UBAYD MALEEK 2

Advertisement

 

*_UBAYD MALEEK_*

_(Royalty versus love)_

_*Mamuhgee*_

*2*

Treat/repair  your skin with mg’s skincare today,are you battling with pimples, 

Advertisements

Black spot

cream reaction

eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg’s skincare is the plug for you,mg’s skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg’s skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet’s/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don’t HV anything mg’s skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰

Soap price:3k

Chat 08062991549 to plc ur orders

Call:08064532391

We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏

 we can’t wait to be a part of your beauty story🤭

*******

Advertisements

Fuskewa abal yayi Yana dauke kai daga zancen padima din ya maida hankali kan NURU dake tambayarsa lafiyarsa da qafarsa dake ciwo sbd yawan tsayuwa daya kashe qafafun sbd wani lokacin yakanfi awa uku hudu a tsaye a delah gurin aikinsa gakuma manyanci sai qafafun sukeson fara gazawa.

Fira sukahau Yi sosai da abal dinsu kafin daga baya NURU ta miqe tayi gurin ammynsu Dan tayata aikin sabuwar dahuwar dare datakeyi sbd abal din daya dawo badan haka ba kunun madarar raqumi sukeyi susha abinda da daddare sbd ‘yaya matansu basacin abinci me nauyi da daddare a al’adarsu sai kayi aure kafara hayayyafa tukuna.

Sai magriba suka kammala lokacin padima hartayo wankan yamma tana zaune dakinsu tana shafawa jikinta mai batareda NURU ta kalletaba ta ajiye kallabinta data zame daga kanta dogon gashinta ya bayyana Wanda yasa padima turo Baki sbd Bata baiyi tsayin na NURU din ba,

Abu uku ne NURU takedashi duk nata kyawun takejin dama ita Allah yabawa duk ta hada,

Dirarriyar shape din NURU dayafi nata sosai sbd hips da Allah yabawa NURUn da qarin cikin NURUn dayafi nata shafewa sbd ita tafi NURU jiki sai gashin Nan na uku asalin yelloebrown fatar amhara da NURUn ta dauko Wanda yafi nata.

Wanka NURUn itama tayo taraka meryam itama tayo sukazo sukai sallah dukkaninsu atare kafin suka dungamo tsakar gida suka zauna cin abinci tareda iyayensu.

Kallon yanda sukecin abinci abal keyi Yana karantarsu Dan sake tantance wacce zai bada,

NURU yake kallo sosai Yana sake yaba sanyi da nutsuwarta saidai Sam bazai iya badataba sbd cutatuwa zatayi musamman idan yayi duba da baisan taqamaimai waye acikin delah za’a bawa ‘yarsaba.

Kallonsa ya maida kan padima wadda Kecin abincin a kiyaye batason Bata bakinta sosai Sarai yasan halinta da babban burin son abun duniya shiyasa zuciyarsa ke wasi wasi akanta Dan idan taje giyar daular arziki da mulki suka bugeta Yana tsoron ta zama wata mutum dabam sbd tsananin son duniyarta da jijida kanta yanada yawa kowa yasanda wannan.

Numfashi yasauke Wanda yasa ammi kallonsa sbd tasan tunaninsa tana lure dashi da yanda yake karantarsu,

Itadai tunda abune na dole baza’a taba guje masaba to a gaskiyance gwara abada padima sbd tunda sunada wata ‘yar bazata iya Bari abada NURU ba Dan baqaramar cutatuwa zatayiba,

Bazata iya rayuwa acikin sarautaba sam,

Tsaftatacciyar zuciyane da NURU zasu gurbato musu ita da rudin zalamar mulki da dukiya gwara padima tana zuciyar son abun duniya Dan haka zata iya gwagwarmaya acikinsu ta qwataci kanta dama ‘yayan negestati dazata haifa.

Suna kammalawa dukkaninsu suka hau fira da abal dinsu bayan NURU ta tattare gurin itada meryam suka dawo suka zauna.

_________________

*_No 554 U.MALEEK DELAH Aptmt_*

_Jericho brighton New York City,New York._

Mum””Yar budurwar yarinyar da Bata wuce sha Tara ba ta furta cikin nuna takaicinta da damuwarta a fili tana kallon takardun hannunta data dauka daga gaban madubin bedroom din uwar Tata.

Qarasowa tayi idanuwa na cikowa da hawaye har gaban dining din ta daga takardun dake hannunta tana cewa”

Mum menene wannan??

Cikin wata irin cikakkiyar izza data gama Kama jininta ta dago a natse Kamar Bata fahimci damuwa da tarin baqin cikin data gani atattare da babbar ‘yartaba wadda bazaka taba cewa ‘yartaceba sbd itama tsufa ko wani manyanci ba gama kamata yayiba sakamakon auren wuri na sarauta da akai musu da mijinta shiyasa ‘yartata tazamto Kamar wata qanwarta danma tafi Yar ‘kyawun jiki da itakuma ‘yar tafita kyawun fuska nesa ba kusaba sbd zallar Kamar mahaifinta data dauko.

Kallo daya tayiwa takardun kafin tamaida kallonta kan fuskar ‘yar cikin wani irin sautin zallar iko da mulki tace”

AFIA menene naki akan wainnan takardun dake hannunki?

Wannan tsakanin nida abal dinki ne so stay out of it okay?

Dire mata takardun tayi da qarfi gabanta idanuwanta na cikowa da hawayen baqin cikin halin mahaifiyarta tace”

Mum wannan decision din naki na nufin rabuwa da abal fa,kinsan abal mgn daya yakeyi Wanda idan yayi Babu Wanda ya isa canzawa

Mum are you willing to take that risk?

Idan bakya tunanin kanki da rabuwa dashi mum please kiyi tunanin mu ‘yayanki idanma Ni bakya tunanina kiyi tunanin farhat Mana,

Mum farhat bazata iya rayuwa Babu ‘dayankuba tsakanin ke da abal idan kikai signing wannan contact din Kika tafi Tokyo shikenan fa kinbar delah har abada bazasu karbekiba kokin dawo daga baya please think and think and think mum”” taqarasa mganar hawaye na gangaro mata tanajin Ina zata Sanya zance mum dinta ta aje wannan rayuwar dama tafi ta turawa zama abin tsoro.

Spoon din boiled veggies da aka soya da kwai takai bakinta tareda shanye sauran black lemon tea dinta ta zari tissue ta goge bakinta kadan ta miqe tsaye sai alokacin ta fuskanci afia din dakyau ta kalleta cikin wani irin iko tace”

AFIA tuntuni nasan cewa zanbar delah duk ranarda na karbi contract din santrigo Tokyo na jirane dama sbd ki qara girma kiyi wayonda Zaki kula da farhat idan natafi hakama idan nadawo nasan Zaki tsaya tsayin daka su karbeni,

Santrigo Tokyo babban burinane Dana girma dashi na rayu dashi Dan haka aure bazai hanani cika burinaba ayanzu Dana samu dama,

Idan kinason duk wannan kar ayi azauna lfy kije kiyi convincing dad dinki yabarni naje Tokyo nayi aikina Dan bazan bar aikina Dana dauko shekaru fiyeda goma sha ba inayi akan tsantsar ikonsa da izzarsa ba.

Wani numfashin mamakin mum dinta tasake tana mata kallon mum kinyi nisa ta sake sauke wani numfashin tareda gyara tsayuwa ta kalleta cikin sanyin murya tace”

Mum kinfi kowa sanin mijinda Allah yabaki idan duk dukiyar Tokyo zakije abaki bazaki samu abinda yakai Wanda kike samu agunsaba,

Duk abinda Zaki samu a duniya bazaki samu abinda yakai _*UBAYD MALEEK DELAH*_ ba,

Mum Ina sake Baki shawarar kizauna adaki kiyi tunanin abinda kike Shirin aikatawa,

Zaki rasa mijinki,’yayanki biyu,dukiya,suna da matsayinki na Matar _MALEEK_ na GIZAH Wanda nake ji Miki tsoron rasawa har abada.

Ke mahaifiyatace bazanso ki rasa duka wainnan sbd abal shine abu na qarshe da mace zatai baqin cikin rasa samunsa a rayuwa.

Wani QAYATACCEN murmushi LAILAH tasaki tareda dafa kafadar ‘yarta tace”

AFIA ke yarinyace

Kinason dad dinki fiyeda komai shiyasa kike ganin dukkanin hakan Amma abinda Baki saniba shine dad dinki mutum ne da duk duniya Babu me juyasa sai kakansa Wanda Shima halinsune yazo daya,

Inaga zaifi ki nutsu ki maida hankali kan karatunki ki Kuma kula da farhat Dan zata shiga damuwa sbd bananan Kuma dad dinku is a very busy man.

Kasa cewa komai tayi tabi bayan mum din Tata da kallon damuwa da baqin ciki harta haye sama.

Masu aikin gidan ne kusan su biyar sukazo suka fara tattara kayan dining din suna gaidata cikin tsananin girmamawa duk da dukkaninsu sun girmeta wasuma sun haifeta Amma sbd matsayinta na babbar ‘yar maleek suke Bata mugun girma.

Ko kallonsu bataiba sbd halinda zuciyarta take ciki gabaki daya a jagule take bazataso auren iyayenta ya rabu ba akan iko,izza da isar dad dinta dakuma taurin Kai da burin duniya na mum dintaba,

Farhat kawai take dubawa sbd yarinyace sosai akanta sbd ita yanzu takeda 8years a duniya bazata iya ganin iyayenta sun rabu ba saidai abu daya tasani shine rabuwa kamarma sunyine Dan Babu abinda zai sauya taurin Kai irin na mum 

Dad din Kuma aishi kankat ne Dan yafita zama riqaqqe saidai tana jin tausayinsa sbd mutum ne shi me tsananin qyanqyami na komaima 

Suna rabuwa da mum za’a fara kawo Masa ‘yayan manyan masarautu kokuma ma za’a iya kawo Masa negestati Wanda tasan tsananin qyanqyaminsane ya hanasa qara aure aure kamar sauran ‘yan delah musamman shi dayake ubayd maleek na GIZAH,

Hakan nema yasa ya kebe kansa anan new York da iyalinsa Yana gudanarda rayuwarsa a qaidance yanda yake sonsa ba tarkacen hayaniyar masarauta duk da yasan dole wata Rana zai koma can da zama.

Bedroom dinta ta nufi ta fada kan gado tareda rintse idanuwanta hawayen ciki suka gangaro ta share da qarfi cikin takaici tace”

Bazanyi kukaba mum tunda haka Kika zabar Mana shikenan zamu runguma mu rayu Kamar marayu duk da munada uwa Amma ta zabi duniya akanmu.

Miqewa tayi tafada toilet tayo wanka tana fitowa tashirya a gaggauce ta zari ipad dinta ta fito ta nufi library din karatunsu tana qoqarin fitarda damuwar dake cikin ranta sbd mum tayi nisa batajin Kira sbd sunfi shekara akan wannan mgnar taqi barinta yanxu harta karbi takardun contract din shikenan komai yazo qarshe.

‘dagowa tayi bayan ta zauna cikin library din ta kalli qaton makeken hotonsu na family daya cinye kwatan bangon library din ta qurawa dad dinta fararen idanuwanta da nashine ta dauko Zak,

Bawai Dan tana tsananin son dad dintaba Amma Bata taba ganin mutuminda ya hada irin qualities dinda ya hadaba,

Dad dinta is 99% takowane fanni.

Mum dinta takalla ta rintse idonta ta bude tana cewa”

She’s perfect, she’s beautiful tanada komai but she’s nothing compare to dad Amma takeson barinsa meyasa?

Farhat da kanta takalla a hoton take hawayen datake riqewa suka gangaro mata ta miqe tabar gurin tana fasa karatunma.

________

********NURU”” ammi takira sunan cikin tsoro da fargaba,

Abal meyesa kake ganin zabin NURU shine daidai bayan kasan NURU bazata iyaba.

Numfashi ya sauke Yana gyara kwanciya yace”

Padima gidan sarauta kamarna delah zaisa burinta ya fadada zai iya hallaka tunaninta da tarbiyarta.

Amma Kuma abal NURU tayi rauni da yawa kaduba.

Aa jamila kina dai tausayinta ne Amma itace zata fi mutunci a irin gurin sbd me hkr shine zaici ribar zama a delah.

Riqo hannunsa tayi tana marairaicewa da hawaye cikin idanuwanta sai jikinsa yafara sanyi Sam bayason ganin damuwarta sbd tsananin so da qaunarta dayake,

Kusan sati daya kenan sunata muhawarar wazasu bayar din kafin shi ya yanke NURU itakuma ta yanke padima.,

Ajiyar zuciya ya sauke sbd tunanin dayayi na girman Kai da burin padima na zuwa DELAH GIZAH bazai taba barin ta yardar musu ta yarda subadata a delah tanan ba tsaf yasan bijirewa zatayi sanin haka yasa yacewa ammin ya amince abada padima.

#MAMUH#

*_Haske writers💡_*

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_ZAFAFA BIYAR_💘💘💘

_ZAFAFA BIYAR_💓💓💓

_(ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL)_

_(HUBILMAHX)🧡🧡🧡_

_ASSALAMU ALAIKUM! INA MASOYA MA’ABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA?!_

_TO KU MARMATSO DOMIN NESA TAZO KUSA, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKE KAWO MUKU DA’DADAN LITTATTAFAN NAN ZAFAFA GUDA BIYAR, SUN SAKE ZUWA DA KASHI NA 4._

_SAFIYYAH HUGUMA_

_BILLYN ABDULL_

_MISS XOXO_

_HAFSAT RANO_

_MAMUH GEE_

_RIGIJI GABJI DINFA KENAN, DOMIN WANNAN KARON MA MARUBUTAN SUN SAKE KAWO MUKU WASU DADADAN MASU FADAKARWA, NISHADANTARWA, NISHADANTARWA UWA UBA KUMA AKWAI LAGWADAR SOYAYYAH…_

_*SAFIYYAH HUGUMA:* TAZO DA NATA SALON RUBUTAN MAI SUNA: *ALKIBLA*❤️❤️_

_*HAFSAT RANO:* TAZO DA NATA TAKEN RUBUTUN MAI SUNA: *MABUDIN ZUCIYA*🥰🥰_

_*MAMUH GEE* TA KARA ZUWA DA WANI SAMFURIN MAI SUNA: *UBAYD MALEEK*😘😘_

_NANA- HAFSAT *(MISS XOXO)* TA SAKE ZUWA DA WANI KALAR NA: *DALAAL*💞💞_

_*BILLYN ABDULL* TA KARA ZUWA DA WANI TAKEN MAI SUNA: *MAKAUNIYAR KADDARA*💝💝_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like