MIN QALB 45

Advertisement

 

MQ 45_*

  

Sai Bayan sallar asuba jirginsu ya sauka Nigeria ta dayake ta Kira USI ta ta sanar dashi dawowarta Bata mayi tunanin ganinsaba harta fito zata dauki drop saigashi ya tsaya gabanta cikin wata EOD dark blue sabuwa shine yake tuqin tana ganinsa ta saki murmushin farin cikin ganinsa idanuwanta na cikowa da hawayen murnar ganin ‘dan uwanta Rabin jikinta Kuma abokin shawara,

Dr Usman Saleh usi Wanda shine sunan da akafi saninsa dashi yanzu

Yayi wani irin hasken samun hutu da nutsuwar rayuwa ga wani irin sajen daya Tara da sumar Kai sai qyalli takeyi duk da baiyi wankaba sbd kayan jogging nema ajikinsa ga wani irin girman gabban jiki dayayi sbd geaming dayakeyi kullum shiyasa ya zama wani irin qaqqarfan namiji Wanda yanzu haka ‘yan Mata masu aji da wayewa suke rububinsa musamman sbd kyawunsa dayafi rinjayarsu.

 

Fitowa yayi shima Yana kallonta cikin kulawa da tsananin qaunar ‘yar uwarsa dabaida kamarta kaf rayuwarsa sbd kallon dasukewa juna na uwa daya uba daya.

Advertisements

 

Kai tsaye Yana hango damuwa da rashin nutsuwar zuciya tareda rauni atareda ita musamman yanda idanuwanta sukai laushi ya saki numfashi sbd yariga yasan dawowar Bata lafiya bace ya qaraso kusa da ita ta karbi kayanta ya zagaya ya bude Bayan motar ya sanyasu ya rufe ya zagayo ya bude Mata gaban motar Yana cewa”

 

Bismillah mummy Amatu”ya qarasa fada cikin sigar tsokana dason dawo da dariya da walwalar Amatunsa.

 

Murmushi tasaki tareda Shiga ta zauna ya rufe ya zagaya yashiga ya tayarda motar suka kama hanya.

Suna fitowa daga airport ya kalleta yana qara qarfin AC din motar ganin kamar sanyinsa bai ishetaba sbd ‘dan warware rolling dinta dayaga tayi alamar zafi ya maida kallonsa Kan tuqi Yana cewa”

 

Gida ko zabeera?

 

Batareda ta kallesaba tace”

 

Advertisements

Uban me zanyi a zabeera tunda ko can farkon auren ba tarewa nayiba acan daga gidanmu na tafi Greece Dan haka daga Greece gidanmu zani.

 

Dariya tabasa ya murmusa Yana cewa”

 

Amah Wai meyasa bazaki canza ba bayan kinriga kinzama uwa fa.,

Wanda yake tareda miji for morethan 3 years now Amma kike cewa uban me zakiyi a gidansu.

 

Muguwar hararar data sakar Masa tasashi yin shiru Yana dariya ya kamo wani zancen har suka iso sabon gidansu da batasan dashiba duk da acikin dai anguwarsu din ne Amma tsarin ginin yafita dabam da kusan duk gidajen anguwar sbd kyawunsa duk da baida mugun girman Nan Amma ba qarami bane yanada nasa kalar girman.

 Tsohon gidansu dake gefen sabon ta waiwaya ta kalla cikin yanayi na farin cikin dawowarta gida cikin Yan uwa da abokanan hurdar arziki dasuka taso taredasu aka buga gwagwarmayar rayuwa iri iri ta arziki data rashin arziki data rigingimu iri iri musamman fadace fadacen dasuka Saba Wanda duk anguwa an shaidi gidansu da zaman masifa da tashin hankali kafin shigowar Dr khalil zabeera cikin rayuwarsu Wanda ya fahimtar dasu mahimmancin zaman lafiya da qaunar abokin zama tareda mutunta juna Wanda yakaisu ga zama tamkar zuria daya yanzu.

 

Juyowa tayi ta kalli USI da shima wasu abubuwan yake tunowa sbd fahimtar itama baya take tunawa cikin shauqi da tausayi da baqin cikin wata rayuwar dasukai a baya.

 

Kayanta yaja yafara shiga dasu cikin gida dayake katangarsu ta gate irin guntuwar Nan ce me qarafuna wadda ake ganin komai na waje Wanda kawune yace hakan yakeso sbd yaringa sanin komai dake wakana cikin anguwa tunda yasaba zaman qofar gida yanzu kuwa cikin harabar gidansa yake zama Kan kujerunsa na musamman da USI yasiyo Masa na zaman Shan iska Yana ganin komai na waje daga cikin harabar gidansa da surukinsa guda sukutum ya gida Masa da MAHMOUD ZABEERA tareda zuba musu furnitures na alfarma dajin dadin rayuwa Dr USI Kuma daya Fara cin qashin kansa yanzu shine daukeda nauyin komai na Jin dadin rayuwarsu yanzu Dan tuni ya ware kudi ya Kai iyami babbar kasuwa ta saro kayan siyarwa buhuhuwan takalman Yara Dana manya sosai Kuma kasuwancin nata yakeci shiyasa komai nasu yanzu sai hamdala Dan kuwa yanzu sune masu taimakawa wasu,

Anty salamatu dama marainiya ce gaba da baya Dan haka tuni tadawo cikinsu kodan irin dawainiya da wahalar datakewa Amatu da Muhammad.

 

Anty salamatu ce tafito daga kicin riqeda kofin Lipton data hado Yana hayaqi zata Sha sbd ciwon Mara data kwana dashi na period dinta dazaizo taga USI Yana shigowa palon janye da akwatina Niki niki ta tsaya tana kallonsa zatai magana saiga Amatu tashigo daga bayansa

Cikin tsananin mamaki dakuma farin ciki tasaki ihun ganinta tana Kiran sunanta da qarfi Wanda yasa Amatun washe baki cikin murna da farin ciki suka rungume juna saiga iyami da kawu sunfito daga palonsa harsuna rige rige Jin an ambaci sunan Amatun gakuma muryarta dasuke jiyowa.

 

Iyami na ganinta ta tsaya idanuwanta na cikowa da hawayen tsantsar farin cikin ganin ‘yarta bayan shekaru gashi yanayin yanda take ganin ‘yar tata tazama yaqara habbaka farin cikinta ga bayyanuwa saijin Amatun tayi ta fado jikinta da qarfi ta qanqamesa tana fashewa da kukan farin cikin ganinsu itama.

 

Kukanta yasa iyama maida hawayenta tana washe baki da farin ciki take cewa”

 

Meyene na kuka Kuma abun farin ciki da murna.

 

Dukkanin annashuwar kawu da haqoransa a bayyane suke Yana kallon Amatun cikin kewa da farin cikin ganin dukkaninsu sun Sami nutsuwa a rayuwa.

 

Zama sukayi dukkaninsu a palon Amatu na zaune tsakiyar kawu da iyami sai kallonsu take tana washe bakin farin cikin yanda suka sauya sosai tace”

 

Kawu nayi kewar gida sosai nakuma ji dadin ganinku.

 

Saikuma zuwa ba sanarwa Amatu” iyami tafada tana kallon Amatun da USI daya daukota.

Iyami bazata nakeson muku Danma anty salamatu ta Bata bazatan tawa so nayi saina saikun fito zuwa anjima ku ganni kawai zaune Ina cin abinci kokuma Ina muku Ina kwana saigashi ihunta yasa kunji kunfito musamman kawu so nayi Yana fitowa yaganni ya dauka inuwatace zuciyarsa ta kusa harbawa.

 

Dariya dukkaninsu sukayi kawu yace”

 

Wlh zuciyata na harbawa kun shiga uku Dan uwarku ma tata bindigewa zatayi kunga kunzama marayu kenan har gwara ke kina gidan mijinki shi wannan qaton banzan gantalewa zaiyi gurin siyan abinci ma kawai it’s kuwa salamatu zaman tunanin kadaici kawai ya isheta Dan haka gwara ku taru kuyita yimin adduar tsawon kwana.

 

Kaikuma dason tsawon kwana kullum adduarka kenan”cewar iyami.

 

To karar kwana kikeson nayi fata?

Zaki Fara halin naki kenan muyi Abinda nace nadaina.

 

Dariya sosai Amatu tayi tana sake jinjina halinsu kawun da basa taba canzawa.

 Daqyar dai aka tsagaita tasamu Shiga dakin iyami inda aka shigar Mata da kayanta tashiga tana kallon tsarin dakin dayayi Mata kyau sbd simple furnitures dinsa ta zauna bakin gado tana zare doguwar rigarta tareda warware Daurin gashinta Dan taji sauki ta miqe ta Shiga toilet sbd fitsarin daya Fara matsarta ta fito ta kwanta sbd hutun gske take buqata take bacci ya dauketa bayan Tasha magungunan ta.

 

Sai kusan azahar ta tashi bacci shima sbd qarar loudspeaker da ake Kiran sallah Wanda ta manta rabonta dajin hakan ta tashi tayi wanka ta sanya riga da skirt na atampar cikin kayanta data Bari tun na legend auren Dr khalil Kuma cikin ikon Allah sun Mata saidai sun Dan kamata kadan ba sosai ba sbd ita acan din Bata qara jikiba saidai kyau da gogewar da fatarta tayi sai cikowar albarkatun jiki.

 

Fitowa tayi Palo ta tarardasu anty salamatu da iyami saisu maman junior dasuka shigo ganinta aikuwa Nan aka hau ihu da hayaniya ba itaba ba mutuniyarta maman junior ba hadda junior daya girma yafara zama Dan saurayi Nan suka hau fira tana cin lafiyayyar sakwara da miyar Ganda da maman junior din takawo Mata da zafinta iyami dai Dole Takoma palon kawu tabar musu Nan sbd shegiyar firar iya shegen da maman junior tafara kawo musu suna dariya tana sake fesowa Amatu kalolin iya shegen da akeyiwa miji.

 

Firar nawa anty salamatu da maman basiru Dadi hakama Amatun datake sauraronta tanajin qaruwa aciki Amma sai tanajin abin wani irin banbarakwai sbd ba sa’aninta bane duk da duk kwamacalar duniya sunsaba yinta tare tun Ada can Amma wannan sbd ta rayuwar aurece sai kamar tanajin nauyi Amma dayake maman junior din ba ruwanta Dole wani abin saikayi dariya ba qaqqautawa.

Sai magriba majalisar palon tasu ta watse suka tashi yin sallah tukuna iyami tasamu kanta duk da wata firar tasu tanaji sama sama wani abin saidai ta girgiza kanta sbd rashin kunyar tayi yawa.

 

 

 

**_Athens GREECE_

 

 

Kiran wayar USI yake sakeyi kusan akaro na goma sha wani Abu Amma Bata shiga yakoma Kiran anty salamatu itakuma tanata ringing Amma sbd suna Palo fira tayi Dadi Bata jiba yasaki tsoki ahankali ya Nemo numbern kawu yakira shikuma ya fita waje tsohuwar majalisarsa tasu alhaji mande yabar wayar gida.

Ki yayi kamar ya fasa wayar hannunsa ya rintse idanuwansa dasukai jajir ya budesu ya miqe daga zaunen dayake a palon zai bar gidan Dan Yana buqatar ticket din Nigeria koman dare idan dai akwai flight zai tafi.

Da sauri anty zarah takira sunansa zatai magana ya juyo yayi Mata kallo daya da idanuwansa dasuka Sanya gabanta faduwa yace”

 

Please zarah karki Bari nayi Miki fada kizo kema ki qaramin wani ciwon Kan sbd idan maganata tana daidai you are completely at fault anan,

How can you be so selfish kina kallo ta fita Amma baki daga wayana kin kiraba you’re telling me ma har bankwana tayi Miki Wai zata tafi

A woman who had a miscarriage kice Wai kin dauka na sani zata tafi kona sani ke baki fahimci batada cikakkiyar lafiyaba bai kamata tayi tafiya ahaka ba Kona barta tunda kinada hankali bazaki nada shawaran abar tafiyarba hartaji sauqi Amma Zaki ce Wai you thought nasani to hell with your thoughts…

Please I need some air kije daki kema ki kwanta ki huta kada wata damuwa ta baki matsala kema idan munsamu tickets zamu tafi gida I don’t feel like staying Kuma sbd inada aikin da ake nemana a gaggauce.

 

Ahankali ta iya bude baki tace”

Sorry. Kafin ta juya ta nufi daki tashige tana Hana kanta Jin damuwa ko haunshin zancensa sbd ta yarda kaman yanda yafada tanada laifi sosai anan,

Ko tambayanta ya jiknta bataiba,

Rintse Ido tayi tana cewa”

Zarah meyasa Kika kasa tunani anan.

 

Dakinsa ya nufa bayan yayi booking tickets dinsu na tafiya saidai bazasu samu jirgin Nigeria ba direct yanzu saisunyi kwana biyu kafin su Isa sai an tsaya qasashe dasu Dole ya amince ya zauna Yana dafe kansa dake neman bugawa sbd tension,

A rayuwarsa baisan gwagwarmayar rayuwar aureba da fadan yau da gobe da ake cewa sai yanzu,

Gabaki daya sai yanzu yasan me ake nufi da hakuri a zaman aure Dan gashinan kansa na neman kamawa da wuta Yama rasa ta Ina zai faro da kowaccensu ka taba sai wannan tace taji haushi,

Babban burinsa dai yanzu kada Amatu tadauka zafi da yawa Dan baisan ya zaiyiba idan ta dauka zafi Dan saukowarta qila saiya hada da neman agajinsu Andi.

 

Wayarsace tayi qara baiyi niyar dubawa ba Amma sbd jiran kira daga gidansu Amatun saiya duba wayar cikin sa’a kawu ne Dan haka ba Bata lokaci ya dauka suka gaisa Yana tunanin ta inda zai Fara tamabayar ko Amatun ta iso sai kawun ya rigasa da cewa”

 

Saiga Amatu tazo baku sanar Mana ba  MAHMOUD,

Ana zuwan bazata ne a irin wannan doguwar tafiya saika biye Mata kaima kaki fada Baku kyautaba gskia.

 

Ajiyar zuciya ya sauke yabawa kawun  hkr kawai a taqaice kafin suka Dan qara gaisawa suka aje wayar yana Jin wani irin nauyi na raguwa daga zuciyarsa da kansa.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 12

Advertisement  *_MIN QALB 12_* _Mamuhgee Kasa riqe hawayenta umme tayi suka gangaro Kan fuskarta ta shafa cikin firgici…

MIN QALB 1 (mamuhgee)

Advertisement  *_MIN QALB_* _Mamuhgee_ 1 Bismillahir-rahamanir Raheem. Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo…

MIN QALB 43

Advertisement   Daqyar Amatu ta iya daga hannu takai wuyanta tana Dan sosawa akunyace zuwa kanta sai alokacin…

MIN QALB 46-47

Advertisement   MQ 46/47_*     _INA MASU SHA’AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA…

MIN QALB 39

Advertisement   MQ 39_*     Direct wani kebantaccen guri suka nufa daga bayan joint din inda aka…