MOON 61-62

Advertisement

 *MOON*

                           _61-62_✍️

          Saurin zare jikinta tayi ta nasa ta shiga haɗe fuska, Murmushi Faizak yay mata yana jin ransa babu daɗi cikin ƙasa da Murya yace “Am sorry,i can’t control myself idan muna tare” banza tai masa sai hawayen da suke shiga zuba daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta,da sauri kuma ta fara tafiya tabar masa lambun gaba ɗaya, iska ya fesar kafin yace “what should I do?” Ya faɗa yana dafe kansa dake juya masa,da sauri shima yabar cikin lambun kai tsaye ɓangaren dawakai ya nufa ya samu sarkin dawakai suka fara


mgna kafin a ɗauko masa wani farin doki ingarma mai girman gaske,da sauri ya kama silken dokin ya hau cikin sauri kuma ya saki linzamin dokin yay waje da gudu.. washegari ta kama Friday tun asuba ta tashi da wani irin ciwon ciki mai a zabar gaske ga wani kumburi da mararta tayi mata, ciwon kai zazzaɓi duk suka taro waje guda sukai mata yawa, da ƙyar ta lallaɓa tai sallar asuba ta koma ta kwanta a hankali bacci yay gaba da ita sbd baccin da bata samu tayi ba, cikin baccinta taji amai na tasu mata da gudu tai bathroom ta shiga kwarara amai a cikin sink kamar zata amayar da abinda yake cikinta, Fulani dake bakin ƙofar bedroom ɗin ta tura ƙofar a hankali ta shigo, kamar zata shiga bathroom ɗin kawai saita zauna bakin bathroom ɗin ta shiga bin ɗakin da kallo, tana rawar sanyi ta fito daga cikin bathroom ɗin da sauri Fulani ta riƙeta tana faɗin “dabe careful” kwantar da ita tayi ta rufeta da duvet kafin tace “how long baki da lfy?” Bakinta yana rawa tace “jiya ne” miƙewa tai tace “Am coming” tana faɗin

Advertisements

 hakan ta fice daga cikin bedroom ɗin. Fulani na fita ta nemi mai Babban ɗaki tai mata iso a wajan sarki, babu daɗewa mai Babban ɗaki tace ta shiga, yana zaune a saman wata ladduma  mai taushi da kuma laushi, sanye da shigar ta Alfarma ga takubin Sarauta a gefensa yay kyau sosai kamarsa da Moon ta ƙara bai yana fiye da kullum, zama tayi cikin ƙasa da murya tace “Salam my king” murmushi yay mata yace “Salam Queen Maryam” kallonsa tayi tana sakin Murmushi shima kallonta yay domin kaf cikin matansa babu wanda yake so sama da Queen Maryan yace “what’s the matter?” Kanta a ƙasa tace “My king Autar ka ce babu lfy,shiyasa na nemi iso domin nazu na gaya maka” da sauri ya mike tare da ɗaukan takubinsa yace “what exactly wrong with you Queen Maryam? Shine tun safe baki faɗan ba sai yanzu, let’s go” ya faɗi hakan yana kama hannunta cike da izza da taƙama yake tafiya zuwa flat ɗin ƴar tasa,tun a hanya ya kira Dr Masarautar ya faɗa masa yana nemensa yanzu, babu jimawa Dr ya ƙarasu har cikin ɗakin Princess Moon or Queen Maimunatou, bayan ta dubata sosai ya tabbatar da abinda yake damunta drip yasa mata bacci ya ɗauke ta, Faizak dake tsaye yace “meke damunta?” Dr yace “time ɗin prioud ɗin ta ne ya fara” da mmki Yakumbo tace “kana nufin bata fara Al’ada ba sai yanzu?” Jinjina kai Dr yay yace “that’s what I mean” tace “da matsala idan haka ne” Dr yace “matsalar me? Bari kiji cikakken bayani akan Al’ada: 1

Menene Jinin Al’ada? Jinin al’ada jinine da yake fita da karan kansa daga gaban macan da a al’dance zata iya daukar ciki ba tare da ya wuce kwanaki goma sha- biyarba. Wannan shi ake nufi da jinin al’ada, da akace ‘jinine da yake fita da kansa’ kenan idan ya zamana ba da kansa ya fitaba kamar ace cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jinni ya balle mata to wannan bai zama jinin al’adaba. Da akace ‘Ta gaba’ kenan idan ya fita ta dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin al’adaba. Da akace ‘Wacce a al’adance

 zata iya daukar ciki’ kenan idan ya fita daga wacce a al’adance ba zata iya daukar cikiba sabo da yarinta ko girma to wannan shima bai zama jinin al’adaba. Amma da aka ce ‘Ba tare da ya wuce kwanaki goma sha-biyarba’ kenan idan ya wuce kwanaki sha-biyar to bai zama kuma jinin al’adaba. Wadannan nau’uka da akace basu zama jinin al’ada ba kenan hukuncin jinin al’ada bai hau kansu ba za su yi sallah domin jinin ciwone sai a nemi magani, Allah ya sawwake.

Mafi Karancin sa: Malamai sun karawa juna sani kan mafi karancin jinin al’ada, mafi karancinsa shine ‘dugo guda’ kenan idan ya duga sannan ya dauke, shikenan ta yi al’ada kuma ta dauke.

Mafi Yawan sa: Mafi yawan kwanakin jinin al’ada shine kwanaki goma sha-biyar kenan idan ya wuce haka to bai zama jinin al’adaba muddin ba ciki take da shiba.

STORY CONTINUES BELOW

Advertisements

Mata Dangane da Al’ada: anan mun sani mata suna da halaye biyar musamman idan muka yi la’akari da shekarunsu domin auna jinin da ya zo na al’adane ko bana al’ada bane, kamar haka: 1. Kasa da shekara tara: Idan jinni ya zowa yarinyar da take kasa da shekara tara to malamai sun tabbatar da wannan ba jinin al’ada bane, jinin ciwone sai a nemi magani.

2. Tara Zuwa Sama: Idan ya zamana jinin ya zo ne ga wacce ta cika shekara tara zuwa zamanta budurwa, to a irin wannan lokaci sai a tambayi kwararrun mata da likita domin a fayyace jinin na al’adane ko na ciwo. Kada mu sha’afa yanayin abinci da kuma yanayin zafi da sanyi da hutu da wahala suna tasiri.

3. Budurci Zuwa Sheka 50: Idan jinni ya zo daga lokacin da ta zama mudurwa zuwa shekaru hamsin (50) kai tsaye malamai sun tabbatar da cewa wannan jinin na al’adane.

4. Daga 50 – 69: Idan jini ya zowa mace a tsakanin wadannan shekaru wato daga shekara hamsin zuwa sittin da tara (50-69) to malamai sukace za’a tambayi kwararrun mata da likitoci domin sanin wannan jinin na ciwone ko na al’ada.

5. Daga 70: Idan jini ya zo bayan mace ta cika shekara saba’in (70) zuwa sama to malamai sukace wannan kai tsaye ba jinin al’ada bane. Ashe tantance shekarun haihuwa ba karamin abu bane domin tuni musulunci ya gina hukunce hukunce akansu, kuma ana ginine akan tsarin kalandar musulunci, wadannan bayanai na karkasuwar mata har zuwa gida biyar kamar yadda ya gabata haka malam Adawi ya kawo a cikin littafinsa ‘Hashiyatul Adawi’, Allah ya ji kansa da gafara.

Ina dada jadda cewa yanayin abin ci da da abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri matuka, dukkan abinda ba’a fahimta ba dangane da yana yin zuwan jinni ko daukewarsa yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi bayan da cewa yanada alaka da hukunce hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da aka saka zata iya kammala idda akasa da watanni uku. Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama shine zuwansa na farko sannan ya tabbata cewa jinin al’adane to ta sani ta balaga, dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau kanta, idan ta yi salatin Annabi za’a rubuta bata lada idan kuma ta bari samari suna jagwalgwalata ita za’a rubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai ta yi aure sannan za’a fara yi mata rubutu, kenan har azumi sai ta ranka wanda ta sha.

Tabbatuwar Jinin Al’ada: Shifa abinda ya shafi jinin al’ada al’amari da Allah madaukain sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur’ani mai girma, Allah yana cewa: Kuma suna tambayarka dangane da al’ada, Kace: Shidinnan cutane, ku ninci (saduwa da) mata a lokacin al’ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka (suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba kuma yana son masu tsarkaka. Bakara, ayata: 222. Haka kuma ma’aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace; (Wannan) Wani abune da Allah ya dorawa mata ‘ya’yan Adam. Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane ai sanadiyyar da yasa mata suke al’ada shine wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa’u ta ci a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala’ikane ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya amayar da abin shi yasa maza basa yi. Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur’ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci itaciyar. Shifa jinin al’ada kada amanta jinine da yake fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu, Allah madaukakin Sarki ya haliccishi domin ya zama abin ci ga yaro a lokacin da yake cikin mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da karfinta ya ragu sosai, sa Allah ya sanya shi ya zama abinci ga reshi, shi yasa dakyar kaga mace tanada juna biyu (ciki) kuma tana al’ada. Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar da shi nono jaririn yana sha amatsayin abin ci, shi yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa kuma suna al’ada. Idan ya zamana mace bata da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya kasance ba inda zaii je to shine sai ya taru a mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah- gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.

STORY CONTINUES BELOW

wannan yadda jinin al’ada yake kwarara kenan daga jikin wata baturiya

Karkasuwar Mata: Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al’ada, kashi na farko; itace wacce ta fara, kashi na biyu kuma; wacce ta saba, sannan sai kashi na uku; mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka:

ɗigon Jinin al’ada

1. Wacce Ta Fara: Ita wacce ta fara al’ada ya zama yinta na yanzu shi ne ganin al’adarta na farko a rayuwarta, to abinda dake kanta zata zuba idone ta ga kwanaki nawa zauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-biyarba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al’adaba, kenan mafi yawan kwanakin da zata saurara sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama (Isthala) cuta sai a nemi magani, anan nake cewa iyaye su kara sa ido akan ‘ya’yayansu mata su dungu tuntubarsu suna fahimtar da su tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko makamantan haka, wata babbar macece amma bata san menene jinin al’adaba ita dai kawai tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganinshi.

2. Wacce Ta Saba: Abinda ake nufi da wacce ta saba itace wacce ta gabatar da al’ada sau uku a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al’adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai muce sunanta wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki sanannu. Amma idan ta yi al’adar karo na farko kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar karo na uku kwanaki shida to ba za’a kira wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da tsayayyun kwanaki.[5] Ita wacce ta saba wato wacce take da sanannun kwanakin al’ada to wadannan kwanakin sune kwanakin al’adarta, idan kwanakin suka cika al’adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada, amma idan kwanakin suka cika al’adar kuma bata daukeba sai ta kara kwanaki uku, haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki shabiyar su cika, misali idan al’adarta kwanaki biyarne sai kuma jinin bai daukeba a kwanaki biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan takwasdin sun zama sha-daya idan bai daukeba sai ta kara uku sun zama sha hudu idan bai daukeba sai ta kara kwana daaya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al’ada ko ya dauke ko bai daukeba domin kwanakin al’ada makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma sun cika, abinda ya ci gaba da zuwa ba sunan shi jinin al’ada ba sunanshi jinin cuta (Istihadha) sai a nemi magani.

Adukkan wadancan kare-karen kwanaki da aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na saurare sai ya dauke a kwana na daya cinkin hukun shikenen sai ta yi wankan tsarki. Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al’ada bai wuce kwanaki goma sha- biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.

3. Mai Juna-biyu (Mai ciki): Galibin mata masu juna biyu basa al’ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga al’ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita . Idan al’ada ta zowa mace mai junabiyu to idan cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin al’ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al’adar zata iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha’afa wurin tuntubar likita idan ana da juna biyu kuma aka ga jini. Tanbihi Na Daya: Idan mace jini yana mata wasa wato ya zo yau gobe sai kuma ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abinda zata yi anan shine, ta tsaya ta yi karatun ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al’ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki domin da hakane zata cika kwanakinta na al’ada, misali kwanaki tara; sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al’adar kwana biyar a cikin kwanaki goma, wannan matar ita ake kira (Al-Mulaffiqa) alarabcin mata masu al’ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da dawowarsa to na biyun zai zama sabon jinine kenan, ba na dane ya dawaoba. Alamar Daukewar Jinin Al’ada: idan jinin al’ada ya dauke akwai alama da shara’a ta sanya domin ya zama shine manuniya akan cewar al’adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, sune kamar haka:

STORY CONTINUES BELOW

1. Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gabanta ta fito da shi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata al’adarta ta dauke.

2. Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari mai laushi da yake zuwa karshan al’ada, idan mace ta ga irin haka a karshan al’adarta to ta sani ta kammala. Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al’adar mace, idan mace bata taba ganin al’adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki ba sai ta jira farar kumfaba, amma idan wacce ta saba ganice sai ta ga bushewar gaba to malamai sukace zata zata dan saurara kadan domin jirar faran kumfa, amma jinkirin ba zai kai ga fitar zababban lokacin sallah ba. A dunkule dai kowanne daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai ta yi wankan tsarki domin ta ci gaba da ibada, domin idan bata yi wankaba ko da jinin ya dauke mijinta ba zai sadu da itaba ba kuma zata yi sallaba, da dai sauransu. Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga-diddiga bayan daukewar jinin al’ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma idan a karshen jinine to wannan ba komai, Ummu Atiyyah medakin ma’aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: ((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi- fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune)). Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa’i, Hadisi Na: 368, Ibnu Majah Hadisi Na: 647, Darimi Hadisi Na: 865. Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar asuba, amma ba’ace ta tashi cikin dareba domin ta duba.

Idan mai al’ada ko mai biki (jinin haihuwa) ta ga tsarki kafin rana ta fadi to sallar azahar da la’asar sun hau kanta, hakanan kuma idan ta ga tsarki kafin hudowar alfiji to tabbas za ta yi sallar magariba da lisha. Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai- al’adaba: Anan za’a lissafa abubuwan da basu halatta mai al’ada ta yi su ba ko ayi mata ba, wadannan abubuwane guda goma:

+

1. Sallah: Bai halatta mai al’ada ta yi sallaba farilla ko nafila, idan kuma tayi ta yi ba’akarba ba sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta kammala al’adar ba zata rama sallolinba.

2. Saki: Baya halatta matar da take al’ada a saketa, wannan ya sabawa karantarwar musulunci, saboda haka koda yana son ya saketa to ya bari sai ta kammala al’ada kafin ya sadu da ita sai ya saketa, kuma dai idan ya saketa tana jinin al’adar to sakin ya yi amma za’a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai kai ukuba.

3. Dawafi: Bai halatta mai al’ada ta yi dawafin Ka’abah, amma zata yi sauran dukkan abinda maniyyaci yake yi, kamar tsaiwar Arafah da kwanan mina dana muzdalifa da jifa da Labbaika, da daidai sauransu.

4. Zama A Masallaci: mai al’adah ba zata zauna a cikin masallaciba, domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu.

5. Azumi: Bai halatta mai al’ada ta yi azumi na farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yiba, saboda haka zata lissafa azumin da ta sha bayan watan ya wuce sai ta ramasu. Ba’a ajiye azumi domin tsammanin gobe al’ada zata zo, amma dazaran ta zo to dazaran ba azumi, dazaran bata zoba to dazaran akwai azumi, ko da kin ji tafiyar jinin ajiki amma bai fitoba to biki fara al’adaba, sai ya fitane za’a fara lissafi.

6. Daukaa Alkur’ani: mai al’ada bata dauka Alqur’ani kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.

7. Karatun Alkur’ani: mai al’ada bata karanta Alkur’ani, dudda cewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karantashi da ka domin kada ta manta sabanin dauka.

8. Saduwa: Bai halattaba saduwa da mace tana al’ada, idan ta ki yadda da mijinta ya sadu da ita domin tana al’ada ba za’ace ta sabawa Allah ba asalima ta yi biyayyane ga reshi, bai halatta a sadu da mace tana al’adaba har sai al’adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki, kenan koda al’adar ta dauke amma batayi wankaba to bai halatta a sadu da itaba. Ya halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin matarsa alokacin da take al’ada bayan ta yi kunzugu inbanda daga cikbiyarta zugwiwarta wannan kan bai halattaba har sai jinin ya dauke kuma tayi wanka, hakanan itama ya halatta ta taba ko ina a jikinsa duk da tana al’ada.

9. Tabbatar Da Rashin Tsarki: Al’ada tana tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.

10. Wajabta Wanka: Al’ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar da ta yi al’ada kuma al’adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta. Daga wadannan bayanan da suka gabata ya bayyana a fili cewa lalle jinin al’ada bakaramin hukunce-hukunce yake da shi ba, kuma lalle idan aka kyalleshi yadda ake sakaci tsakanin maza da mata akan abinda ya shafi wannan al’amari to lalle abin yanada ban tsoro.

Allah ya datar damu yasa mu dace. Allah shine mafi sanin.

Gaba ɗaya suka jinjina kai alamar gamsuwar da bayanin da Dr yay masu,gdy sukai masa daga nan ya haɗa kayansa yabar cikin gidan. Babban club ne baka jin komai sai ƙarar D.j dake tashi, wasu na karta wasu na shan shisha wasu kuma na rawa haka dai,zaune yake saman wata kujera da kulbar win a hanunsa, yana sanye da wando 3gauther da wata ƙaramar riga sai ƙatuwar sarƙa a wuyansa,ya sanya wani baƙin glass a saman idanunsa, wani dake gefensa yace “Og yanzu mene abinyi tayaya ka tabbatar Deen yana raye?” Dry Farouk yay yace “kana wasa dani, Deen yana raye bari kaji abinda baka sani ba, akwai wata yarinya mai suna Salmerh ɗaya daga cikin yaran dasu Oga Taju sukai safarar, tana son Deen sosai kasan akwai yarona a cikinsu wato Ovasi, shike gayan komai, to a lokacin da bom ɗin ya kusa tashi ita Salmerh ta fita daga cikin ɗakin da aka ɓoyesu da gudu ta fita ta shiga cikin tana shiga ta samu Deen ya lumshe idanunsa banda kalmar shahada babu abinda yake, tana zuwa ta fara ƙoƙarin ɗauke dutsen cikin Sa’a kuma ta zare dutse miƙewa Deen ganin saura 50seconds bom ɗin ya tashi yace “let’s go Salmerh” Murmushi tai masa bata nuna masa ƙarfen ɗaya riƙe mata riga ba tace “i love You so much ban san yaya zan gaya maka son da nake maka ba, kullum ina ƙoƙarin danne abinda ke zuciyata a game dakai,hakan yasa yau na yanke nuna maka tsantsar soyayyar da nake maka,babu lokacin ya kamata kamar wajan nan” kafin yay magana tasa hannu ta hankaɗa sa ta cikin window’n dake kusa dasu a dai-dai lokacin kuma bom ɗin ya tashi da Salmerh dukkan wani part na jikinta sukai pecies….

To be Continued…

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

MOON 65-66

Advertisement   *MOON* _✍🏾65-66_ DON ALLAH SUBSCRIBE MY YOUTUBE CHANNEL  Advertisements https://youtube.com/channel/UClywbagpRx5qlVyOy0ZPPDA Ware idanunsa Mutumin dake tsaye gefen…