UBAYD MALEEK 5

Advertisement

 *_UBAYD MALEEK_*

_(Royalty versus love)_

*_Mamuhgee_*

Advertisements

*5*

Zubewa AFIA tayi kan kujera tana sake wani irin kuka tana cusa kanta cikin tafukan hannayenta dasuke rawa.

Kamar zai wuce saikuma yaji afian na buqatarsa ayanxun sbd yasan tana cikin radadi.

Cikin takunsa na zallar nutsuwa ta asalin jinin sarauta yatako ya iso gabanta tareda miqa mata hannu batareda yayi mgna ba ta dago jajayen idanuwanta dake tsiyayar hawaye ba kakkautawa ta damqe hannunsa tana Kiran sunansa ahankali cikin kuka mara sauti.

Janta yayi farhat na jikinsa ya haye sama dasu zuwa ainihin babban bangarensa dake daukeda qaton palon farko Dana biyu Wanda baiyi girman na farko ba acikin palon na biyu Nan qofar qaton master bedroom dinsa yake ita Kuma lailah qofar bedroom dinta na tun a palon farko sukuma su afia din sukeda manyan bedrooms dinsu guda biya ata cikin Palo na biyu dake qasa ita daya farhat daya Amma a dakin AFIA din take kwana da farhat sbd tazama tamkar itace uwar farhat din duk da akwai tarin Nanny’s da masu aikin dake kula dasu duk su duka din sbd Sam tun tashinta kafinma haihuwar farhat mum dinsu tabarwa masu renonsu dawainiyarsu Sam batada lokacin kantama bare na ‘yayanta shi koyaushe tana gurin aikinda zata Gina sunanta duniya tasan da ita shiyasa acikin kadaici afia ta taso harsai bayan uwan farhat duniya tasamu sauqi sbd duk da akwai masu kula da farhat itakam Bata barmusu ragamar farhat din dukaba musamman da watanta goma cif aduniya lailah ta yayeta daga Bata nono tun afia Bata iya dawainiyar farhat ba harta iya shiyasa farhat din duk duniya tafi shaquwa da afia da dad dinta duk da tanason mum dinta Amma tafison dad dinta da afia itama afian sbd sanin mum ba lokacinsu takedashiba yasa girman dole yahau kanta duk da qananun shekarunta tazama itace madam din gidan dole masu aikin gidan kaf umarninta kawai suke jira sbd ita suka gani Matar gidan ko lokacin jininta tayi baresu masu aikin shiyasa basa Sonta bakuma su tsanetaba tunda batai lokacinsu bama bare musgunawa ko wulaqantawa da tozartawa ‘yayanta dai Kam suna tsananin sonsu da qaunarsu tareda tausayinsu duk sbd mahaifinsu UBAYD MALEEK Wanda suke tsananin jin dadin aiki a qarqashinsa duk da tsananin miskilancinsa da ikonsa mulki dake jininsa Amma baida tsanani ko tsauri ko kadan.

Table din lunch aka gama gyarawa yaja ‘yayansa suka isa dining room din farhat Kam harta sakewarta ganin ga dad dinta ga afia to itakam batada damuwa tunda dama haka suke rayuwa mum batanan koyaushe.

AFIA ce dai Saida qyar ta iya tuttura abincin Shima yacine kawai saidai Babu Wanda ya isa yace ya karanto kokuma ya fahimci halinda zuciyarsa da tunaninsa suke ciki cikin nutsuwarsa kaman koyaushe yaci abincinsa.

Ranar baisake fita ba yini yayi da yaransa cikin tsananin kulawa da qauna har dare sukai dinner sukaje sukai sallah da wanka suka kwanta AFIA na rungume farhat cikin jikinta sabbin hawaye masu zafi suna gangaro Mata.

Washe gari ma tare sukai breakfast da dad dinsu su suka fara wuce school da driver dinsu kafin shi daga baya ya fice.

Advertisements

 

Ahankali kwanakin suka fara tafiya damuwa tashigi afia sosai sbd yanda ta Sanya rabuwar iyayenta cikin ranta har abin ya tabata yafara taba karatunta komai Bata ganewa a makaranta tun Ana Mata mgn har Saida school din suka nema dad dinta sukai Masa bayanin kwata kwata Bata gane komai na karatu ko exams dinta gabaki daya Babu Wanda taci hakan yasa ya ragewa kansa aiki sosai sbd samun lokacin zama da yaransa Dan afia idan akai wasa zata iya samun matsalar qwaqwalwama.

Kullum takan Kira mum dinta Amma Bata wani Bata lokacin mgn she’s always busy with aiki aiki aiki hakan yafara Sanya afian jin haushi musamman da ita mum din Bata taba kiraba saidai ita takira ta bangare daya ga dad dinsu Yana iya kokarinsa duk kasancewarsa me tarin abubuwan Yi Amma duk ya taqaita sbd su ‘yayansa sai hakan yasa tafara dawowa hankalinta taji inama dad zaisamu farin ciki Kamar kowane mijin aure.

Ahankali ahankali trauma din rabuwar iyayenta yasaketa sbd watanni da aka ‘diba tuni ta sakewarta yanzu suna rayuwarsu cikin walwala musamman Mum Sarah dake kulawa dasu sosai yanzu kamar itace ta haifesu matarda tun haihuwar AFIA Amman UBAYD ta Aiko musu da ita daga delah gizah gashinan haryanxu tana taredasu tana musu aiki danma ta zama Kamar kakarsu Amma Mum Sarah suke ce da ita sbd tun afia na qarama da farko ma ta dauka itace ta haifeta saidatai wayo tasan lailah ce ta haifeta Amma duk da haka qaunar kamr uwa da ‘yace tsakanin afia din da mum Sarah,

Yanzu gidan rayuwarsu suke Kamar dama haka suke Basu taba rashin waniba agidan hakan yasaka hankalin dad dinsu kwantawa ya maida hankali kan harkokinsa musamman idan Yana dubin shekarun sauka mulkin NEGES ABDUL-SAMAD MUH’D KALEEB wato sarki na yanzu qanin mahaifinsa Kuma mijin mahaifiyarsa Wanda sbd Yana yarone mahaifinsa yarasu shiyasa akabada mulkin wa qaninsa kafin shi dansa ubayd ya girma Wanda Sam shi yanzu ba wani mulki dayakeso ko yake gabansa shiyasa bai taba sha’awar zama kusada mulkin ba yayi nesa dasu sbd ma kada son abin yasamu damar shigarsa Amma gashi lokaci na son qaratowa.

Ana cikin hakan kaleeb yaga lokaci nata ja zaman maleek guda baiyi Masa ba Babu mace ataredashi ma’ana Babu gurin sauke buqatarsa Sam Sam ubayd shine jika mafi soyuwa a rayuwarsa Kuma Wanda yakeji cikin ransa fiyeda ‘yayan daya Haifa Dan haka bazaiso wata mishkila ta bangarensaba ko kadan zai Masa shirin negestati yatafi da ita inda yake kafin yafara nazari da duban inda zai samo Masa matarda duniya zata shaida UBAYD MALEEK yayi matarda ko indatake akace matarsa lailah data watsa Masa qasa a ido ta kalla tasan tayi babban kuskurenda har abada bazai gyaruba.

A jiya ‘daya daga cikin amintaccin bayinsa da tun iayayensu nada rai sukai Masa bauta yai tunanin yonas Wanda cikin wainda aka bawa sauyin ‘yanci shikadai ne me ‘ya mace wadda zataso amatsayin negestati…..

wani irin numfashi ya sauke ahankali Yana gyara kishingidarsa akan qatuwar shimfidar babbar dardduma me tsananin laushi dayayi sallah bai tashiba Yana adhkar ya numfasa tareda daukar wayarsa dake gefensa ya Kira numbern daza’ayo Masa Kiran tsohuwar jakadiyar marigayiyar matarsa.

Cikin qanqanin lokaci saigata ta iso akai Mata iso tana shigowa ta zube qasa tana kwasar gaisuwa batareda ya dagoba cikin wani irin iko na tsohon sarki yace”

Akwai sabuwar sauyin ‘yancin bawai ta negestati ‘ya daga wajen bawa yonas ‘dan tsohon amintaccen bawana ilyas gasasshiyar tabbarwa nakeso Kuma a sirrance zancen zaizama kije kidubota da kanki ki tabbatarda igancinta idan ta isa ta zamo wadda UBAYD MALEEK zai iya hada shimfida da ita wadda zai iya tafiya da ita can qasar dayake kafin asamo wadda zata maye gurbin igiyoyin aurensa idan yarinyar Bata kaiba atara bayi Mata azabi wadda tafi tsohuwar matarsa komai a killaceta anan cikin delah afara kulawa da ita Ana Bata gyara kafin zuwansa yatafi da ita kokuma kafin na aika Masa da ita.

Angama Kaleeb me delah me gizah.

Juyawa tayi da hanzari Dan zuwa cika umarninsa cikin sauti me amo taji yace”

Babu Wanda zaisan ubayd maleek ya rabu da matarsa hakama babu Wanda zaisan negestatin ta ubayd maleek ce.

Da saurin ta zube qasa cikin girmamawa da tabbarwa tace”

Duk ranarda wannan zancen yafita ta hanyata na bada kaina acire fansar cin amanar danayi.

Jinjina Mata Kai yayi ta miqe tafice tana sake basa gaisuwa.

*************

Zaune suke jigum jigum fuskokinsu cikeda damuwa da baqin ciki Babu me iya mgn se sautin kukan padima dake fita ahankali ahankali tana roqon abal da ummi dasu yafe Mata tsautsayi ne.

Cikin nauyin zuciya abal ya dago ya kalleta da idanuwansa dasukai jajir kafin ya kalli ummin da ita shita kalla da idanuwanta dake cikowa da hawaye tana maidawa sbd batason zubarwada padima hawaye kada Allah ya kamata da laifin sakasu zubda hawaye abin yamata yawa,

Fahimtar abinda abal ke nufi da kallon dayai Mata yasa ta bude Baki daqyar cikin nauyin nurya data toshe da baqin ciki tace”

Padima mune iyayenki da bazamu taba zabar Miki abinda zai cutatar dake Dan haka kiji tsoron Allah kifada gskiar abinda yake faruwa,

Nice na haifeku duk ku duka Kuma nasan halin kowannenku fiyeda ku kanku tun ranarda akai maganar badake delah zuciyarki Bata amintaba Kuma shine dalilin dayasa Kika Hana kanki sukuni koba haka ba???

Tsit tayi tana Dan share hawayenta cikin jin tsoron anfara ganota takasa dago Kai ta kalli kowa cikin tsananin fushi da baqin ciki abal yace”

Hakane koba haka ba?

A kidime cikin tsoro tace”

Eh Hakane.

Dukkaninsu wani sabon baqin cikine ya turniqesu musamman NURU da hawayenta suka fara gangarowa.

A qyamace ummi tasake jefa Mata kallon baqin ciki tace”

Sbd baqyason abadake delah shiyasa jika bawa wani kanki yayi Miki ciki sbd ki nuna bamu isa dakeba duniyar dakikeso ita Kika saka gaba….

Da sauri ta girgiza Kai tana fashewa da kuka tace”

Ummi kuyi hakuri wlh banda ciki Amma..Amma…Amma tsoron hukuncin kasheku danima idan naje delah aka….aka..aka gano…yasa nace inada ciki sbd NURU ta yarda taje ta yanda Babu abinda zaisamu kowa wlh ummi sharrin shedan ne Kuma….

Wani wawan gigitaccen Mari abal ya sauke Mata guda biyu Wanda yasata zubewa kwance tana hadiye sauran maganar cikin tsananin tashin hankali sbd yaune karo na farko da aka taba lafiyar jikinta.

Kasa mgn ummi tayi sai hawaye sbd sunkasa riquwa yanxu Kam,

Cikin baqin ciki abal yace”

Sbd son ranki Kika siyarda mutuncinki,

Kika ringa wasa da amfani da qaunarda ‘yar uwarki ke Miki harkina qarya da zance me girma na cewar kinada ciki Dan kawai bakyaso.

Kinyiwa kanki padima,

Kinyiwa rayuwarki,

Ban Miki bakiba Amma wannan abinda kikai shine babban kuskure mafi girma dazakiyi danasani akansa Amma tunda ke Kika zaba hakan ‘yar uwarki zataje delah kekuma idan kingama tsare tsaren burikan naki amed din yafito zanmuku aure dashi Allah yabawa kowa alkhairinda yake fata.

Miqewa yayi Rai bace ya fice yabar gidan ummi ma qala batace Mata ba ta miqewarta meryam na riqeda hannunta.

Ba kunya padima ta tashi zaune tana share hawaye duk fushinda za’ayi tasan kowa zai sauko itadai tunda buqata tabiya angama me wahalar.

Kallon NURU tayi zatai mgn NURUn ta miqe batareda ta kalletaba zuciyarta na Mata zafi da radadin abinda padima tai Mata baqin ciki goma da ashirin ga tafiya delah ga abinda padima tayi ita rayuwartama ta ruguje gabaki dayanta sbd shikenan ta tabbata batada rabon zama acikin igiyoyin aure idan taje delah tariga tazama negestati idan ba Allah ne yayi Mata raboba tasamu damar shiga inuwar aure.

Gabaki daya gidan rikicewa yayi Babu me farin ciki bare walwala tundaga ranar sai padima data bushe ido tasakewarta da walwalarta da komai tunda buqatarta tabiya kowama yayita baqin cikinsa duk zasu dawo daidai idan komai yasake wucewa.

NURU ta sauya sosai gabaki daya yanxu batada walwala kullum cikin damuwa da tunani take idanuwanta harsum bushe da kukan tayi tayi tagaji harta daina saidai ido.

Ranarda jekadiyar Kaleb tazo duba NURUn tayi Mata kallo harna qurulla take tagama tabbatarda NURUn itace mafi cancantuwa Nan take takaiwa Kaleb rahoto yabada umarnin afara gyaranta tun agidansu kafin kwanakin daukota su cika.

Al’amari yadawo sabo sbd irin zarya da matakan tsaro da bayin da aka kawo aka zuba a gidan yasa al’amarin yafara bawa kowa tsoro da mamaki itadai padima ko ajikinta matsuwartama ayi ayi agama NURUn ta tafi sbd tsoron karma wani abu ya gitta aqara dawoda abun kanta.

Hankalin iyayensu yafara tashine sbd tunanin wannan tsananta tsaron da matakan dasukai yawa da wuya idanba gizah za’a Kai NURU ba sbd sai ‘da mafi kusanci da sarauta akewa irin wannan taka tsantsan din Amma dai Babu iko ko hurumin tambaya.

Cikin kwana goma sha daya dukkanin Wanda yayiwa NURU kallo daya baya sakewa a qaidance idan ba hakaba hukunci zai hau kansa sbd wani irin sauyi me yawa datayi,

Fatarta ta sauya fiyeda tsammani,

Haskenta ya ninku komai nata santsi yake musamman gashinta dako dankwali baya zama sbd tsantsi ga sutura ta alfarma da aka kawo daga Kaleb Kai tsaye a sirrance.

Ayau tun safiyar jiya take kuka har idanuwanta basa iya gani sosai sbd yaune ranar tarewarta/ma’ana tafiyarta,

Ammi da abal kwana sukai Bata nasihu da rarrashinta ita ammin ma Kamar yanda NURUn ke kuka hake takeyi Daren farko lafiyayyun motaci biyar sukazo daukeda dukiya da abinci tareda sitiru na alfarma wa iyayen negestatin kafin aka dauketa a sirrance tareda mahaifinta yakarata yakaita har gaban Kaleb Wanda yasake narkawa abal din dukiyar tukaici rakiya aka nufi wani kebantattcen sashe na musamman daya gama hada jin dadin duniya da NURUn tareda sabbin masu kula da ita su shida cif cif ha’di da jekadiyar Kaleb Wanda ke sake yaba zabinsu na NURUn.

##MAMUH#

*Last free page*

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_SAFIYYAH HUGUMA_

_BILLYN ABDULL_

_MISS XOXO_

_HAFSAT RANO_

_MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like