SIRRIN MU 9-10

Advertisement

 

*SIRRIN MU*

*BY*

_✍🏾 NIMCYLUV_

Advertisements

     _Ina ganin masu cewa ko yaya zaman Sheikh Imam hamdan Balarabe da Aljarsa Airah zai kasance??? To kada ko damu you’ll be surprised Habibaties kawai a hanzarta payment free pages dai babu yawa😍👌🏾share And share and share_

Pay #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment

08119237616 ga ƴan Niger sai su nemi wannan number 84506476

  🆓P   

Advertisements

EPISODE9️⃣-1️⃣0️⃣

Sheikh Imam bacci yake mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, da zarar yay mutsi zai ji an ƙara shigewa jikinsa ga wani ɗumi dake ratsa jikinsa seriously zai ce ya daɗe bai yi bacci mai daɗi irinsa ba, bai tashi daga bacci ba sai da yaji muryar Granny saman kansa tana faɗin “Yau na ga abin da yafi ƙarfina ni Faɗimatu, wanne gantalallan bacci ne wannan Fisabilillahi? anayi ana nishi kamar bai zazzaɓin masharshara?” Buɗe idanunsa yay da ƙyar yana ɗan dafe kansa da yaji yana masa ciwo kallo ɗaya yay wa Granny yay saurin ɗauke kansa tare da juyawa side ɗinsa,ganin babu kowa a gefensa yasa ya kalli Granny ya ce “Granny where is she?” Keɓe baki tayi ta ce “meye kuma Shaa? Kaga Imamu babu ruwana da wannan Ingilishin naka maza tashi ka shirya Ranjun yace min yana hanya,yanzu ya kira a sailolar dake palo” shiru yay kawai yana sauke tagwayen ajiyar zuciya ji yay ransa duk babu daɗi saboda da rashin ganinta da bai ba, yana da tabbacin tafiya tayi bayan ta sashi ya yi bacci, Granny ta taimakamasa yay wanka tare da ɗaura alwala, yana gaban dressing mirror Granny na shafawa fatara versiline “haka kurum baka san darajar fata ba kace a shafa maka wani losha,meye ma wani losha fisabilillahi” Shidai bai ce komai ba domin a karo na farko kenan yaji bai ji daɗin yadda Granny ke shafa masa mai ba,ji yay gaba ɗaya yana da bambanci da wanda Airah ta shafa masa da Asuba, comp ta ɗauka ta taje masa sumar kansa ta kwanta sosai har saman goshinsa,kana tai hanyar wardrobe tana faɗin “Uhm kai kaji wani zance Imamu” idanunsu akan madubi yana kallon yadda jikinsa ya ƙara buɗewa sosai kamar wanda yake yin risilin, jin yay shiru bai magana ba yasa Granny ta ce “Idan bakai miskilanci ba ai sai Allah ya ka maka wlh, domin Ubanka Did…,” Sai kuma tai shiru ta cikin madubin ya kalleta ya ce “Speak up Granny,meye Did…?” Girgiza kai tayi tace “A’a babu ruwana da gulma haramun ne wlh,daman wani zance nake som tsegun ta maka da naji Barista ya faɗa” gaba ɗaya attention ɗinsa ya bata yana faɗin “Uhm” wani tissue ɗin yadi mai masifar kyau ta ɗauko masa mai manyan zane gashi shara shara domin komai na jikinsa ana iya gani,wajansa ta ƙarasa tare da sunkuyawa ta bashi boxer ya saka sbd daga shi sai pad,tun yana yaro haka ya tasu kakarsa ke masa komai, shiyasa ba yajin akwai abinda zai iya ɓoye mata a jikinsa sai dai tsaraicinsa, farar singlet ta bashi ya zura a jikinsa bakinsa ɗauke da addu’ar sanya kaya,sai kuma wandon yadin shima yasa rigar mai ɗinkin Jamper ta bashi ya saka, sannan ta miƙa masa babbar rigar kayan, girgiza mata kai yay ya ce “No! Granny ban so” Juyawa babbar rigar tayi tace “Wallahi baka isa ba,ba zan wahalar banza ba ka ga yadda kai kyau kamar dai ɗan firazdat ko ɗan sarki? Kai ma sha Allah” Murmushi yay mata yana ɗaga hanunsa saboda parfume ɗin da take saka masa, lokacin ɗaya ƙamshin Arabian Ohud ya cika cikin bedroom ɗin nasa, harami ta ɗauko masa ya ce “bari sai Friday bani jar darata” wata hula ta bashi mai kyau tana ɗauke da gashi,a saman sumar kansa ya ɗura kana ya sanya farin bluetooth da farin glass ɗinsa yay wani kyau he look like king of Saudi Arabia, baƙin covert shoe ta saka masa a farar ƙafarsa, sai da ta gama masa komai sannan ya kalleta ya ce “Jazakillah bilkhair Granny” zama tayi ta ce “Ni dai amana zan gaya maka wlh,idan kaci kai da Allah babu ruwana da shiga hurumin Ubangiji” lumshe idanunsa yay ya ce “Uhm feel free what’s is the matter?” Tagumi tai sai kuma ta ce “Barista ya kitsa abu babu shawara fa, wai Gwamna ya nemi a baka auran ƴarsa,kullum tana jin zantukan ƙaryar da kuke a redio,sai ta kamu da sonka hankalinta duk ya tashi hakan yasa Gwamna ya ce ta gaya masa tace ai Sheikh Imam hamdan take so, to ashe ma ya san Ubanka Barista shine fa ya ce da Barista yana neman sa a govmat house,to Ubanka dai ya yarda ni da waccan ɓarauniyar kuma bamu amince ba” Kallonta kawai Sheikh yake sam bai mamaki ba domin Arjun ya faɗa masa cewa ana yawan kiransa ace Imam ake nema kuma macace,wani lokacin messages harta email ɗin Arjun,to babu mamaki yarinyar ce, Granny tace “banda gantalewa ta yaran zamani yaushe mace take cewa tana son Namiji? To wlh zamanin mu sai an kaika ɗakin mijin kake sanin wa kake aura,kaga ina da shekara 9 akai min aure hatta nono wannan a ɗakin Mijin na samesa” wani ƙawataccen Murmushi Sheikh yay yace “Am hungry” Granny tace “Me kace?” Idanunsa ya mayar bakin ƙofa ya ce “yanzu 12 past 23 yunwa fa” miƙewa tayi bayan ta gama gyara wajan kana ta tura Wheelchair ɗin zuwa tsakiyar haɗaɗɗan parlour’n gidan, har gaban dinning ta ajjiyesa kana ta shiga zuba masa abin breakfast ɗin, Arish ne da meat shawarma sai tea da yaji kayan ƙamshi da na’a na’a tai tashin ƙamshi yake, bisimillah yay yasa yatsun hanunsa guda huɗu ya fara cin meat shawarma bayan ya gama cin abincinsa Granny ta kawo karamin bowl ya wanke hanunsa ya goge da tissue kana yay hamada.

Bayan Sheikh yana mutane sallar zuhur Arjun ya koma cikin gidan su ya ɗauko ɗaya daga cikin sabbin motocin Sheik wata ƙarama mai ash color sabuwa dal, Arjun na mazaunin driver Sheikh na ɗaya side ɗin idanunsa akan littafin Zajid zaujain, sosai Arjun ke gudu da motar sbd yasan Sheikh bai son tafiya a hankali “Buddy wallahi aure nake sonyi na gaji a matse nake,Am tried pls daga nan mu huce gida ka tayani roƙan Ummi ta barni nai auran tunda ina so” lumshe idanunsa Sheikh yay lokacin ɗaya yaji tunanin Airah ya faɗo masa, Where is she? Shine tambayar da yaywa kansa, one day kenan yaya kenan idan ya kasance da ita na adadin sati guda kamar yadda ta ce? A haka suka shiga cikin gidan redio’n Arjun yay parking kana ya fita daga inda yake zaune,a back side ya ɗauko wheelchair ɗin Sheikh kana ya taimaka masa ya zauna, har cikin reception ɗin gidan redio’n suka shiga,kowa ya ga Sheikh sai ya tsuguna ya gaishesa,hatta ga wanda suka girmi Sheikh babu a abin da ya siya masa mutunci face Iliminsa sa hqrinsa haɗi da taimako da kyautatawa talakawa, da sauri ya fara gabatar da program ɗinsa na LAFIYAR MU, Mutane da yawa sun buƙaci ya buɗe masu wata ƙungiya ko kuma gruop wanda zai iya yi masu wani bayanin idan yana free,wasu kuma sukace ya basu number wayarsa, Shi dai murmushi yay kawai domin yasan a redio kawai suke jin zazzaƙar muryarsa,amma shi gaba ɗaya bai san yadda zai iya using da wata waya ba,ya wake dashi? Bashi da wanda zai nemasa a waya,a haka suka gama program ɗin shida Arjun kana suka ɗauki hanyar gidansu Arjun. Ummi ta ce “Haba Imam i don’t think is nacessary,idan Arjun yay aure bazai samu lokacin kula da komai naka ba” wani abu mai ɗaci Sheikh ya haɗiye idanunsa akan Ummi mahaifiyar Arjun yace “No! Ummi i trust Arjun zai iya komai nawa,yin aurensa bashi ke nuna zai ƙi kula dani ba” Murmushi kawai Ummi tayi tace “Imam ka manta da shirman Arjun fa,and think yourself mana,kalli condition ɗinka,babu wanda ya dace da yay Aure sama dakai,yana da kyau ace kafin wani yay maka wannan mgnar kayiwa kanka” idanunsa ya lumshe kafin ya sauke numfashi yace “Try to understand us Ummi, the way mutum yace zai aure to let him do” Arjun yace “please Ummi i lover so much i need her i want marry her wlh ina sonta” harara Ummi ta watsa masa tace “kai dai Arjun anyi mara kunya,akan na hanaka shi ne ka ɗauko bawan Allah yana cikin hutawarsa,wlh baka da kunya ka kiyaye ni Arjun” Murmushi kawai Sheikh keyi,shi ina ma yana da uwar da zata hanashi abu aida yaji daɗi,he need mother new mother yana son yaji ɗumin uwa mahaifiya,yana son yaji uwa ta rungomesa inda zai samu yayta kukan saman ƙafaɗarta,baya da wannan ƴan cin bashi da uwar daza taji damuwarsa bare harta bashi shawara mai kyau,babu uwar da zata kwantar dashi zaman ƙafaɗarta tasa yay kuka mai yawa ko yaji sauƙin zuciyarsa, tagwayen ajjiyar zuciya ya sauke kallon Ummi yay inda take faɗin “Shikenan yaje yay aure Allah ya sanya albarka,Amma Imam kai ka nemu matar Aure” zoben hanunsa ya kalla ya ɗan murza kaɗan yace “bana da interested Ummi” ganin yanayinsa ya sauya yasa ta rabu dashi, farin ciki sosai Arjun ya shiga rungome Ummi yay yana faɗin “thank you so much Ummi” murmushi tai tana shafa kansa tace “kuje daining ga lunch na jera maku” girgiza kai Sheikh yay idanunsa a ƙasa yace “Am full Ummi” Ummi ta ce “daman koda yaushe you’re full” dariya Arjun yay ya ce “Rabu dashi Ummi,ko a gida yake baya cin abinci iyanzu sai dakakkiyar fura” miƙewa Ummi tayi tace “ta kwana gidan sauƙi ai,ina da fura wlh” kwaɓe fuska Sheikh yay bai ce komai ba “Ummi ko kin dama bai zai sha ba indai ba Granny tayi ba” yana faɗin hakan ya nufi hanyar fita daga parlour’n yana tura Sheikh dake zaune saman kujera “To ai shikenan Allah ya baka lafiya Imam Ubangiji ya kawo ƙarshen wahalar” da Ameen ya amsa har suka fice daga parlour’n Ummi na zabga masa addu’a.

Da daddare Barrister ne zaune shida Mami da Granny wacce take yankawa Sheikh apple a plate, Sheikh na zaune yana farcing mahaifin nasa yana kallon yadda suke cin abincin su hankali kwance,idanunsa ya mayar kan Granny wacce tace “Fisabilillahi ace ƴar ƴan itatuwa sune abinci? Gsky wannan ba halin zama ba ne Babana” Mami ce ta ajiye spoon ɗin hannunta ta ce “Granny ai wannan sun fi sanya jiki lafiya” “au haba? To Allah ya taimaka nikam wannan sakalcin ba dani ba” shiru sukai mata harta gama surutun da jan plate ɗin Sheikh yay tare da sanya fork ya caki apple,amma ya kasa kaiwa cikin bakinsa sai juya Apple ɗin yake, Barrister ne yace “Yadai son?” Kallon Mahaifin nasa yay ba tare da yay magana ba ya ɗauke kansa a hankali kuma ya tura Apple ɗin cikin bakinsa,duk son sa da Apple yau jiyaye batai masa daɗi ba, he’s lost his appetite gefe guda kuma tunanin Airah ne fal a zuciyarsa tun safe rabonsa da ita he’s worried, bisa dole ya ci gaba da shan Apple ɗin dan bai son kwana da yunwa yasha rabi ya ture plate ɗin gefe yana hamdala, kallonsa kawai Mami take can kuma ta ce “Sorry my soul kana fushi dani ko? Kasan yanayin aikin nawa” bai ce komai ba ya danna wani abu a gefen Wheelchair ɗin a hankali ta fara tafiya sai da yaje parlour sannan ya tsaya, BBC news yakai ya fara kallon labarai, gaba ɗaya suma suka dawo parlour’n Barrister yace “My son” ko kallansa Sheikh bai ba idanunsa akan cenema ya ce “Uhm” Barrister ya ce “be ready you getting marry soon” ba Sheikh har Mami sai da ta kalli Barrister kasa daurewa tayi ta ce “what wrong with you Barrister? Yaya kake magana ɗaya tun safe? Wanne irin Aure wai ana zaune lfya gaba ɗaya Imam nawa yake ne?” Bai kulata ba yace “kana ji na ai?” Jinjina kai Sheikh yay still idanunsa na kan cenema, Barrister ya ce “Governor da kansa yake neman alfarma gareni akan haɗin Auren daya keso muyi,ƴarsa Nana tana sonka sosai” nan ma shiru Sheikh yay sai murza zoben hanunsa yake yana jin zuciyarsa nayi masa zafi, miƙewa Barrister yay ya ce “ka shirya Nidai na amince” kai tsaye Sheikh ya ce “Ni kuma ban so” da sauri Barrister ya ce “meye baka so ɗin?” Kwallon Granny Imam yay ya ce “Granny bacci zanyi” miƙewa tayi tana faɗin “to Babana yau Ubanka ina ga ƙaryarsa zai gwada a kanka” tana faɗin haka ta tura Wheelchair ɗin zuwa flat ɗin Sheikh,wani Murmushi Mami tayi ta ce “Ina raye Imam yay aure?.over my died body” tana faɗin hakan itama ta nufi flat ɗinta,a tsaye ta samu Barrister ya gama shirin bacci hucesa tayi ta nufi bathroom tai wanka ta shirya cikin kayan bacci, a parlour ta samu Barrister ta ce “Gud night” da mmki ya kalleta ya ce “what the you mean by that? Kisan ke nake jira wai meke damunki ne? Rabuna dake yau wajan sati biyu kenan ko an gaya maki dutse ne ni?” Kallonsa tayi tace “kayi hqr Barrister ban jin zan ƙara baka jikina babu abinda kake tsinana min ko 30mins da ƙyar kakeyi a jikina no test gaba ɗaya salam kake i can’t waist my time akan wanann” tana faɗin hakan ta nufi bedroom ɗin ta, Juyi kawai Imam yake ya kasa runtsawa shi kasansa bai san dalili ba a karo na farko ya kejin wani a zababban fellings a tare da shi mararsa har wani kumbura tayi tana ɗagawa, jin bai taɓa jin abu makamancin haka ba yasa ya tashi zaune tare da dafe kansa ya shiga fesar da numfashi,ji yay an dafa shi da sauri ya ɗaga kansa idanunsa ne ya sauka akan Airah wacce take tsaye tana masa Murmushi, fuska ya kwaɓe mata ganin haka yasa ta zaune kusa dashi tana faɗin “Am sorry my life na barka da kewata ko?” Kasa mata magana yay sai hanunsa daya sanya ya jawota jikinsa ya rungome ƙamƙam kamar wani zai kwance masa ita…

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

SIRRIN MU 11-12

Advertisement *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ _It’s #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment…

SIRRIN MU 7-8

Advertisement  *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _This book is for sale it’s #500 via 0116886423 sulaiman Naima…

SIRRIN MU 1-2

Advertisement  *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_    _Jazakillah bilkhair for taking your time to check out my book,I…

SIRRIN MU 5-6

Advertisement  *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _This book is for sale it’s #500 via  0116886423 Sulaiman Naima…

SIRRIN MU 13-14

Advertisement   *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _it’s #500 via 0116886423_ _Sulaiman Naima s union bank evidence…

SIRRIN MU 17-18

Advertisement  *SIRRIN MU* *BY* _✍🏾 NIMCYLUV_ Advertisements _it’s 500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of…