JUHUD 14

Advertisement

 

*JH014 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*

 

*Regular group 300  VIP 600 via bank Account  0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank  or card for This number  09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*

*Ga yan Niger da suke son  wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*

_Barkanmu da sallah baki daya al’ummar musulmi fatan munyi sallah lfy ubangiji ya maimata Mana da Alkhairi🙏🏼_

Advertisements

Da sauri har tana neman faduwa ta fice daga dakin gabanta naci gaba da faduwa ta nufi qasan ta aje kayan abincin ta nufi dakinsu Ya’isha ce a dakin tana waya ta nemi guri ta zauna ta rafsa uban tagumi tsoronta ya nunku yanzu wanne irin hukunci Baffa’am din nata zashi dauka akanta shine damuwarta yanayinsa ya nuna baiji dadin ganin wannan gantafalfalin hoton ba gashi kusan irinsu sunfi hamsin a wayar tata, “dana sani na goge” ta furta batare da tasan kalmar ta fito ba Ya’isha ta aje wayar tace “meye Kuma ya faru?” Numfashi ta sauke tace “Baffa’am ne yace nakai mass abinci shine ya amshi wayana bansan meye yakaishi Gallery ba kawai sai gani nayi Yana kallon wannan dan iskan hoton da Amrah tayimin a Swimming shekaran jiya” dariya Ya’isha tayi tace “tabdi yau Big Cele an samu kayan dadi a bagas wlh in nine shi kwana zanyi Ina kallo harsai na samu nutsuwa tunda kin hana mutane su lolewa dadinki kinata nuqu² da kaya waike mumina” tsaki tayi ta miqe ta shige bathroom tayi wanka ta dawo tasa rigar baccinta ta kwanta saboda tanason ta tashi tayi karatu da dare tana kwanciya kuwa bacci ya dauketa.

Da safe ta riga kowa tashi tayi wanka tayi brush ta shirya dake alhamis ce azumi ta tashi dashi suka fita domin tafiya makarantar lkcn shima ya fito zai fita tun daga nesa ya zubanta ido yanda take tafiya a nutse yana karyar da zuciyarsa bata lura dashi ba Muntaz ne tagani yana training a harabar gdan ta dauke fuska hakanan takejin tsanar Muntaz don ta fahimci shima ba qaunarta yakeyi ba driver ya gama saita motarsa domin kaisu yaji an kirashi ya juya da ladabi cikin isarsa da izzarsa ta jini yace “kaje kayi abinda ke gabanka zan saukesu” jinjina kai Mal Wada yayi Kareem dake fitowa yace “Ya kabari kawai zan kaisu…..” Dagowa yayi ya sauke idanunsa masu firgita mazan gaske akansa bai samu arziqin Amsa ba yace.

“Ku shiga” Gabadaya Juhud a firgice take da yanayinsa suka bude baya suka shiga dukkansu yaqi tashin motar ya dora qafarsa saman sitiyarin ya kashe A.c ya kwantar dakansa saman kujerar ya lumshe idanunsa shi kadai yasan irin azabar da zuciyarsa takeyi masa game da yartasa yanajin tsoron yin abin kunya a tunaninsa kamarshi ya bude baki yace yanason Meenah matsayinsa da darajarsa ta fado bawai don bata isa ba aa kawai shi tsarinsa ne hakan babu macen data isa yace yanasonta a duniyarsa Yana ganin hakan matsayin raini da rashin aji.

Amrah ce tayi qarfin halin cewa “yaya takwas zamu fara paper fah Kuma yanzun bakwai da arba’in” batare daya dago ba ya furzar da iska yace “Meenah!” Yanda ya ambaci sunan ba itaba hatta su Ya’isha Saida sukaji yar a jikinsu suka dubeta ta dago a kasalce tace “na…na’am” ajiyar zuciya yayi yace “idansu qanne nane ke meyece a gurina?” Tambayar tazo mata a bazata, cikin rawar murya tace “ya” ya miqe ya zubawa fuskarta ido ta cikin mirrow yace “kuma kikeso na zama driven ki” bata fahimci abinda yake nufi ba Ya’isha tace “ki koma gaba don Allah mu samu yakaimu” sai yanzun ta fahimta ta bude motar ta fita ta bude gaban ta shiga ta rufe ya juyo ya kalleta ya dauke kai ya tada motar suka bar gidan”

Advertisements

Tunda suka taho babu me cewa qala har suka isa makarantar yayi parking suka bude zasu fita ya riqo hannunta ta zauna ta juyo suka fuskanci juna ta sunkuyar da kanta yace “ina kwana” da sauri ta rufe idonta kunyarsa ta lullubeta yayi murmushi yace “nawa zanke siyan gaisuwarki ne Meenah?” Dariya tayi ya kafeta da ido nandanan ta shiga hankalinta yace “idan kun tashi ku jirani kar wacce ta tafi” jinjina kai tayi ya bude mata ta fita yace “ki kulamin da kanki” sake jinjina masa kai tayi ta nufi cikin makarantar yabita da ido baija motar ba Saida ya daina ganinta sannan ya tafi.

Hudu saura suka fito daga exam din Ya’isha da Amrah suna Shirin kiran driver Kira ya shigo wayar Ya’isha ta daga da sallama jin muryar yayan nasu yasasu shiga taitayinsu yace kuzo Ina jiranku inda na saukeku, Basu so ba donsu nufinsu ba gda sukayi ba gdan Aunty Hamida zasu wucce ganin babu hali yasasu  nufar inda yayi parking suka bude suka shiga.

Hudu saura suka fito daga exam din Ya’isha da Amrah suna Shirin kiran driver Kira ya shigo wayar Ya’isha ta daga da sallama jin muryar yayan nasu yasasu shiga taitayinsu yace kuzo Ina jiranku inda na saukeku, Basu so ba donsu nufinsu ba gda sukayi ba gdan Aunty Hamida zasu wucce ganin babu hali yasasu  nufar inda yayi parking suka bude suka shiga,

Yana driving din yana satar kallonta inda ita Kuma gabadaya hankalinta yake akan titin har suka isa gdan babu me cewa qala suna zuwa ta bude motar ta riga kowa fita saboda kanta da yake ciwo “idan kun shiga kuce ta kawomin abinci” abinda ya fada kenan suka fita shima ya fito ta baya yabi ya shiga bangarensa ya zauna a falo kallo yakeyi Amma hankalinsa baya gane komai tsayin lkc yaji ana qwanqwasa qofar yabada izinin shigowa ta murda ta shigo da sallamarta ya Amsa mata idanunsa akanta wasu riga da skirt ne na atamfa sunyi mugun karbar jikinta ta ajiye abincin ta dago tace “barka da hutawa Baffa’am”

Lumshe idonsa yayi ya bude akanta yace “kamar wani abu na damunki ko?” Dagansa kai tayi ya gyara zamansa yace “meye shi?” Sunkuyar dakai tayi tace, kaina ke ciwo sosai” sake quranta ido yayi yace “kinsha magani?” Girgiza masa kai tayi ya miqe ya bude bedside drower ya dauko magani ya miqa mata ta karba ya tsiyaya mata ruwa a cup ya bata tasha ya sauke numfashi yace “ki gyaramin dakin nan” miqewa tayi ta fara gyara dakin ta wanko bathroom din ta fito Yana zaune inda tabarshi ta rusuna tace, na gama” jinjina kai yayi ya nuna mata abincin ta zuba masa ta miqa masa ya karba ya faraci kamar bason cin yakeyi ba itadai tana zaune so take yabata damar tafiya saboda shima kallonsa ya fara takurata sosai ta kasa sakewa maimakon hakama sai ce mata yayi “wacce paper kukayi yau?”

A gajarce tace “English” yaja gemunsa yace Kuma kina ganewa?” Daga masa kai tayi ya dauki wayarsa ya kunna wata waqa ya miqa mata yace “inason ki saurari waqar nan sosai ki fadamin meye kika fahimta game da ita?” Sauraron waqar takeyi cikin nutsuwa a hankali ta kwantar da kanta saman dayar kujerar tanajin kalaman baitocin da mawaqin yakewa masoyiyarsa suna ratsata musamman wani baiti da yake cewa “kece ta farko, kece ta qarshe kece kike samin nishadi! idan na waiga ke zana  hanga kada ki kasa cikan muradi!! sonki na kama bani nadama kyawun hawan doki da sirdi!!! in kika yarda dani bazani yarda ki wahala ba Rahma!!!” Akwai dalili zanyi misali sunnarki yau na cika buri! nayi su’ali nakwance qulli kedayace zan baiwa sirri!! Samun halali boye da fili,,, shine yakesa rai sururi inda na shaqu dake aso bazaiyi na makara ba!!!…….” 

Sakkowa yayi ya karbe wayar yasa hannu ya dago kanta idanunta suna lumshe yace “me kika fahimta?” Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tace “baitukan sun kashemin jiki Baffa’am Amma ban fahimci komai ba” iska ya furzar yace “bakisan soba ko Meenah?” Daga masa kai tayi ya zuba mata ido Yana lasar lips dinsa yace “nikuma Yana wahalar dani sosai Meenah son wata yarinya Yana neman tarwatsamin zuciya abin takaicin ni jarumi ne a filin daga na iya riqe kunamar bindaga da sakin ruwan harsashe Amma a gabanta matsoraci nake zama na kasa fada mata Meenah” 

Cikin yanayin tausayi ta dago tace “Allah sarki Baffa’am meye yasa bazaka fada mata ba to babu wani abin tsoro a lamarin soyayya Kuma ma fah zai iya yuwuwa itama tanasonka bazata iya fada maka bane” tunda ta fara mgnr yake kallon bakinta har tayi shiru yaja zuciya ya dafe kuncinsa yace “idan tanasona me yasa bazata fadamin ba ita tunda ni nakasa?” Murmushi tayi daya qara bayyanar da sihirtaccen kyaunta tace “kaima dai Baffa’am to kaima namiji da aka sanka da jarumta akan muradinsa ka kasa tararta ka fada mata sai ita da take mace da aka sani da yakana da kunya kaima kasan bame yuwuwa bane ai”

Sake sanya hankali yayi akanta yace “ta yaya zan gane idan tanasona Meenah ita yarinyar ta kasance tana matuqar ganin girmana fiye da kowa tana mutumtani batason bacin raina batason damuwata har tana kirana da babanta…….. Dagowa tayi da sauri yayi murmushi yace “haka nake nufi sunan babanta ne dani babana haka take kirana a gaban kowa Meenah wlh inason Aminatuh fiye da son da nakewa kaina banjin zan iya rayuwar aure da wata mace ba Aminatuh ba na Raina kaina ranar dana fahimci ba shaquwa ce tasa nake tsananin kishinta ba sone, nayi qoqarin mayar da lamarin mafarki Amma ya faskara har takai zuwa yanzun duk wani fitar numfashi nawa da tunaninta yake fita please ki bani shawara ya zanyi na fahimtar da Aminatuh inasonta?”………

*Oum Hairan*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

JUHUD 4

Advertisement   *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE FOUR 4* *SUBSCRIBE* Advertisements…

JUHUD 21

Advertisement  *JH0021 Bonus*   *Regular group 300  VIP 600 via bank Account  0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank  or…