MOON 59-60

Advertisement

 

*MOON*

   _✍🏾By NIMCYLUV_

59-60

Advertisements

*SIRRIN MU*

 *coming soon🔥*

_Masoya littafin MOON a Mutsa nasan in sha Allah zaku biyo ni a Wannan book ɗin, i hope hajiyoyi masu jiran Moon ba zaku ban kunya a wajan siyan SIRRIN MU ba??_ *the romantic and love story* _wlh don’t missed it tunda akace SIRRI kun san akwai abubuwa Musamman 💋❤️ wanda ya keson yin payment zai biya #500 acct number 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 🤙🏽 ga masoya na NIGER suyi mgn a wannan number 84506476 sai na jiku_

Ƙara ƙanƙame ta yay kamar wani zai kwance masa ita banda rawa babu abinda bakinsa keyi, cikin rawar murya ya ƙara faɗin “Maimunatou…!!” Budurwar daya kira da Maimunatou ta ware idanunta tare da juyasu zuciyarta fal mmkinsa, tayaya yasan sunanta ko dai yana jin dukkan abinda suke faɗa ne idan sunzo wajansa? Amma abin da mmki ƙoƙarin zame jikinta tayi ya ƙara riƙeta ɗaga kai tayi zuwa saman fuskarta zaro ido tayi sbd ganin hawaye na tsiyaya daga cikin idanunsa zuwa saman innocent face ɗinsa.

Da sauri ta sanya hannunta ta cire masa hawayen dake fita a idanun nasa tace “Am sorry” shagwaɓe fuska yay a hankali kuma kamar me raɗa shima yace “Am sorry” Murmushi tai masa tace “For what?” Wani ƙawata taccen Murmushi yay wanda ya kusa sumar da ita sbd yadda ainayin kyansa daya baiyana,  lumshe idanunsa yay wanda ya riƙa ya zame masa ɗabi’a yace “For what?” Baki ta saka why yake maimaita dukkan abinda tace? Tayi tunanin tunda ya kira sunanta ya gama dawowa hayyacinsa, zame jikinta tayi daga nasa tare da zama saman kujera, zuciyarta na bugawa sosai sbd kwarjinin da yay mata yana da girma da jiki sosai ƙirar jikinsa kamar ta samudawa,

Advertisements

 idanunta a ƙasa tace “Sit” kallonta yake sosai yana ƙara sakin murmushi yace “Sit” juya idanunta tayi cike da tsoro  kafin a hankali ta miƙe tsaye zuwa inda yake tsaye tace “Come,idan nace sit ina nufin ka zauna like this” ta faɗa tana zama kan kujerar, kamar tsoko shima ya zauna saman cinyarta kamar yadda ta bashi example, saurin

 runtsa idanunta tayi sbd shock ɗin daya kamata ba,dukkan jikinta ya ɗauki rawa da ɓari tace “Ba..ba..ba a nan zaka zauna ba” shima zare ido yay yace “Ba…ba..ba a nan zaka zauna ba” hannu tasa ta miƙar dashi itama ta miƙe tsaye tace “Ina nufin ka zauna a nan” ta faɗa tana nuna masa saman bed kana tace “Ba’a zama saman cinyar mutum wajan da babu kowa kamar nan”ta ƙara nuna masa saman gadon tace “A nan ake zama,kuma ka dinga yin mgn ba wacce mutum yay ba”.

Shiru yay mata kamar dai yana fahimtar abinda take cewa idanunsa cike da hawaye yace “Maimunatou” Murmushi tai masa tace “Yeah! Dat’s my name Maimunatou Khalid” Kallonta ya ƙara yi ko ƙifta ido babu ya ƙara faɗin “Maimunatou” ya faɗa yanayi miƙa mata hannunsa.

Dr Joseph ne da wani magidancin mutumi bayansa kuma matashiyar mata hannunta riƙe da ƙaramar yarinya suka shiga cikin room ɗin, Magidancin mutumin yace “When kake expecting dawowarsa cikin

 hayyacinsa?” Dr Joseph yace “A gsky bana da masaniyya,amma zama kusa da wanda ya sani da kuma ƙoƙarin tuna abubuwan da suka gabata, Alhaji Khalid” Alhaji Khalid yace “Tayaya zamu san wanda ya sani?

bayan an faɗa maka tsintarsa akai a gaɓar Kogin Pakistan wanda yake iyaka” Dr Joseph yace “Haka ne,amma idan abinda ya faru dashi a baya harya shiga wannan condition ɗin a baya ya sake faruwa a kan idanunsa sai muga ya dawo hayyacinsa” Mumy dake baya tace “ikon Allah yafi gaban wasa,dama idan ba mutuwa kayi ba ance ba’a gama maka halitta ba, Allah dai ya bashi lfy” Ahj Khalid yace “Ameen” miƙewa Maimunatou tayi tace “Wlcm Daddy” ta faɗa tana bashi side hug, kanta ya shafa yace “ya mai jikin naki MAIMOON?” Dry tai tana kallon sa sbd shima miƙewa yay tsaye kamar yadda ta

 miƙe tace “Daddy baya magana, tunda na shigo yake faɗin sunana dukkan abinda na faɗa shi yake faɗa” Dr Joseph yace “ƙilan time ɗin da abun ya samesa da tunanin mai sunan ya faru dashi, ko kuma yana da relative da mai sunan ba’a min mmki bane ace a kanta ya shiga wannan yanayin, kinga kowa manta sunanta abune mai wahalar gaske garesa” kafin kowa yay mgn Dr Joseph ya ƙara faɗin “dole sai an ƙara koya masa komai domin yanzu dashi da jariri dai-dai suke,a yadda aka kula dashi a haka zai

 tafi,cin abinci Sallah,wanka azumi mgn duk dai” ƙara lafewa yay a bayanta tare da riƙe waist ɗinta da hannayensa cikin ƙasa da murya yace “Maimu..natou….” Ahj Khalid yace “da matsala tunda zai na kasancewa da wacce ba muharramarsa ba” MAIMOON dake tsaye ta kalli yadda ya riƙe mata ƙugu sosai sai rarraba idanu yake ga wata ajjiyar zuciya da yake saukewa “Don’t scared am with you” lumshe idanunsa yay tare da ɗura kansa a saman wuyanta, Mumy ta kalli Ismat kana ta kalli mijin nata tace “Ko

 sunansa bamu sani ba” Ahj Khalid na latsa waya yace “I think I’ll give him my son’s name, my lovely son that i missed” Murmushin jin daɗi Mumy tayi tace “Wow dear thank you so much” ta faɗa tana bashi hug, kallon Bayan Maimunatou yay yace “now you’re my son, my son is back wlcm IMAM (SIRRIN MU )”

Mumy tace “Wlcm back to your house My love Imam” ta faɗa tana rungomesa, kwaɓe fuska yay da sauri kuma yaja baya yana maƙalewa jikin Maimoon…Moon ce ta kalli Fulani wacce akace itace real mother ɗinta, ɗauke kai tayi tana jin kunyar mahaifiyar ta ta, Fulani ce ta sa hannunta ta ɗago kanta tace “talk to me my dear, Am your mother ba zan bari komai ya sake faruwa dake ba, i promise” idanun Moon ne suka kawo ruwa tana jin nauyin da zuciyarta tayi mata,

 tayaya Abbanta zai yake masa wannan hukuncin ta yarda zata Paris karatu,amma bam bata Amince da auren Yayanta Faizak ba,bata jin zata iya yiwa Dad ɗinta kishiya a zuciyarta, ba’a duba kankantar shekarunta ba,abinda ko prioud bata fara ba ai mata auren Farko bata sani ba yanzu miƙin

 zuciyarta bai gama warkewa ace za’a aura mata wani,gaba ɗaya bata huce 16yrs amma ai mata aure har kashi biyu ba’a duba kankantar shekarunta, ina sam ba zata iya ba.

Wasu hot tears ne suka fara fita a idanunta, Fulani tasa yatsarta ta sharce hawayen kafin tace “Am your mother Maimunatou u can hide anything to me, gayamin damuwarki” kuka Moon tasa tare da shigewa jikin mahaifiyarta Uwa uwa ce koda a bula take, tayi missed jikin mahaifiyarta a lot missed, ajjiyar zuciya ta fara saukewa, shafa kanta Fulani tayi tace “Cry my dear cry da dukkan zuciyarki da ƙarfin ki, yi kuka Maimunatou yi kuka mai yawa” wani gigitaccen kuka tasa jikinta har rawa yake ta ƙanƙame Fulani,ita kuma sai shafa sumar kanta take.

Almost 10mnt ta ɗauka tana kuka kafin ta shiga sauke ajjiyar zuciya mai ƙarfin gaske “What wrong with you Mamana?” Kwaɓe fuska tayi tace “he’s my brother to me, how is he going to be my husband?? Fulani bazan iya zama dashi ba i can’t Ammi” ta faɗa tana sake sakin wani sabon kukan.

Shiru gaba ɗaya sukai kowa da abinda yake damunsa, Faizak yaron kirki ne ɗa ne wajan Tiraki tun yana Ƙarami yake hannu Sarki Aliyu Al’amin, a sanda aka haif Moon akai masa al’ƙawarin aurenta,yasu Moon kamar ransa lokacin da aka nemeta aka rasa kusan haukacewa yay da ƙyar aka samu kansa, bayan wasu shekaru kuma shine ya bar ƙasar yaje bautar ƙasa,yanzu kuma yana ganin Moon ta dawo masa cikin sauƙi tayaya zaiyi saken da zai rabo da ita? Ai bazai taɓa yin wannan kuskuren ba tabbas,bata san yaya akai tai bacci ba sai saukar

 numfashinta mai zafi da taji a jikinta, gyara mata kwanciya tayi tare rufe mata ƙofar ɗakin tai waje..Washe gari da safe gaba ɗaya familyn suna breakfast a danning Area, Arish ne da tea with egg gabanta sai juya spoon ɗin hannunta take ta kasa kai koda abu guda bakinta,a zahiri idanunta akan Sarki Aliyu Al’amin yake amma zuciyarta ta tafi tunanin ALIYOU ENEYE AHUOYZA tana tuna dadɗan kalaman sa masu daɗin saurare a kunanta,tana son Aliyou sosai a age ɗinta bai dace ace zuciyarta taso wani ɗa namiji ba,when? a ina? Ta fara son Dad ɗin nata shine abin tambayar? Lumshe idanunta tayi tare da sauke ajjiyar zuciya cikin ƙasa da murya very slowly tace “My Aliyou my Gwarzo I missed your sweet lips, i missed you so much please come back to me, i wanted to cry on your shoulder” sai kuma hawaye shaaaa!!! Sarai Faizak yaji me tace amma ya share yay kamar bai ji ba down heart ɗinsa zafi kawai yake masa, daga ƙarshe ma miƙewa yay tare da ficewa daga cikin gidan baki ɗaya, Sarki Aliyu Al’amin yaja numfashi yace “Ki shirya next week zaki huce Paris” kasa magana tayi sai kallonsa kawai take kafin a hankali ta ajjiye spoon ɗin zata miƙe tsaye yace “Kul karki fara,yadda kowa yake cin abinci kema ki zauna kici bana son shirme irin

 wannan,kuma ki sani an gabatar da Engagement ɗinku kina kammala makaranta za’ai bikin” runtsa idanunta tayi sbd wani abu mai ɗaci ya tukare mata a maƙoshi, ranta babu daɗi ta fara danna soyayyan kwan a cikin bakinta.. Ahj Khalid ya kalli Matar sa Mumy yace “Ina tsoran yadda Imam ke shigewa Maimoon, ban mene gaba zai iya faruwa ba” gorar ruwan dake hannunta ta ajjiye bayan ta gama tsiyaya ruwan a cikin glass tace “ina wannan tunanin nima,amma ya kamata tun farko aiwa tufkar hanci kafin abin yay girma” Alj Khalid yace “Mene tunaninki?” Tace “a haɗa su aure kamar dai zaifi ko?”  Yace “abinda nake tunani kenan,amma ki fara jin ra’ayin ƴar taki” Mumy tace “In sha Allah” miƙewa tayi tare da nufar parlour’n a zaune ta samu Maimoon gefenta kuma Imam ne yana riƙe da hannunta kamar wani zai kwance babu laifi ya ɗan sake amma ba sosai ba kuma ya fara iya wasu abubuwan fiye da farko “Me kuke haka?” “Mumy yana kallon series film ne” zama Mumy tace “i want ask you

 something” Maimoon tace “All ears Mumy” Mumy tace “the like Imam?” Shiru Maimoon tayi tana kallonsa yana zaune sa 3gauther sai riga Armless wacce ta fito da six packs ɗinsa mai bala’in kyau, ya ƙara fari sai kuma ya koma very weak dry magana sam ya garara yi, kullum ba kinsa Maimunatou  “bafa kallonki nazu yi ba,hasali ma

 mahaifinki ya turo ni” “Mumy bro he’s nice person i like him bashi da matsala” Murmushi Mumy tayi domin tasa da wahala ƴarta ta tace bata son sa “But Mumy am scared” ware ido tayi tace “Akan me?” Maimoon tace “ban san wata rana ko zai ƙi ni ba” miƙewa Mumy tayi tace “ki nama kanki kyakkyawan zato” da ido Imam ya bita tana fita ya ɗura kansa saman shoulder ɗinta yace “Maimunatou….!!”

Tsaye Faizak yay a bayanta yana sanye da maroon ɗin Alƙyabba mai kyau sai sheƙi yake sam bata son da shigowar sa cikin lambun ba ta ware ganta ne domin ta samu cikakken tunani akan abinda zuciyarta take so kuma take muradi, mai yasa kullum take mafarki dashi yana miƙa mata hannu yana kiran sunanta,data ƙarasu wajansa sai kuma wata ta shiga tsakaninsu me hakan ke nufi is he still alive or what?? Wanna shine tunanin daya gama damun zuciyarta harta rasa yadda zatai da ranta “so the you miss me right?” Ta tsinkayi muryarsa a bayanta rufe idanunta tayi zuciyarta na halbawa da ƙarfi kamar zata faso ƙirjinta ta fito, kasa mutsawa tayi harya ƙarasu gabanta yana leƙa fuskarta, hannu yasa zai goge mata hawayen tayi saurin juyar fuskarta gefe, danne abinda ya keji yay harga Allah bai son careless ɗin da take nunawa akan

 soyayyarsu amma dole ya bita a hankali, fuskarsa ya shafa yace “Nasan dai wanda ya mutu baya dawowa,kuma bake ɗaya kikai rashin Aliyou tun kafin kisan Aliyou na sansa so ko zaki nuna zafin mutuwar da ka ɗan zaki fini, kin san am going to be your husband soon dear why kike banza da lamari na,ko ni ban cancanki ki so ni bane? Ko kuma ni ba miji na gari ba ne??” Ya faɗa yana rage muryarsa zuwa lokacin tuni 

 hawayen da take maƙalewa ya wanke mata fuska,  hannu yasa ya juyar da ita zuwa gabansa yace “Yasubuhanallah! Kuka? What making you sad?” Girgiza kai tayi tace “Am not sad am angry” sai kuma ta fashe da kuka, jikin sane ya fara rawa domin babu abinda ya tsana irin ya ganta tana kuka, ganin babu kowa a wajan cikin sauri ya jawota gabansa tare da haɗata da jikinsa…..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MOON 25-26

Advertisement   *⚡ MOON⚡* _✍🏻 Wattpad Nimcyluv_ _25-26_ Advertisements *DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV* https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ Kafin Eki ta sauke…

MOON 67-68

Advertisement  *MOON* _✍🏾67-68_ Please Subscribe my YouTube channel *Nimcyluv T.V* https://youtube.com/channel/UClywbagpRx5qlVyOy0ZPPDA Advertisements SIRRIN MU love and romantic story…