Advertisement
*SIRRIN MU*
*BY*
_✍🏾 NIMCYLUV_
Advertisements
_This book is for sale it’s #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616, ga mutan NIGER sai suyi mgn a wannan number 84506476_
🆓P
EPISODE7️⃣-8️⃣
Mami na barin parlourn Arjun ya sauke numfashi, tare da tura Wheelchair suka nufi cikin parlourn. Granny ce kwance saman bed tayi ɗai-ɗai sai bacci take abinta hankali kwance, da sauri Arjun ya juya ya nufi inda Sheikh yake yana shan coffee a parlour, with much shock Arjun yace “Buddy i don’t understand what’s going on?” A hankali Sheikh ya zame bakinsa daga kan glass cup ɗin ya ajjiye saman center table ɗin dake gabansa kafin yace “Meke nan?”, Arjun yace “na je flat ɗinka na ga Granny ciki tana mopping, har muka gaisa yanzu kuma kace na ɗauko maka zuma a fridge ɗin Granny nai sallama bata amsa, hakan yasa na shiga cikin bedroom nayi expected wahala take, abun mamaki sai na sameta saman gado tana bacci da alama ko sallah asuba ba tayi ba”, ya kai maganar yana kallo reaction ɗin Sheikh, sai bai ga komai ba sai ma murmushin da ya ga yanayi “Ohh!! Ni ka maida wawa ko?” da blue eye balls ɗinsa ya kalli Arjun yace “Oh! come on dear me zance maka” Arjun yace “More explanation about two of them” ware ido Sheikh yay yace “Laa adaari” cikin fusata Arjun yace “what the you mean by that?,bayan kana gidan kuma Granny ita take maka komai” taɓe baki Sheikh yay idanunsa a kan cenema yana kallon labarai a Aljazeera yace “La takaffafuu” kai tsaye Arjun yace “wallahi sai ka faɗa min”, a ɗan fusace Sheikh ya kalli Arjun domin ya fara kai shi Ƙarshe bai son mita, da kuma nanata magana, calming yay yace “dole ne nasan komai? Ko zaka saka nai bincike akan abinda bana da iko dashi ne? Wallahi Arjun ka kiyayi kanka ka cigaba da shiga sabgar da babu ruwanka, ni nan ƙarya nai maka or what???” SHI ma Arjun yace “Ashe ba zakai hankali ba Imam? Baka tunanin lafiyar ka, ko ka manta situation ɗin da muke ciki, kullum kai ne zaman gida da tsaron Soldiers saboda gudun abinda zai cuce ka da kuma wanda zai sanya ai maka wani abun, amma kake ganin laifi na, wlh if i find out the truth you’ll regret my dear” yana faɗin hakan ya nufi flat ɗin Granny da ido kawai Sheikh ya bisa harya ɓace wa ganinsa, Arjun na tafiya ya ci karo da wata farar mage mai kyau gwanin sha’awa ɗauke kansa yay daga kallon magen yaci gaba da tafiya, wayarsa ce ta fara ringing hakan yasa ya tsaya da tafiya kana yay answering call ɗin, yana tsaye magen ta huce da sauri ta nufi flat ɗin Granny, lokacin Granny ta farka tana ta sallami tana faɗin “A’a da mutanan gidan nan Arna za ai, babu tsoran Allah a ransu ace nai ta bacci kamar matacciya babu wanda ya kula da sabgata, kamar dai mara gata? To Allah dai yaga zuciyata ba ina sane naƙi sallar safe ba makara nayi wallahi tallahi, daman ita wacce ba’a gama sanin a wanne ɓangare take ba tuni na sallama ta, shi ma Barista dake gantalalle ne sai ya rabu dani ko na mutu ko nai rai duk uwar ubansu ɗaya, kai Allah gani gareka ni Faɗimatu da miji da mata duk babu na gari gwamma shi ƙarya yake rabtawa, ita kuma kuɗin jama’a take kwashewa tun da dai naji a banki take aiki, kai amma dai anyi gantalallun mutane wlh” tana faɗin hakan tai cikin bathroom, “ni dai wallahi cikina kamar anyi min sata, babu komai sai hanji wannan da shayarwa ne ma sai naji labari”, tana shiga bathroom farar magen na shigowa cikin bedroom ɗin Granny, da ido magen tabi Granny da shi, kafin a hankali magen tai girgiza sai gashi ta koma siffar Granny tatasss babu abinda ya siffanta ta, Arjun ne ya shigo yana faɗin “Mrng Granny” kyaɓe Granny tayi tace “bana son gulma da fi’ili meye kuma Munin Ranjun? Kana gani ba’a mai dani komai a gidan nan ba,ai wlh Imamu da babu ni daya shiga uku, bashi da kowa da komai sai ni,Allah gatansan ni ce gatansa bawan Allah kenan”, murmushi Arjun yay yace “haka ne fa Granny, kamar yanzu kika tashi ko makara kikai ne??” Wani kallo Granny tayi masa sai kuma tace “Yaushe ka arnantar dani Ranjun? Ka dai dinga jin tsoron Allah wallahj, babu ruwana sharrin da kai min ma ya ishe ka, yoo sharri mana da hankali na da komai shekara wajan 85 ai ba wasa kawai sai na zauna na makara a sallah, ai ni nan lokacin walaha nake jira kawai”, jinjina kai kawai yay yace “bari na shige sai anjima na zo kai Buddy gidan Redio”, “to to Allah ya kaimu ka gaida Sadiya” yace “za ta ji” yana faɗin hakan ya fice daga cikin bedroom ɗin, da ido ta bisa yana fita ta rikiɗe ta zama magen kamar yadda ta shigo parlon.
Advertisements
Dawowa parlon Arjun yayi ya samu Sheikh yana shan ƴa ƴan inibi masu sanyi yace “am going Buddy sai zuwa anjima” plate ɗin hannunsa ya ajjiye yace “ok mai dani falt ɗina” ba musu Arjun ya kama Wheelchair ɗin suka nufi flat ɗin Sheikh, wanda yafi ko wanne flat kyau da kuma tsaruwa a cikin gidan, idan kaga abubuwan da suke flat ɗin Sheikh saika ɗauka shi ɗin wani lafiyayye ne, har cikin bedroom ɗinsa ya shigar dashi komai tsaf Granny da gyara amma a yadda suke tunani, da taimakon Arjun Sheikh ya kwanta saman makeken gadon sa, har Arjun ya juya sai kuma ya dawo,da ɗan sauri yasa hannu ya zarewa Sheikh jallabiyar jikinsa sannan ya cire masa singlet ɗin,fresh white skin ɗinsa ya bayyana ga santala-santalan ƙafafuwansa da cinyoyinsa da suka bayyana duk a waje, Arjun na gamawa yace “bye” idanunsa Sheikh a rufe yace “Jazakallah bilkhair” yana fita waje yana faɗin “it’s my pleasure” Shiru Sheikh Imam yayi domin duk sonsa da bacci a lokacin kasawa yay, sai a yanzu mafarkin da yay ya shiga dawowa cikin brain ɗinsa, idan ya fahimta wacce ta kai shi bathroom da asuba ba Granny bace, domin ya daɗa fahimtar wani abu ɗazu,hakan magen data zo kusa dashi ba asalin magensa bace Wannan AIRAH ce, kenan mafarkin da yayi gsky ne yake ganin abun a mafarki ko yaya? Maganar Airah ce dawo masa cikin ransa inda take faɗin “Am pregnant with your unborn child Sheikh” ta yaya? Yaushe yayi tarayya da ita da har zata samu cikinsa, yasan cewa koda wasa babu wata halitta ko a jinsin Aljanu da ta taɓa ganin Manhood ɗinsa, Lumshe idanunsa yayi yana jin yadda kansa ke masa ciwo ga wani nauyi da yay masa, ji yay gidan yay masa girma dama yace Arjun ya tafi dashi gidansu, ko dai waya zai sanya Abbansa ya sai masa? Idan ya riƙe waya yayi me da ita, babu abokai family kuma iya Abba da Mami da Granny Fareeq Buhaiyya ya sani sai kuma Arjun daya zame masa komai, mirginawa yayi tare kifa cikinsa ya rungume pillow, iska ya ji tana kaɗa gashin kansa can kuma ya ji an dafa fresh back skin ɗinsa, bai Motsa ba saboda yayi tunanin Granny ce domin ya san Mami sai 6 zata dawo Abba kuma sai dare, Murmushi Airah tayi saboda farincikin yau zata kasance da mijinta kuma abin alfahari gareta, zama tayi bakin bed ɗin dai-dai kansa, bai tai kuskuren magana ba sai kansa data kama a hankali ta ɗaura saman cinyarta, ajjiyar zuciya ya sauke yana ɓata fuska yace “Granny!!” Yatsun hannunta ta tura a cikin sumar kansa ta shiga shafa masa sumar tana ɗan wargatsa ta, sosai Sheikh ya ji daɗi saboda daman kan ciwo yake masa, ƙara matsawa yayi jikinta ko zai samu yay baccin gadon da bai samu ya ɗauke sa ba, kasa yin shiru Airah tayi tace “why kake tsoran faɗawa Arjun kana da mata” da sauri ya ɗaga kansa zuwa fuskarta kasa ɗauke kansa yay saboda wata ƙyakkyawar halitta daya gani, zai iya cewa bai taɓa ganin mace me kyau da kuma tsarin halitta irin ta ba, ba fara bace ba baƙa bace za’a iya bata Chocolate tana da dugun gashi wanda ta ɗaura masa siririn veil, duk inda kake neman mace first class Airah ta kai sai yake ganinta kamar ba mutum ba, bakinsa yana rawa “who are you?” Kansa ta mayar saman cinyarta tace “why are you worried Rayuwata?” ji yayi zuciyarta ta buga da ƙarfi amma sam bai nuna a fili ba yace “Uhm” hannunta ta cire a cikin sumarsa tace “So daga juya zuwa yau harka manta dani ko?” Girgiza mata kai yayi yace “No! Kawai am trying to remember you” kallonsa Airah tayi tace “Lemme help you to, Am Airah your wife,Nasan abin zai zo maka kamar a mafarki but is not a dream is reality , tabbas na ɗauke ka da hannuna har zuwa dajin Sambisa an ɗaura mana aure Tijama da Tuɓe da kuma necklaces ɗin daka bani sune shaida” shiru yay mata ya shiga murza zoben hanunsa wanda tun ɗazo baya gajiya da kallonsa can kuma yace “what again now?” Tace “na kasa jurewa tun bayan na dawo dakai gida da Asuba,sai ya zamana na kasa bacci, hakan yasa nazo gare ka a suffar Granny bayan na sanya Granny bacci mai nauyi, sannan duk abinda kuka faɗa kai da Arjun ina jin ku, hakan yasa na zama mage domin bana son ya fahimci wani abu kamar yadda kai ma baka so, ina zuwa falt ɗin Granny na samu ta shiga bathroom sai na koma siffar ta da Arjun yazo ban sha wata wahala ba” shiru tayi sai kuma tace “Amma mai yasa kace?” Yunƙurawa yayi, ya miƙe zaune yana ɗan yamutsa, ƙafarsa ta kalla da sauri tasa hannayenta ta gyara masa ƙafafuwansa, fuskarta ya kalla yace “Tun Asuba nasan ba Granny bace, duk wanda yasan aljani farin sani ya ganki yasan ke ɗin ba mutum bace, na ƙara tabbatar da haka ne ta cikin mirror’n dake maƙala a cikin bathroom ɗina, kuma Granny bata iya English ba” jinjina kai tayi tace “Ko mugwaye Aljanu ai basu isa su ɓoye maka ba, bare ni da nake shirin taimaka maka” hannunta ya zame daga nasa kana ya koma ya kwanta can ya ƙara cewa “i don’t have any feelings about women, balle aljana tayaya kike tunanin zan iya rayuwa dake matsayin mata a gare ni? Ta yaya kike tunanin zan baki kulawar daya dace ko wanne namiji ya bawa matarsa? I can’t bana son kowa kamar yadda babu mai sona” kamar zatai kuka Airah tace “stop saying that Rayuwata,i promise u, I’ll make you happy, ka bani 1week idan har a lokacin kaji baka sona nai baka al’ƙawarin zan rabu dakai”, hanunsa yasa yaja sajensa yace “sure?” Kai tsaye tace “Yeah” zamewa yayi ya kwanta duk yadda yasu yay baccin daya saba kasawa yayi, har 11 tayi lokacin tashinsa a bacci kallon Airah yayi wacce har yanzu tana zauna tana shafa masa sumar kansa yace “zanyi Sallah” miƙewa tayi tare da jawo Wheelchair tana son ta kaisa da kanta amma bata son tai abinda zai firgita da ita, bayan yay alwala yay Sallah ya koma ya kwanta kallonsa tayi tace “Breakfast fa?” Girgiza kai yay yace “No i want to sleep” Yana faɗin hakan yana jan duvet ya rufe jikinsa, hawa bed ɗin tayi tace “i want to sleep with you” bai kulata ba yaja idanunsa ya lumshe yana jin yadda ta ja duvet ɗin ta shiga ta yadda ta ware hannayensa daya rungome a ƙirjinsa kana ta shige jikinsa tana Murmushin jin daɗi sosai take farin cikin kasancewa da shi, tsakani da Allah take son Imam bada wata manufa ba, rungomesa tayi sosai ta shiga shafa kansa tana masa waƙa mai daɗi a haka har bacci ya ɗauke sa wanda ya daɗe bai mai daɗinsa ba, ganin yay bacci yasa Airah miƙewa ta cire kayanta kana ta koma wajan Sheikh da yake kwance ta rungume sa sosai tare kissing bakinsa…….
GIPHY App Key not set. Please check settings