo Ta Fada ce tace lalle na saka..”

“Oh please…”

Komawa yai gefe yana toshe hancin sa da handkerchief, Idanun sa sun kawo ruwa sosai, Da alamun dai dagaske baya son hayakin. Na kuma yunkurin Ficewa ya dakatar dani,

 “Zo nan..”

Sirrin tsaki na saki a hankali na koma nesa dashi na tsaya, Can na zauna tunowa da shi din sarki ne, Ac sai duka na take, Take bacci ya fara dauka na. Na bingere ina lumshe idanu, 

Ganin tayi bacci Salman ya mike ya koma inda take,Kallon ta yake sosai, A hankali yasa hannun sa ya gyara mata kwanciyar da tai kar wuyan ta ya sage, Hannun sa yasa ya shafa kwantaccen gashin kan ta ahankali, wani irin kallo yake mata wanda bai taba yiwa wani ba, Can kamar an tsukule shi ya dora tausasan labban sa akan kumatun  ta ya sakar mata kiss…

Dai dai lokacin da na mike zumbur, Ji nai tamkar an doramin abu me ruwa a kumatuna, Ganin yasha kunu a gefe bansamu damar tambayar sa ba,  Na mike ina murza idanu na, Indai ba magagin bacci nake ba tamkar dai Salman ba a inda nake yake a zaune ba, Fuskar sa a murtike ya mike. 

Komawa yai inda yake zaune ya daga pillow sai ga alkyabbata awajen. Da sauri naje na dauka na zura na fuce na barshi inda yake, Dan renin hankali kawai, Saka alkyabbar nayi na fice na koma sashe na. Abdullah na gani a tsaye yanata yiwa hadimai na masifa kan lalle sai sun fitomin da kaya na, shi kuma ya shiga ciki tunda ai sashen sa ne…

Mamaki ya kamani ganin yadda ya tsare bayina wadanda suke a durkushe a gabansa kamar zasu masa sujud. Sun sanar da shi cewar amaryar sarki ce a bangaran yace musu besan da wata amarya ba shi Shaheedah kawai ya sani matsayin matar sarki. Ina shiga muka hada ido, ya kalle ni na kalleshi ya juya ya kalli bayin yana tambayar su cikin tsawa.

“Kai wai wannan wacce ce ne a cikin masarautar nan?” Duk suka yi tsit ya daka musu tsawa wacce tasa d’aya daga cikin su yin magana.

“Allah ya taimaki yarima, wannan itace amaryar sarki mai wannan sashen.”

“What…?!”

Ya furta a razane idanunsa a waje, banda kallo na babu abin da yake yi. Na kalli hadiman nawa tare da sallamar su nace su tafi, sannan na maida hankali na kansa tare da yi masa kallon sama da kasa nace.

“Kasan dai ko fita aka ce wani ya yi a cikin mu sai dai kai ka fita, saboda ni Yayar ka ce a yanzu. Kaji ka samu dan uwanka yasan yadda zai yi da kai.”

Ashe duk wannan abun baya cikin hankalinsa ni ban sani ba sai da naga ya yo kai na gadan gadan yana niyar shako ni. Ganin yana tangadi alamar yashayo abar, yasa na matsa da sauri ina dafe kirji. Tunda nake ban taba ganin dan maye ido da ido ba sai dai a film ko a labari. Cikin tashin hankali nake kallonsa baki na yana rawa na ce da shi.

“Subahanallahi menene haka?” Cike da rai ni na nuna rashin hankali yace.

“Sai na yi maganin ki, zaki san da wa kike magana.”

Ya yi tangal-tangal ya fada kan kujerar da ya taso, take bacci ya yi awan gaba dashi. Kai na dafe ina mai tausaya masa, wannan wace irin rayuwa ce ace duk cikin yaran ka babu na kalla kaji dadi? Lallai Ammi tana ganin rayuwa, kaddarori kala daban-daban ita kam ta gansu. Amma komai nisan dare gari zai waye…!

Littafin kibiyar ajali yana tafe da wani irin salo na daban…. Sannu a ahankali komai zai warware kansa. Salman&Khadija2021❤️❤️

..

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 28

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 32

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 21

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR…

KIBIYAR AJALI 18

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…