MIN QALB 49

Advertisement

 

#*_MQ 49_*

 

 

 

*_THE FLAVORLAND BY ACEEY_*

Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:

Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa

Advertisements

Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma

Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama

Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:

Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA

Gashe gashe da soye soye kamar su

Kaza

Kifi

Nama

Doya

Dankalin turawa/hausa

Awara

Danwake

Advertisements

Gurasa

Kwado da dai sauransu….

Ba Mu tsaya anan ba——

The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da

Hoppers wato Fara

Milky candies wato alawar madara da kuma

Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata…

Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka

IG: @the_flavorland

Whatsapp:08104673847

Sending Some treats your way…. l

 

Let us satisfy your cravings:

We Deliver anywhere and everywhere.

 

 

 

************

Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda nauyin baccin dabai Gama isarta ba sbd sai Bayan sallar asuba ne tasamesa tana Gama budesu da kyakkyawar fuskarsa tafara cin karo daf da tata numfashinsu na sarquwa cikin na juna,ta kalli idanuwansa dake lumshe ta gangaro da idanuwanta Kan lips dinsa wani gajeran murmushin samun nutsuwa ya subuto Mata ta motsa hannuwanta dake sarqe cikin nasa taji yasake matsesu ta maida kallonta Kan fuskarsa da mamakin da alama idanuwansa biyu kenan?

Hancinsa taji akan nata ya hade fuskarsu ya Dora mata ta Kai idanuwanta Kan idonsa daidai Yana budesu cikin kasalar baccin dabai Gama sakinsa ba ta dauke idanuwanta ahankali daga nasa zata sake zamewa yasake qin Bata damar motsawa.

 

Ahankali ta bude bakinta dake daidai kunnensa cikin qaramin sautin daya qarasa kashe jikinsa da saukar Masa da kasalar tace”

 

Yunwa.

 

Daqyar ya iya bude idanuwansa dasukai laushi da yanayin yanda dumin numfashin bakinta ke shiga cikin kunnensa ta maganar datai Masa.

A kasalance ya saketa ta tashi zaune ta sauka daga Kan gadon ta nufi toilet ta Shiga.

Wanka tayo tana fitowa daureda towel brown ta nufi closet dinsa ta dauko wani sabon towel din qarami Tana sake goge kanta ta nufi gaban mirror Yana duba dryer Amma Babu a dakin ta waiwaya ta kallesa taga idanuwansa qyam akanta Yana binta dasu kamar wani mayen qarfe saita fasa tambayarsa sbd ganin hadda miskilancinsa daya hanasa tashi bare Magana sai binta yake da idanuwa ta nufi qofa ta fice zuwa bedroom dinta sbd akwai acan taganta jiya gaban mirror.

 

Tana Isa dakin ta zauna gaban madubin ta jonata ta kunna ta hau busarda gashin tana kallon fuskarta dake wani irin blushing da qyalli ta cikin madubi,

Tana gamawa ta gyara Kan ta daure ta shafa Neutrogena oil sai bodymist dasu spray ta qara da humra me sanyin qamshi ta miqe takoma jikin wardrobe ta bude Bata wani tsaya zabe ba ta dauko wani plain drylace peach ta saka riga da skirt ne saita fito Palo tana qoqarin nufar kicin akai Knocking ta nufi qofar ta bude,

Cikin sa’a kuwa abinci ne anty zarah ta aiko musu Dan haka saita fasa aikin ta ajiye a dining ta Kama hanyar zuwa tadoshi aka Kuma knocking taje ta bude wani abincin ne daga umme itama ta karba duk ta hada ta ajiye a dining tana juyowa da nufin zuwa tadosa saigashi yafito shirye tsaf cikin wani milk yadi me tsananin taushin daya bayyanarda tsadarsa fili ya nufota Yana kallon kwalliyarta tareda nuna yabawarsa a fili Yana Mata kallon qasa qasa daya sanyata Jin kunya me tsanani sbd kallon ya qunshi yagama da saninta cikinta da wajenta ga sauke Kai daga kallonsa tana juyawa ya riqota ya dawo da ita gefensa suka nufi dining din Yana kallonta qasa qasa da wani irin murmushi harsai data gaji cikin muryar shagwaba tace”

 

Dady Allah zantashi na tafi.

 

Qaramar Daria Mara sauti ko kadan yadan saki Yana sauya kallonsa daga kanta yace”

 

Ok sorry sorry na daina Zo Nan lemme feed you.

 

Akan cinyarsa taci abincin tana bashi Yana Bata sai sake kashe Masa jiki takeyi da rashin zamanta guri daya ajikinsa daqyar dai aka gama cin abincin ya dauketa suka koma daki tana wani zille zillen daya qarasa juyar dashi daga MD ZABEERA.

 

 

Qarfe goma sha daya harda kusan rabi suka fito tana riqeda hannunsa ta sauya wasu kayan sbd wani wankan datayi tayi simple makeup da wani irin hot red lipstick daya zauna daram Kan lips dinta dayaketa saukar hankalinsa Amma Dole ya dauke Kai suna shiga palon zarah ya saki hannunta ya nufi sama inda hafsatu tace musu tana can yatafi yabarta tana kallon hannunta daya saki domin zuwa ga wata wani rashin Jin Dadi ya taso ya rufe zuciyarta ta zauna Kan kujerun dake palon Ahankali tana Kiran sunayen Allah tareda kore shedan daga cikin Kai da tunaninta taji motsin saukowarsu ta daga Kai tana kallonsu hannuwansa duka biyun riqeda zarah din suna saukowa yanajin kamar ya daukota gaba dayanta ya sauko da ita sbd ganin yanda take tafiyar sbd tace Masa da ciwon qafafu ta kwana.

 

Har Kan kujerar yakaita ta zauna Rana kallonsa cikin farin cikin kulawarsa gareta tace”

 

Thank you MD.

 

Murmushi me sanyi ya sakar Mata Yana zama kusada ita yace”

 

Akwai godiya tsakanin miji da Mata ne?

 

Dariya tayi tana kallon Amatu dake qaqalo murmushi tace”

 

Amatu Yana tambaya tayani bashi amsa sbd zaifi ganewama idan Kika fada Masa Dan Naga yafi gane yarenki.

 

Maganar ta daki zuciyarsu daga Amatun har shi Musamman shi ya tsura Mata idanuwansa yanajin wani irin yanayi me nauyi na rashin Jin Dadi wato tariga da ta amincewa kanta yafi son Amatu kokuwa yafi daukar Amatun da mahimmanci akanta ko me?

 

Amatu ma Jin tayi nauyi da rashin Jin Dadi ya dabaibayeta take sbd maganar antyn Magana ce data fito dauke da raunin da zuciyarta ke ciki batareda tasani saitakejin sabon mutuncin antyn na sake shigarta koba komai haryanxu anty mutum ce me tsananin mutunci da ganin qimar Dan Adam duk wannan auren na bazata da akaiwa mijinta da qanwar data ke yiwa kallon uwa daya uba daya bai canzata zuwa wata daban hakama vai sauya kyawawan halayenta ba.

 

Kallonta tayi taga cikin Yar dariya tai maganar bakin gskiyarta batasan tayi mgnar da wata manufa Abinda yake gskia ta fada Dan haka sai itama ta qirqiro murmushi cikin batar da zancen tace”

 

Anty baya buqatan amsa yasan akwai godiya tsakani ma’aurata musamam ma keda kikeji da Rabin ranki godiya bakomai bace.

Dariya anty zarah tayi tareda kallon Amatun tana jinjina sunan Wanda rabonta dataji tun zamansu asibiti jinyar Muhammad.

 

Yanason fita Amma sbd yakira Dr Fatima yasa ya jira harsaida tazo ta duba zarah din ta tabbar Masa da bakomai bane duk cikin laulayin cikine sai nauyi da cikin zai Fara shiyasa Dan haka bayan fitar Dr Fatima fita yayi shima ita Kuma Amatun ta Dan jima kafin ta tafi sbd qafafun anty zarah din ciwo sukai Mata sosai Sai data Dan tattausa Mata su tasamu tayi bacci kafin ta fito Takoma tayi sallah ta kwanta tanajin bacci.

 

Da daddare Takoma tasake dubo anty zarah din duk da ba wani Abu dake Mata ciwo kawai qafafun ne acan tabarosa tadawo Saida antyn tayi bacci yadawo sukai wanka suka kwanta.

Washe gari zai bar sashenta yakoma na anty zarah Dan haka tun safen bai fita ko Ina ba suna Palo suna shiririta ita ala Dole saiya lallasheta yasata bacci kafin yatafi haka dai suka shiririce har sallar magriba tayi ya tafi.

 

Zarah duk yanda tayi tunani da Shirin dauriyar abubuwan dazataita gani tareda daukarwa kanta alqawarin dangana tayi Shirin zaman hkr sai abin yazo Mata a baibai yabarta da mamaki sbd MD sauya Mata yayi daga MD ZABEERA zuwa asalin miji,

Ya sauya ta bangarori dabam dabam,

Babban mamakinta ayanxu shine zaman gida daya koya sosai yake zama agida wani lokacin Yana yini guda cikin zabeera bai fita ba Yana tareda iyalinsa ga yawan fara’a daya samu kansa aciki Abu daya datake maimaitawa shine Bata taba Tunanin ummanta datace Mata wata kishiryar kamar alheri ce sbd tana gyara maka mijin daka jima Yana wahalarda rayuwar aurenku hakama wasu yancin naki wata kishiyar itake kwato muku keda yayanki gurin miji ta hanyar sauyasa,

Tabbas ta yadda da hakan,

Akwai Abinda bazaka iyaba arayuwar zamantakewarka da mijinka sbd ka kashe zuciyarka Dan haka kodai duk wadda za’a auro kingama cutarta sbd kin sabawa mijin da yin shiru akan haqqinki Dan haka itama bawani dadinsa zataji ba kokuma kisamu wadda zata sauya mijin kisamu rayuwar dabaki samuba abaya,

Kishiya ko wace iri kasamu ta gari ko akasinta tasan da akwai ciwo Amma dai duk da hakan tana jinjinawa Amatu sbd ta taimaketa tanan Dan ita dai daza’a barta saidai suyi rayuwarsu sugama ayadda suka Fara bazata iya yiwa MD hayaniya ko yunqurin sauyashiba sbd yafison rayuwar kadaicinsa kamar tafi Masa nutsuwa takega shiyasa batason shige Masa sosai.

 Abu dayane data lura dashi shine wen ever Amatu is around idanuwansa akanta suke sbd bazai iya Hana zuciyarsa Abinda takeso ba saidai Bata damuba sbd itama aduk lokacinda take kusa to hannuwansa bazasu iya zamaba sai acikin nata Koda Amatun na kusa Wanda hakan ya tabbatar Mata da tanada nata bangaren me mahimmanci a rayuwarsa.

 

Anasa bangaren kuwa yasamu kwanciyar hankalinda baitaba samuba a rayuwarsa tun bayan rasuwar mahaifiyarsa tabarsa,

Yasamu nutsuwar zuciya da rayuwa,

Yasamu kwanciyar hankali data ruhi,

Rayuwa cikin iyalin dakake matuqar so suke sonka tareda baka nutsuwa shine asalin Abinda baisaniba sai yanzu,

Amatu ce takawo sauyi arayuwarsa da zuciyarsa Amma Kuma zarah ce abar jinjinawa kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwar dasuke sbd itace ta   dauki komai da salama da dangana tareda sawa kanta nutsuwa batareda damuwa ko tashin hankali ba azaman Wanda yasa ake zaune kalau,

Da Bata bada wannan gudunmawarba da duk yanda suka Kai ga tsananin son juna shida Amatu bazasu samu wannan kwanciyar hankalinba da nutsuwar zaman lafiya.

Nuratu tazama tamkar aminiyarta yanzu sbd kusan kullum gurinta ma take yini hardai ranarda anty salamatu tazo gidan yini sukeyi fira USI ma da tintini yarinyar ta fice Masa arai sbd kusan itace silar komai tun Yana shareta har suka Fara sabawa sbd Amatu dakuma yaganta Dr salman dayake babban abokin shawarar USI dabaida amintaccen Dan uwa irinsa da hakan dai suka Fara sabo da ita sosai.

 

 

Satinta hudu da tarewa tafara Shirin komawa sbd school karatunsu yadauki zafi Dole zata koma Dan haka duk sukabi suka wani sukukuce musamman ita dazata Koma ita kadai ko Muhammad gurin umme zaiyi zamansa daqyar ma dadynsa yabari Dan acan yaso sanyashi school Amma ummen ta toqa hakama shima Muhammad din yafison gurin ummen yanzu sbd tana sakaltashi da yawa gashi Kuma yaga Yana ganin dadynsa anan.

 

Ita kanta anty zarah zatai kewar Amatun sbd sunyi sabon sabo duk da har abada zasu taba komawa yanda suke Ada ba Amma ko yanzu sunyi sabon shaquwarsu suna tsananin mutunta juna da gujewa Shiga haqqin juna.

 

A gidansu ta yini Daren ranarda zata koma canma Saida tayiwa su iyami kukan barin gida kafin yazo da daddare ya dauketa suka koma gida.

Washe gari Saida tayiwa kusan kowa dake cikin zabeera bankwana kafin suka wuce USI ne dakansa yakaisu airport suka wuce yadawo.

 

Sbd son cire Mata damuwar data sanyawa ranta yasa Basu koma Greece ba direct suka nufa US.

Wata irin rayuwar Jin Dadi da sakewa sukai a US tamkar turawan qasar Dan sai alokacin tasake sanin asalin waye MAHMOUD ZABEERA sbd wani bangarensa data gani na dabam wato Dan rayuwa.

Duk yanda zatai rayuwa bazata manta wainnan kwanakin dasukai a US ba sbd ya shayar da ita soyayyarda har abada bazata barta ba,

Ya sanyawa zuciyarta wani sabon maganadisun sonsa da qaunarsa.

 

Kwanansu takwas suka tattara suka nufi gida saidai Kuma kamar karsu dawo tunda suka dawo tafara zuwa school kwana biyu shikenan ciwon zazzabin dare ya sanyota gaba sunyi yawon asibitin hardai aka tabbatar musu da ciki ne Dan haka ba wani magani haka suketa fama duk wani aikinsa ya ajiyesu jinyar matarsa yake cikeda kulawa da tsananin qauna.

 

Ganin harya share kusan wata daya da rabi yasa ta daure ta bawa kanta qwarin ta nuna Masa ta warke sarai kafin yafara maganar komawa sbd tarin ayyuka da Kiran dayaketa faman Sha dazai tafi ita dakanta takaisa airport suka fito motar ya kamo hannunta ya matso da ita cikinsa Yana kallonta da fararen idanuwansa dake bayyana newarta tun kafin ya tafi ya bude baki ahankali Yana shafo cikinta cikin laushin murya yace”

 

I will miss you wife.

 

Dan dago qafarta tayi sbd yafita tsayi takai bakinta Kan nasa ta Dora ahankali ta zura Harshenta tabashi wani irin kiss tana kallon cikin idanuwansa tace”

 

I will miss you More.

 

Rungumeta yayi tareda sauke ajiyar zuciya Yana shafa Bayanta yace”

 

I love you.

 

Qanqamesa tayi kalmarsa na sake kashe jikinta.

Sun jima ahakan kafin lokacin tafiyarsu yayi yabata kiss a goshi ya wuce tana kallonsa harya shige ta juya jiki amace ta shiga mota tabar airport din tana Jin kewarsa kamar tabisa.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 23

Advertisement   *_MQ 23_*   *_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN…

MIN QALB 36

Advertisement  MQ 36_*  Umme da kanta tabata abinci abaki taci tana qara jinjina zancen Dr Fatima data fada…

MIN QALB 18

Advertisement   *_MQ 18_* _Mg_       Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya…

MIN QALB 9

Advertisement  *_MIN QALB 9_* _mamuhgee_ Gabaki ‘daya hankalinsa nakan fuskar amatu da ita Kuma hankalinta nakan usi da…

MIN QALB 40

Advertisement  ##Mamuh#*_MQ 40_*  Kasa daukarta bacci yayi Kuma ko juye juye takasa tadaiyi lamo cikin lullubin duvet tana…

MIN QALB 8

Advertisement  *_MIN QALB 8_* _mamuhgee_ Kallon tsantsan mamaki da firgici yanzu takewa amatu din tana kallon qafafunta zuwa…