MIN QALB 42

Advertisement

 

MQ 42_*

 

 

Da lakabe anty zarah takai kanta cikin daki sbd dishi dishi da idanuwanta ke ‘dan gani hakama kaf kuzuri da qarfin qafafunta sun Gama sarewa tun kafin ta Isa bakin gado ta zame ta zauna tareda sakin wani wahalallen kukan dakeson fito Mata tun lokacinda MAHMOUD yabude baki yafara Mata mgn.

 

Shikuma fridge ya biya ya dauko freshmilk me sanyi da ruwa ya nufi bedroom dinsa yanajin wani irin walwala da nutsuwa na qadatuwarsa.

Har lokacin kwance take cikin lullubin data rufe jikinta da Babu riga tayi zuciyarta na qoqarin zuqar numfashin dake neman gagararta,

Advertisements

Tasan tabbas anty zarah ce tadawo shiyasa ya, yafi kowa@’ try da kansa and xa

zuwa ga bude Mata qofa batareda yasamu ko damar ce Mata Yana zuwa ba,

7 ya tube yashiga bai wani jima ba yafito ya sanya kayan bacci kamar koyaushe farare tas dasu yazo ya zauna Yana duba saqonni ta laptop da aketa kiransa akai yanashan freshmilk data rage sanyi yanayi Yana kallonta cikin kulawa tunaninsa tayi bacci.

 

Rufe aikin yayi ya miqe tareda qarawa AC din dake aiki qarfi sbd lullubin dazaiyi shima ya nufi gadon yahau tareda shigewa duvet din inda fatar bayanta da Babu komai ta hadu da fatar qirjinsa dake bayyane sbd rufe botiran rigar baccinsa da bayayi a qaida.

 

Rufe idanuwa da qarfi tayi zafin zuciyarta na tunzuro Mata da fitar da yayi dazun ta yunqura zata matsa daga jikinsa saiga wayarsa na qarar data sanyasu tsayawa su dukan musamman ita data gama sanyawa ranta Anty zarah ce sbd idan ba ita matarsa ba waye zai kirasa cikin dare daidai wannan lokacin.

 

Shi Sam baida niyar ko kallon wayar sbd Koda Rana ma daukar wayarsa ganin dama ne bare yanzu da dare,

Katsewa Kiran yayi yakai hannu ya dauko wayar da niyar kashewa saiga shigowar massage daga umman zarah ne ya tashi zaune Yana duba Kiran daya katse yaga ita ‘dince takira saiya koma ya bude massage dinta,

 

“_Mahmoud Dan Allah kaje kayi mgn da zarah ka fahimtar da ita qarin aurenka ba Wai qarshen rayuwarta bane tanata kuka hankalina yatashi nakasa samun nutsuwa nasake kira Bata dagaba morethan 8times. _”

Advertisements

 

Yana Gama karanta saqon ya ‘dan dafe goshi Yana Jin tun yanzu kamar kansa na neman qullewa,

Ta Yaya zarah zata damu kanta da kuka Bayan bawai yanxu ne akai aurenba,

Auren da shekara uku yanxu Amma tanason saka Masa ciwon Kai ga Amatun ma yaga alamar ita buga kansa zatayi ma da rigimarta.

 

Bai sake kallon Amatun dake kwanceba har lokacin taqi motsawa ya sauko Kan gadon ya zura slippers tareda aje wayarsa ya fice dakin.

 

Yana fita ta rintse ido sai alokacin hawayen dasuka bushe Mata suka Fara gangarowa ba qaqqautawa

Zuciyarta wani irin radadi da bugu takeyi kamar zata fasa qirjinta,

Wannan wace irin qaddarace tahadata auren Dame Mata,

Wace irin masiface wannan takejin kanta ciki sbd tiririn dake fita daga qirjinta Jin takeyi gwara ta mutu tabi Dr khalil dinta ba aure da wannan masifa,

Uban me yasa zai ajiyeta Dan ya ringa barinta Yana tafiyarsa saikace wata Mara sanin ciwon Kai.

 

Ta sauko daga gadon tabar dakin ma takasa sbd Sam ko qafafuwanta bataji ajikinta sbd rufewar zuciya,

Hawayentane ke tsananta gudu suna jiqa pillon da kanta yake kai.

 

Tashi zaune tayi ta kalla agogo idan tana qirgen mintuna daidai to yafi mintuna talatin da barin dakin.

Tana Nan zaune idanuwanta na sake rinewa har tsawon awa daya da mintuna ta miqe tsaye ta janyo towel ta daura ta nufi qofa ta fice bayan ta share idanuwanta dasukai jajir ta nufi dakinta.

 

Tana Murda qofar dakinta Yana fitowa dakin anty zarah din ko kallon inda yake bataiba ta shige kafin ta rufe saigashi a bayanta Yana kallon idanuwanta dasuka bayyanar Masa da halinda take ciki ya riqo hannunta ta janye batareda ta dago ta kallesaba ta nuna Masa qofa tace”

 

Bacci zanyi can you leave please.

 

Kallon fuskarta yasakeyi yanason ta kallosa su hada Ido Amma taqi saima gado data nufa ta haye zata kwanta cikin qosawa da fitinarsu yace”

 

Akan zarah ne??

 

Tsayawa tayi tareda dagowa tayi Masa wani irin kallo sai alokacin shedan ya lurar da ita kamar rigarsa jikinsa tayi squeezing ta maido kallonta Kan fuskarsa tace”

 

Meya kawo sunan anty zarah anan?

And akan wani dalili zaisa naji haushin kebantuwarka da matarka bayan nafo kowa sanin kanada iko zuwa inda take aduk lokacin dakaga dama Koda kuwa waye agabanka ko atare dakai.

 

Idan kinsan hakan then wats all this drama da kukan nan.???

 

Wani mugun takaici ne ya ciyota ta sauko Kan gadon tazo gabansa ta tsaya tace”

 

Idan har kana tunanin nayi kuka kokuma kukan danayi akan kaje gurin matarkane then u’re dreaming sbd hakan baya gabana and idan kana buqatan kebewa da ita meyasa ka zabi zuwa Nan da ita akwai guraren dazakuje da basai ka tsaya yiwa wani bayanin Abinda yakaika dakin matarka,

Matark,Matarka,Matarka,Matarka please spare my life nagaji da Jin wanna hayaniyar infact inaga I will have to give you guys a break ta yanda zaka……

 

Will you just keep quiet” yafada a Dan hasale shima sbd tashin hankali da fitinar daya samu kansa ciki kaf rayuwarsa wannna shine karo na farko da wani ya tsaye yake fada Masa magana mace ma kuma bama namiji ba shi baima taba sa’insa da wani ba.

 

Kukane ya balle Mata tace”

 

Nazamar muku lalura da zamana atsakaninku Nima kun Hana zuciyata nutsuwa da shigowarku cikin rayuwata ta bangaren aure..

 

So yayi yai Magana Amma yafasa sbd juyawar da kansa keyi tuni idanuwansa suka sauya ya juya yafice daga dakin.

Bakin gado ta koma ta kwanta tareda sakin wani sabon kuka tana Kiran sunan Dr khalil daya tafi yabarta har haka ta sameta.

 

 

Washe gari gidan kaf cikinsu Babu Wanda yayi bacci musamman shi da sautin kukan daya baro tanayi ya hanashi ko rintse idanuwansa Wanda ya haifar Masa da ciwon Kai me tsanani Dan haka Koda gari ya waye ya yanke shawarar zaiyi tafiya kozai samu samu nutsuwar zuciya data cikin kansa.

 

Tun kafin su tashi Amatu tariga kowa tashi ta wucewarta makaranta bayan ta barwa anty zarah note din ta tafi school bakin qofar dakinta Dan batai niyar Shiga dakinba sbd kada antyn ta fahimci halinda take ciki,

Itama zarah din daga ciki ta rufe qofar yau batada niyar budewa Amatun sbd kada ta fahimci halinda take ciki sbd nemawa kanta sauqi ma cikin Daren tayiwa kanta booking ganin likita a _Santorini_ ta Dan samu tabar gidan na kwana biyu ko zata samu nutsuwa Dan haka tanajin ficewar Amatu itama ta tashi ta shiga wanka tana fitowa ta shirya ta dauki duk abin buqata ta dauki waya takira numbern MD cikin sa’a kira ‘daya tana daf da katsewa ya dauka tafara gaidashi cikin sanyi da nutsuwa

Ya amsa Mata kamar ko yaushe kafin tayi Masa bayanin tafiyarta ganin likita yayi shiru da farko saikuma yadan gyara murya kadan yace ta fito idan tashirya su tafi tare sbd shima Dana Santorini din yayi niyar zuwa.

 

Jin hakan ta fito cikin farin ciki harta hada musu tea saidai itakadai Tasha yace shi Yana azumi.

Wayar Amatu yakira so daya Bata dauka ba sai kawai yayi texting dinta kafin suka wuce

itadai Anty zarah mamaki da ikon Allah kawai take kallo MAHMOUD dinda wani lokacin saiya Isa inda zaije yake fada Mata yayi tafiya wani lokacinma sai idan taga baidawoba takira yace Mata sorry ya aiki yadauki hankalinsa bai fada Mata yayi tafiya ba bayanan Amma gashi agabanta yake Kiran Amatu zai sanar da ita zaiyi tafiya ‘yar ikon Kuma taqi dauka qarshe ya qare da rubuta text.

 

Jin tayi tafiyar tafita ranta Amma Kuma sbd lafiyartane Dole zataje kodan Allah yabata haihuwar Nan dai itama ko ALLAH zaisa hankalin MD din ya tsaya akanta itadake son abinta.

Lokacinda Text din ya shigo wayarta tana zaune cikin wani restaurant tareda annah sunacin abincinda Sam batamada appetite cin kawai takeyi tana karanta massage din tagama tabbatarda MAHMOUD ZABEERA qarshenta yakeson gani wato ta mutu ya huta,

To baza’a yi hakaba zaisan dawa yakeyi.

Gida Takoma ko makarantar Bata komaba tana zuwa tahau hada kayanta tana qoqarin danne hawayenta daga saukowa.

 

Saidata hada kayanta acikin akwati biyu kafin takira annah tace ta tayata ayi Mata arranging room a hostel zata dawo Nan.

Ba musu suka shigarda application din accommodation akace sai Nanda 7 to 8 days zata samu.

Dole ta hakura har zuwa lokaci tanata fatar asamu kafin dawowarsu din.

 

Daina fitama tayi Sam tana tsumayin jiran akairata akan angama Mata arranging komai na zaman hostel din wani gefen Kuma har yanzu zuciyarta batada nutsuwa bare sukuni gashi tun Yana Kira Bata dauka harya tattarata ya share dama baiwani Saba da duk irin wainnan abubuwan ba.

 

Kwanansu biyar suka dawo da anty zarah kawai ta gaisa ta shigewarta Bata sake fitowaba sai dare data fito cin abinci tagansu a dining ta wucewarta kicin ta dafa noodles taci tafito ta wuce daki

Anty zarah data fahimci da akwai matsala wato a tsakaninsu taso yin Magana saikuma tafasa tana cewa”

 

Kama kanki zara’u kafin abin ya juyo kanki Dan abin juyi juyi ne kowa da ranar baqin cikinsa indai zaman kishi ne.

Data lurada shima ko kallon inda Amatun tabi baiyiba saita sake Kama kanta da shishigin shiga tsakani karta jawowa kanta fitinar da gwara tasu musamman da yanzu magungunan da likita ya dorata akai yace ba’a son tana saka damuwa ko kadan shine zasufi aiki da yardar Allah zata samu ciki Dan haka saurin dauke kanta tayi akansu ta maida himma taci abincinta ta qoshi Tasha ruwa Tasha magani tana satar kallonsa sbd kobai Bari angani ba a fuskarsa tana iya hango tension ataredashi.

 

Kwana biyu gidan ana zabga rayuwar ba ruwan wani da wani tsakaninta dasu anty zarah ce kawai take zuwa har daki ta gaidata musamman dataga tana Shan magunguna ta tambayeta batada lafiyane ta sanarda ita na neman haihuwar tane take ta Kama kanta saima taji son komawa hostel dinta yaqara qarfi.

 

Duk wata hanyar haduwarta dashi ta toshe duk da dai yanzu futowarta take Palo tayi abindake gabanta sai hakan yaso ya daga hankalin anty zarah Kuma yanayin shegun kayanda Amatun ke sawa kamar wata baby ko ita dake mace idan taganta dasu dauke Ido takeyi bare ace namijine yaganta ahaka.

 

Ranar daya dawo  idanuwansa suka sauka akanta da wata riga guntuwa Mara hannu tana kicin tana dafa taliya saura kadan yafadawa anty dake Masa sannu da zuwa ta kallesa tana mamakin irin yanda idanuwansa suka kasa daukewa daga Kan Amatun sai kawai ta juyawarta tabarshi tsaye Yana nufar hanyar kicin din

Amatu hangosa tafe ta sauke abincin ta fitowarta tana dauke kanta daga kallon inda yake harta gotashi taji yadawo da ita gaba dayanta ya matse cikin jikinsa Yana kallon idanuwanta datake dojewa kallon cikin idanuwansa tana qoqarin janye jikinta ya matseta dakyau cikin jikinsa gudun zarah ta fito tagansu wani aikin yasamesa yasashi dagata gabaki daya ya nufi dakinsa da ita bai sauketa ko inaba sai Kan gadonsa yaqi sauketa daga Kan jikinsa Kai tsaye yace”

 

Ankirani daga hostel na makarantarku cewan ur accommodation is ready,

Abinda banganeba anan waye zaikoma hostel din?

 

Sai alokacin ta dago da idanuwanta ta kalli cikin idanuwansa tace”

 

Nice zankoma hostel.

 

Wani wadataccen murmushin da Bata taba ganin yayiba yasaki Yana sake tungumarta yace”

 

Keep dreaming.

 

Daure fuska tayi tana qoqarin qwacewa daga jikinsa tace”

 

Nagaji da zama anan zantafi I need a break.

 

Serious yayi da fuskarsa Yana sakinta yace”

 

You are not going anywhere ki cire ran zama koina.

 

Masifa takeson suyi Dan haka Kai tsaye tace”

 

Bazan zauna anan ba nafi son zama can din.

 

Kallon fuskarta ya Dan Yi zuwa lokacin ransa ya Dan Fara baci ya sauko Kan gadon Yana cire agogon dake hannunsa tareda links din rigarsa yacire takalmin qafarsa ya nufi toilet Yana cewa”

 

Zangani idan kina zaman kanki ne coz I can see hankali bai isheki ba ita wadda kike kishin tafiki iya son mijin sbd tana kiyaye bacin ransa.

 

Kadan ya rage ta Dora hannu akai ta kurma ihun Abinda yafada idanuwanta sukai jajir ta sauko gadon ta nufi qofa ko gani batayi sosai sbd masifa ta fice tana cewa”

 

Yau wallahi bazan kwana a gidan Nan ba tunda dai kafito fili kafada Banda amfani.

 

Tana shiga dakinta ta janyo jallabiya baqa ta sanya tareda janyo akwatinta dasuke dama a shirye ta adauki Jakarta tafara Jan akwatin tana fitowa dasu ta nufi qofa idanuwanta na zubo cikowa da hawaye taji anriqe anruqota ta baya tareda zagayowa gabanta Yana mamakin fitinarta da yanda rigima Bata isarta ya rasa ma yazaiyi Mata azauna lafiya gabaki daya neman zaitashi take ya karbe akwatin hannunta cikin sarewa yace”

 

For God sake AMATULLAH meke damunki?

 

Qin Magana tayi tana qwace hannunta yasake riqewa Yana rintse ido cikin rashin sanin mafita yace”

 

Kince kin gaji da Nan ko

To Zan canza Miki gida Zaki zauna ke kadai Babu Wanda zaizo ya zauna shikenan..

 

Kallonsa tayi zatayi Magana cikin wani irin sanyin murya dake nuna galabaitarsa da rigumar yace”

 

Please”

 

Yanayin yanda yayi maganar yasa jkinta neman mutuwa ta dauke Kai tana cewa”

 

Bance haka ba nidai bazan kwana agidan Nan ba kawai ka…

 

Daukarta yayi gaba daya har handbag dinta ya nufi dakinsa da ita Yana cewa”

Wannan kishin naki Mara dalili ne Bari na nuna Miki wani Abu tukuna saikiyi me dalilin.

Tanajin haka tayi saurin kallonsa daidai lokacin dayake shimfideta Kan gadon Yana sakar Mata wani sahirtaccen murmushin daya kashe jikinta Nan take ya hanata motsi saima lumshe ido datayi tana lafewa cikin jikinsa ya shafa kanta ahankali ya furta”

 

My stubborn wife kina mantawane ke uwa ce kokuma duk zafin kishine zaisa ki zauce ki zauta MAHMOUD ZABEERA,

Rufe idonta tayi qasa qasa tace”

 

Waye zai jawo to?

 

Wani murmushin me sanyi Yakuma saki Yana shafo gashinta da Rolling dinta ya zame yakawo bakinsa daf da kunnenta ahankali yace”

 

Tell me meyasa?

 

Bude Ido tayi ahankali ta zuba Masa ta kalli bakinsa dake daf da nata tasan ko budewa tayi zatai magana sai lebanta ya hadu da nasa ta sake maida idanuwanta cikin nasa saitaji kunyarsa na shigarta ta juyar dakai ahankali tana kallon ta rufe Ido taji saukar hannunsa Kan cikinta taja numfashi daqyar tana rufe Ido ya Kai bakinsa ahankali yayi kissing din idanuwanta dasukadaine suka Isa su kalla cikin nasa idanuwan ya gangaro ya Dora bakinsa Kan nata Yana qarasa janye doguwar rigarta daya jima da zarewa zip din gaba ya jeho rigar qasa Yana shafa hooks din white lace push-up bra dinta dazai balle ya balle ya jehota qasa itama tayi saurin qanqamesa tana sake rintse Ido wani numfashi me wahalar fita na fito Mata shikuwa haduwar qirjinta da nasa Babu Kaya yasa numfashinsa daukewa na daqiqu kafin ya zura hannuwansa bayanta zuwa wuyanta.

 

Qarfe Tara da mintuna hudu tasamu damar fitowa daga dakinsa tana tahowa ahankali sbd gajiya da Kuma uban tsamin da jikinta keyi da akwatunanta na jiyan tafaracin karo a Palo kafin anty zarah dake zaune tana Shan maganinda daqyar yake samun hanyar wucewa a maqoshinta sbd Abinda ya tare Mata maqoshi sukai turus sunayiwa juna kallon kallo

Amatu wata irin masifaffiyar kunya da girman anty zarah data iya zama gidan datake kallon mijinta da wata hartana iya bacci tabbas tana qara jinjinawa antynta babu kamar anan kusa itakuma anty zarah wani irin kallone takewa Amatun zuciyarta ma takasa daukar tunani daya acikin tunani fiyeda dari data keyi akanta.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 43

Advertisement   Daqyar Amatu ta iya daga hannu takai wuyanta tana Dan sosawa akunyace zuwa kanta sai alokacin…

MIN QALB 11

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 1 (mamuhgee)

Advertisement  *_MIN QALB_* _Mamuhgee_ 1 Bismillahir-rahamanir Raheem. Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo…

MIN QALB 8

Advertisement  *_MIN QALB 8_* _mamuhgee_ Kallon tsantsan mamaki da firgici yanzu takewa amatu din tana kallon qafafunta zuwa…

MIN QALB 46-47

Advertisement   MQ 46/47_*     _INA MASU SHA’AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA…