19

Advertisement

 *THE GOVERNOR’S WIFE*

…… MATAR  GWAMNA….

 *©Azizat Hamza*

 wattpad Azi_zat 

Bismillahir Rahmanir Rahim

Advertisements

Book one

19

Da dare kusan ƙarfe goma COS ya je wajen Yallaɓai, batun tsige Gwamna da ake shirin yi ya kawoshi. Ya sani Umaru Kwom ne da wannan shiri amma kuma yana da yaƙini akwai sa hannun Mr Paul a ciki.

“Yallaɓai baka ce komai ba. Kana so a tsige Saifuddeen ne?”

Yallaɓai yai dariya yace “Lamara kenan, kana ganin za su iya tsige shi ne?”

Advertisements

“Amma tunda suka fara maganar ai sun shirya wa abun ne”

” idan sun shiryawa abun ai Alhaji Sani Kachallah ma a shirye yake”

“Hakane kam, amma nayi mamaki da kace kada na faɗawa kowa cewa Asiya ta haɗa hannu da Umaru Kwom”

“Wannan rikicin cikin gida ne, mu zuba musu ido kawai”

“Yarinyar fa abin tsoro ce, kada gaba ta zo tana bamu matsala”

“Ina ganin akwai rawar da Asiya zata taka a gwamnati Saifuddeen Kachallah, The girl has Charisma”

Yallaɓai yai maganar yana shafa gemunsa.

***

Maganar tsige Gwamna da ake yi ya ja hankalin ƙasar kan siyasar jahar Congo. Ko’ina ka shiga maganar ake yi. Mutane da dama sun yarda Saifuddeen Kachallah mutum ne adali, yayinda wasu maganar albashin ‘yan fensho da ba a biyaba ya sa suke ganin ya gaza.

A ɓangaren Asiya ko ɗar ba ta ji ba da Ubayd ya mata magana akan kada ta aikata abinda tayi niyya. So take ayita ta ƙare, ana tsige shi za ta nemi takardar saki idan ya ƙi bata kuma kotu zata kai shi a musu Khul’i.

Ba abinda zai sata farinciki sama da ta ji yau ance mata an tsige Saifuddeen daga muƙaminsa na Gwamna. Ranan ƙila sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

A ɓangaren Bilkisu kuwa ta rantse babu wanda ya isa ya tsige mijinta. Idan aka tsige Saifuddeen  tamkar an mata tsirara ne a kasuwa. 

Shima Alhaji Sani Kachallah ya shiga ya fita akan maganar dan har wajen party chairman na ƙasa yaje sun bashi tabbacin indai Saifuddeen bashida laifi ba wanda zai tsigeshi.

Wannan magana yasa Alhaji Sani ya gane akwai mutane masu fiska biyu, kai har uku ma a tafiyarsu, kuma da sannu idan ƙura ta lafa zai yi maganin ‘yan banza.

Sun zaɓi ranan da Gwamna zai je buɗe stadium da aka gyara a matsayin ranan da za a wallafa dalilin daya sa za a tsige Gwamna.  Lokacin da Umaru Kwom yace zai sa a jefi Gwamna Asiya tayi na’am da hakan. Duk abinda zai ƙasƙantar da Saifuddeen Kachallah to tana so.

Abinda Asiya bata sani ba shine, shirin da take da Umaru Kwom daban, shima shirin da yake da nasa mashawartan daban. Ita burinta ta ɗau fansa akan Gwamna Saifuddeen ne shi kuma burinsa ya hamɓarar da Saifuddeen saboda ya samu ƙarfin gwiwa a zaɓen da za ayi. Idan ya tsaya takara da Saifuddeen to ba makawa zai rasa kujerar amma idan da wani daban ne yana da yaƙinin zai ci zaɓe.

***

Ranan Asabat ƙarfe tara da rabi Gwamna ya fita daga gida zai fara zuwa Kachallah house kafin ya wuce Stadium.

Asiya ta zauna a ɗaki tana jiran komai ya tafi yadda aka tsara.

Ƙarfe goma saura kwata wayarta ya fara ringing, ta ɗauka da sauri ganin Fou’ad Salisu ke kiranta. Bayanin da ya fara mata ne ya sata miƙewa tsaye da sauri dan ta tabbatar dai kunnenta ya ji dai dai.

“Hello kina jina? Na ce ba Gwamna ke da wannan account ɗin ba. Alhaji Sani Kachallah ne. Account ɗin Sa’ad Kachallah an buɗeshi lokacin Gwamna yana shekara goma a duniya, bashi da masaniya akan account ɗin. Na gayawa Umaru Kwom amma ina ganin kema ya kamata ki sani”

Tabbas ta ji shi a karo na farkon da yai maganar. Ɗimuwa, kiɗima da gigicewa shine ya sa ta daskarewa a wajen.

Asiya ta tunɓuke ɗankwalin kanta ta yi cilli da shi lokacin da wayar da ke ɗare a kunnenta ya faɗo ƙasa.

“Na shiga uku ni Asiya” ta faɗa tana dafa ƙirjinta

*idan labarin nan ya fita, sunana zai kafa tarihi a duniya. Zai kafa tarihin cewa ni ce Matar Gwamna ta farko a tarihin ƙasar nan da na yaƙi mugun Gwamna na kawo ƙarshen sa*  

Abinda ta faɗawa Ubayd kenan ranan da ya mata magana a kan abinda take shirin yi.

Kalamansa suka fara dawo mata filla filla a kwanyarta.

“Asiya ki dena abinda kike yi. Babu kyau. Gwamna adalin mutum ne, shi ɗan Adam ne, zai iya yin kuskure kamar kowa, ki masa uzuri. Kar ki manta fa MIJIN KI ne. Ko ban aureki ba Asiya har gobe ke ƙanwata ce, dan haka ba zan taɓa bari kiyi abinda zai jawo miki dana sani ba. Ki riƙe mijin ki da kyau ki dena ƙoƙarin hamɓarar dashi. Ki rungumi mijinki Asiya, we are not meant to be”

Ta durƙusa ƙasa ta ɗauki wayarta da sauri. Hannunta ɓari ya ke lokacin da take ƙoƙarin kunna wayar saboda ta mutu lokacin da ta faɗi ƙasa.

Wayar na kunnuwa ta shiga lalubo numbar Mr Bassey, tana danna numbar ta ƙara wayar a kunnenta, ga kowanne ringing da ke fita yana dai dai da dokawar da zuciyarta ke yiwa ƙirjinta yana ƙoƙarin barin mazauninsa.

“Hello. Mr Bassey. Kar a fitar da labarin nan. A dakatar da komai” ta faɗa da iya ƙarfin muryarta.

“Miya faru Hajiya?” Ya faɗa cike da mamaki bayan awa biyu da su ka wuce aka gaya mi shi cewa ya wallafa labarin.

“Dan Ubanka na ce a dakatar da komai, komai na ce”

Ɗif dodon kunnenta ya buga saboda dena jin komai da ta yi na wasu daƙiƙu.  Lokaci guda ta yi fatan inama kaman Umma Allah yayi ta marar ji marar magana.

Durƙusawa ta yi ƙasa, ƙafafuwanta da gwiwowinta su ka nitse cikin lallausan Italian carpet da ke ɗakin. A yanzu maimakon laushin carpet ɗin kaushin sa take ji, ji ma take kamar a cikin harawan dabbobin Umma ƙafafuwanta suke.

*” Hajiya, ai kusan minti talatin kenan da wallafa labarin a website ɗin mu da shafukan sada zumunta. Yanzu haka an fitar da jaridan kasuwa”*

Bata iya cewa Mr Bassey komai ba saboda aikin gama ya gama.

Idan labarin nan ya isa ga Gwamna zai yi bincike, ba za a daɗe ba zai gano cewa itace da wannan aikin, ita ce take yiwa jaridar Climax rubutu. Idan aka jefi Gwamna ba lallai ya san akwai hannunta a ciki ba, tunda yana da maƙiya dayawa zai ma ɗauka  mutanen Umaru Kwom ne da wannan aikin. Amma idan ya san ta haɗa hannu da Umaru Kwom wajen hamɓarar da shi…

Ta sa hannu ta dafe ƙirjinta da tuntuni ya ke ta bugu da ƙarfi. Ɗumi ta ji a kumatunta hakan ya sa ta shafa wajen da sauri.

Karo na farko kenan tun zamanta MATAR GWAMNA ta yi hawayen danasanin abubuwan data aikata.

Idan komai ya fito fili sunanta a tarihi zai koma Maƙaryaciya, Mayaudariya kuma Munafuka.

Kyakykyawan fiskar Gwamna ta hango yana faɗin “Asya WHY?”

T V dake ɗakinta ta yi saurin kunnawa ta nemi remote ta lalumo tashar Hill TV dan ta san za su bayyana koma minene dalla dalla. 

Daga wajen da ake kawo rahoton kai tsaye na buɗe filin wasan ƙwallon ƙafa da aka gyara suka yanke zuwa labari da ɗumi-ɗuminsa. An bayyana dalilin daya sa ake son tsige Gwamna Saifuddeen. Shekaru shabiyar da suka wuce ya ci zarafin wata yarinya lokacin da ya ke koyarwa a Jami’ar Congo.

Asiya ta zaro ido ganin abinda aka rubuta da kuma abinda mai karanto labaren ke faɗi wanda bai kama hankali ba. Ba abinda ta rubutawa jaridar Climax kenan ba. Ta yi saurin jawo wayarta ta duba website ɗin jaridar Climax ta ga  suma labarin cin zarafin da Prof. Saifuddeen yai wa wata ɗalibarsa Lami Ninja suka wallafa. Kanta ya kulle dan abu daban ta rubuta abu daban aka wallafa. Wacece ma Lami Ninja?.

Ta nemo numbar Umaru Kwom ta danna masa kira, ba a ɗauka ba sai a bugu na uku.

“Alhaji Umaru ban gane abinda ake faɗa ba. Na ɗauka maganar kuɗi ake”

“Kuɗin Alhaji Sani ne ba nashi ba,  ba za a tuhumeshi da wannan ba shiyasa muka nemo abinda zai hamɓarar da shi cikin sauƙi”

“Miyasa ba a gaya min ba, miyasa ka barni cikin duhu?”

“Siyasar kenan Yarinya ” daga haka Umaru Kwom ya sa dariya ya kashe wayar.

Asiya tayi taga taga kamar zata faɗi. 

Kenan Ubayd yayi gaskiya da ya ce zai iya yiwuwa duk abinda ake Gwamna bai sani ba, ƙila kisan Saminu Bacchi ma bai san komai akai ba. 

“Ki yiwa kanki adalci Asiya, a iya zaman da kika yi da Gwamna Saifuddeen kinga alamar zai iya kisa saboda mulki, kinga alamar kuɗi da dukiya za su ruɗe shi?”

Tambayar da Ubayd ya mata kenan amma ta bari ƙiyayya da son zuciya suka sa ta amsa da cewa “eh, Saifuddeen Kachallah zai iya duk abubuwan daka lissafo”

“Ko kin san saboda ya kuɓutar da ke daga hannun Umaru Kwom ya aure ki. Abba ya faɗa min komai, kuma na yarda cewa saboda ya tseratar da rayuwarki ya aureki. He’s protecting you Asiya. Umaru Kwom amfani da ke zai yi ya yar.  Idan kika gama masa aiki juya miki baya zai yi…”

“Tatsuniya kenan Ya Ubayd, ni yarinya ce da zai kareni, wani irin kariya ne da ba zai iya bani ba har sai ya aureni?”

 

 Dana sani ƙeya. Da ta saurari Ubayd ranan da duk wannan bai faru ba.

A iya zaman wata biyu da sati ɗaya da ta yi a gidansa ta zalunce shi, ya mata laifi, amma ita laifin data masa ya ninka nasa sau dubu.

Ta kai dubanta ga talabejin inda aka nuna Gwamna na buɗe Stadium daya gyara, hannunsa riƙe da Almakashi zai yanka ribbon ɗin da aka sa. Ta ƙura masa ido kaman yau ta fara ganinsa, tabon sallah da ya fito dal a saman goshinsa, dimple ɗinsa da ya ke lotsawa idan yana magana, sajensa da gemu da suka ƙawata fiskarsa. Bata taɓa yarda ba idan mutane na faɗa amma yau zuciyarta da idanunta sun amince Saifuddeen Sa’ad Kachallah yana da kyau.

Ta rintse idanunta lokacin da ta tuno cewa Umaru Kwom ya tsara za a jefi Gwamna da zaran ya gama hidimar buɗe Stadium.

Ta jawo wayarta ta yi abu na ƙarshe da take ganin zai fishsheta.

“Allah Sa’id ni” ta furta a hankali, ta kwanta kan gado ta fashe da kuka mai ɗaci…

A nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya a labarin Matar Gwamna.

*Shin za a jefi Gwamna?*

*Wani hukunci zai biyo bayan abinda Asiya ta aikata?*

*Ya maganar tsige Gwamna?.*

*Shin Hansa’u zata samu abinda take nema a wajen Bilkisu Kachallah?, wacece ma Hansa’u*

*Shin Umaru Kwom zai yi nasara akan Gwamna Saifuddeen?*

*Wacece Lami Ninja da aka ce Gwamna Saifuddeen ya ciwa zarafi lokacin da yake koyarwa?*

*Shin Gwamna zai iya yin gaban kansa kuwa? Ko dai Alhaji Sani ne zai cigaba da juya shi*

*shin Bilkisu Kachallah zata bari tauraron Asiya ya haska kuwa?*

*Yaushe Asiya za ta gane cewa ita ce Attaruhu?*

*Akwai yiwuwar soyayya mai daɗi tsakanin Gwamna Saifuddeen da Asiya Shahidah. Kuwa?*

*kaɗan kenan daga cikin batutuwan da za ku gani a kashi na biyu*

*Ga mai buƙatar cigaban labarin a matsayin update na page by page ta WhatsApp group zai biya #400 dan samun kashi na biyu dana uku.*

*Account details*

*account number: 0008219237*

*Bank: Jaizbank*

*account name: Azizat Hamza*

*Ko kuma a turo katin Mtn na #400 zuwa 08137311900*

*za a tura shaidar biya zuwa ga wannan numban 08137311900*

*Za a fara Update ranan Asabat 12/06/2021 Insha Allah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like