JUHUD 11

Advertisement

 

*JH011*

*(Pure love sex nd romantic story)*

*Free page ya qare idan kinsan baki biya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*

 

Advertisements

*Regular group 300  VIP 600 via bank Account  0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank  or card for This number  09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*

Cikin fusata Kareem yake qoqarin qwacewa yana huci Yana cewa “an fada maka kowa ma irinka ne mara Imani mara tsoron Allah Wanda zina tayiwa kanta cikin rayuwarsa” rirriqeshi suka sakeyi Dogari Ado ya kama Muntaz yasa a mota suka fice asibiti yakaishi akayi masa dressing din wajen da Kareem ya faffasa masa kai suka juyo sai huci yakeyi Yana furzar da iska baqin ciki ya hanashi furta ko kalma daya, Wai akan wannan tsintacciyar yarinyar Kareem ya fitar masa da jini wani huci ya furzar ya dunqule hannunsa ya daki dayan dashi yace “wlh saina wargaza wannan yarinyar tunda abin ya zama  rashin mutunci ni zaaciwa mutumci akan wata banzar bafulatana mara galihu” 

Shidai Ado bai kulasa ba har sukaje gda fada suka wucce domin amsa Kiran Mai Martaba acan suka tarar da Kareem suka watsawa juna wani mugun kallo na kiyayi kanka, Mai Martaba ne  ya nunawa Muntaz guri ya titsiyesu akan su fada masa meye ya hadasu har suke neman illata junansu?” Kareem irin mutanen nan ne masu baqar zuciya idan ransa ya baci baya mgn shikuma Muntaz ko hauka yake bazaice don yayiwa Juhud tayin shaidana bane yasa aka illatashi, tsawa Mai Martaba ya daka musu yace “ku tashi ku bani guri tunda bazakuyi mgn ba sakarkaru kawai” miqewa sukayi kamar zasu bangaji juna suka fita a daidai inda zasu rabu kowa ya shiga bangarensa Muntaz ya dafa Kareem yace “mu hadu a filin qwallo sabon wasa zan take leda ko ta tsiya kota tsiya tsiya” 

Murmushi Kareem yayi sai yanzu zuciyarsa ta fara sauka yace “bazan hanaka mummunan tunaninka ba saidai inaso kasani ita zina yado takeyi idan kayi da yar wani zaayi da taka idan kayi da matar wani zaayi da taka kazalika idan kayi da qanwar wani zaayi da taka wannan kadai ya ishi me hankali nutsuwa Aminatuh ba kowa bace marainiya ce me rangwamen gata idan da Allah yaso ta lalace saiya barta tayita galantoyi a duniya har ta samu abokin lalacewarta so baiso hakan ba saiya jefata hannun Big Cele duk da gurbatar yanayinsa ya kawar dakai gareta domin riqe amanar Allah kullum abinda yake fada a kula da ita itadin tanada qarancin hangen nesa kaico abin tur wai ace a gdannan zata lalace……”

Dakatar dashi yayi da cewa “Dama kaje ka dauki speaker ka fara tafsir a masallacin fada qila da ka samu sadaka Dan m qauye kawai da ya kasa fahimtar rayuwa”  shigewa yayi part dinsa ya banko qofar yabar Kareem tsaye cikin tsananin mamakin wannan qazamar rayuwar ta yan’uwansa qwafa yayi ya shige dakinsa ya fada gado Yana juyi tabbas akwai aiki a gaban maza shikam da Abba zai barshi daya nemi auren Juhud cikin lkc qanqani kodon ya tseratar da ita daga sharrin Muntaz Amma yasan abune ma bame yuwuwa ba tunda bai gama karatunsa ba a burin irin na Mai Martaba ba mazaba yaransa mata na bayayi musu aure sai sun hada degree certificate maza kuwa sai sunyi Masters degree ya samawa kowa gwaggwaban aikin yi.

Advertisements

Lumshe idonsa yayi cikin yanayina tausayin kai da Kuma abar qaunar tasa shikam zaiyi qundunbalar furta mata koda bazaa Basu damar soyayya ba Allah ya jarabceshi da muguwar qaunarta baiji a ransa zai iya sakacin Bari ta kubce masa ba, da wannan tunanin yaji ana Kiran sallar magrib ya tashi ya fita domin zuwa masallaci ya jima a masallacin sannan ya tashi ya nufi cikin gdan a falo ya tarar dasu dukkansu suna kallon wani Indian series gabadaya hankalinsu ya bayu ga kallon da sukeyi duk cikinsu babu me motsin kirki.

Ya jima tsaye akansu bai gano Juhud ba can ya hangeta kwance a kujera da littafi a hannunta da alamun nazari takeyi, zuciya yaja ya nufeta inda Momy tabisa da kallo ya tsaya akanta ya sanya hannu ya zare littafin ta dago idanunta ta saukesu akansa ta kawar dakai, sake jan numfashi yayi ya zauna a gefenta yace “Ina Ya’isha da Amrah?” Miqewa tayi zaune ta duba bata gansu ba ta dawo da dubanta gareshi tace “bansan sanda suka fita ba” jinjina kai yayi yace “wato Addah kun qyale yarannan suna abinda sukeso babu me iya tsawatar musu basuda aiki saidai suyi wanka su fice su kwaso wannan su kwaso wancan samari saikace budurwar karya idan anyi mgn Momy tace farin jini ne don Allah wannan wacce rayuwa kuka zaba musu a matsayinsu na mata da zasu tafi gdan wasu?”

Dubansa Addah tayi tace “nikam bansan da wanne yare zan ganar dakai ka gane ba Abdulkareem wlh nafika jin ciwon wannan abin da yarannan sukeyi to baka isa kayi mgn bane kawai sun samu daurin gindi daga Mai Martaba abinda sukaga dama shi sukeyi kayi mgn suje su fadaka dashi yazo yayita fada shiyasa na tattara na zubansu ido kaima yanzu nemanka yakeyi sunje sunce masa kaine ka hana Aminatu zuwa chilling” 

Jinjina kai yayi ya bude littafin ya fara dubawa ya dubeta yace “ni ba turanci na karanta ba Amma zanyi bakin qoqarina wajen ganar dake abinda Allah yasa na fahimta ki tsara lkcnki  da safe zanke miki darasin addini da dare Kuma na boko hakan yayi miki?” Rufe fuskarta tayi tana dariyar jin dadi tace “wlh yayi Ya Kareem na gde Allah yabarmana kai” murmushi yayi yace “dole saiya kasheni tashi muje ki nunamin assignment dinku na qarshe da Muntaz nagani saina samu gabar dora miki”

Miqewa tayi tayi tsalle ta rungume Addah Abulle tace “idan na zama gwamna Ya Kareem zan fara kaiws makka” dariya sukayi Momy tace “baki rabo da shirme me sunan  yaya to Ina kika baro Baffa’am din naki ni kwana biyu ma banjinsa ko yanayin aikin ne?” Cokalo baki tayi tace “bayan ya daina sona ko waya ya Kira baya cewa abani” murmushi Mom tayi tace “ai kedin ce da hayyata kimbi kin damesa yaushe zai dawo naji yace saura wata biyu ya samu hutu ya dawo gida” tsallen murna ta kamayi tace “na kusa na kwanta a jikin Baffa’am dina me dadi Allah duk duniya banga Wanda yafi Baffa’am dina iya rarrashina ba sai Ya Kareem da yake kwatantawa……” 

Fuzgarta yayi yace “kin cika surutun banza Amina to shidin muharraminki ne da zakike kwanciya a jikinsa dan wauta idan kinyi a baya yanzu shima yasan kin wucce wannan shirmen dubeki fah mace daya da rabi haba wannan ai shirme ne” murguda masa baki tayi tace “eh dai dan baqin…..” Bugu yakai mata suka zuba a guje yana cewa sai kin fadamin waye dan baqin ciki yarinya itakuma tanayi masa gwalo da haka har bangaren Mai Martaba tana shiga ta shige bayan Mai Martaba tana dariya shima dariyar yayi ya janyota ta lafe a jikinsa yace “ya akayi ne Aminatu sarkin wasa kekam kamar ba yar soja ba” tana haki tace “ba Ya Kareem ne yakemin baqin cikin hawa cinyar Baffa’am dina ba don Mom tace saura wata biyu ya dawo” murmushi Mai Martaba yayi yace “aifa kaima ka taro March inakai Ina shiga tsakanin ya da ubanta wannan ai sai Allah” gwalo ta qarayi masa yace “to kagani fah Mai Martaba gwalo takemin” daquwa ya watsa mata yace “tayi din kaine babban kwabo ai” zama yayi shima suka fara karatun anan inda batayi daidai ba ya ranqwasheta kafin su gama duk ya tara mata gajiya ta narke tace ita bacci takeji dakansa ya rakata har qofar falon Muntaz na tsaye a harabar gdan fuska duk tayi dameji yayi qwafa ya shige dakinsa shikuma ya qarasa rakata ta shiga dakin nasu sukayi sallama.

Goma da rabi Amma babu kowa a dakin daga Amrah har Ya’isha kayanta ta cire ta daura towel ta fada wanka tayi wankanta cikin nutsuwa ta bude qofar zata fito taga duhu dakin tace “subhanallah An dauke wuta Bari na jira a kunna inj…..” Mgnr qin qarasa fitowa tayi qirjinta ya doka da qarfi jin motsi a dakin cikin rawar murya tace “Am…rah…. Ya’isha yaushe kuka daw…..” Nan ma kasa qarasawa tayi jin an rungumeta ta baya a razane tace “please Amrah nace miki banson wannan wasan ki daina Allah zan fadaki……” Wutar jikinta ce ta dauke jin an Sanya hannu an janye mata towel din jikinta an dora hannu saman qirjinta ta bude baki tasa ihu nandanan taji an saketa daidai lkcn da su Ya’isha suka banko qofar da sauri Amrah a lkcn ne Kuma wutar ta dawo tayi tsaye sangalgal babu komi a jikinta sai rawar baki data jiki takeyi da sauri Ya’isha ta matsa ta dauki hijjab ta zura mata suka dubeta sukace “yadai Baby meye ya faru?” Sai lkcn kuzarinta ya dawo ta fara dube² a dakin cikin firgici suma dube²n suka fara suna  tayata ta fara bankada labule itane har qarqashin gado Amma bataga kowa ba suka dubi juna Ya’isha tace “wai meye kike nema?”  

A wahalce tace “mutum” kallon juna sukayi sukace “mutum Kuma?” Jinjina kai tayi sai lkcn taji hawaye ya qwace mata tace “wanka na fito kawai naga wuta ta dauke Ina tunanin kune naji an rungumeni ta baya kafin na gama saita natsuwata aka yagemin towel shine inayin ihu naji kamar an fita da gudu Kuma sai gaku kun shigo don Allah ko kune kuka tsorata Ni?” 

Numfashi suka sauke a tare Amrah tace “wlh bamu bane muma da muka shigo ihunki ne yasamu takowa da gudu wannan gdan wani banzan gdane kowa Yana bangarensa sai a saceka ma baa sani ba”

Zama tayi cikin mugun tashin hankali suma suka zauna Amrah na binta da kallo tace “kece da shekiyar gardamarki da kin bimu Aida bakiyi gamo ba Kuma ko banza kyaga gari” numfashi ta sauke tace “to waiko inada Aljanu ne?” Dariya abin yabasu Ya’isha tace “to waye ya sani ni Amrah fito Mana da qwalam dinmu mu dan lasa Amma wlh yau Shafiq ya wahalar dani shege inaga magani yaje yasha ya gaji da miyar da nakeyi masa baya qosar dani” Amrah ce ta cafe da cewa “ke yau ni kinsan sabon kamu nayi wani alhajin birni infada miki quarter million yasamin a account yace next week zai dawo” tafawa sukayi itadai tana zaune tana kallonsu suka dauko ledojin da suka shigo dasu suka baje Ya’isha tace “sauko kici rabonki” girgiza kai tayi suka miqe sukace “aikuwa baki isaba yarinya dole kici” danna mata tsiren sukayi a baki ta lumshe idonta tana taunawa suka sata a gaba suna dariya saukowa tayi tasa hannu sukaci sukayi hani’an.

Bayan sun nutsa ne Ya’isha tace “nayiwa Saleem alqawarin gobe zan taho dake yace dubu dari zaibani tukuici idan Kuma kin amince yazo gda” dagowa tayi tace “aa nidai kar yazo banason zuwansa wancan zuwan da yayi Ya Kareem kamar zai cinyeni saboda masifa har cewa yayi zai fadawa Baffa’am” 

Tsaki sukaja a tare Amrah tace “ke muguwar bahuwa ce waike meye yasa bazaki waye ba koda yake dama ance sai mutum ya shekara arba’in yake wayewa badon hakaba kawai kita nuqu² da kayan dadi a jikinki saidai ki wanke kisa masa pant yayi gashi ki aske babu me mora” watsa mata harara tayi tace “ai cikar mutuncina kenan” wata dariya suka kwashe da ita sukace “sakarya ita ajiya yanzu haka mijin da kike adanawa ma yana kwance da wata zaa daura masa aure dake Kinga ta banza kikayi, tabe baki tayi tace “eh shida ubangijinsa nidai nafiso na hadu da nawa salin alin murmushi sukayi sukace ai saikitayi aikine be isheki ba duk gindin da baayi masa susa ya zama sorry rayuwar ga ta hutawa daga duniya sai Habuja aljanna tamai rabo” 

Da wannan tasa rigar baccinta ta juyansu baya tayi kwanciyarta tanajin kowacce na waya da saurayinta itakam ko a jikinta washegari da wuri ta tashi tayi wanka tayi sallah ta fito ilai kuwa ta iske malamin nata a falo yana duba wani littafin addini ta isa gabansa ta zauna suka gaisa cikin larabci kamar yanda ya sabar mata ya zuba idanunsa akanta yanajin saqon daya dade yanayi masa yawo a zucci na tasowa hadda take kawo masa shikuma hankalinsa nakanta Saida ta gama ta dago taga yanda ya kafeta da ido taja numfashi tare dakai hannunta idonsa ya qifta da sakin wata babbar ajiyar zuciya ya fara Bismillah sannan ya fara yimata qari bayan ya gama biya mata suka koma Hadith suka sake gangarawa tajweed haka ya rinqa karbar haddarta mataki mataki yana sake ware injin idonsa akanta gabadaya yau kallon da yakeyi mata yasa ta kasa sakewa dashi suna gamawa ta miqe ya riqo hannunta yace “na takura miki ko?” 

Qasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta yaja numfashi ya qara rage sautin muryarsa yace “wasu fararen kyawawan furanni ne suke sauka saman shararriyar hanyar da babu komai a samanta sai wasu korayen bishiyu da suka kewayeta gefenta Kuma ruwa ne yake kwaranya ta saman wani farin dutse a gefen dutsen wata yar bukka ce irin taku ta fulanin asali tsuntsaye nata shawagi dangin su Kanari Dawisu Jimina Alhuda’huda dadai sauransu”

Gabadaya ya dauke mata hankali da lbrn nasa jin yayi shiru ne yasata dagowa ilai kuwa idanunta ya fada cikin nasa kwarjini yayi mata irin zaman da yayi saman kilishin dole ne ka kiyayeshi yayi murmushi yace “ina tafe cikin nutsuwa Amma zuciyata matse take data isa inda wannan bukkar take wacce ta gefenta ruwa yake gudana take, Ina isa naja na tsaya saboda wata busar sarewa me kashe jijiyoyin jiki dake tashi ta cikin wannan bukka tare da wata zazzaqar murya tana rera waqe cikin harshen fullanci” sake tsagaitawa yayi ya hadiyi yawu can yaci gaba da cewa “bansan wace a ciki ba Amma zuciyata ta kwadaitu dason ganin mamallakiyar wannan murya me saukar da kasala Kuma me irin suffar matan aljanna, Aminah ba fadamin akayi ba a Raina naji koma wacece zata kasance haskenta kamar na hurul’ayn, Ina shiga kinsan wa idona ya ganemin?” Girgiza kai tayi cikin matsuwa dajin qarshen labarin ya daga hannunsa ya nunata da yatsa yace “kece Aminatuh….” Zaro ido tayi ta dafe qirji tace “ni Kuma Ya Kareem?” Matsowa yayi numfashinsu na gwamuwa yace “na’am Juhud kene na gani a dakin Kuma aka mallakamin ke matsayin matata ta sunnah tunda nake bantaba mafarkin da naji dama ban farka ba kamar wannan naso naga irin rayuwar da zamuyi da rayuwata a wannan kyakkyawan muhalli Aminatuh Wlh tallahi billahil lazi la’ilaha illahuwa Inasonki sonda bantaba yiwa kaina ba soyayya ta aure”……………

*Oum Hairan*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

JUHUD 4

Advertisement   *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE FOUR 4* *SUBSCRIBE* Advertisements…

JUHUD 1

Advertisement   *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* *(LOVE AND ROMANTIC STORY)* Advertisements *FP ONE* *Tunatarwa* Abubuwa kan faru da yawa…

JIHUD 8

Advertisement  *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE EIGHT 8* *SANARWA* Wannan littafin…