JUHUD 4

Advertisement

 

*JUHUD*

*(OUM HAIRAN)*

Advertisements

*( Pure love sex nd romantic)*

*FREE PAGE FOUR 4*

*SUBSCRIBE*

Advertisements

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*TUNATARWA*

Tabbas gafalalle shine wanda yake take laifinsa yake kallon na waninsa asara da tabewa ta tabbata garesa, kada ka damu da kuskuren wani domin bakasan boyayyen sirrin dake tsakaninsa da Allah ba, yi qoqarin ganin ka samu kusanci da mahaliccinka wannan shine cikar hankali🤏🏼

Dubanshi takeyi da yanayi na gushewar hankali tanason ta bude bakinta tayi magana amma yayi mata nauyi gabbanta gabaki daya rawa sukeyi na tashin hankali zuciyarta tayi matuqar quntata, daqyar ta iya hada kalmar Moddi sun kashemin Innatu me tayi musu kana ina ka bari suka kashemin Innatu na Moddi shin Ina gatana???” Tana mgnr ne cikin gushewar hayyaci inda shikuma yaketa qoqarin janyewa daga gareta har ya samu ya yakice ta ya juya yana tsiyayar da hawaye batare da ya iya bata amsa ba.

Saida ya bata tazara sosai tana tsaye kamar sassaqe sannan ya tsaya batare daya juyo ba yace “ki miqe hanyar nan tabbas nasan zasu biyoki koma suna kusa ki tafi Juhud kada su hallakaki burinsu ya cika banason burinsu ya cika nafiso su rinqaji a ransu cewa bayan Haro da Indo akwai wani abu da ya zame musu alaqaqai din da suka rasa samun damar cimma buri akansu tabbas taimakon Allah zai riskeki ta inda baki zata ba…..”  Daga haka bai kuma cewa komai ba ya tafi yabarta a kan kwanar ta durqushe a gurin ta rushe da wani marayan kuka na tunanin rashin madafa wanda bataji yana bawa zuciyarta sanyi ba saima qarin tafasa da takeyi.

Haka tanaji tana gani Moddi ya rinqa ratsa Kalgo da Sabara har ya bacewa ganinta haka ta wanzu a gurin tsayin lkc tana dama ace itama Allah ya aiko abinda zashi dauki rayuwarta ta huta, yanzun idan tabar guringa ina ta nufa…….

Tana tsaka da wannan tunanin ta rinqajin qarar yayi alamun tahowa akeyi gareta tayi saurin saita nutsuwarta duk tsoro irin nata yau zuciyarta ta soye mutuwa tafi buqata fiye da rayuwa, ji tayi an tsaya can ta fara hango duhun mutane har uku Muryar Baffa Ribado tajiyo yana cewa “yawwa gata cen….” Ai bata gama jin cewarsa ba ta zabura ta miqe daidai lkcn da suka zagayeta kowa da makami a hannunsa jikinta ya dauki tsuma ta dubi fuskokinsu zatayi mgn kawai Manga yakai mata sara ta goce ta fadi qasa warwas.

Ya sake daga Addar Hannunsa ya saita qirjinta ta rintse idonta tanajin saukar saran daya sanyata sakin wata razananniyar qara data cika dajin.

Ya sake daga Addar zai qara mata suka ga wani haske me dogon zango ya haskesu tuni suka saki makaman suka juya da sauri suka tsuke suka shige cikin duhun dare domin a lkcn magaruba ta jima da wuccewa.

Hasken yaci gaba da kusantota har ya iso daf da ita cambala qafarsa da yayi a cikin jini ne yasashi saurin haska qasa yaga jinine yake malala a qasa kamar ruwa, da sauri ya saita fitilarsa a wajen da yaga jinin yana gangarowa ya matsa da sauri ya zubawa yar fulanin ido tare da russunawa ya haske fuskarta da fitilarsa sosai yaji faduwar gaba daidai lkcn da ruwan saman ya kece da qarfin gaske, yace “Cornel Rasheed yar fillon da kasai nono a gurinta ne dazun”

Safa ya zaro cikin jakar dake goye a bayansa yasa a hannunsa ya daga  rigarta tare da zaro ido waje saran ya shiga sosai, jinjina kai yayi tare da zaro wata qatuwar waya a aljihunsa ya danna wasu numbers ring biyu aka daga bai jira cewar me mgnr ba yace “ku tsare dukkan qofofin dajin nan guda hudu akwai yan ta’adda a cikinsa yanzu na tsinci wata sabuwar gawar bafulatana da alamun sun kasheta ne sukaji motsina suka gudu….” Qit ya kashe wayar ya sanya hannu ya sake gyara mata rigarta ya miqe ya debo ganyen bishiya ya rufa mata ya tsallake ya tafi.

Ajiyar zuciyar da yaji ta saki ne yasashi tsayawa cik tare da juyowa ya haske fuskarta da wannan dalleliyar fitila tasa yaga ta bude idanunta ta sake mayarwa ta lumshe hakan ya tabbatar masa da sauran rayuwarta, raba daya biyu zuciyarsa keyi akan ya taimaka mata ko yayi tafiyarsa? 

Ji yayi zuciyarsa ta karye tabbas Dan’adam daraja ce dashi maybe idan ya taimaketa Allah ya qadarta tashinta idan kuma ya tafi yabarta wasu halittun na daji zasu iya zuwa su qarasa ta, da wannan tunanin ya tsugunna ya sanya hannunsa ya dagota cak ya sabata a kafadarsa ya miqe ya nufi Camp dinsu da ita, tafiya ce me tsayi sosai tsakanin gurin daya tsinci Juhud da camp dinsu haka yayita kurdawa cikin wannan duhuwa har ya fito sarari ya fara hango Camp din nasu kuratan sojojin da suke basu fita duty ba suna zazzaune cikin ruwan sunata hirarsu da iface²nsu.

Duk inda ya gifta kallonsa akeyi da fuskar mamaki idan ya wucce su kalli juna su gimtse saboda sanin tsagwaron rashin imaninsa yanzu ne zai sabawa mutum halitta ko yabaka gwale²n da sai kayi sati kana ruwan dumi, kai tsaye clinic din Camp din ya nufa ya wucce kowa ya shiga har dakin duba marasa lfyr ya kwantar da ita saman gado ya juya zai fita Likitan dake kan aiki yayi qundunbalar cewa “Tnks Sir” jinjina masa kai yayi yace “kayi aikinka akan wannan yarinyar banason a samu matsala ka bari ta mutu kaima saika mutu domin alamu sun nuna zamu samu wani haske game da yan ta’addan nan da suka damemu” sake sara masa yayi cikin ladabi ya sanya kai ya fice wani Soldier ya dafashi yace “A tsarin aikinmu babu dauko petiant mu kawoshi garemu domin magani Cornel Rasheed meye yasa kayi hakan shin baka tunanin matsala zata iya afkuwa?”

Fuskarnan kamar hadari yace “nayi ne don inada ra’ayin hakan kuma hakan nakeson yi saboda haka ayi hakan kawai” yana fadin haka ya juya ya sake nufar dajin domin yin abinda ya fitar dashi dazun, bashi ya dawo Camp din ba sai 11:30pm sabe da wata qatuwar gada a kafadarsa yana zuwa ya cillawa kuratan sojojin da ido yabasu umarni suka mike suka fara gyarata tantinsa ya nufa ya cire kayansa gabadaya ya fito dagashi sai gajeran wando ya nufi wani zagayayyen guri ya watso ruwa ya dawo ya shafa mai ya fesa turare yasa wasu kayan shan iska ya kwanta a dan gadonsa ya lumshe idonsa zuciyarsa na kai kawo tsakanin Joss Da Katsina Birnin Daura ya kwana hudu rabonsa da mahaifarsa yanason zuwa amma aiki ya riqeshi.

Taba qofar akayi alamun ana neman sahalewar shiga garesa yayi juyi tare da cewa “a shigo” shigowa likitan yayi ya qame a gabansa yace “Sir wannan Petiant din aikinta yafi qarfinmu saidai akaita Barreck ayi treat nata saboda ciwon nata babbane akwai abubuwan da bamu dasu anan da dole sai dasu zaayi amfani”

Baice masa komi ba ya dauki wayarsa ya kira wata number ba bata lkc aka daga yace “ya nemi izinin gaggawa na komawa barreck cikin yan mintuna aka basa ya miqe suka fita da likitan yana tafe yayiwa drivernsu mgn ya Zama ready ya shiga da kansa ya zare ledar jinin da suka sanya mata ya sabeta ya fita yasa a mota suka dauki hanyar cikin gari barrack dinsu nesa take da gari sosai hakan yasa basu isa ba sai daya saura suna zuwa kai tsaye asibitin ya kaita likitoci sukayi mata cah aka fara jorner mata na’urori saida aka gama saita komi sannan ya juya a gajiye ya nufi gdansa, budewa yayi ya shiga ya bude qofar Falon ya tsaya yana qarewa falon kallo yanajan qwafa.

Wato Christiana bata gyara masa gidan ba tunda ya tafi, iska ya furzar me zafi ya bude dakinsa ya shiga shima kaca² Tsaki yayi ya cire kayansa ya dauki towel ya daura sai yanzu asalin siffarsa ta bayyana dogone  kakkaura kirar mazan faman gaske wankan tarwada shiba fari ba shi ba baqi ba, yana da fadin qirjin sosai me cikakkun nonuwa da suke rangaji kamar na mace gargasa ta kewayesu abin gwanin sha’awa gabadaya jikinsa lullube yake da suma fuskarsa me qarancin fara’a faffada me madaidaicin tsayi hancinsa dogone amma ba kamar biro ba lol.

Yayi daidai da dan qaramin bakinsa me dauke da siririyar wushirya a tsakiyar shiryayyun haqoransa sajensa baqi sidik daya hade da gajeran gemunsa sumarsa baqa kwantacciya ta fulanin asali ta qara armasa sirrin boyayyen kuma bayyanannen kyansa.

Cornel Rasheed Mahfuz kenan haifaffen garin Port-Harcourt da asalin Jahar Katsina cikin Daura L.g.a Wanda aikin soldiar yakai General Mahfuz wato mahaifinsa da mahaifiyarsa Salma Part-Harcourt ta haifesu su shidda acan, Captain Salman shine Babba Sai Dr Arman da yake bi masa sai Hamida Sannan Raseed sai Muntaz sannan auta Ya’isha, 

Zainab matar babansu ce wacce suke kira Adda Abulle tana da yara hudu Kareem Shine Babba baikai Rasheed ba ya girmin Muntaz sai Fadila da Urwat sannan Auta Amrah, shekaru sunata turawa har zuwa lkcn ritayar Gen Mahfuz ritayar tasa tazo daidai da lkcn da Wansa da yake mulkar masarautar Daura ya rasu hakan tasa aka nadashi matsayin sarkin daura, dole ya dungumo ya dawo gida domin gudanar da mulkinsa.

Babbar matsala da take damun wannan Fam shine rashin qwaba asalin wata rayuwa akeyi da ake cewa uwa ba kwaba uba ba harara duk abinda da yaran sukaga dama shi sukeyi Qa’idar Gen Mahfuz ce ko hararar dansa mace tayi saita fuskanci fushinsa to itama Momy Salma kusan tafiyarsu daya Adda Abulle ce kawai me iya tsawatar to itan bata samu goyan baya daga gurin mai gidan da kuma abokiyar zamanta ba hakan yasa ta dauki mataki mafi rauni shine qin abun a zuciyarta.

Gen Mahfuz mutum ne na mutane me taimakon talakawansa babbar matsalarsa da kowa ya sani itace ta gidansa ya kasance kowa abinda yakeso yakeyi babu me cewa wani gyara domin kowa abinda zuciyarsa ta saqa masa yake aikatawa daga mazan har matan da kayi musu mgn zasuce maka Life is Freedom…….

*THIS BOOK IS NOT FREE… REGULAR GROUP 300  VIP 600 VIA BANK ACCOUNT  0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER  09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*

*Shares Please*

*Oum Hairan*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

JUHUD 6

Advertisement  *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE SIX 6* *SANARWA* Wannan littafin…

JUHUD 2

Advertisement  *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* *(LOVE AND ROMANTIC STORY)* Advertisements *FP TWO* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ Advertisements https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ…

JUHUD 3

Advertisement  *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FP THREE* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_…

JUHUD 9

Advertisement   *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* Advertisements *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE NINE 9* *SANARWA* Wannan…

JUHUD 21

Advertisement  *JH0021 Bonus*   *Regular group 300  VIP 600 via bank Account  0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank  or…