SAI A LAHIRA 42

Advertisement

 

*🎀SAI A LAHIRA🎀*

              *NA*

*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

Advertisements

            *🅿️age 42*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_

Advertisements

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 *_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

……..Tuni yan Matan Amarya da ita Kanta amaryar suka dauki wanka na tashin Sens sai walkiya suke inda baby tata kwalliyar tafita da ban saboda kyallin amarci Amma Kuma kyawun na zahiri adubi siyama wadda tayi sharr da ita cikin lemon green din material fuskarta fresh bata cikawa fuka fente fente kamar baby wadda in kaga yadda take Bata lokaci sai kayi zaton zata sauya tsarin fuska

Siyama ta dubi baby da ta tsira gwaggwaro akanta yayin da gashinta ya sauke kwance a gadon bayanta Yana walwali

“Masha Allah anty baby Wallahi kinyi kyau”

Ta fada da murmushi a fuskarta inda baby ta Kuma Shan kunu tamkar kushe ta akayi ba kambamawa ba

Zeenat tace “kema dai Kam siyama ai Masha Allah in baccin da Baki Dora gwaggwaro ba ai da ke ce Amaryar sak irin wannan kyau haka? 

Abinda baby ta tsana kenan ace baby tafita kyau……

“Kai anty zeenat Banda zolaya fa Amarya fa ba ta boyuwa ko Ina take …..

“Amma ai kin San Baki da fari akwa banbamci ko? Siyama ta Kuma yin murmushi “haba dai anty zeenat fari fa ana SHIGA kanti a siyo kalar su anty baby kuwa Nan gani Nan Bari…..

Batun ya cikawa baby ciki inda kadan kadan zata duba wayar ta don ta samu Kiran bashir har dai tayi sa a takwas da minti Sha biyar  Kiran shi ya shigo wayarta ta dauka tana cin daci don haushin sa ne fal a cikinta

“Kin shirya”? Ya fada bayan ta daga 

“Eh  mun shirya ” ta bashi amsa

“Yo ke dawa kuka shirya? Ah yo Ni da kawaye na su humaira Mana ! “Oh to fito kiji don bama bukatar kowa sai Amarya

Ta Mike zumbur Jin zai Kuma kunsa Mata  wani bakin cikin na Wai amarya kawai suke bukata.

Ta dubi su humaira dake kallonta tana cin daci

“Ga bashir Nan yazo Bari inje in dawo  ta fada tana ficewa daga dakin tana rausaya

Ta fito ta iske bashir ya bude mata mota ta shiga inda ya rungumo ta Yana son Yaba kwalliyar ta.

“Kinyi kyau baby my bride”

Ta ya mutsa fuska tana kallon shi ta kasan ido

“Naji kamar kace mu dawa muka shirya ? “To Ina da Wanda suka fi su humaira ne? Duk sun shirya dama Kai kadai muke jira Kuma sai naji kamar kana fadin Wai Amarya kadai ake bukata?

“Ya kuma rungumo ta Yana fadin 

“Eh amarya kawai ake bukata Banda gayyar kawayen ta ko Yan uwanta….

Ta dube shi a zabure tana Kara Jin wani bakin ciki na naushin zuciyar ta

“Ban Gane abinda kake nufi ba bashir? Munyi namu taron Wanda ka kassara Mana shi da Rashin halarta sai Kuma yanzu wannan da zamuje su huce wan can haushin shima Kuma Banda su kenan? Wai wace irin abotace daku irin wannan da saboda ita kake son saka min ciwon Kai akanta? Wane irin muhimmanci ne da ita da har kake fifita su akaina?

To gaskiya sai dai ka San yadda zakayi damu don gaskiya ban da idon duban su ince musu Wai Banda su a wurin hidimar……

Karki damu my zee bride tunda kin fito muje kawai in yaso sai ki Kira su ki basu hakuri….

Wayar shi ta dauki tsuwwa inda ya daga ake sanar dashi su kadai fa ake jira don haka yayiwa mota key ya soma tafiya yayinda baby take Jin tamkar tayi Aman zuciyar ta takaici ya Hana ta tankawa har suka iso wurin party fuskar ta ahade inda Kuma tayi karo da wasu Bakin abubuwa na abokan bashir masu Jan ido da wankan ruwan bagaja giya da karisha tayi Mata har zuwa inda suka Tara Mata dalolin amurka  da Miko Mata hannu Wai suyi musabiha har zuwa ficewa da sukayi daga wurin party inda yake sanar da ita Wai zai Kira gida ya ce abawa Yan rakiyar amarya hakuri ya wuce da ita gidan shi har fecewar su da karisha amota zuwa hotel da Kuma kwanan hotel din da ya kaita Ramin zakuna da kuraye na ganin karshen wulakacin arawa abokan da ya fifita  abinda Bata taba ji ko gani ba Daren farkonta a hotel da wani can da ban ba angon ba Kuma Wai da yarda da amincewa hakan ta faru….

Inda Kuma can gida abin ya zamo bakon lamari akan Wai ango ya wuce da Amarya.

Kafin Nan ma su humaira dake ta dakon dawowar baby sukaji ta shiru siyama ta leko bataga motar bashir din ba ta dawo take sanar dasu babu fa motar bashir din a waje inda su duka suka fito suka tabbatar baby ta Shanta su ta bi angonta inda suka dawo ciki suka soma Kiran wayarta Amma saboda bakin cikin dake dankare aranta ba ta ma ji Kiran ba inda su Kuma sukayi zaton dama ta shurya wulakanta su tunda gashi Taki daga wayar sai burari take

Da dai suka ga dare na tafiya sai suka wuce gida abinsu inda siyama ke ta Basu hakuri

Goggo kuwa da taga dare yayi ta damu da dadewar baby wurin wannan party inda Kuma baba shitu ya fito daga daki yake fada Mata Wai Bashir ya kirashi yake cewa ya wuce da baby gidan shi inda shima ya nuna Rashin Jin dadin shi da wannan sabon salon

Haj Azumi tace duk laifin baby ne don Naga ta kagara ta Isa gidan miji irin Rawar Kan da takeyi Allah yasa gidan ta ne ai sai kowa ya watse tunda har ta iya bin mijinta walimar ma na San basa bukata to zaman me mutum zaiyi tunda dama masu gidan basa bukatar mutane su rabe su  in basu harareka ba sa zageka in ka juya sai aci na kuya aci na bakin gado. Goggo na jinta Amma Bata tanka Mata ba don ita Bata dauki Azumi mace me hankali ba  

Da haka gari na wayewa tayi tafiyar ta gida Baki ma suka soma Kama gababsu Inda kuma goggo da siyama ke Kiran layin baby Amma basa samu saboda tana cikin hargitsin abokan miji da sabon salon su me bada yaji a ido da Kuma saka zuciya cikin tararrabi…..

Baby ta dubi tsohuwa iya idonta sharkaf da waye 

“Iya kinji yadda na faro duk da ban San yadda Zan Kare ba…………

.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like