KIBIYAR AJALI BOOK 2 PAGE 6-7

Advertisement

 _

ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE.. INA KUKE YAN UWA NA MATA? TO KU MATSO KUSA DOMIN GA DAMA TA SAMU.. KAI BAMA MATA KADAI BA, HAR IYAYEN MU MAZA, ZAKU IYA KAWO SISTERS DINKU, DAUGHTERS DA MA WIVES DINKU. KAI HARDA BAE DA KE SHIRIN ZAMA MRS🤩😉…!_

_UMMU AYMAAN’S KITCHEN, UMMU AYMAANS’S KITCHEN, UMMU AYMAAN’S KITCHEN…_

_INA YAN UWANA MASU SON SU KOYI BAKING DA DECORATIONS? TO NESA TAZO KUSA.. UMMU AYMAAN’S KITCHEN ZATA KOYAR DA MATA MASU SON SU KUYI BAKING DA DECORATIONS NA KWANAKI BIYU. AKAN FARASHI ME RAHUSA, NAIRA DUBU 6 KACAL, (6k)._

 

_ZATA KOYAR NE A UNGUWA UKU LAYIN MAIFATA, ZARIA ROAD KANO.. PRACTICAL CLASS NE, SANNAN AKWAI GARABASA DA NA NESA DAKE SON SU KOYA SUMA ZASU IYA KOYA TA ONLINE DUK AKAN NERA DUBU SHIDA KACAL, DUK ABUNDA YA KUNSHI BAKING ZATA KOYAR KAI HAR MADA BONUS NA DECORATIONS._

Advertisements

  _*CLASSES DIN KWANA BIYU NE, AKWAI PRACTICAL DA ONLINE, CLASSES DIN ZA’A YISU NE RANAR 5 DA 6 GA WATAN YUNI WATO 5&6 OF JUNE (NEXT MONTH)RANAR WEEKENDS ASABAR DA LAHADI*_

_* 2 DAYS DEMO CLASS ON BIRTHDAY CAKE.. (BAKING AND DECORATIONS)* YAR UWA HANZARTA KI BIYA KI KOYA KEMA KIN HUTA DA BIYAN BAKERS, DA KANKI ZAKI IYA YIN NAKI, DA DUBU 6 ZAKI IYA BIRTHDAY CAKES KALA KALA, WANDA BA KARAMAR SANA’A BACE, IDAN YARAN KI KO KANNENKI ZASUYI BIRTHDAY KIN HUTA SIYA SE KEYI DA KANKI, KIYI KI BIRGE MAI GIDA AS SUPRISED GIFT.. INA YAMMATA? IRIN CAKE DINNAN ME HEART KI KOYA KIYI KI BAWA BABYN BABY🥰 LOVE IS LIFE, CAKE IS LOVE🙃._

_BA ANAN KADAI TA TSAYA BA, TANAYIN DUK WASU MOUTHWATERING SNACKS AND CONTINENTAL DISHES😋, AKWAI NA YAN GAYU IRIN SU CAKE PARFAIT, CUPCAKES, SAMOSA, SPRING ROLLS, MEAT-PIE, DOUGHNUTs, DUKA WADANNAN TANAYIN SU NE NA BUKUKUWA, SUNA, SHAGULGULAN TARO, KAI DAMA NA CI HAKA KAWAI😋_

_BA ANAN KADAI TA TSAYA BA, TANA CLASSES NA GIRKIN ZAMANI DANA GARGAJIYA, MOUTHWATERING DISHES NA YAN GAYU, MESA KISHIYA KWAFA, WANDA FACCALA ZATA DINGA CIZON YATSA, IRIN HADADDEN GIRKUNA MAI SA KUNNUWAN MAIGIDA SU MOTSA. KAI HARDA NA BUKUKUWA KUNA IYA ORDER TA MUKU SHI_

_INSTAGRAM HANDLE DINMU:_ Ummu_aymaan_kitchen

_DOMIN KIRAN NAMBAR TARHON MU DAN KARIN BAYANI DA BIYAN KUDIN SHIGA SAI A TUNTUBEMU TA: 08032964266_

Advertisements

_MUNA TURA KAYAN SNACKS DINMU A KOINA A FADIN NIGERIA, 100% TESTED AND TRUSTED.._

_UMMU AYMAAN’S KITCHEN IS YOUR NO 1 STOP KITCHEN FOR MOUTHWATERING DISHES, BAKES AND SNACKS_

____

_*KIBIYAR AJALI….🧚🏻‍♂️🥰*_

_(SULKE BAYA TARE TA, SAI TA WUCE..)_

_BOOK 2_

_PG:6 & 7_

_LITTAFAN ZAFAFA NA KUDI NE, MALLAKI NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, KI GUJI KARANTA NA WANDA BA’A BAKI NA DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA DAMA MASU RUBUTAWA_

….

Cikin tsananin tashin hankali sai ga Ammi ta aiko a kirawo ni, Kila wani ne ya sanar mata halin da ake ciki. Tafiya nayi, Sashen nata Ina zuwa ta kamo hannu na muka shiga cikin dakin ta . Bata saki hannu na ba har sai da muka karasa kujerun dake harabar dakin. Cikin tsananin tashin hankali ta shiga ban hakuri,

 “Kiyi hak’uri Khadija.. Dan Allah s..”

“Dan Allah kiyi hak’uri Ammi Kiyi shiru, Nasan komai, Kuma wallahi nagane ba a hankalin sa yake ba. Insha Allah nan gaba kadan komai zai daidaita da yardar Allah..” Na karasa fada ina mai rik’o hannun ta na zaunar da ita a kujera, Na koma na dakko ruwan sanyi na zuba a cup na mika mata. 

“Sha Ammi.. Ki kwanta dare yayi.”

Murmushi tayi da alamun taji dadin maganganu na. Daga kasa na nemi waje na zauna, Tv na kunna na kai tashar karatun AlQur’an, A hankali sautin kira’ar sudeis ya dinga tashi. Haka muka kusan raba dare da Ammi, Sannan tace naje dakin gefen nata na kwana aciki. Ba musu na mike don wallahi bacci nakeji, Sai da nayi sallar nafila sannan na kwanta, Bacci mai nauyi ya dauke ni…

Wasa wasa, Sai da na kusa shafe sati biyu a sashen Ammi, Kemadagas Abdullah ya kafe kan wallahi ba zai bani sashen sa na zauna ba aciki ai nasa ne. Ban wani damu ba, Saboda dama wajen Ammin yafimun dadin bacci cikin kwanciyar hankali. Bansan wanda ya gayawa Sarki Salmaan bana kwana a sashe na ba, Ranar wata sanyayyar asabar da asubah naje turara magani kawai ya same ni da maganar…

Kasa kasa ya shiga kallo na ina hankalce dashi,

 “Ancemin bakya kwana a sashen ki, why? Aina kike kwana.”

“Sashen Abdullah kasa aka kaini… So yanzu ya dawo yana bukatar wajen sa. Awajen Ammi nake kwana, Da magana ne?”

Na bashi amsa a gatsine haushi yake bani, Sanyin sa yayi yawa kamar ba sarki ba. Shiru yai yana danna ipad dinsa can ya dago yace,

 “Ki shirya komai naki… Duplex (ginin bene) din dake kusa da wannan an gama gina shi, Ki kwaso kayan ki ki dawo..”

Na gwalalo idanu ina girgiza kai,

 “Akan wane dalili? Gaskia gaskia banason nan, Kayi hak’uri.”

Wani kallo ya watsamin ya ajiye ipad din hannun sa, Mikewa nai daga gefen da nake nai hanyar fita ina mai ajiye burner din dake hannu na. 

 “Ke zo nan..”

Ya fada cikeda kasaita, Wai ke! Seka ce yar aikin sa, Na tab’e baki na tsaya inda nake ban jiyo ba. Takowa yai har wajen kofar da nake, Na matsa can karshen k’ofa na takure, Kasa jure kallon idanun sa nai dake saqale ta cikin gilashi. Yasa hannu biyu ya tokare ni a tsakiya yana taune k’asan leben sa,

 “Kikace me? Maimata abunda kikace.”

Na hadiye kakkauran abu a wuyana, K’amshin turaren jikin sa da nawa suka hadu suka bada wani kamshi na daban. Nadan kauda kai na gefe kirji na sai dukan uku uku yake. Bakin sa ya kawo daidai kofar kunne na:

 “Scaredy cat.. Me kike cewa?..” 

Shiru nai kaman an jika dan tsako a ruwa, Sai raba idanu nake. Banda iskanci meye namin haka? Numfashin mu sai had’uwa yake yi. Na takure hannuwa na a kirji don na lura kamar yafi kallon sama na. Yadda glass dinsa yake kallon saitin wajen.

 “Kwalelanka dai wallahi..”

Bansan nayi sub’utar baki na fada ba..

Murmushi yai kawai yana nuna ni,

 “Mekika ce?”

Na shiga girgiza kai ina kara matsawa jikin kofa Sosai,

 “Ki hada komai naki… Ki dawo sabon ginin da akeyi.. Kafin ma..”

Bai karasa ba aka turo kofar da sauri ya koma baya yana sosa k’eyar sa. Shaheeda ce ranta a matuk’ar bace,

 “Honey… Me naji kana cewa? Kunnuwana ne suka jiyemin ba dai dai ba ko kuwa? Bangane ba..? Wane gida zata dawo? Nace wani gida zata dawo?”

Ta karasa fada a dan tsawace, Na tsaya ina binta da kallon mamaki, Toshe kunnen sa d’aya yai da yatsan sa karami,

 “Haba.. Banason tsawa please.. Shaheedah! Meye haka?”

 “Meye wani meye haka? Hakan ce ta kawo haka Salman, Bangane cin amanar da kakemin ya wuce tunani na ba sai yau.. Ta dawo sabon gidan fa kace, Lalle ka taro babban balai. Kana nufin kace dama mallakinta ne ko kuwa.”

Bai amsa taba ya koma kujera ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, Na lura mutum ne shi marar son hayaniya. Gashi ita kuma tanada kwakwazo da mita.

Kallo na tayi ta zabga min harara, Zan rama kenan naga ya dago glasses dinsa yana kallon mu, Na fashe da kuka ina mai komawa jikin kofa, Nasa hannuna na dora kai na akai ina kuka.. Ya mike da sauri ya yo waje na yana dafa kafadata,

 “Menene… Uhm? Meta miki? Eh..!?”

 “Kutmar kan babban balain can, Ke ni zakiwa sharri? Uban me nayi miki! Kai kuma sannu sharukhan baban soyayya, Daga ta fara kuka ka mike jiki na rawa kana tambayarta, To koma ka zauna bamu gama magana ba…” 

Zai koma kenan, Nayi sauri na rik’o hannun sa, Ni zata nunawa isa? Lalle zan nuna mata na ninkata a kissa.. Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya, Na rintse idanu na fada kan faffadan k’irjin sa, Duk da yanda gabana yake faduwa abunda bantaba yi ba, Haka na cije don karta gane ba abunda ya taba shiga tsakanin mu. Shi kansa Salman yayi mamaki, Na zagayo da hannu na ta kugunsa na rike shi sosai, Ahankali na kwantar da kai na akan kirjin sa, Na barwa banza ajiyar ta.. 

Wani shegen marayan kukan shagwaba na saki da har sai da Shaheeda taja dogon tsaki tana cizon yatsa, 

 “Ke ni zaki nunawa bariki.. Kai kuma ka tsaya sakatoto mace na maka makirci. Salman magana nake..”

B’angaren  Salman kuma kasa cewa koma yayi, Ga kyakkyawar rungumar da Khadija ta bashi mai ratsa magudanar jini da tsoka dan dadi, Gashi k’amshin turarukan jikin ta sai kara saka masa kasala suke, Bugun zuciar sa sai kara yi yake yi… Da sauri da sauri, Zuciar sa bata taba bugawa wani dan adam haka ba fyace Khadija.. Dama ita kadai ransa da zuciar sa kai harda jikin sa suke begen samu. Wani lokaci kalilan yake jira ya bayyana mata komai, Amman yanzu ba zata taba ganewa yana kaunar taba. 

Shaheeda tasa hannu ta janyo shi cikin izza da bacin rai,

 “A gabana? A gabana zakuyi bariki, Ba’a haife ki ba wallahi. Ke ba ki isa ki shigo ki raba ni da miji na ba.”

Ahankali ya hanya hannaye na ya koma kan kujera ya zauna, Daman nasan ai badan na ri’ke shi ba saki na zaiyi, Nan gaba kadan zaka zayyanemin abunda yasa ka auroni, Sannan kaban hak’uri da doriyar takardar saki na. Bazan iya auren wulak’anci ba. Yanzu ma inayin hakane sahada Shaheedah, Idan ban muna ba wata kofa a tsakanin mu ba to zatai saurin shiga tsakani. 

Gefen inda yake zaune ta zauna tana shafa fuskar sa da hannun ta na dama,

 “I’m sorry please, Kasan idanuwana da zucia ta bazasu juri ganin ka da wata ya mace fyace ni ba. Uwa uba waccen low class din. Da har take ganin zatai takara dani.. jokes apart maganar ginin can. Karka sake yinta. Ni acikin week dinnan zan dawo ita ta koma sashe na, Karka manta nice matar ka tafarko my love..”

Daria abin yaso bani, Yadda yake kallon agogon hannun sa yana cije lebe da alama ko sauraranta ba yayi. Nima agogon dake saqale ajikin bango na kalla ganin karfe 7 Saura kwata na safe yasa na matsa kusa dasu, Caraf na zauna akan cinyar sa, Dai dai saitin kunnen sa na shiga fada ahankali yadda zata iya jiyowa,

 “My whole world….”

Dak’yar na karasa shi kansa Salman Sai da ya kware na bubbuga bayansa saboda tsantsar mamaki, Shaheeda kuwa tacika tayi fam zata fashe..

 “Uhm.. Ashe dagaske kake agaban matar ka ba zaka iya kira na da sugarplum ba.. Anyways! Ni zan koma sashe na, Nagaji sosai kasan jiya bamuyi baccin kirki ba anata abu d’aya.. Zan dawo later mu karasa daga inda muka tsaya.. Oh yes maganar sashe na… Zan dawo ayau ba sai next-week ba. Bye. Ka kulamin da Kan ka..”

Light kiss na sakar masa a gefen kumatun sa na fice da sauri ina kambama kokari na, Ina jiyo kwakwazon Shaheedah tana surfa zagi da masifa, Na gimtse daria ta na koma sashen Ammi.. Ni kai na nayi mamakin acting dina.. Dole na bawa Addah Maryamah labarin abunda ya faru, Don duk koyarwarta ce. Sai karin rashin tsoro na na dije Oganniya.. ‘kaya nake bansan na gida ba. Oganniya yar baffanta.. Ta gajiyalle mai yar hakiya…! 

      Tamkar sabuwar mota haka shaheeda tafice daga sashen Salman zuwa nasu gimbiya Huwaila, Tana tafe tana share hawayen takaici. Lalle Khadija ta taro World Cup, Zatayi dana sanin shiga ragarta. Shi kuwa Salman bawan Allah shiru yayi yana nazarin kalaman Khadija, Yasan duk dan saboda takonawa Shaheedah rai ne tayi haka.. Amma meyasa nayi haka? Ya taambayi kansa.. Saboda kana kaunar ta. Zuciar sa tabashi amsa. Kishingida yayi akan kujerar sa yana shafa inda ta sumbace shi, Daya shafa sai yai murmushi kamar zararre. Dak’yar ya iya mikewa ya hau sama.. Aka shirya shi ya shiga fada.. 

       *FADAR SARKI SALMAAN ALIYU SALMANU*

..

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 22

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR AJALI…..!_…

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…

KIBIYAR AJALI 23

Advertisement   __I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…