MIN QALB 50

Advertisement

 

#*_MQ 50_*

 

 

https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg

Please subscribe to our YouTube channel 👆👆👆

 

 

 

Advertisements

Tana komawa gida kwantawa tayi tun anan Palo tana waya da anty salamatu akan maganar zuwan datakeson tayi suna gamawa anan palon bacci ya dauketa.

Bacci me nauyi tayi sai kusan yamma ta farka ta tashi zaune tana Dan dafe kanta dayayi Mata nauyi sbd baccin datai dakuma Dan ciwon dayake Mata.

Miqewa tayi ta nufi daki Kai tsaye toilet ta wuce tayo wanka dan jikinta yasaki tayo alwala tafito ta sanya riga da wando me Fadi ta sanya dogon hijab tahau dadduma ta tayarda sallah.

Bayan tagama sallar kicin taje ta hado tea da biscuits tazo ta zauna Tasha tana kallon agogo tasan zuwa yanzu ya Isa sauka Amma bazata kiraba zata Bari idan yahuta yasamu lokaci zai kirata.

 

 

Washe gari da wuri ta wuce school sbd akwai asibitin dazasuje daga school din,

Tunda safe shine ya tayarda ita daga bacci suketa waya Saida zata Shiga wanka suka aje tana Shirin fitowa yasake kiranta harta Isa school suna waya har Anty zarah yabata suka gaisa tayi Mata ya jiki daga Nan daqyar tasamu yayi hanging wayar ta maida hankali Kan Abinda yakawota,

 

Sai yamma likis ta dawo gida amatuqar gajiye Dan haka ko abinci Bata tsaya Ci ba wanka tayi ta kwanta baccin gajiya da daddare data tashi bayan tayi komai tasake komawa ta kwanta suna waya ta rikice Masa akan sai anturo Mata anty salamatu wlh bazata iya rayuwa ita kadaiba.

Dole ya amince wa buqatarta yaje yasamu kawu da kansa yayi Masa roqon zuwan anty salamatun wannan karon hadda iyami ya roqa taje tadubota tunda batada lafiya zataji dadin ganinta sosai.

Advertisements

 

Kawun bedai cemasa ya amince da zuwan iyaminba tukuna Amma dai ita salamatun zataje itama bazata jimaba sbd maganar neman aurenta da Andi ya nemawa alhaji qarami Wanda yake autansu Modibbo basason doguwar bidia kamar a taqaice suke son ayi auren.

 

Da kansa yasa akawa anty salamatun shirye shiryen tafiya sbd kusan shima a matse yake dataje din yasamu me kula Masa da Amatun Dan gabaki daya hankalinsa ba’a natse yakeba Jin yake kamar yaje da kansa yayi jinyar abarsa Amma Kuma ayanzu zarah dake kusan haihuwa tafi buqatarsa shiyasa ma duk wasu tafiye tafiyensa ya rage saita haihu sbd Bata kulawar datake buqata.

 

Duk yanda yaso anty salamatu ta Isa cikin kwanaki qalilan bai yiyuba sai bayan sati biyu da maganar ta tafi tareda USI dazaiyi 6month program acan aikuwa Nan suka dasa sabuwar rayuwa a Greece hakan kuwa ba qaramin nutsuwa yabawa MD din ba Dan dama shineya tsayawa USI akan zuwa Greece din yin program dinsa acan infact ma shine yadauki nauyin komai sbd kawai Amatun tasamu Yan uwanta atareda ita hakan ne kawai zai bashi cikakkiyar nutsuwa sbd yanayin datake ciki.

 

Zaman USI agarin tareda zuwan anty salamatu ya kawarda duk wata damuwarta da rage Mata kewarsa sosai Dan haka saita kwantarda hankalinta take karatunta cikin kwanciyar hankali da bada himma musamman yanzu da cikinta yafara girma Dan kusan wata hudu cikin na biyar kenan ita Kuma zarah ayanzu tana gab da shiga cikin watan haihuwarta shiyasa Koda yazo gurinsu bai wani dadeba yakoma yasake barinta cikin sabuwar kewarsa Dan har wata qaramar tafiya sukai dayazo din.

 

Zaune suke apalo tana duba wasu textbook na school anty salamatu Kuma tana yanka Mata gwaibar data siyo daga wani superstore ahanayarta ta dawowa school suna Dan fira sama sama sbd Rabin hankalinta nakan books din wayarta tayi ringing tun daga Kan kalar ringtone din tasan waye me Kiran ta Kai hannu ta dauki wayar tana sake wata qaramar ajiyar zuciyar son mijin nata ta daga cikin kasalalliyar murya tace”

 

AMATULLAH’s husband..

 

Duk da Yana cikin wani yanayi na damuwa Saida yadan murmusa hartaji sautin murmushin ta cikin wayar ahankali tace”

 

Barka da yamma.

 

Barka wife,

Hw are you and my baby?

Ya anty salamatu hope duk Kuna lafiya?

 

Yes lafiyanmu kalau it’s just that we’re missing you badly.

 

Numfashi ya sauke Wanda yasata Dan gyara zama tana ajiye books din jikinta cikin sauti me nutsuwa tace”

 

Lafiya kuwa? You sound worried.

 

Dafe goshinsa yayi cikin yanayi na damuwa yace”

 

Zarah na asibiti tun safe she can’t deliver by her self itama aiki za’a yi Mata.

 

Faduwa gabanta yayi cikin tsoro da damuwar itama zatazo wajen ga tausayin anty zarah din sai jikinta yayi sanyi da rawar murya tace”

 

Yanxu tun cikin dare anty zarah take cikin wannan halin Amma baka fadaminba dady sai yanxu?

Wlh na tausaya Mata yanxu kenan suna ZABEERA specialist?

 

Yes yau sukeson ayi aikin sbd qarfinta harya qare nagaji da ganinta cikin wannan halin.

 

Kwantar da murya tayi cikin tausayawa anty zarah din da tausayinsa shi kansa sbd tana iya Jin irin damuwar dayake ciki a muryarsa tafara qoqarin kwantar Masa da hankali tana sake bashi qwarin gwiwa akan Allah yasa ayi aikin lafiya akuma dace.

 

Bayan sungama waya tana fadawa anty salamatu tana lalubo numbern umman zarah din ta Danna kiranta,

Tana dauka ta gaidata cikin ladabi ta Dora da cewa”

 

Umma Ashe anty zarah haihuwar tazo wlh bansaniba sai yanzu dady yake fadamin tun safe Kuna asibiti.

 

Amatu antynki Kam tanajin jiki kitayata da addua Allah yarabasu da bbyn lafiya.

 

Inshallah Allah lafiya kalau zasu rabu

Allah yasa ayi aikin cikin sa’a

Nasan bazata iya mgn yanzu ba Ina Mata sannu zuwa anjima zansake Kira naji Inshallah.

 

Shikenan Amatu angode Allah yayi albarka.

 

Amin umma ngd sai anjima.

 

Aje wayar tayi tana kasa cigaba da karatun ta shiga damuwa da tunani tasake Kiran MD din takuma kwantar Masa da hankali.

 

Haka Takoma sukuku tunda sukai Magana takasa sukuni sbd hadda tsoro tsoron zuwan tata haihuwar yake sake shigarta takasa zama sai kiransu takeyi akai akai tana tambaya har lokacinda aka shiga aikin da zarah Amatun kiransa takeyi tana Kiran umman zarah din harsaida umman tace Mata”

 

Amatu ki kwantarda hankalinki tunda kema bake kadaiceba kada ki daga hankalinki wata matsalar ta taso Kuma ku rabawa mijinku hankali Kashi biyu.

 

Ana fitowa sallar magriba aka fito da lafiyayyan jaririn zarah cikin qoshin lfy sai kuka yakeyi cikin qoshin lfy aka wuce dashi sukai duk aune unen dasuke buqata kafin aka shiryasa cikin fararen overall masu kauri nurse ta fito dashi fuskarta daukeda murmushi ta nufo inda MAHMOUD yake tareda mahaifinsa Modibbo daya iso asibitin alokacin tareda umme da Haj maryam.

 

Modibbo aka miqawashi ya karbesa cikin farin cikin ganin jikinsa ‘da na farko ga MAHMOUD dinsa.

Addua yayiwa jaririn kafin ya miqawa MAHMOUD da idanuwansa suke Kan fuskar yaron Wanda tunda nurse tafito dashi kafin yashigo hannunsa zuciyarsa tagama cika da soyayyar ‘dansa.

Zarah tabasa farin cikin rayuwarsa,

Ada baidamu da samun ‘dan kansaba Amma tun Bayan haihuwar Muhammad zuciyarsa ta cika dason Tara zuriar me yawa kodan ya Gina tashi zuriar sbd fita rayuwar kadaici.

 

Addua yayiwa yaron tareda Masa huduba yakirasa da sunan Muhammad DAHEER Modibbo.

Godiya Modibbon yayi cikin Jin dadin takwaran da akai Masa.

Nan kowa yafara karban yaron ana Yaba kyawunsa da kamannin babansa daya Dan dauko.

 

Saida aka gama murnan samun Modibbo aka koma murnar samun nasarar aikin da akayi umman zarah kuwa farin cikinta a bayyane yake ganin yanda kowa ke murnar haihuwar ‘yarta.

 

Babban tashin hankalin dasuka shiga na samun mugun labari daga bakin likitoci shine ba lallai zarah din tasake haihuwa ba sbd rashin qwarin mahaifarta data fashe kafin Cs din.

Hankalin ummanta yatashi sosai hakama da duk Wanda yake gurin Saida jikinsu yayi sanyi Amma ganin MAHMOUD dakansa ya dauki qaddarar ya dauki juriya yasa kowa ya hkr suka buge da tarairayar zarah wadda tayi kukan wannan mugun labarin MAHMOUD na aikin lallashinta cikin nuna Mata tsananin damuwarsa Dole qarshe ta dangana tabarwa Allah akan hakan shine qila mafi alkhairi.

 

Amatu data sake Kira kusan karo na biyar kenan bayan haihuwar sai yanzu tasamu damar Magana da anty zarah din Tai Mata barka tana sake Mata sannu daga Nan suka Dan gaggaisa da jamaar dake asibitin ta kashe wayarta.

 

Kallon babynta takeyi idanuwanta na cikowa da hawayen farin ciki Dana damuwa taji an zauna gefenta tareda zagayeta da hannunsa har ita har Modibbon Yana kallon Modibbo dake baccinsa cikin nutsuwa ya shafa fuskarsa tareda maido kallonsa Kan fuskarta Yana riqo hannunta cikin kulawa da nutsuwa yace”

 

Zarah ki daina damuwa akan Abinda ba Allah ne yafadaba,

Banson Baki empty hopes Amma Dan ance bazaki sake haihuwa ba ba lallai bazaki sake haihuwar ba sbd ba fadan Allah bane ki dauki qaddara ki rungumeta Allah nason bayinsa masu yadda da qaddara.

 

Dago jajayen idanuwanta dake tsiyayar ruwan hawaye tayi ta kallesa cikin tunani daban daban Wanda ya kunshi irin hope din data hangowa kanta na samun soyayyarsa ta hanyar Tara zuria me albarka dashi sbd gano burinsa da qaunarsa tason Tara Yara.

 

Kamar yasan Abinda take Tunani ta ganin irin kallon datake Masa ya rungumeta ahankali tareda shafa Bayanta cikin murya me taushi yace”

 

Zarah yanzu ke ba matata ce kawaiba ke uwar ‘yayana ce,

Ayanzu kin riga kinzama wani sashe na rayuwata da zuciyata,

Samun haihuwa a tsakani wani alamarine me girma Dan kuwa kinriga kinzama tamkar jagoran zuriar dazan Tara a gaba ko ba naki yayanba,

A da ke zarah ce matar MAHMOUD yanzu Kuma ke zarah ce matar MAHMOUD uwargidansa Kuma uwar Dan haka ki cire kowane irin tsoro ne kikasa acikin ranki sbd mi MAHMOUD DAHEER ZABEERA Ina baki tabbacin mutuwace kawai zata cireki daga rayuwata.

 

Wani irin kuka tasaki tana sake qanqamesa zuciyarta na cika da farin ciki da nutsuwar zancensa….

 

Ahaka ummanta tashigo tagansu Dadi yasake kamata ta karba Modibbon ta fita dashi sbd su iyami dasu maman junior dasukazo ganinsa.

 

 

Kwanansu shida a asibitin aka sallamesu suka dawo gida inda kowa keta zuwa barka da farko gida taso komawa MAHMOUD din yace tazauna a gidanta bayason zuwanta ko Ina.

 

Amatu kullum tana kiransu Jin takeyi kamar tazo Amma Babu dama Dole saidai take ganinsu ta hotuna shikansa MAHMOUD din bataga alamar zai barta tabiyo hanyar zuwaba sbd ko school yanzu ya hanata tuqi da kanta anty salamatu ke kaita wani lokacin Kuma USI idan yanada time kenan sbd akusa da street dinsu yakama apartment yake zaune.

Ranar data Fara Masa maganar tanason zuwa Kai tsaye yace”

 

No,Babu inda Zan iya Bari kije until you deliver.

 

Dama tasan haka zai fada Dan haka Bata wani damuba ta bar zancen ta maida hankali Kan rainon cikinta da karatunta ta bangare daya ga MAHMOUD din dayanzu wani soyayya yakeji kodan itama lokacin haihuwarta ya matso ne Amma sam yanzu ko barinta bayayi ta sarara akan Kiran wayarsa.

 

Bayan sunan Modibbo da sati uku yayi daidai da Gama exams dinsu tana gida kwana biyu Babu inda take fita ga nauyin cikinta ya dameta ma gabaki daya.

 

Zaune take ita kadaice agidan anty salamatu sunfita da USI siyayyar wasu daga cikin kayansa na lefe dayake siya tun anan sbd Shi da Nuratu sungama daidaicewa tsakaninsu yana dawowa yakeson ayi idan son samunsanema to ahade aurensu danasu anty salamatu sbd dagashi har nuratun kamar zasu cinye juna sbd soyayya shiyasa itama yanzu nuratun kamar ta hadiye Amatu sbd qauna Dan sai yanzu take qara sanin mahimmanci Amatu agurin USI da irin tsananin qaunar junansu dake tsakaninsu.

 

Kallon wani tv program na likitoci takeyi a CWTv hankalinta rabi nakan waya sbd tun safe take kiran wayarsa Bata shiga Kuma shima tun Daren jiyan raban daya kirata.

 

Sake Danna kiransa tayi akaro ba adadi still Bata shiga tana qoqarin sake Kira taji ana qoqarin bude qofarsu ta shigowa ta juyo tana kallon qofar da waya a hannunta sukai Ido biyu itada shi ta Dan zaro Ido tana kallonsa tareda miqewa tsaye komai nata na bayyanarda mamakin ganinsa shikuwa kallonta yakeyi cikin kewa da soyayyarta ya tsaida kallonsa Kan cikinta dayayi girma cikin wata free doguwar rigar masu ciki data saka wadda batakai qasa ba sbd kada ta takurata ya ware Mata hannu Yana kallon fuskarta daukeda boyayyan murmushi da gudun dabatasan zata iyaba tayo kansa ta fada jikinsa ya rungumeta Yana Dan dagata sama cikin farin ciki da murna tace”

 

I love this surprise of urs Husband.

 

Sauketa yayi tareda Kama hannunta suka qarasa shigowa taso karban luggage dinsa ya hanata suka nufi dakinsa tafara gyarawa Yana tayata suka gyara dakin duk da Babu Abinda yayi ‘yar qurace kawai.

Wanka yashiga ta fita zuwa kicin hada Masa abincin dazaici.

Cikin farin ciki tafara dafa Masa pasta da carrots sai beef meat ta hado Masa Kan tray takawo Masa har bedroom dinsa yaci tana zaune tanata tambayarsu Modibbo Wanda kamar ubansu daya da Muhammad sbd suna dibar kamanni.

Yana gamawa ta kwashe kayan ta maida ta dawo ta zauna Kan cinyarsa tana sake tambayarsa meyasa be fada Mata zaizoba.

 

Fuskarsa ya Dora kan tata Yana sauke ajiyar zuciya a boye yana kallon cikin idanuwanta da itama shi take kallo ya Dora hannuwansa Kan cinyoyinta Yana shafawa cikin malalacin sauti yace”

 

Sbd inason ganin farin cikin bazata a kyakkyawan fuskan matana.

 

Murmushin Jin Dadi tasaki tana sake shigewa jikinsa ahankali tana qara cukuikuyesa qasa qasa da murya tace”

 

Ko acikin barci MAHMOUD ZABEERA yazomin farin cikina bayyananne ne bare ganinka a zahiri so lovely husband zuwan bazatanka ya tafi da zuciyan AMATULLAH K.

 

sake matsota yayi cikin jikinsa Yana shaqar qamshin jikinta ya shaqi numfashinta dake sauka Kan fuskarsa sbd matsuwar dasukai da juna ya Dora bakinsa Kan nata Yafara kissing dinta Yana zame hannuwansa zuwa wuyan rigarta.

 

Koda anty salamatu suka dawo da daddare guraren 9 Bata tareda wata gajiya sosai sbd sun Dan bibbiya guraren hutawa sun shaqata bataga Amatun ba a apalo ta shige da kayan zuwa dakin Amatun inda sauran kayan lefen suke Nan na Bata ganta ba sai tayi tunanin toilet Dan haka dakinta Takoma ta fada toilet itama tayo alwala tazo ta tayarda sallah.

 

Jin shiru shiru ba motsin Amatu yasata fitowa tana zuwa kicin ta duba ko tana can,

Ganin anyi sabon girki a kicin din yasata bubbudewa tana dubawa tafito  Palo ta nufa dining tana ganin plates da kayan da akai amfani dasu ta fahimci oga kwata kwata ya taho kenan ta fito kicin tana kallon hanyar zuwa dakinsa tasake tabbatarda shi dinne yazo ta wucewa daki tana cewa”

Naji dadin zuwanka nasamu yanzu nabi usi next week idan zaije gida.

 

 

Washe gari tana kwance cikin jikinsa tana bacci cikin nutsuwa sbd irin kyakkyawar rungumar da yayi Mata suna bacci cikin baccin tafara Jin kamar ciwo ciwon Mara na damunta Wanda yasata bude idanuwanta tana sake saurarawa Abinda takejin saitaji da gaske ciwon yake ta yunqura zata tashi zaune yabude idanuwansa Yana kallonta ta yunqura ta tashi zaune ya tashi shima Yana riqota yace”

 

Lafiya kuwa?

 

Kallonsa tayi da sauri tana dafe qasan cikinta a Dan tsorace tace”

 

Ina ganin labour ne….. kasa qarasawa tayi cikin tsananin azaba da firgici tace”

 

Hospital hospital hospital take me” duk arude take maganar a jujjuye batareda tasaniba

Ganin hakan ya sauko gadon ya nufi wardrobe ya dauko shirt da wando yasaka cikin sauri tareda dawowa ya dauko Mata riga kamata ya sanya Mata suka fito tana sake dafe cikinta cikin azaba tana Kiran sunan Allah Dana MAHMOUD din cikin ciwo.

 

Jin dogon salati da qarfi yasa anty salamatu fitowa daidai qarasowarsu tsakiyar palon a Dan rude ta kallesu tana maida kallonta Kan Amatun daketa faman salati ba qaqqautawa cikin mamaki tace”

 

Subhanallah haihuwar ce ko me?

Lafiya kuwa?

 

Muje asibiti”kawai ya iya furtawa anty salamatun Yana nufar qofa da matarsa.

A gigice suka Isa asibiti musamman da ciwon ya taso Mata gabaki daya suna Isa ruwan haihuwa na fashewa akai labor room da ita.

 

Zama yayi Kan kujerun jira Yana kashe wayarsa sbd baya buqatan ko hayaniyar ringing waya.

Suna zaune saiga USI shima ya iso Nan suka Fara zaman jigum jigum cikin zullumi da fargaba,

Wannan zaman jiran dayakeyi yau yana daya daga cikin ranakun tsananinsa na rayuwa sbd gabaki daya Jin yake kamar nutsuwarsa zata bar jikinsa Amma haka dai yake zaune shiru kamar ba Wanda ke cikin tension ba.

 

USI da anty salamatu ne ke samun damar waya da Yan gida sunajin yaya kota haihune?

Zaman awa uku sukayi cikin ta hudu kafin Allah yabata ikon haihuwar baby girl lafiyayya da ita saidai ba qatuwa bace sosai sai kuka takeyi aka shiryata aka miqowa familynta ita ya karbeta Yana kallonta cikin wata irin nutsatsiyar sonta da qaunarta ya shafa Dan qaramin kumatunta Yana Mata adduoi da murmushi akan fuskarsa yace”

 

De symbol of my love FADIMATU ZARAH MAHMOUD ZABEERA.

 

Aikuwa cikin farin ciki anty salamatu itama ta karbi babyn tana kallon fuskarta cikeda murna tace”

 

MAHMOUD wannan ‘ya da yayunta take Kama.

Murmushi kawai yasaki zuciyarsa na sake wanzuwa da farin ciki sai alokacin ya bude wayarsa da atake Kira suka Fara shigowa ya fice Yana amsawa.

 

Yana dawowa ya tararda anfito da Amatun ankaita dakin hutawa ya shigo Yana aika Mata da wani irin kallon samun nutsuwa ya qarasa bakin gadonta ya zauna tareda Dan rungumota yabata kiss agoshi yace”

 

Thank you.

 

Murmushi tasaki tana Dan harararsa tace”

 

Bazan qaraba daga wannan.

 

Dariya maganar tabawa anty salamatu takuwa ringa qyaqyata dariyarta shikuma wani guntun murmushi ya sake Yana sake kissing hannunta dake cikin nasa batareda yace komaiba.

 

Acan Nigeria kuwa cikin both families din haihuwar ta Isa kunnen kowa akaita Sanya alkhairi da yiwa FADIMATU ZARAH adduar Allah ya raya Akan sunna,

Zarah da akaiwa takwara kuwa rasa abin cewa tayi sbd farin ciki shiyasa ma tace zatazo taga takwara da kanta.

 

Kwananta daya a asibitin suka sallamota suka dawo gida Nan anty salamatu tayita hidima dasu ganin suna hutu Kuma gashi umme da zarah hadda Nuratu since zasuzo yasa ya yanke shawarar su dawo gida bayan ko 30days ne saita dawo.

 

Kwana biyar da haihuwar suka dawo Nigeria Nan aka kacame da sabuwar murnar zuwansu ‘yan barka suka Fara sintiti musamman aminanta su maman junior da kullum saisun Zo iyami ma kwana biyu ta jera tana zuwa Saida akai suna tukuna suka samu sauqin baqi sai alokacin tafara samun kanta.

 

Yau satinsu uku da zuwa tuni tafara Shirin komawa musamman ganin yanda ogan yafara shishige Mata tanason Takoma tasamu matakin dauka kafin wani abun yasake Shiga sbd taga alamar son dawowa bakin aiki yake.

 

Ana gobe zata koma tafito palonta zuwa sashen anty zarah saigasu taci karo dasu sunfito itada MAHMOUD din Yana daukeda Modibbo hannunsa daya Kuma Yana riqedana ZARAn sunci ado cikin traditional attire sai murmushi suke ta qaraso suka hade tana murmushi ta gaida anty zarah tana cewa”

 

Fita zakuyi?

 

Eh Amma ba dadewa zanyi ba gurin umma zai ajeni.

 

Ok to adawo lfy Ina gaida umman bansamu nazo nayi Mata bankwana ba.

 

Kallonsa tayi shima tana sauya kalar murmushinta zuwa na neman mgn tace”

 

Take care.

 

Fuskar fadimah ya shafa Yana gyada Kai.

Suna wucewa Takoma ciki taqarasa sauran parking din da bataiba.

 

Washe gari anty zarah ce takaisu airport suka wuce dagacan ta wuce gidansu gurin ummah.

 

Bayan dawowarsu Greece da sati biyu yakoma bayan sun dauki me aiki da Nanny hakan saiya taimaka Mata sosai sbd samun damar maida hankali ga karatunta.

 

Rayuwa ahankali tafara sauri fadimah tayi wayo sosai tana cikin final exams dinta ta fahimci tanada wani cikin hankalinta yatashi sbd fadimah Bata Isa yayeba Dan haka taso cire cikin saigashi kamar Wanda aka fadawa yayi Mata zuwan bazata cikin sa’a kuwa kafin yatafi Saida yasanda zaman cikin Wanda yasama ya daga komawarsa yaqara kwanaki Saida tagama exams dinta akai duk wata hidimar daza’a yi ta karbi takardunta suka dawo Nigeria sbd shagulgulan bikinsu USI da aka Fara Wanda aka hade danasu anty salamatu Dan haka biki sosai akeyi a zabeera Koda ta iso ta fada cikin hidimar gadan gadan sbd dama amatse ake ta iso sbd wasu abubuwan da akeson gudanarwa Wanda suke buqatar kasantuwarta bikin USInta guda dakuma antynta anty salamatu.

 

Ranar asabar aka gama bikin amare kowacce ta tare gidanta

Anty salamatu zabeera ita Kuma Nuratu cikin sabon qaton sabon gidanta da USI ya Gina musu Wanda zasu zauna tareda iyayensa.

 

Ana kammala bikin ta yaye fadimah wadda anty zarah ce ta hadasu ya yaye tareda Modibbo takwashesu suka koma gurin umma tace sunyi yayen acan.

 

Ganin zarah batanan dazaiyi tafiya saitace zata bisa takuwa shirya tabisa suka tafi sudan.

 

Satinsu biyu suka dawo anty zarah ta karba miji daganan zaman ya Dore ahaka cikin kwanciyar hankali ba hayaniya sbd kowacce ta shafawa kanta lafiya sbd fitinar wani lokacin Hana komaima takeyi a tsaya guri daya akasa gaba akasa baya.

 

Lokacin haihuwarta nayi ta haifi baby boy aka saka Masa sunan kawu suna kiransa ABBA bayan haihuwarta da wata shida anty salamatu ta haihu a hannunta a asibitinsu wadda MAHMOUD yasake sauya Mata tsari da girma tafara aiki tun bayan haihuwar ABBA shiyasa itacema ta karba haihuwar antu salamatun data samu BBY girl itama bayan sunan anty salamatu da sati biyu Nuratu ta haihu itama a hannunta tasamu Me sunan kawu DR USMAN K SALEH yasawa babyn.

 

Fadimah a hannun anty zarah take Dan haka ita ABBA ne kawai agabanta  Muhammad ma tuni yafara zama saurayi Yana gurin Rabin ransa umme  wadda takejinsa fiyeda sauran ‘yayanta Dan haka Babu me tabasa.

Shima ABBA Yana Isa yaye iyami ce tayi yayensa Nan MD yasata gaba akan sabon baby yakeso tanajin yafara fadar haka taso daga hankalinta Saida anty zarah Tai Mata waazin damace Allah yabata tayi haihuwar ta huta tunda gashi ita tanaso Allah be Bata ba.

 

 

Kallonsa tayi lokacinda tafito daga toilet daureda qaramin towel da ko Gama rufeta baiyiba ta qaraso inda yake zaune Yana aiki da laptop ta zauna Kan cinyarsa tana tanayi kamar zata saki towel din ta marairaice murya tace”

 

Positive.

 

Dagowa yayi Yana kallonta da fararen idanuwansa Yana Mata kallon are you serious?

 

Daga Masa Kai tayi yayi saurin rungumeta Yana zura hannu cikin towel dinta Yana cewa”

 

Thank you love.

##Mamuh#

 

 

ALHAMDULILLAH.

 

Da yardar Allah anan mukazo qarshen wanann littafin namu me suna MIN QALB wato DAGA ZUCIYA,

 

IDAN NAYI MANTUWAR WANI ABUN DABAN QARASA FADABA A LABARIN KUMIN UZURI KU DAUKESA AMATSAYIN AJIZANZI IRIN NA DAN ADAM.

 

INA ROQON ALLAH YABAMU IKON AMFANI DA ABIN ALKHAIRIN DAYAKE CIKI SABANINSA KUMA ALLAH YA MANTAR DAMU YAKUMA YAFE MANA,

 

AKWAI WAINDA TUN BAAZO QARSHE BA SUNA MAGANAR DANGINSU AMATU DA USI,

ANSAN KOWA BA DAGA SAMA YAFADO DUNIYA BA AMMA KADA KU MANTA AKWAI MARAYUNDA ADUNIYA HARSU BARTA BASUSAN ASALINSUBA BARE DANGINSU,

AKWAI WAINDA SUKE RAYUWA BATAREDA SUNSAN ASALINSUBA KO INDA SUKA FITO AMMA SAI ALLAH YABASU IKON GINA TASU RAYUWAR SU GINA ZURIAR KANSU DAN HAKA KU SANYA SU AMATU AKAN MASU IRIN WANNAN QADDARAR SBD A DUNIYA BAKOMAI KAKE SAMUBA.

 

ALLAH YA GAFARTAMANA

AMIN.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MIN QALB 38

Advertisement   MQ 38_*       Anty salamatu da umme dake qoqarin fitowa mota jikinta duk a…

MIN QALB 43

Advertisement   Daqyar Amatu ta iya daga hannu takai wuyanta tana Dan sosawa akunyace zuwa kanta sai alokacin…

MIN QALB 48

Advertisement   MQ 48_*   *_THE FLAVORLAND BY ACEEY_* Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements…

MIN QALB 17

Advertisement   MQ 17_* _Mg_     Ana qoqarin turata motar Yan sandan ta hangosa tareda mutane Yana…

MIN QALB 11

Advertisement  _*MIN QALB 11*_ _mamuhgee_ Babban palone na alafarma irin tsarin sarautar zamani daya dauke setin royal kushins…

MIN QALB 8

Advertisement  *_MIN QALB 8_* _mamuhgee_ Kallon tsantsan mamaki da firgici yanzu takewa amatu din tana kallon qafafunta zuwa…