MOON 63-64

Advertisement

 *MOON*

_✍🏾 Nimcyluv_

63-64

ELEGANT ONLINE WTITERS

Advertisements

Jan gemunsa Farouk yay yana sakin Murmushi wanda kana ganinsa kasan na mugunta ta ne kana yace “Lokacin hutawarsa ne yanzu, kaje ka huta King Aliyou Eneye Ahuoyza Deen”Wanda ke kusa dashi yace “Oga yanzu yana ina? Babu da sauran time kafin ace ya dawo gareta yana da kyau musameta ko?” Baya Farouk yay idanunsa akan wata budurwa dake rausayawa yace “A.j kasan dole zan san inda Aliyou yake,banyi niyyar kashe fa shiyasa har na bari aka taimakesa,a lokacin da bom ɗin ya tashi ni masa Ovasi ya ɗauke sa sbd duguwar sumar da yay,abinda basu sani ba duk wannan faɗan da ake nima ina cikin ƙasar, bayan Ovasi ya ɗauke sa ne ya kaisa can bakin ruwa inda manyan masu kuɗi suke hutawa,amma inda ba za’a a ganshi ba, bayan ya kaisa ya dawo yake faɗa min ya kaisa to a nan Ovasi ya kamamu nida budurwa sa ganin babu yadda zanyi kawai ɗauke masa numfashi da bindigar dake jikin, to kafin na ƙarasa wajan Deen wasu Mutane sun ɗauke sa a mota,nabi diddigi kuma na gane inda suke” murmushi A.j yay yace “gsky Oga kana da brain ba duk kai ba serious” murmushi Farouk yay yana jin daɗin ƙudirinsa na shekara da shekaru na gaf da cikawa, gyara zama yay yace “bari na baka labarin waye Farouk Bashir Yahya gidan iko..

#flash back.

Sunana Farouk Bashir Yahya gidan iko, nine frist Born wajan iyaye na sai ƙanwata Yasmin,daga nan iyayenmu basu ƙara samun wani ɗa/ƴar ba,ina da Shekara goma a duniya a primary school muna zaune bayan an fita breakfast, wani abokina mai suna Khamis ya bani sweet, girgiza masa kai nayi nace “No thank you!” Ɓata fuska Khamis yay yace “why” nace “haka nan” kamar zai kuka yace “please kasha ko sau ɗaya ne” ganin yadda ya sauya fuska yasa na amsa na sha,tofa wannan wannan sweet ita ce silar jefani halin da nake ciki a yanzu,ashe mahaifin yaron ɗan mafiya ne shike bashi alawa yana rabawa friends ɗinsa,kwana nayi kai na nayi mani ciwo cikin dare zanji shawo na yawo saman bedroom ɗina yana kiran sunana, na shiga tashin hankali sosai sbd ban saba dajin hakan ba, kwanci tashi naje makaranta Lokacin ina ss3 bayan an tashi wata mota tai parking gaba na, banyi wani musu ba na shiga motar daga nan kuma ban ƙara fahimtar komai ba sai farkawa nayi na ganni a cikin wani babban ɗaki tare da tarin maza da mata sanye da jajayen kayan  ga wasu manyan ƙoƙona a hanunsa ɗauke da jini.

Wani babbansu wanda yake saman kujera yay dry tare da faɗin “wlcm Farouk Bashir Yahya gidan iko” nidai tsaye nai ina kallonsu kafin na kalli aboki na Khamis da sauri ya janye idanunsa,a nan dai suka faɗa min abinda suke so kasa yi masu nai a take a wajan kuma nace na bada cikin dake jikin mahaifiyata.

Tun daga nan komai ya lalace kusan rabin familyn mu na bada jikinsu mugwayen kuɗi nake samu bana wasa ba, kuma kai na ya ƙare wayewa,bayan kamar shekara huɗu haka aka ƙara kiranmu meeting, nan dodo ya bada izinin a samo masa wata yarinya kuma babu wanda aka bawa aikin sai ni, photon yarinyar aka ban tare sunanta a jikin photon aka rubuta MOON da jan jini, aikin da hatsari da kuma sharaɗi dole ni zan kawota idan har ban kawota ba za’a fanshi jinina bisa nata da aka rasa, idan na sameta san zama shugaba gaba ɗaya a nan jahar Kano, a lokacin kusan 100.m aka bani..,” murmushi Farouk yay yace “Tayaya kake ganin zanbar wannan dabar da barni,abun mmkin yadda mahaifina bai taɓa tambaya ta komai ba,hakan yasa wata rana da aka kira meeting na gayawa dodo damuwata,dry yay sosai tare da yin wani ihu,cikin ƙaramin lokaci ya buga wani abu sai ga vedio’n Abbana ya bai yana a tsakiyar wasu mata suna ta shafasa,mmki ya cika ni,ban bar wajan ba sai da aka gayamin dukkan abinda Abbana yake,sai naji farin ciki shima yana aikata hakan bare ni,san da su Moon suka tare a gidan dake farcing namu farin ciki ya kamani sai ban nuna sosai ba sbd nasan mahaifina nada buri a kanta, infact bai san nasan na ganta ba,haka akai lokacin da Deen yazo kallo guda nai masa nadan cewa ba asalin aikinsa kenan ba,akwai manufar data kawosa gidanmu,yin duniya Abbana yaƙi korar Deen, Aliyou Eneye Ahuoyza yana da kaifin basira fiye da tunanin mai tunani, duk yadda kakai da gane mutum da wahala ka fahimci inda Deen ya dusa gane asalinsa da abinda yake shirin yi shine Abu mai wahalar gaske tabbas, wannan dalilin yasa na ƙara sanya idanuwa na a kansa, nasan soon or later I know everything about him tabbas,dalinsa na ƙarar da dukkan familyn namu domin duk sanda aka buƙaci Moon nace a ƙara min lokaci to dole sai na bada jinin wani matsayin toshiyar baki”.

Jinjina kai A.j yay yace “tabbas abun babba ne basan san lamarin ya kai haka ba wlh”  ka faɗa Farouk ya ɗaga irin whatever ɗin nan… Yakumbo ce ta kalli Sarki Aliyu Al’amin tace “nikam gani nake yarinyar nan kamar bata son haɗin da kakeso kayi na shekara da shekaru” gyara zama Sarki Aliyu Al’amin yay tare da sakin lallausan murmushi kana yaja numfashi yace “Na lura da wannan amma yaya kikeso naiwa Faizak kina sane da irin son da yake mata ai?” Yakumbo tace “Allah ya ƙarawa Sarki lfy, amma ya kamata aji ta bakinta domin ba za’ai mata auren dole ba, ko Fulani?” Girgiza kai Fulani tayi tace “A’a Yakumbo duk abinda kuke dai-dai ne” Murmushin jin daɗi Sarki Aliyu Al’amin yay domin ya yarda da karamcin matar tasa, miƙewa Fulani tayi tace “Na barku lfy” daga nan ta bar turakar Sarki,ganin babu kowa yasa ta nufi ɗakin Moon zaune ta sameta a gefen gado tana taje sumar kanta, Murmushi tai mata tace “wanka kikai?” Kanta a ƙasa tace “Eh” shiru Fulani tayi can kuma tace “kin gama prioud ne?” Kasa bata amsa tayi hakan yasa fulani yin Murmushi tace “look! Am your mother babu buƙatar ki ɓoye min wani abu, idan ban san abinda ke ranki ko yake damunki ba wane ya dace ya sani? So sharing your feelings with me kin gane, kin gama al’ada? Ma’ana farin ruwa ya biyo bayan jinin?” Kai Moon ta ɗaga kamar zatai kuka duk ta marai-raice fuska tace “eh” “ok kwana nawa kikai? Kin iya wankan ai?” Kwaɓe fuska tayi tace “Ammi” haɗe fuska Fulani tayi tace “bana son shashanci Maimunatou” da sauri Moon ta runtsa idanunta sbd sunan Maimunatou da Fulani ta ambata, duk sanda akace Maimunatou sai ta tuna gwarzon jaruminta wanda ya salwarta da rayuwarsa a kan tata, hawaye ne suka fara taruwa a cikin idanunta, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta fara zafi da raɗaɗi haɗi da ƙona, shiru Fulani tayi domin tasan abinda yake damun yarinyar ta ta, numfashi ta sauke tana gyara zaman Alƙyabbar ta tace “Yayinda kike jini ki kiga kumfa wata farin Ruwa ya fito Wannan alama ce take nuna jinin ya tafi saura wankan tsarki, idan kin iya wankan to idan ba kiyi ba yanzu dai zan maki bayani;

YADDA AKE YIN WANKAN HAILA DANA JANABAH

Idan Mutum ya shiga Ban-‘daki (bathroom) Zai fara ne da wankewa Najasar dake tare dashi.

Advertisements

Ma’ana, Zai Fara wankewa Al’aurarsa. Da kuma duk Guraren da Maniyyi (ko jinin) ya taba ajikinsa.

(Misali tun daga Cibiyarsa har zuwa cinyoyinsa).

* Kuma Zai Qulla niyyah ne yayin da yake wankewa Al’aurarsa.

* Sannan Sai ya wanke Dukkanin Gabobinsa na Alwala. Amma sau dai-dai.

* Idan kaga dama zaka bar Qafafunka, Sai akarshen wankan.

* Sannan Sai Wanke Kayinka Sau Uku. (tare da Wuyanka da Fuskarka gabadayanta).

* Sai ka Wanke Tsagin Jikinka na Dama. Har Zuwa Kafarka ta dama.

* Sai kuma Tsaginka na Haggu, ka hada har Qafarkata haggu din.

* Ya zama ka chire zobe daga hannayenka (Idan ya matseka) kuma dole ka Tsetsefe Dukkan yatsunka na hannu da na Qafa.

* Ka chuda Kafarka sosai. Musamman ma in har kanada kaushi.

* idan kazo wankewa kowanne tsagi, ka tabbatarda cewa kana Chutchuda Bayanka sosai.

* Idan kuma hannunka baya iya kaiwa, sai ka samo wani Tsumma ko Kyalle mai tsafta, Ka Jiqa-shi, Sannan ka Chutchuda dashi.

* dole ne ka chutchuda Ko ina ajikinka. Musamman ma idan kana da Qiba.

* Dole ne Ka wanke Duburarka sosai tun farko. Kada kayi la’akari da cewar”Ai ba ba-haya kayi ba”.

A’a. Ai nan dinma jikinka ne. Idan baka wanke ta ba, to wankanka bai yiwu ba.

* Ka kula da Ramin cibiyarka. Ka tabbatar cewaRuwa ya shiga har nan.

* Ya zama dole ‘yan uwa mata su tabbatar cewa Ruwan ya ratsa har cikin Kitsonsu yayin wankan.

* idan kuma kana da gemu, to lallai ne ka tabbatar cewa ka Tsetsefe shi komai Kaurinsa da duhunsa.

 ~~ ~~ ~~ ~~ ~~ ~~ ~ 

NOTE: Zaka iya amfani da wannan alwalar wacce kayiyayin wankanka. In dai har baka sake ta’ba al’aurarka ba bayan kayi alwalar.

HAKA AKE YIN WANKAN JANABA, HAILA, NIFASI, DA KUMA WANKAN SHIGA MUSULUNCI.

“Daga nan saiki fara sallah azumi riƙe Kur’ani, tana faɗin hakan ta miƙe har taje ƙofa ta tsaya tace “Abbanki yace ki shirya za’a fita ran gadi dake”. Tana faɗin hakan ta fice zuciyarta cike da tausayin ƴar ta…. Tsaye yake da shadda ruwan madara yay kyau ba kaɗan ba, ya ɗura jar dara a saman kwantacciyar sumar sa wacce ya ɗaure ta da ribbon, hanunsa sanye da agogo Patek philippe, lumshe idanunsa yay tare da jin gina da jikin dressing mirror a hankali kuma ya sanya hannunsa a saman forehead ɗinsa yana ƙoƙarin tuna wani abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwarsa amma ya kasa, jin kansa na sarawa sosai yasa ya fesar da numfashi a hankali kuma ya juya a tsaye ya ganta tana sakar masa Murmushi, Kallonta kawai yake yana ganin kamar akwai abinda bai gama cika a jikinta ba,farin glass ɗin daya gani yasa ya ɗauka tare da maƙala mata a fuska, sakin murmushi yay wanda ya haddasa bai yanar dimples ɗinsa, can ƙasa yace “kinfi kyau a haka Maimunatou” dry tayi tace “No ban so” juya fararan idanunsa yay yace “basshi sbd ni,kuma ai kin saba sawa ko?” Kallonsa tayi tace “eh yanzu ne kawai naji bana so,but zan barshi sbd kai” Jinjina kai yayi hannu ta miƙa zata riƙe nasa yay saurin yin gaba yana sakin Murmushi mai sauti…. Shirye shiryen tafiyar Moon Paris ya kan kama, domin ya gama shiri tsaf yau jirginta zai tashi da Misalin biyar na yamma..biyar dai-dai kuma suka isa airport Sarki Aliyu Al’amin Yakumbo, Mai babban ɗaki, sai Faizak idanunta cike da hawaye ta maƙale jikin Sarki Aliyu Al’amin sai shasshekar kuka take,kanta ya shafa yace “Afuwa Mamana Soon Zaki dawo ai” kuka ta sanya masa da ƙyar ya lallashe ta, Faizak kam baka gane halin da yake ciki domin harga Allah baya ƙaunar tafiyar Moon, kallonsa tayi yay saurin ɗauke kai, itama batai yunƙurin zuwa wajansa ba, a haka ta shiga cikin jirgi ya tashi da ita zuwa Paris.

Paris

Paris, France’s capital, is a major European city and a global center for art, fashion, gastronomy and culture. Its 19th-century cityscape is crisscrossed by wide boulevards and the River Seine. Beyond such landmarks as the Eiffel Tower and the 12th-century, Gothic Notre-Dame cathedral, the city is known for its cafe culture and designer boutiques along the Rue du Faubourg Saint-Honoré. 

Ƙasa ce ta ƴan gayon gaske masu ji da kuɗi ilimi,sun haɗa komai da komai, alrdy an gama mata dukkan wani cike cike, hatta hostel an kama mata..washe gari da safe misalin 10:30 ta fito sanye da wata shiga ta alfarma green ɗin lace ne a jikinta na ubansu kana ganinsa kasan an kashe kuɗi wajan siyansa, yana da milk ɗin torch ta sanya veil milk sai flat shoe milk hannunta riƙe da wayar da faizak ya siya mata, kai tsaye cikin makarantar ta nufa Université de Cergy-Pontoise,tana zuwa ta nufi office ɗin exam officer,a nutse take tafiya tai kyau kamar ka ɗauke ta, a sanyaye ta tura ƙofar ta shiga, wata budurwa ta gani wacce zasu iya zama age mate, Murya a sanyaye ta gaida Exam officer ɗin,shiru tayi kafin tace “Sir yau zan fara ɗaukan lectures” jinjina kai yay yace “wanne cous kenan?” Shiru tayi tace “Low” abubuwa ya fara dubawa yace “your name please” kaita ɗaga tace “Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza Deen” da sauri budurwa dake kusa da ita ta ɗaga kai sai kuma tace “wlcm takwara am Maimunatu Khalid” Murmushi kawai Moon tai mata, exam officer ɗin ne yace “Top 10 Best Pre-law Majors (see also: what did most law school students major in?)

Political Science – 9,612 admitted. … 

Other – 2,917 admitted. … 

Psychology – 2,960 admitted. … 

Criminal Justice – 2,220 admitted. … 

English – 2,564 admitted. … 

History – 2,657 admitted. … 

Economics – 2,373 admitted. … 

Philosophy – 1,858 admitted.” Moon na  gyara saman glass ɗin idanunta tace “okey! Sir” daga nan ta miƙe bayan ya gama yi mata bayani, tare suka fito da Takwararta Maimunatu Khalid, tana mata hira ƙasa², tunda suka fito Moon taji gabanta na faɗuwa sai rutsa idanunta take, suna gaf da shiga hall ɗin da zasu ɗauki lecture a ciki taga Maimunatu Khalid ta tsaya, itama tsaya tayi kafin ta lumshe idanunta sbd ƙamshin daya daki hancinta,can dai ta buɗe ido slowly idanunta ya sauka a kansa wata gigitacciyyar ƙara ta saka tare faɗuwa a wajan….

_RANAR KUKE JIRA YAU GASHI TAZO💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽INA MASOYA LITTAFIN MOON INA MASOYA NIMCYLUV YAU RANAR KU CE TA NUNA MIN ƘAUNA, DUKKAN WANI MASOYA MOON YANA DA KYAU YAY PAYMENT SABON LITTAFI NA *SIRRIN MU* NASAN DA YAWA KUN FARA KARANTAWA KUNJI YANAYINSA TO BA KUJI KOMAI BA DOMIN KO RABIN LABARIN BAMU SHIGA BA,SOYAYYA YAUDARA CIN AMANA ZANMA CIKIN AMINCI DUK ZAKU SAMU A LITTAFIN_

*PROMO*

YAU 2/SEPTEMBER/2021

DAMA GA MASOYA MOON DUKKAN WANDA YAKE DA BANK ZAI IYA TURA MIN 300 MAI MAKON 500 IDAN KUMA BAKA DA BANK SAI KA BADA KATIN MTN NA 500 WANNAN DA MACE GARE KU KAFIN NA KAMMALA FREE PAGES😍 PLEASE WANDA YAKE DA ACCT KAWAI SHI ZAI BADA 300 WANDA BASHI DASHI 400 RANAR DANA GAMA FREE PAGES KUMA NA GAMA PROMO NA.

ACCT NUMBER

0116886423

SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616 GA MUTAN NIGER SAI SUYI MGN TA WANNAN NUMBER  84506476 a nuna min soyayya masoya💋

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like