SIRRIN MU 3-4

Advertisement

 

*SIRRIN MU*

*BY*

_✍🏾 NIMCYLUV_

Advertisements

EPISODE3️⃣-4️⃣

With much surprise wanda aka kira da Sheikh Imam hamdan ɗin yake kallon fuskar Airah, har kawo lokacin kuma ya kasa cewa komai he is just watching at her face like he is try to remember something fast, but he can’t, dukkan abinda Airah take he couldn’t understand her, shi dai yana nan a yadda ta ɗauko sa kuma ta ajjiye sa, murmushi tai masa kafin cikin nutsuwa tace “i knew baka san wacece ni ba, so don’t mind me, kawai ka saurari me zance maka ya shugabana” fararen idanunsa wanda suke ɗaukan hankali mata harda maza ya juya mata irin kallon am with you ɗin, nan ya baza all ears ɗinsa kawai yana jiran ya ji menene za tace masa, dariya Airah tayi tace “You know what? Sheikh Imam Hamdan! ” kamar soko haka ya girgiza mata kansa, hannunsa ta kama a hankali ta shiga murza soft fresh skin ɗin tafin hannunsa, kamar mai shafa masa mai, wani wahalallan numfashi ya sauke mai ƙarfin gaske, lokaci guda kuma yaji kansa ya sara masa, da sauri ya runtsa idanunsa wanda one time jijiyoyin kansa suka fito a saman forehead ɗinsa sukai raɗa-raɗa kamar an zana su, da sauri da sauri ya shiga sauke ajjiyar zuciya yana jin wani sanyi na ratsa cikin farar fatarsa zuwa cikin nama jikinsa haɗi da ɓargon dake sarrafa cikin ƙashinsa, wanda hakan ya haddasa masa afkuwar wani zazzafan zazzaɓi mai ƙonar da jinin Mutum, duk abinda yake tana kallonsa, kuma tana fahimtar komai dake faruwa dashi, abu ɗaya da ta gagara yi shi ne ta haɗa ido da shi, she can’t, yana da wasu sexy and killer eye balls, wanda anytime suke a lumshe kamar mai jin bacci ko wanda yake shaye-shaye, wanda bai san shi ba idan ya kalle sa zai ɗauka he’s always sleeping ne, but ba haha bane, kawai dai he’s  strong Man, cikin ƙasa da murya tace “Kai mutum ne, ni kuma Aljanna ce, amma mene yasa nake jin ina da relation da kai?, Ina jin kamar na sanka tun da kamar na taɓa rayuwa da kai, tambayar shi ne where? mene yasa nake jin feelings a kanka?, my grandma told me bil’adam suna da son kansu da yawa, basu da tausayi ko imani, basu tausayawa na ƙasa dasu, kowa hope and wish ɗinsa a kansa yake ƙarewa, sometimes nake ɓadda kama zuwa Bil’adam just to watch the people, but seriously they’re all many different types of people in your society, kamar dai kai you have a good heart, baka da damuwar kowa burinka kowa ya amfana daga baiwar ka, amma idanun jama’a na kanka mai yasa mutane duniyarku ke son cutar da rayuwarka ne SHEIKH IMAM HAMDAN?”, duk maganar da take idanunsa a lumshe suke yana jin yadda take ta zuba ita kaɗai kamar parrot, wato a Aljanu ma akwai masu shegen surutu kenan?? Ware idanunsa yayi a kanta sosai a hankali kuma ya fara ƙoƙari Motsa jajayen laɓɓansa, runtsa idanunsa yayi a hankali kuma yayi taking deep breath, cikin harshen larabci yace “Wacece ke?” Ƙasa Airah tayi da kanta, saboda yadda zazzaƙar muryarsa ta daki dodon kunanta, ba abin mamaki bane dan ta ji muryar so sweet and cool saboda tasan muryarsa cikin baccinta, amma Wannan ya sha banbam da wacce, wannan is real not dream shi ne a gabanta yake magana da   harshen da kowa yake fata da muradin ace ya samesa,domin yazo turanci ya zama ruwan dare, kasa bashi amsa tayi sai ƙasa da tayi da kanta, ganin tai masa shiru yasa Sheik Imam Hamdan saka tafin hannunsa zuwa saman fuskarta ya tallafo haɓarta su kai facing juna sosai kamar mai kunyar magana yace “Answer my question who are you?” Hannunta ta ɗura saman bakinsa tace “shiiiiiit!!” sai kuma ta janye hannunta tace “You asked me at the right time ya shugabana” ganin yadda taƙi yarda su haɗa ido kamar dai wata mara gaskiya yasa Sheikh gyara zamansa a hankali kuma ya kai dubansa zuwa ƙafafuwan ta wanda basu gama komawa na mutum domin ga jelar mesa nan yana gani, ɗauke idanunsa yay yace “Look at me, look into my eyes, akwai wani tarayya daman tsakin mutum da Aljan bani da labari?” girgiza masa kai tayi idanunta na kawo ruwa domin sosai ta ji ta fara shakkar Sheikh saboda jarumtarsa da kuma ƙarfin addininsa, kamar zatai kuka tace “sunana Airah is long story please just keep it on your mind one day I’ll tell you everything” kafaɗa ya ware irin “I don’t care”ɗin nan, numfashi ya sauke yace “first tell me miyasa kika kawo ni nan?” wani ƙawataccen murmushi tayi sai kuma tace “Yanzu Allah ya nufa ka ganni but every time, every second, every minute you’re in my heart,kullum da kai nake kwana” “Uhm” yace kawai yana ƙara ware rikitattun idanunsa a kanta sannan tace “what i mean kullum tare muke kwana a bed ɗinka, bana samun cikakken bacci mai nutsuwa da kwanciyar hankali indai ba’a jikinka nai bacci ba, duk sanda kayi nisa dani ina jin kamar ƙarshen rayuwata yazo ne, ɗomin jikinka kawai ke sawa na samu nutsuwa da kwanciyar hankali, na so faɗawa Tijama sai kuma na fasa saboda wannan SIRRIN MU ne, ni da kai, i thought it was  a play ashe ya wuce haka, I’m in love with you Sheikh Imam Hamdan ,i love You too much dear, i love You till the rest of my  life Imam ,na ɗauka bani da hankali ko kuma shirme, why Aljana za ta so jinsin mutane, mutum kamar Imam, to muma ai Ubangiji ya halicce mu kuma ya sanya mana zuciya kamar yadda kuke da ita, kaga ba abin mamaki bane dan zuciyata ta kamu da sonka Imam, please accept me as your wife Imam, zan zame maka komai babu wanda zan bari yasan cewa ni Aljana ce, zan ta baiyana gareka da kuma danginka a matsayin mutum just like you’re, bawai haka ne kaɗai burina ba, ina son baka kariya akan kariyar da Ubangiji yake baka, ba lallai kasan abubuwan da suke ɓoye ba amma ni nasan komai naka, dan Allah accept, kada ka juyan baya, kamar yadda Mamana da Abbana sukai min,Tijama da Juɓe sune kaɗai suke supporting nawa” ta ƙare maganar tana saka masa kuka tamkar ba Aljanna ba, sosai zuciyarta da kuma hurinta haɗi da gangar jikinta suke ƙaunar Sheik Imam,tun tana zanin goyo wata rana ta ji Iyayen ta na magana akan haƙurinsa da kuma jarumtar sa da taimakon da ya kewa talakawa , tun a sannan ta kamu da soyayyarsa mai wahalar gaske, bata da magana sai ta Sheik, wata rana tayi suffa irinta Bil’adam ta shiga cikin gari, tashin farko gidansa ta nufa tai rashin sa’a lokacin ya je sauke farali a ƙasa mai tsarki, bata tsaya ɓata lokaci ta nufi makkah a nan tai arba da shi a cikin harami gaban ka’aba yana sanye da fararen kaya masu ɗaukar ido, surar jikinsa a bayyana ga six packs ɗinsa abin birgewa, fari ne jajirr kamar ka taɓa shi jini yay tsartuwa haka yake, ko ina na jikinsa gargasa ce kwance sai sheƙi take gwanin sha’awa, is too young domin bazai wuce 23 zuwa 25 ba,t a ɗauka babba ne sosai, amma yanayin hutu da kuma cima mai kyau yasa ya zama cikakken Namiji mai jini a jika da kuma lafiya, yana da faɗin ƙirji wanda duk rabin ƙirjin sa gashi ne kwance lub-lub, kana ganinsa kasan yana gyming  yana da wasu kalar fresh pich lips  wanda suke very soft and  shinny he’s behaving like king of Saudi Arabia, eye lashes sunyi zara-zara har saman girarsa, babu abinda ya bawa Airah mamaki sai ganin sa da tayi saman wheelchair da alama yana da nakasa bashi da ƙafa, tun a lokacin taji tausayinsa ya kamata sosai, gashi dai babban mutum yana da komai na rayuwa kuɗi, ilimi both boko da Arabic yama fi ƙarfi ga Arabic domin a nan Saudi’a yay karatunsa, maganar kuɗi kam ba’a magana, bai rasa komai na rayuwarsa ba, babu abinda ya nema ya rasa, amma ya rasa farin cikin sa uwa uba babu ƙafar taka wa, a nan ta gama kallonsa ta koma cikin dajin da suke da zama, tun daga ranar ta ɗaura lalurar duniya a kansa sonsa take sosai, taɓa ta da yayi yasa ta sauke ajjiyar zuciya mai ƙarfin gaske, kafin ta ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi, saurin ɗauke kanta tayi saboda ba zata jure kallon cikin idanunsa ba, maganarsa ta dawo da ita hayyacinta inda yake faɗin “Ashe baki da tausayi ke mai son kanki ce ban sani ba? tayaya zan iya soyayya da Aljana what kind of rubbish ?” Cikin hasala itama tace “You can Sheikh Imam Hamdan ,sau nawa kana tarayya dani a Matsayin mata” da sauri ya kalleta Murmushi tayi tace “Yeah! I’m pregnant with your unborn child Sheikh, bana da niyyar cutar da kai ko kuma cin zarafin ka, bana son na haifa maka ɗan Haram domin dani da kai duk Halartattun ƴa ƴa ne, sai da aka yi Aure aka haife mu, mai yasa ni kuma zan zaɓi haifar ɗan zina? Ko kayi accepted ɗina as your wife ko kar kayi kasan ina da ƙarfin ikon da zan zauna da kai na saka kayi tarayya dani, ask me why banyi haka ba? kasan dalili shi ne ina sonka Imam, so mai ƙarfi da kuma girman gaske, tunda na bar iyaye na ai ya kamata ka karɓe ni, ka zame min gurbin dana rasa, nima na baka farin cikin daka rasa na shekara da shekaru, ina sonka saboda Allah! Burina bai huce na kula da lafiyarka ba, zuwa yanzu kasan baka da kowa sama dani saboda nice matarka!” Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya, murmushi kawai ya saki kafin yace “Na ji mai dani gida” kuka ta saka masa tare da zubewa ƙasa ta riƙe ƙafafuwansa tace “dan Allah dan girma ALLAH! Ka so ni kwatankwacin yadda nake sonka, wallahi zan iya mutuwa idan baka amince dani ba, kuma ɗanka dake ciki na ba” wani bala’in tausayinta ne ya kama shi, ace wai Aljana ita take sonsa har tayi tarayya dashi ya sanya mata ƙwansa a cikin ta, yaya zai yi da rayuwarsa yanzu shi?ta yaya zai iya rayuwa da ita a cikin gidan su? Yadda take masa kuka sosai da kuma yadda take begen nasa akan ya so ta yasa bai san lokacin da yace “Okey! Imam hamdan accepted you as his wife” cikin farin ciki da Murna Airah ta ƙwala wani uban ihu tace “Didn’t i told you Tijama, bana gaya maki cewa my Imam has a good heart ba” kallan yadda take tsalle da murna haɗi da ihun yasa cikin ƙasa da Murya yace “Don’t scared your Husband” tsayawa tayi da rawar tana jin wani farin ciki na ratsa jikinta, cikin tsananin farin ciki tace “Thank you so much Sheik, thanks once again i can’t stop loving you you’re my everything”  lumshe idanunsa yana jin abinda ya aikata kamar ba dai-dai ba ne,amma yaya zai yi da ita? Ba zata taɓa barinsa ba indai ba amincewa yayi ba, shi yasan bazai taɓa yin tarayya da ita ba, shiru yay kawai yana sauraren bugun zuciyarsa, ganin tai masa shiru yasa ya buɗe  idanunsa da sauri ta ɗauke idanunta wanda tun ɗazo ta ɗaura su a kansa, kamar zai kuka yace “gida Please” wajansa ta ƙarasa tare da durƙusawa a dai-dai ƙafafuwansa ,kana ta saka hannunta ta ɗura saman laps ɗinsa tace “Why are you so worried ?” Shiru Imam yayi mata yana tsareta da fararen idanunsa, Murmushi tayi tace “don’t worry, yanzu za’ai mana bikin” ware idanunsa yay sai kuma yay calming yace “Owk” miƙewa tayi kana ta haɗe hannayenta waje guda ta shiga tafa hannayenta, cikin ƙaramin lokaci Tijama da Tuɓe suka bai yana, dariya Tijama tayi tace “Congratulations Airah, congratulations Sheikh Imam Hamdan ” bai ce komai ba sai hannunsa daya miƙawa Airah kamar yadda ta buƙata,wani ƙaramin ring wanda yayi dai-dai da yatsansa, kana ganin zoben kasan cewa an kashe kuɗi wajan yin sa, banda haske da ƙyalli babu abinda yake, a saman Ring ɗin a rubuta I&A, fuskarta cike da farin ciki ta sanya masa zoben, kallonsa tayi tace “Now is your turn” jikinsa ya shiga lalubawa yaji babu komai sai wani sirin sarƙar gold, cirota yay a jikinsa kana ya nuna mata sirin sarƙar,wajan sa ta ƙarasa tare da durƙosawa dai-dai ƙafafuwansa tai masa nuni da wuyanta, A hankali ya sanya mata sarƙar, tafi Tijama da Tuɓe su kai tare da faɗin “Congratulations Airah and Imam Masha Allah!” Haka nan dai yaji ya samu kansa cikin farin ciki shima, kallon Airah yayi suka haɗa ido ganin yadda idanunta ya cika da hawaye yasa a hankali ya ware mata hannayensa da sauri ta zo wajansa tare da faɗawa jikinsa , a tare suka sauke ajjiyar zuciya, shiru Sheikh yayi yana duban agogon hannunsa yasan yanzu Subhi ya kusa yana buƙatar komawa gida, ƙasa yayi da murya dai-dai fuskarta yace “Can i go?” Fuska ta marairaice tace “babu wani gift?am your wife Sheikh” taɓe baki yay yace “me zan maki?” Dariya tai tace “ok lemme give you a special kiss Rayuwata” zaro ido waje yayu tace “Yes! Sabon sunanka ke nan a gareni RAYUWATA” lumshe idanunsa yayi kafin ya saki jishi tare da faɗin “Uhm” Sumar kansa Airah ta shafa a hankali kuma ta sanya bakinta cikin nasa da niyyar bashi hot kiss…..

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

SIRRIN MU 11-12

Advertisement *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ _It’s #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment…

SIRRIN MU 13-14

Advertisement   *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _it’s #500 via 0116886423_ _Sulaiman Naima s union bank evidence…

SIRRIN MU 15-16

Advertisement  *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _it’s #500 via 0116886423 Sulaiman Naima s union bank evidence of…

SIRRIN MU 5-6

Advertisement  *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _This book is for sale it’s #500 via  0116886423 Sulaiman Naima…

SIRRIN MU 17-18

Advertisement  *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _it’s 500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of…

SIRRIN MU 19-20

Advertisement   *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements Dan Allah kuyi SUBSCRIBE na youtube channel ɗina mai suna …