JUHUD 13

Advertisement

 *JH013 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*

 

*Regular group 300  VIP 600 via bank Account  0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank  or card for This number  09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*

*Ga yan Niger da suke son  wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*

Advertisements

Hadiye wani abu tayi me daci a fili tace “Allah yanaji yana gani” daga haka bata Kuma cewa komai ba ta miqe taje ta kwanta ba bacci takeyi ba tunanin sauyin yanayin Baffa’am din nata ne kawai yake addabarta itakam zataje ta sameshi ya fada mata laifinta don ta kiyaye yimasa irinsa a gaba.

Da wannan tunanin bacci ya dauketa da safe kafin kowa yazo Kareem yazo tanajinsa tayi likimo kamar me bacci ya qaraci mgnrsa ya fita bayan fitarsa kadan Rasheed din ya shigo daga sallama miskilin baice da kowa komai ba ya gama kalle kallenshi ya juya ya fice Ya’isha ta tabe baki tace “miskili kafi mahaukaci ban haushi” dagowa Amrah tayi tace “wato daga jiya zuwa yau gabadaya Big Cele baya cikin nutsuwa na fahimci ba iyakar Juhud yakejin haushi ba kowa ma fushi yakeyi dashi Kuma kinsan dalili?” Girgiza kai Ya’isha tayi tace “akan mgnr auren da Mai Martaba ya matsa masa yayi ne Kuma yace ya zaba masa Zulaihat kinsan tun da can ma Big Cele ya tsani yarinyar nan kamar masifa Ni bansan azal din data haushi ba da Zabin Mai Martaba ya qare akanta” 

Tunda suka fara mgnr qirjin Juhud yake dukan tara² aure Baffa’am dinta  zaiyi?” Maimakon taji tana farin ciki sai taji ta cika da tausayin kanta a hankali tasa hannu ta share hawayen daya gangaro mata ta yunqura ta tashi zaune cikin dakiya da nuna jarumta tace “a tunanina uba kamar Mai Martaba bazai taba yima dansa Zabin dabai dace dashi ba banga aibin Aunty Zulaihat ba da kuketa mgn akanta ni sainaga ma ta dace da mijin nata zasu dauki kala sosai Ina ganin muyi musu fatan Alkhairi yafi tsayawa wannan surutun da kukeyi Kuma ma Ni banji araina don wannan Baffa’am yake fushinsa ba kawai dai nice na bata masa”

Qwafa Amrah tayi ta fahimci duk yanda zakaso daka ganar da Juhud bata ganewa garama ks qyaleta a cikin duhun da take, Addah ce ta shigo musu da abin karyawa suka karya aka sallamesu suka tafi gda ranar bataje makaranta ba yini tayi a kwance da tsamin jiki bata da aiki sai murdo ruwan zahi a hitter ta gasa jikinta da yayi rudu² abinka da jar fata, abinda yake bata mamaki tun ranar da Rasheed yayi mata duksn mutuwar baya yarda su zauna guri daya da yaga ta fito yake tashi yabar gurin itakuma tsoro ya hanata ta tunkareshi ta fahimci neman abokin mutuwa yake shiko Kareem kullum qara fito mata da salon qaunarsa gareta yake baya boye soyayyarsa a gaban kowa sai gaban Rasheed shima don ya fahimci baya happy da lamarin ne.

Sun shiga jarabawa gadan² kawunansu sun dauki chargi matuqa musamman Juhud data Hana kanta sakewa da farko sunci gaba da zama suna lesson da Kareem tunda ta fahimci duk lkcn da suka zauna Baffa’am din nata zaita zagaye a gurin Yana qwafa yasa dole ta hqr ta janye ta koma yiwa kanta lesson da kanta tanashan wahala Amma saboda baqin nacinta taqi ta hqr hakanan take tursasa kanta, ganin hakan yasa Mai Martaba ya siyo mata tamfatsetsiyar waya Infinix hot 10 yabata tare dayo mata download na manhajoji na bincike da zasu taimakawa brain dinta taji dadi sosai ranar yini tayi da farin ciki a ranta tanajin itama ta faso gari su Ya’isha sa daina daga mata kai.

Advertisements

Da magrib Mom da tayi tafiya zuwa qasar Mali garin babanta ta dawo tana falo anata kwasar gaisuwa Juhud ta fito sanye da wata baqar doguwar riga me matuqar kyau da daukar idanu tana danna wayar da aketa Kira tun dazun ta qarasa gaban Mom tayi kissing hannunta tace “wlcm Mom munyi missing naki long time kin manta damu” murmushi Mom tayi tace “me sunan Yaya kina burgeni jarabawar nan da alamun bata baki kashi dadi tayi miki kinyi wani fresh dake kamar auduga sabon toho” da murnarta tace “alhmdllh Mom dama rashin lesson ne yake wahalar ni Kuma Mai Martaba ya sharemin hawaye ya siyamin sabuwar waya ya saukemin manhajoji ina samu Ina karatuns cikin kwanciyar hankali raba dare nakeyi Ina karatu sai biyun dare nake nafila na kwanta da asuba da Dora da karatu kafin kowa ya tashi ns tsinci abinda na tsinta.

Jinjina kai Mom tayi tace “lallai Mai Martaba yanaji daku sosai kuna sha’aninku muga wayar taki” miqa mata tayi ta fara dubawa tana dariya tace “aa kaga barrister Aminatu Haroon Moddibo wadannan zafafan hotuna haka” rufe idonta tayi tana dariyarta me daukar hankali Rasheed dake zaune ya miqe saboda hakanan idan ya cika kusanci da yarinyar yanzu yake rasa nutsuwarsa har ya taka step na farko ya juyo yace “Meenah” gabanta yabada wani rass ta dago da in….Ina tace “na…am Baffa’am” hadiye wani yawu yayi yace “ki kawomin wayar nan zan duba wani abu ki hadomin da abinci”

Babu wanda ya kawo komai tace “to Baffa’am” ta miqe ta shiga kitchen ta dauka abincin nasa ta dawo ta karbi wayar ta nufi saman a bude ta tarar da qofar hakan ya bata damar sakai tare da sallama yana tsaye yanata kaiwa da komowa shigowar tata yasashi tsayawa ya harde hannunsa a qirjinsa ya zubanta ido tayi saurin kawar da kanta saboda baqin kwarjininsa baya bata damar Sanya idanunta a cikin nasa.

Tsugunawa tayi ta aje abincin cikin ladabi ta dago ta miqa masa wayar ta miqe zata fita har ta murda handle din taji ya Kira sunanta da wata irin murya data sanya tsigar jikinta tashi taja ta tsaya ta kasa motsawa daga inda take qirjinta yana duksn Sha hurhudu, bai tsammaci juyowarta ba hakan yasashi takawa a hankali ya isa bayanta ya zubawa mazaunanta da faffadan qugunta idanu yanajin sautin bugun zuciyarsa da ya zame masa jiki game da ita yana qaruwa.

Hannu yasa ya murda key din qofar ya zare tare da hadawa da kyawawan dogayen yatsunta data qawata da baqin lalle me ratsin ja ya riqe a cikin nasa ya juyo da ita ya hadata da qofar yana qara rage girman idanunsa akanta a hankali yace.

“Haqiqa ko a tarihi bantabajin lbrn yar da take neman zabar duniya fiye da babanta ba Meenah abubuwa da dama suna bani mamaki na yanda sama da wata guda kikayi watsi Dani a gdannan ko arziqin gaisuwa bana samu daga gareki kawai saboda Ina qoqarin karenki mutumcinki ko?” Hawaye yafi komai arha a rayuwarta nandanan idanunta ya ciko da qwallah yasa hannu ya dago kanta yace “bance kiyimin kuka ba Meenah ai kin girma na gama aikina saura naki gashinan Kuma kin fara babu abinda na isa na sani game dake saidai najishi a gari kamar yanda barori da bayin gdannan zasuji babu abinda na isa kizo ki sanar dani matsalarki yanzun ta zama ba tawa ba kin fifita matsayin kowa saman nawa duk Ina kallonki”

Da sauri ta dago bakinta Yana rawa tace “wlh ba haka bane Baffa’am tsoronka nakeji banason na sake bata maka rai shiyasa kaga Ina gujewa kusantarka…..” Zubawa bakinta idanu yayi yana ayyana abubuwa da yawa kafin ya furzar da iska ya janye daga gareta daqyar ya koma ya zauna yace “rabona da cin abinci na qoshi tun Ina Benin shima din ba qoshi nakeyi ba Meenah kawai hqr nakeyi saboda tunaninki yafimin cin abincin dadi komai nawa kece nakasa samun sukuni sabodake hatta abokan aikina sunsan idan ba Meenah sukace min ba basa ganin walwalata meye yasa ke kika kasa sanya Rasheed aranki kika kasa bashi matsugunnin da bazai goge ba a ruhinki abin baqin cikin wai kewarki ta hanani sakewa na taho domin ganinki Ina murna yata ta girma kawai ki rasa da labarin da zaki tareni saina samarinki haba Meenah alqawari yace haka?”

Duk da babu abinda ta tsinta cikin kalamansa wadanda ta gane Basu taka Kara sun karya ba Amma taji jikinta yayi sanyi a haukanta ta yarda batayi masa adalcin ba tace “kayi hqr bazan qara ba” murmushi yayi dama abinda yakeso kenan a duniyarsa yanason abashi hqr koda kuwa shine me laifi, fara zubansa abincin tayi ta dauka ta miqa masa ya lumshe idonsa tare da budewa yace “hannuna ciwo yake ya kamata a fara ramawa kura aniyarta” yanda yayi mgnr ya bata dariya tayi murmushinta me kashe masa jiki ta miqe ta zauna a gefen gadon ta rinqa bashi abincin da hannunta yanaci Saida ya qoshi ya kawar dakai ta turo baki tace “kuma ai baka cinye albarkar ba” murmushi yayi ya miqe yace “inason kiyi albarka nabar miki ki hada da taki” babu yanda zatayi tasan qin cinye abincin ma sabuwar masifa ce hakanan ta rinqa turawa Saida ta cinye ta miqe ta wanko hannunta ta dawo tana hada kwanukan ta dago domin yimasa mgn taga ya bude wani hotonta da tayi da rigar bacci da dare Amrah tayi mata a swimming din gdan a jiqe take gashinta ya manne a jikinta riqar me santsi ta kwanta itama a jikinta tayi luf cinyoyinta a waje santala santala kamar na balarabiya babban abinda ya fadar mata da gaba babu ko bra a jikinta hatta shatin pant dinta ana iya gani idan kuwa ka tsayi yima hoton qurillah har kan nononta baqi zaka iya hangowa.

Gabadaya ta gama firgita duk jikinta ya dauki Bari tasan ta kade har ganyenta yau dagowa yayi ya sauke idanunsa akanta cikin sarqewar murya yace “waye yayi miki wannan hoton?” A gaggauce tace “Am….Amrah ce shekaran jiya a Swimming munje wankan dare…..” Mgnr ce ta maqale lkcn da taga ya miqe taja baya da sauri tunaninta dukanta zaiyi maimakon haka sai taga ya bude qofar ya nuna mata hanya yace “jeki Saida safe”……………..

     

*Oum Hairan*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

JUHUD 4

Advertisement   *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE FOUR 4* *SUBSCRIBE* Advertisements…

JUHUD 21

Advertisement  *JH0021 Bonus*   *Regular group 300  VIP 600 via bank Account  0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank  or…