JUHUD 2

Advertisement

 *JUHUD*

*(OUM HAIRAN)*

*(LOVE AND ROMANTIC STORY)*

Advertisements

*FP TWO*

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

Advertisements

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*TUNATARWA*

Tarihin ka zai zama cikakke ne daga randa ka mutu,  Don haka kar ka rudu da kyawawan ayyukan ka,  Mai rai baya amince wa gobensa,  Don haka ka guji dagawa ko alfahari, kai dai kayi fatan samun kyakkyawan qarshe🤏🏻

*CIGABA*

Tuni jikin Juhud ya dauki rawa qirjinta yana bugawa da qarfi hawaye ya fara sitirya a kuncinta tace “Aradun Allah Hammah manga bantaba bawa waniba do Allah kada kaci mutuncina kagani fah Lariya ta gdan Baffa Inde da wani yaci mutuncinta da akayi amranta korota akayi….” Murmushi yayi ya matsota yace “toke waye zashici mutuncin naki ai dama nine zani amreki kuma nine na bare abuna….” Wani qunci Juhud takeji duk lkcn da aka hadata da Hammah Manga wai a matsayin zabin da Baffa Bangel yayi mata bayan sunfi kowa sanin halinsa bashida kamun kai gashi har cikin ruhinta shi take zargi da kashe mata Baffanta…….

Wata qara ta saki daidai lkcn daya matseta bisa jikin garun dakin yayi saurin dora hannunsa a bakinta ya toshe yakai dayan hannunsa bisa qirjinta yana laluben tudun madaidaitan nonuwanta na fulanin asali da basu cika girma ba saida daukar ido da sanyawa zuciya qawar kasancewa dasu, wani radadin zafi taji lkcn daya cafki matsotsin kasancewar ita a rayuwarta bata taba sanya bra ba balle ta kareta daga harin kwaf daya. Ture hannunsa ta farayi shikuma yana qara luguiguice mata nono jikinta sai tsuma yakeyi tanajin azaba irin wacce kowacce budurwa keji karon farko da aka damqi nononta.

Hannu ya sake sawa ya matse mata baki ya kama yar yaloluwar rigar fulanin dake jikinta ya daga nonuwan suka fito gabaki daya yaja wata ajiyar zuciya tare da sunkuyawa zaikai bakinsa tsoronta ya wanzar mata da wani qarfi ta angijeshi ya fada saman karan gadon kafin ya tashi ta hankade shingen qofar ta kwasa da gudun masifa tana kuka tana ihu inda ya rufota a mugun guje shima kayan aikinsa a miqe yana tanqwarasu, shegen gudune da yarinyar kamar filfilwa ya kasa cimmata gashi harta ishe gari yaja ya tsaya yana qwafa lallai Juhud tazo da raini tunda kuwa taqi bashi hadin kai ta maslaha tabbas zai banqareta a gaban uwarta ya sokanta tsuliya tunda dama Itama innatun ai abinda takeyi kenan inta dauka tallen nono ta shiga maraya.

Ganin ya daina hangen qurarta yasashi komawa jikin wata bishiya yana mayar da numfashi yana saita kansa kafin nutsuwarsa ta dawo ya koma dajin

Itakuwa tana isa gda ta fada Bukkar da Innatu take ciki ta zube jikin Innatu tana wani irin kuka me tafasa zuciya, sosai hankalin uwar tata ya tashi cikin muryarta da bata fita tace “meye kuma ya faru Juhudah” cikin kuka ta fara bata lbr girgiza kai kawai Innatu takeyi zuciyarta na zafi daidai lkcn Baffa Buba ya shigo da qwaryar nono a hannunsa ganinsu a wannan halin yasashi cewa.

“Assha Assha! Indo mine kuma ya faru?” Cikin kuka tayi masa bayanin komai shima hankalinsa ya tashi yace “lallai yaron nan yakai dan iska wato Bangel bazai rinqa tsawatar masa ba iskancin da yakeyi a birni shine yazo dashi rugarmu zai bata mana tsatso idan so yakeyi yayi mgn mana ayi amren tunda kunkai dukkanku…..” Kallonsa tayi da sauri tace “aa Baffa Moddi harfa taba yakesha nikam Baffana yace koda wasa bashi yimin auren dole kahin Baffa ya shude yace ko Kado n kawo amramin shi yakayi gsky Baffa Moddibo banison Hammah Manga nikam”

Daquwa ya watsa mata yace “to dan qaniyarki kinhi so ya tareki a lungu inda bazaki iya qwatar kanki ba ya qwaquleki?” Shusshura qafa ta rinqayi tana kuka tana cewa “Aradun Allah baniso nikam banisonshi Baffa indai aka amramin shi to ya tabbata banida gata” 

Murmushi yayi ya miqar da ita yace “ayyah Aminatu ba hakane nuhina ba shikenan tunda bakiso zanje na samu Bangel da Ribado sujawa yaron nan kunne inba hakaba da hakuma zan hadashi akanki ga kindirmon nan nasa Jumai ta gyara maki gobe ki dauka kikai birni kwa samu na sabulun scollar

Murna ce ta cika Juhud ta karba tayi masa gdy ya fice ta koma ta zauna tace “Innatu gobe munada Kudi Yarima Biyu Baffa Moddi yabamu kinga dubu uku kenan har maganin ciwon jiki zan sawo naki a birni da tsire me quli” itadai Innatu kallonta kawai takeyi harta ida ta tashi zata fice ta kamota tace “zauna Aminatu” zama tayi jikinta a Sanyaye karo na farko kenan da Ta tabajin Innatu ta kirata gatsal.

Hannunta ta dauka ta dora saman kanta tace “inayi miki fatan nasara a rayuwarki ta gaba Aminatu a duk halin da zaki samu kanki a ciki ki riqe maraicinki tabbas Allah zai dafa miki inaji a jikina watarana zai wucce, duk abinda kikaga ya samu shamuwa watan bakwai ne yaja mata baffanki bai rabu da yan’uwansa lfy ba duk da yayi bakin qoqari akansu basu gani ba basa sonki basa qaunarki Aminatu dazu naji sanda suke tattaunawa ba domin Allah sukeson hadaki da dan’uwanki Manga aure ba saboda su cinye dukiyarki ne da tayi saura  nikam ba damuwata dukiyar ba damuwata tsiranki da mutuncinki idan kikayi aure a wagga ruga tarihi zaita maimaita kansa ubayenku basason halwar Haro bazasu tsaya miki ba a yayin da Uwayenku suke cewa ni mayyah ce…….”

Kukane ya kwacewa Innatu ta sake riqe hannun yar tata tace “Wallahi billahillazi la’ilaha illahuwa Aminatu niba mayya bace banida nasaba da maita amma uwayenku sun liqamin tun farkon kawoni wagga ruga taku saboda kawai su quntatani su quntata rayuwata kamar yanda suka quntata rayuwar Baffanki Haruna, na dade ina boyenki wani abu da kika dade kina tambayata yau naji a raina ya kamata na sanar miki koda zai kasance itane kalmata ta qarshe nasan zatayi miki amfani a gaba”

Idanunta nakan Innatu dake qoqarin tashi zanne ta matsa ta taimaka mata ta tashi suka kalli juna na tsayin lkc kafin daga bisani Innatu taja fasali tace “zan baki labarin asalin abinda ya wargatsa zumuncin gdanku abubuwa sun faru tun farkon kafuwar wannan Ruga taku wanda kamar yanda na sanar dake kakanku Moddibo Wand’u shine asalin wanda ya gadar da wannan boyayyiyar gabar da ba kowane yasan da itaba” fasali taja sannan ta lumshe idonta taci gaba da cewa.

*WAIWAYE*

Garin Chadi qasace babba me zaman kanta wadda take da shugaban qasa gomna da sarakunan gargajiya qasar tana dauke da lardi lardi mabambamta wanda fulani suke rayuwa a wadannan gurare, Asalin sunan Kakanku Moddibo Wandu ya samo asali ne daga sunan yankinsu tun asalinsu maihaifin moddibo Wandu ke jagorantar wannan yanke bayan shudewarsa ne aka nada Kakanku Ali A matsayin Moddibon wannan lardi sun zauna a wannan guri na shakaru masu tsayi inda Moddibo ke fita fatauci qasashe maqota kama daga Ghana Senigel Niger Nigeria a wannan yawo nasane Allah ya hadashi da wani gawurtacce bafataken me dukiya mai suna Doda wanda a haife ya kusa haifar kakanku ya kama Moddibo ya riqe hannu biyu idan yawon Fataucinsa yakaishi Senigal a gidansa yake sauka wata tafiya ne da Wandu zaiyi Baffa Doda ya kirashi suka kebe yake tambayarsa Matansa nawa? Cikin mamaki yace masa Matarsa daya da yara biyu Abubakar da suke kira Buba Sai Mamuda wanda suke kira Bangel a wannan lkcn gwaggo Lami bata haihi Ribadu ba.

Sunyi shiru na wani dan lkc kafin Baffa Doda ya dago ya dubi Wandu yace “ina iya baka Auren diyata Aminatu?” Cikin farin ciki Wandu ya karbi wannan aure batare da Aminatu ta sani ba wadda take ya ta biyu  gurin Baffa Doda kuma ta qarshe kasancewar Allah bai azurtashi da haihuwa da yawa ba yaransa Biyu Baffa Habu wanda ya kasance mahaifi a guri na.

A wannan rana akayi komai aka gama Batare da sanin Aminatu ba kwanaki uku tsakani Aka shirya masu kayansu da tarin shanayenta garke guda suka dunguma suka nufi Chad tafiya yau kwana anan tashi anan haka Mahaifina da yar’uwarsa da mijinta sukeyinta har Suka isa Chad. Sarkin yankin na wannan lkc amini ne ga Baffa Doda hakan yasa saida aka fara saukar amarya Aminatu a gidansa akayi biki sannan ta tare a rugarsu.

Lkcn da akayi wannan aure Aminatu bata wucce 14 ba hakan yasa sukayita wasan buya da Wandu har tsayin shekaru inda zama yaqi dadi tsakanin Aminatu da Gwaggo Lami, ita Gwaggo Lami batada shanu saita tatsi na mijinsu sannan takai kasuwa ta siyar ta samu na cefane ita kuma Aminatu yawan shanunta yasa bata fita tallen nono yarane da ita da suke dauka mata suke saidawa su kawo mata kudin.

Wannan abu yana ciwa Gwaggo Lami tuwo aqwarya gashi ta rasa yanda zatayi da Aminatu ga wata kulawa da Maddibo Wandu ke bawa Aminatu ta musamman kinsan abinka da lamarin maza idan suka auro yarinya wannan abu ya taru ya hadu ya haifarwa da Aminatu baqin a gabadaya rugar domin kowa Bayan Lami yakebi sai ya kasance shikuma Moddibo ya koma bayan Aminatu, kwatsam ana haka sai aminatu ta fara rashin lafiya ana shawara ce basir ne ashe cikine da Aminatu a haka dai ba tare da kowa ya ankara ba har cikin Aminatu ya isa haihuwa cikin dare ciwo ya turnuketa gashi Maddibo bayanan a lkcn ya tafi Nigeria sawo wasu shanaye.

Gwaggo Lami tanajin Aminatu tanata nishin ciwo amma taqi ko leqota saida Buba ya fito fitsari yajiyo ya nufi dakin da sauri ya isheta cikin mawuyacin hali a lkcn ta gama jigata kan da ya sawo kai amma yaqi qarasa fitowa aikuwa ya ruga da gudu yaje ya taso wata dattijuwa me suna Suwai suka taho tare kafin kace wannan dakin Aminatu ya cika da mutane amma ko qeyar Gwaggo Lami Cikin ikon Allah ana kiran Assalatu aka samu  Aka ciro yaron daqyar Amma Aminatu batasan wake akanta ba gashi jini yaqi tsayawa Suwai tayi iyakar qoqarinta zamani bana asibiti ba amma ina saida ubangiji yayi ikonsa Aminatu bata ko kalli fuskar danta ba Allah ya karbi rayuwarta………

Mutuwar Aminatu ta girgiza duk wani mutum dake rayuwa a wannan ruga hakana aka tashi Manzo ya tafi Senegal ya sanarwa da iyayenta suka taso suka taho tare, tabbas Baffa Dodah ya tausayawa Moddibo matuqa da irin halin dimuwar daya riskeshi a ciki daqyar da qarfin Addu’a ya dawo daidai amma duk da haka daya kalli Jaririn da Aminatu ta tafi tabar masa sai ya kama hawaye kwana sittin da haihuwar jaririn aka rada masa Suna Haruna  su Baffa Doda sunso tafiya da Haruna amma Moddibo yaqi yasa musu kuka yana roqonsu idan sun barshi zaike dauke masa kewar Aminatu.

Badon ransu naso ba suka tafi sukabar masa wannan jariri  hakanan Wannan yaro yaci gaba da rayuwa tun yana tsumman goyo cikin rashin kulawa da qyara indai kinga anyiwa Haro wanka to Dattijuwa Suwai ce ta daukeshi a qarshe ma dole Maddibo barmata shi yayi itake kula dashi da komansa duk da cewa kwana Saba’in da rasuwar Aminatu Gwaggo Lami ta haihu hakan baisa taji tausayin maraici ta bawa wannan yaro nono ba watsin da tayi da wannan jariri yasa shikuma Maddibo ya dauki qaunar duniya ya dora masa komai ya samo na Haro ne Buba dake yarone me hankali kuma ya dan fara tasawa bai damuwa da wannan fifikon hasali ma tausayin Haro yakeji inda Bangel ya taso da qiyayyar haro shima Rubado daya tashi qarami da wannan aqida da uwarsu ta koya musu ya tashi Haro ba mutunne me hayaniya ba wannan tasa ko fita sukayi kiwo sai su kamashi su zaneshi da zarar sunga Buba ya kauce haka zai dawo gda yanata kuka Suwai da Moddibo suyita rarrashinsa.

Rayuwa tayita tafiya a haka har suka tasa sukakai munzalin girma Al’adarmu ta fulani yaro yana kaiwa sha takwas akeyi masa aure suyita tsalle tsallensu da matarsa har hankali ya iso musu su rungumi junansu wannan ce ta faru da Buba da Bangel buba yanada Sha tara bangel yanada Sha bakwai akayi musu aure Buba aka aura masa Jumme shikuma Bangel Asubi Jumme mace ce me kawaici da hqr itakam Asubi irin mijinta ce sai ya kasance Haro ya tare a gdan Buba komansu tare sukeyi ko shawara buba zaiyi baya shawara da yan uwansa da suke ciki daya saidai Haro saboda nutsuwarsa tasa tunanin manya yakeyi.

Rayuwar ta farayi mawa Haro dadi ya saki jiki da Jumme sosai duk abinda ya samo daga Jumme sai Suwai lkcn da shekarunsu suka kai ne aka daura masu aure Lariya itace matar da aka bawa Rubado shikuma Haro aka aura masa ni nima kamar yanda aka dauko Aminatu daga Senegal haka nima aka daukoni aka kawoni jumme ce tayi murna da zuwana ita da Suwai sune suka karbenu hannu biyu surukarmu kam ko kallo ban isheta ba mijina kuma dan’uwana dan qanwar mahaifina Haro ya qaunace ya nunamin kulawa dayake dama ba qarama sosai aka kawoni banyi wannan bambadancin da amare sukeyi ba muka zauna lafiya da mijina a hakanne Jumme ta Haihu haihuwar farko ta haifi Abdullahi wanda kuke kira da Hammah Audi shekaru biyu kuma Asubi ta haifi Rubado basa jana nima bana shiga cikinsu daga asubi har lariya Jumme ce kawai muke mutunci matuqa ana haka na samu cikina na farko nasha wahala sosai da yakai haihuwa Na haifi namiji Umaru ya fara girma sosai yakai kusan shekara uku ya kama qyanda wannan qyanda bata barshi ba saida ta tafi dashi munji mutuwar yaron sosai, bayan rasuwarsa ne harin barayin shanu ya addabi Lardin Wandu babu shiri Moddibo ya debo halwarsa muka dungumo Niger daga niger muka tsallako Nigeria muka samu matsugunni a Wannan guri da ya zama sabuwar Wandunmu” 

Bamu jima da dawowa ba ciwon Ajali ya kama Moddibo ansha jinya sosai a lkcn da ajalinsa ya rigaya ne yasa aka kira masa yayansa yayi musu nasiha akan zumunci sannan ne ya ware wani kaso me yawa a cikin shanunsa yace wadannan na  gadon mahaifiyarsa ne Aminatu daya rinqa kula masa dasu sune sukayi yawa haka, nanfah Bangel da Rubado suka kalli juna sukayi qwafa suka tashi suka fice daga dakin bayan fitarsu ne yake sanar dashi cewa akwai wasu shanun da ya bayar aka tafi dasu kudu kiwo da Buba da Haro ne sukaci gaba da jinyar mahaifinsu har kwana ya qare ya tafi yabar baya da qura qurar da itane kema kikazo kika tadda  burbushinta.

Maitar da suke iqirari ta fara ne daga lkcn da nake haihuwa yarana suna mutuwa Asubi ce ta fara cewa wai ni nake cinye kayana saida na haifi yara takwas duk suna mutuwa sannan ne Allah ya bamu ke kika tsaya wai ashe duk yaran dana rinqa haifa maza suna mutuwa Ubayenku ne suka sanya hannu kawai saboda tunanin idan Haro ya mutu yanada da Namiji bazasu samu komai ba kedin ma sunso hallakaki Allah yaqi basu dama kika rayu da tsangwamarsu saboda kyawun da ubangiji yayi miki tun kina qanqanuwa dumurmur dake kamar kazar gidan gona saurin girmanki yafi komai bawa mutane mamaki Hasiya da Adama da Baraka duk sa’anninki ne amma duk kinfisu girma ko tallan nono muka tafi kafin akulasu an kulaki sau dari wannan tasa uwayensu sukejin hasaadar hakan  akwai wani furuci da Gwaggo Lami tayi kafin mutuwarta watarana mun dawo daga tallen Nono wani Alhajin birni yabaki kyautar Yar dolin wasa (yar tsana) kinzo gda kuka fara fada da yan uwanki akanta har kika fasawa Baraka baki, ina daki ta kamaki ta zaneki sannan tace indai su baraka jininta ne to saita lalataki sai kinyi abin kunya a rayuwarki ko tana raye ko bata raye,  badai kyaune yasa kowa yake nannan dake ba to kyawun saiya zame miki fitinar da zata addabi rayuwarki………….

*THIS BOOK IS NOT FREE… REGULAR GROUP 300  VIP 600 VIA BANK ACCOUNT  0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER  09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*

*Shares Please*

*Oum Hairan*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

JIHUD 7

Advertisement   *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE SEVEN 7* *SANARWA* Wannan…

JUHUD 6

Advertisement  *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE SIX 6* *SANARWA* Wannan littafin…

JUHUD 9

Advertisement   *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE NINE 9* *SANARWA* Wannan…