Advertisement
_Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna _
https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg
_This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing you my latest films, and musical videos at lit more_
_Wannan duk daga bakin shahararriyar jarumar nan ce.. NAFISA👆🏾_
Advertisements
_Shin kunsan sabuwar fucacciyar jarumar nan ta film ta bude YouTube site d’inta? *nafisakabdullahi…* Tana kan manhajar YouTube. Sabon shafin tane dake kan YouTube inda zata dinga kawo muku sabbin fina finai da bidiyo da sauran abubuwa na amfani…_
_Ina masoya makaranta books na zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora.._
_Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye._
_DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba…_
_Akwai Facebook site dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi_
_Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: _
Advertisements
_08071172003_
_Please show some love… Follow, Subscribe, View, Click on bell.. Stay tuned🥰🧚🏻♂️_.
_B2_
_PG:26_
*SAS*
Ya kikkira wayarta bata dauka, Hankalin sa ya mugun tashi jin bata kira shi back ba. Ko lapia? Ya shiga tambayar kansa, Ganin bashida amsa ya mike ya haye sama. Falaki ya kira awaya ya gaya masa ya samo mota wadda zasuyi ‘badda kama. Drawer dinsa yaje ya bude ya dakko wata arniyar shadda data sha aiki, Ya taje kansa bayan ya faffesawa jikin sa turaruka, Hular ya rike a hannu ya sauka kasa. Ta kofar baya yabi ya fice. A mota ya shiga nazarin wazai kira ya tambaya me ake kaiwa gidan surukai? Can ya kira Addah maryama ya tambayeta, Ta gaggaya masa. Hade datura masa ta message, A wani mart (shopping mall)suka tsaya, Ya bawa falaki wayar da Addah maryama ta turo list.
Gaba d’aya Salman hankalin sa a tashe yake. Minti kadan ya duba dayar wayar hannun sa ko zata kira shi back.
“Ya rabbi…”
Tunawa yai da number kawun ta, Nan danan kuwa ya kira shi ya sheda masa Khadija nanan kota taho? Hankalin sa ya kwanta lokacin da Kawu daddy ya sanar masa da lapiar ta kalau yanzu za’a kawo ta,
“No…! Ai ina hanya ma.. Dama zanzo na gayshe da ku. To kuma da bata dawo dinba senaga gwara nazo kawai yau…. din.”
Kit ya katse kiran bayan sunyi sallama, Ya sauke wata nannauyar ajiyar zucia jin zawjatin sa na cikin koshin lapia. Falaki ya jasu sai gidan Dr. Isma’el, Har cikin gidan suka shiga da motar. Lokacin Kawu daddy na tare da Mas’oud. Yana bashi ha’kurin ya riga da ya bada auren shukrah.
Takalman sa ya fara zurowa masu matuk’ar tsada da haduwa, Sai kafar kuma ta biyo baya fara sal da ita, Yadin jikin sa hular sa, Kai harda agogon sa, Su suka sanya masoud sakin baki yana kallon me futowa daga motar. Dr. Ismael ya mik’awa masoud hannu amma ina masoud ya shagala a kallon Salman, Shi kuma Dr. ismael bayaso ya tafi wajen Salman basuyi sallama da masoud ba yaji haushi yaga ko ya wulakanta shi.
Cikin takama, K’asaita, Kwarjini. Irin ta matashin sarki mai jini a jika, Haka Salman ya shiga takawa daga inda yake zuwa wajen su Dr. Isma’el. Kamshin turaren jikin sa gaba d’aya ya gauraye ilahirin cikin gidan da wajen sa,
“Ranka ya dade sannu da zuwa…”
Kawu daddy ya zube yana dibar gaisuwa wajen SAS, sarauta sarauta ce koda ta kauyece ballantana sarkin gari baki d’aya. Masoud bai san kowanene ba, SAS ya bashi hannu suka gaysa, Har Masoud ya fuce bai dena juyawa yana kallon SAS ba. Duk gayun sa yau yaga karshen wanka da kwalliyar ado.
Sosai SAS ya sake gaysawa da Dr. ismael domin jinsa yake tamkar mahaifin Khadija. A parlorn sa suka zauna , Shi kuma Dr. isma’el ya shiga cikin babban parlorn ya kirawo su Mami.
Ina zaune na dan fara bacci Kawu daddy ya shiga dokawa sunana kira. Da salati na mike ina gyara mayafi na, Sai da nashiga bandakin kasa na wanko baki na da mouth wash sannan naje parlorn gaba d’aya suna can wajen SAS. Tunda na taho ya kafeni da idanu, kunya duk ta isheni, Har na k’araso na zauna daga can gefe ina jan mayafi na, Muka hada idanu na murgud’a masa baki,
“Barka da dare…”
Nace dashi ina dan rissinawa kadan.
“Zawjatii… Kinci abinci?”
Ta gefen idanu na na wulkita shi, Na hango yadda su Mami suka zuba mana ido shi ko kunyar su bai ji ba. Nayi biris memakon yai shiru bai gane ba ya sake tambayata,
“Naci…”
Na amsa ina masa sign da ido, Shiru yai shi dama ba gwanin magana bane, Sai yanzu na sake tabbatarwa baya iya sakin jiki da mutane ganin yadda idanun sa gaba d’aya akai na suke, Da alamun ni kadai yake kalla yaji sassauci, Lalle yanada wahalar sabo. Sai Kawu daddy ne ya shiga dan kawo magana shi da Mami, Lokaci zuwa lokaci Salman kan tanka sau d’aya sau biyu. Tashi yayi nima na mike, Su Kawu daddy suka shiga godiar abubuwan da ya kawo musu.
“Lalle dije kinyi sa’a.. Kai! Bantab’a kare masa kallo ba sai yau, Kinsan kullum da rawani ake nuno shi ko a tv. Ashe haka yake dakyau.?”
Cewar ya hameeda data matso cikin kunnena tana gayamun. Murmushi nai kawai a zucia ta nace ‘TubarkAllah..’
Har mota suka rakamu, Falaki yaja mu. Muna baya ni dashi, Ya rikeni tamau kamar za’a kwace. Futinar sa ta cika yawa, Inajin sa yana neman magana a cikin jiki na na kyale shi,
“Ya zazzabin? Ya sauka..?”
D’aga kai nayi Ina juyar dashi gefe,
“Da sau’ki….”
“Ai na yiwa Doctor Fiddau magana zata zo ta duba ki… Zuwa da safe..Ko muje asibiti yanzu? Uhm”
Karkada masa kai nayi alamun a’ah
“Nasha magani ai. Malaria ne kawai sai gajiya.”
Kwantar da kai na yayi akan kafad’ar sa yana shafa kwantaccen gashin kai na,
“Sannu my love… Muje gida sai ki kwanta ki huta kinji.?”
“Uhm..”
*MASARAUTAR BASANNABAS*
Ta zauren baya muka shiga wajen tsohon gareji da ake ajiye dokuna. Muka shiga sashen sa ta baya. Muna zuwa kofa ya dauke ni cak da hannun sa, Ya rufe kofar da kafar sa da baya. Yana iya saboda rashin karfin jiki na na tallabo wuyan sa nima. Harkan gadon sa ya ajiye ni yana gyara mayafin daya rufemin fuska. Ya rankwafo Kai na yana gyaramun kwanciya,
“Sannu Zawjatii…”
“Bacci nake ji…”
“Kici abinci..”
“Naci abinci…”
“Tohm ko zaki dan watsa ruwa seki kwanta?”
Mikewa nai ina shafa ciki na,
“Da dai akwai Indomie da naci, Me tafarnuwa.”
Salman ya zaro idanu yana kallo na.
“Munada tafarnuwa?”
“Akwai a kitchen. Zan dafa”
“Noo! Bacci kike ji. Bara nasa Ammi ..”
“Wa? Saboda me zan iya..”
Mikewa nai na sauka kasan yana biye dani a baya.
“Kikace kinci abinci.”
“Tun dazu ne shysa.”
Kad’a Kai yayi, A tare muka shiga ciki na shjga hada komai dazan sawa indomien.
“Zaka ci..?”
“Zan ci…”
Nai saurin hada komai na dafa ta dik muna tsaye, Ya zura hannayen sa ta cikina ya saqale wuyan sa akan nawa. A haka na dafa na juye a plate muka koma sama, A kan dan karamin center carpet muka zauna dirshan, ni kam saboda tsabar zalama ji nake kamar na kafa kai a cikin plate d’in naji indomie ‘din cikin ciki na. Salman ya dauki fork ya debo zai bani, naga gaskiya bazan Iya yin soyayyar cin abinci ba 😂💔na sanya hannu ba tare da na kalle shi ba.
Kafin yaci daya nayi loma uku saboda cinta kawai nake yi hankali kwance. Salman ya tsaya kawai yana kallo na ko ci kasa yi Ya yi saboda tsabar mamakin yadda yaga ina cin abincin. Ko lura banyi ba da cewar ya dena ci, Sai da na cinye na sude plate d’in tare da shan ruwa nayi gyatsa saboda bana son duk wani drinks idan bana kankana ba.
“My love ko a sake dafawa ne?” Ya yi maganar cike da kulawa.
Girgiza kai nayi alamar na koshi, janyo tray d’in da muka doro plate ya kamo hannu na tare da wanke min shi tas. Saboda bazan iya mik’ewa wajen wanke hannu ba, Gado na nufa saboda ciki ya dauka kuma baccin ya fara cin karfi na, kwanciya nayi ba tare da na koma yin wata kwakkwarar magana ba, shima ya kashe fitila yasa ta bacci tare da bin bayana ya rungume ni muryarsa a sarke yake cewa.
“I miss you so much my baby. Please ki dena yin nisa a kusa dani, wallahi bakiji yadda nake cutuwa ba.”
Kasa magana nayi saboda yadda yake min da jiki na, gashi Ina jin wani irin abu yana taso min tun daga ciki na zuwa wuya. Kissing d’in da Salman yake min a fatar bayana yasa abin gabaki daya ya taso min, ashe amai ne, Hankalin Salman ya yi matukar tashi ya zauna da sauri tare da rungume ni ina kwacewa saboda na fara galabaita.
“Subahanallahi sannu my love, sannu.”
Ya dinga min sannu kafin ya sakko daga kan gadon ya kunna haske, a sannan ne hankalinsa ya kuma tashi ganin gabaki daya indomie d’in da naci ta dawo, dakin duk ya baci. Beyi wata wata ba ya dauki waya ya lalibo numbern Dr Fiddau, daman ba wani dare ne ya tsala ba dan lokacin k’arfe goma Sha daya da arba’in na dare. Bugu daya ta dauka tana gaida shi yace tazo yana son ganin ta urgent.
Ni kuma ya koma kusa dani lokacin aman ya tsaya amman duk jikina ya mutu ta yadda ko hannu bana Iya dagawa. Ya cire min kayan jikina tare da dakko min wasu marasa nauyi a cikin trolley dina da yake tana sashen nashi, akan kujera ya kwantar dani yaje ya dauke bedsheet din ya kai cikin washing machine, yana kokarin gyara gurin aman sai yaji kiran waya yana dubawa yaga Dr Fiddau ce.
“Yauwa shigo Dr.”
BA bata lokaci ta shiga bayan ta nuwa masu tsaron kofa Id card d’in ta duk da cewar sun san ko wacece ita. Kwance taga Dije ga kuma amai hakan ya tabbatar mata da cewa akwai wani bayani. Allah ya taimaka cikin akwatin da tazo dashi akwai pt tace tana son tayo fitsari. Daman tana ji dan haka babu musu tace Salman yazo ya kai ta toilet. A bakin kofar ya tsaya saboda Dr Fiddau duk da cewar tana can gurin gyaran aman, Dije tayo fitsarin a cikin wata yar farar roba Salman ya karba ya mikawa Dr. Tana saka pt d’in babu bata lokaci ya nuna mata positive.
Fuskarta cike da murmushin kamar ita ce za’a yiwa albishir d’in ta kalli Salman tana dariya sosai tace.
“Allah ya taimake ka ya kara maka lafiya da nisan kwana. Ranka ya dade! Gimbiya na dauke da juna biyu congratulations…..”
Da sauri Salman ya juyo yana kallo na ido waje baki bude, ni kuma saboda mamaki ban san lokacin da naji karfi a jiki na ba, nabi cikin da yake a shafe da kallo. Salman kuwa kusa dani ya dawo tare da kamo hannaye na ya jani jikinsa ya rungume, hawaye na zirarowa daga cikin kyawawan idanun sa….
***Hannu na ya kama ya kaini wani dakin ya kwantar dani, Na lumshe ido bacci ya dauke ni shi kuma ya shiga bandaki, alwala yayo yazo ya yi raka’a biyu tunda ya kafa goshinsa be dago ba tsawon lokaci yana ta faman yiwa Allah godiya da wannan ni’imar da ya bashi. Yana saka ran karbar duk abinda Allah ya bashi da hannu biyu-biyu mace ko namiji duk wanda yazo yana maraba.
Fita yayi zuwa daya dakin gabaki daya Dr Fiddau ta gyara sai kamshi ke tashi, ya yi alkawarin da safe zai bata tukwici na musamman, dana albishir da kuma na gyaran da tayi wanda bata nuna kyankyami ba. Kayan bacci sa ya saka daga nan ya nufi inda Dije ke ta faman bacci hankali kwance. Salman ya zauna yana kare mata kallo, ji yake kamar ya maida ita cikin sa dan ta riga ta zame masa farin ciki marar yankewa.
Bakinsa ya dora akan nata ya tsotsa, tayi juyi wato tai rigingine ya sake gyara zama yana bin kyakkyawar fuskarta da tai fayau saboda jikin duk ya mutu. Cikin zuciyarsa banda sanya mata albarka babu abinda yake yi, ‘Ina sonki Deejah na, Allah ne ya hada mu a lokacin da banyi tsammani ba, ubangiji ya faranta miki my love kamar yadda kika sani farin ciki, ya jikan iyayenki, yasa suna gidan aljannatul firdausi.
Kyakkyawar runguma ya bata yana lumshe ido, so yake bacci yazo amman farin ciki ya hana shi. Kansa ya mayar kan kirjina ta ya yi pillow dashi, yadda yaji numfashinta yana sauka tare da bugun zuciyarta sune suka sanya shi jin baccin, tunawa ya yi ba ita kadai bace yanzu gashi ya dora mata wani nauyin, dan haka ya koma ya kwanta tare da jayota ta dawo jikinsa, da kyar ya samu a ranar ya runtsa.
Da asuba ma ya riga ta tashi, amman dan karya tashe ta sai shima yaki ya tashi. Ita Kuma da ta farka ko bude ido ba tayi ba, jinta a jikinsa yasa ta cewa.
“Zan Sha tea.”
Salman ya shafi kaina yana magana cike da tausayawa.
“Taho na kai ki kiyi brush da alwala tukunna.”
Na katse shi da sauri dan ni kadai nasan abinda nake ji.
“Dan Allah dan annabi ka fara bani tea d’in na sha, ko tashi bazan Iya ba yunwa nake ji wallahi.”
Jin hawaye a jikinsa ne yasa shi saurin dagoni ya kwantar dani shi kuma ya nufi kitchen. Kettle ya dakko ya zuba kayan dafa shayin ya dara akan electric, be baro gurin ba sai da tea d’in ya yi sannan ya zuba a tea cup yasa madara da milo sai sugar kadan ya taho min da cake. Ina jiyo takunsa na tashi tun kafin ya karasa shigowa na mika masa hannu, be bani ba ya samu guri kusa da ni ya zauna da nufin bani a baki na girgiza kai tare da karba a hannuna Ina jujjuya cup d’in tamkar ban san shi ba. Cikin turo baki nayi kurba daya Ina cewa.
“Yanzu dan wannan cup din Ina zai je min? Kawai dai in yi manage idan na idar da sallah sai na kara.”
Salman ya bude baki kawai yana kallonta, bama tasan yana yi ba saboda yunwar da ke sakularta. Bata sauke cup din ba sai da ta shanye shi tas ko ta kan cake d’in ba tayi ba. Yasa hannu ya karbi cup d’in yana leka ciki yaga babu.
“Bari nayi sallah.”
Na fada Ina kokarin sakkowa daga kan gadon. Shine ya taimaka min duk da cewa naji kwarin jikina amman Sai da ya kaini toilet sannan ya fito ya koma dayan shima ya yi alwalar ya dawo rike da doguwar riga a cikin sabbabin da na siyo a Lagos ya saka min yaja mu limanci muka yi sallah. Waigowa ya yi muka hada ido nayi saurin kawar da kai dan na tuna abinda Dr tace masa jiya wato Ina da juna biyu, ya matso kusa dani tare da dora hannunsa saman cikin yana fadada murmushinsa yace.
“Good morning little princess/little prince. Papa yana gaisuwa mai ban girma, Allah ya albarkaci kome nene a cikin nan.”
Hannu nasa tare da ture nashi daga kan ciki na ina yatsina fuska nace.
“Haka na ce maka haihuwa zanyi?”
“Tunda nayi kokarin aiki aka bani tukwici. A kawo shayin?”
Sai da na harare shi sannan na daga kai alamar eh a kawo min sannan ya ja min hanci tare da sumbatar goshi na ya mike yana cewa.
“I love you Dijangala na.”
Cup din da nasha dazu ya dauka har ya kusan fita nayi saurin cewa.
“Nifa bana son wannan cup d’in, babba zaka zuba min ko na rubber ne.”
“Yadda kika ce haka za ai my Gimbiya.”
Juyawa nayi ban ce komai ba, sai bathroom da na shiga tare da sakarwa kaina ruwa, banyi aune ba naji mutum ya bude kofar ya shigo, nayi saurin juya masa baya ganin shima da shirinsa na wankan ya shigo a rai na nace ‘Salman akwai fiti na kala-kala’. Rungume ni ya yi ta bayan yana goga ruwan a fatar jikina, na rintsa idanuwa kamar yana gani na ya fara magana dai-dai kunne na.
“Wai da wannan gajan na jiya shine Mas’oud d’in da ake ta min fitina akan shi?”
Nayi masa banza dan ba zan Iya magana ba duba da yadda yake wasanni da fitulin kirji na, ga ruwan da yake zuba a jikin mu gashi ya hade mu a guri guda yana wasa da hannunsa a jikina.
“Babe… Jia nata kiran ki bakya dauka. Meyasa? Kinga damuwar dana shiga kuwa?”
Shiru nai masa na matso lavender shower gel dina na shiga wanke fuska ta da shi. Hannun sa yasa ya shiga daurayemun fuskar yana sake tambaya ta. A gajiya na bashi amsa, Gashi ya sosomun inda yake kaikayi wato masoud da ya shukrah kan babban balai.
“Afuwan Yallabai.. Ya shukrah tayi bako shine fa nad’an jira su gama sai na taho. Saboda bamuyi sallama ba..”
Kunsan mata da miji, Dukda ban wani shaku dashi ba sosai, Sai naji bazan iya boye masa ba gaskia. Uwa uba duk wani janye kai na dana dinga yi a baya ina nesanta zucia ta agare shi duk yawanci saboda Masoud ne. Kafin na samu yafuta arai na Salman din ya fara maye gurbin sa, Saboda k’aunar daya ke zubamun. Sai na samu kai na da gaya masa duk abunda yafaru daren jia. Na kar’kare da,
“Shine wanda kagani tare da Kawu daddy awaje. Hak’uri yake bashi saboda yace wallahi bazata aure shi ba ya riga ya mata miji…”
Kyakkywar runguma Salman yayi mun, Ya zuba mun ruwa ajiki na, Yana cigaba da goga mun soso irin me yatsun nan a jiki na romantically…
“Oh haba..? Ko shine wanda nagani da daddy a tsaye. Yanata bina da kallo. Allah yasa dai be gane ni ba.”
“Eh shine..”
“Kin san Allah ni kunya ma naji da naga wanda muka yi takara da shi a neman auranki, saboda dama can ba ajinki bane bare kuma yace zai dama dani a farauto zuciyarki.”
“Kai da kayi murdiya, ai ba zabe akai ba kuma ko campaign baka yi ba kaga kuwa shi….”
Be bari na karasa ba ya toshe min baki da hannunsa tare da juyo dani idona na kuma rintsewa sai kawai naji bakinsa a cikin nawa ya shiga sarrafawa. Toh me zan tsaya yi banda na bayar da kai bori ya hau. Da yake daman tun dare yake son mu kasan ce tare Allah ya kawo amai, shine ya fanshe abinsa yanzu.
Wanka muka yi sannan muka fito tare cikin towel d’aya, sai da muka zo tsakiyar parloun ya fara kokarin kwace towel d’in baki d’aya, nayi saurin rikewa Ina dariya shima dariyar yake yi yana kuma ja.
“Ki bani mana ba nine babba ba.”
“Kai ne fa kaki tsayawa kowa ya dauki daya kace da wannan kawai zamu yi amfani. Ni dai bazan Iya zama a haka ba bu komai ba.” Yana rungume dani yace.
“Toh ni a haka nake son ganin ki yanzu.”
“Na shiga uku dan Allah takawa kayi hakuri, Allah ba zan Iya zama haka ba.”
“Shikenan to ni bari na bar miki, kuma bance ki rufe ido ba.”
Ido na ne yakai kan jallabiyar da ya cire yanzu, Sai kawai na kwace jikina na ruga da gudu na dauki rigar tare da karawa. Shi kuma tsorata ya yi da gudun da nayi shi yasa be yi wani motsi ba sai da yaga ta zauna a bakin gado ya karasa wajan tare da durkusawa a gaban ta ya dora kai saman cinyarta yana magana cikin rauni da karyar da zuciya.
“Please baby dan Allah ki dena irin wannan gudun, ki lallaba min kanki da kuma babyn cikin ki. Ina son ku bana son na rasa ku a rayuwata kiyi min wannan alkawarin na kula da kanki please.”
Ba karamin tausayi ya bani ba, hakika nasan Salman yana matukar so na, kuma nima ba zan ce bana son sa ba saboda Iya kulawa da tarairaya yana bani Iya yinsa. Ban san lokacin da na dora hannu a saman sumarsa ba na shiga wargaza ta ina mikar da ita tsaye tana komawa saboda santsi da sumar ke dashi.
“Karka damu kaci gaba da yi min addu’a, ina tea dina?”
Saman bedside ya nuna min na hango cup d’in ba laifi yafi na dazu girma, saboda ya daga min cinya nasa riga yasa na shagwabe fuska ina cewa.
“Toh ka dakko min na sha.”
Ya dago kai ya kalle ni da idanunsa masu kama da ruwa a ciki.
“Yadda kika ce haka zanyi Gimbiya sarauniyar zuciyar Salman bin Aliy.”
Yana matsawa kuwa nayi saurin mikewa Ina zuwara yana waigowa. Dariya ya yi ganin yadda nake saurin saka rigar dan kar ya gani, ya matso yana cewa.
“Madam wane dare ne jemage be gani ba?”
Ina yatsina fuska nace.
“Ai kuwa be ga na mutuwarsa ba.”
“Wayyo dena ambato min mutuwa yanzu, ina son naga gudan jini na, ina son na nunawa duniya cewa komai lokaci ne dashi, mutum baya fidda rai da rabo.”
Tea dina na karba duk da ya fara hucewa a haka na shanye shi tas, na kalle shi yana ta shirinsa na fita fada nace.
“Naje sashe na saboda babu wanda yasan na dawo.”
“KI bari ki shirya ni mana my love.”
“Amfanin me zanyi ma wajan shiryawar tunda ba Iya nad’a rawani nayi ba?” Yana saka kayan sa na ciki yace.
“Idan Ina kallon ki zan fi samun nutsuwa har na shirya tsab.”
Babu yadda zan yi dole na koma bakin gado na zauna, Tunawa nayi da shifa beci komai ba, na mike na shiga hada masa coffee dan yafi son shi akan tea. Yana gani na ya shafa fuskata tare da cewa.
“Allah ya yi miki albarka dear.”
“Amin na gode.”
Cake din da ya kawo min ban ci ba shi na hada na bawa yaci sannan nayi masa sallama bayan ya sumbaci goshi na ya fita ni kuma na nufi sashe na da sauri dan karma wani ya zo ya ganni da rigar shi.
Ina zuwa sashe na kaya na nema na saka, hijabi na sanyi saboda gani nake kamar Ina fita za’a hango cewa ina dauke da juna biyu. Hankali na duk yana gurin Ammi, na fito, hadimaina suka ganni duk suka zube suna kwasar gaisuwa, zuciyoyon su cike da tambayoyi dan basu san ta kofar da na bi ba lokacin da na dawo, gashi duk babu mai Iya tambaya ta a cikin su.
Zaune na tarar da ita da wasu baki, tana gani na ta sallame su cike da fara’a ta nuna min gurin zama inda dama can ne kamar parmanent seat dina idan naje. Gaishe da ita nayi cike da girmamawa ta nuna min warmer tace na zuba abinci, daman Ina da bukata dan haka na bude karamar naga wainar shinkafa ce tayi kyau sai kamshi take yi. Plate na janyo na diba tare da zuba miya wacce tasha man shanu da tsokokin nama.
Ina ci Muna hira ta tambaye ni yan uwa na, na ce lafiya suna gaishe da ita. Kallo na kawai take da alama tana son ta gano wani abun a tattare da ni, amman zuciyarta taki amincewa saboda tasan babu ta yadda za ai hakan ta kasan ce. Kiran wayar ta shine yasa ta janye idanunta daga kai na, dubawa tayi taga Salman ne, ta dauka ya tambaye ta ita da waye a gurin tace Dije ya sauke numfashi tare da sosa keya kamar yana gabanta yace.
“Ta…dai gaya miki cewa ba ta da lafiya ko?”
“A’a sai dai ni naga kamar hakan, me yake damunta.?”
“Ammie bata wayar.”
Miko min tayi na karba tare da karawa a kunne Ina masa sallama cike da girmamawa har sunkuyar da kai.
“My love ya jikin ki?”
“Alhamdullah.”
Na fada a takaice ina jujuya wainar da na gutsiro.
“Ya baki sanar da Ammi wannan kyakkyawan albishir d’in ba?” Cikin tsantsar mamaki nace.
“Kai! Tabdi wallahi bazan Iya ba da nauyi.”
“KI gaya mata nima kunyarta nake ji.”
“Nima wallahi haka bazan Iya ba.”
“OMG, My Dijah sarkin kunya, ki fada zata baki tukwici.”
“Na yafe wallahi.”
“Shikenan kin samu abinci kici ko? Bana son kina zama da yunwa gashi ba ke daya bace yanzu.” Nasa wainar a baki Ina cewa.
“Gashi Ina ci kaima a kawo Maka?”
“Nooo bawa Ammi wayar.”
Hannu biyu na mika mata sannan na juya naci gaba da cin abincin. Shi kuma yana ta kokawa da zuciyarsa yadda zai yi ya sanar mata zuwan jikanta. Sai da ya rufe ido sannan ya sanar mata Sai jiyowa nayi Ammi na cewa.
“Kai alhamdullah masha Allah, Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana. Ina rokan Allah ya nuna min zuwan sa/ta lafiya, Allah ya tsare mana shi ya sauke ta lafiya.”
Kasa amsawa ya yi a fili Sai a zuciyarsa ya amsa tare da katsewa. Ammie cike da zumudi ta nemo lambar Gwaggo tana fadin.
“Abokin kuka shi ake gayawa mutuwa.” ji kawai nai tana cewa.
“Allah ya yi Zaki ga jika… Eh wallahi yanzu yake gaya min.. Wallahi kuwa Gwaggo.. Amin ya rabbil amin a ci gaba da Taya mu addu’a… Toh shikenan..”
Ai ban bari ta gama wayar nan ba na tashi na gudu saboda kunya da tabi ta dabaibaye ni. Ammie kuwa dariya tayi a gurin kuma ta kafa goshinta a kasa tana yiwa Allah godiya….
*YAREEMAH IBRAHIM-(KHAL)*
*INCHEON INT. AIRPORT*
A tsaye Khal yake, Da akwatunan sa guda biyu, Ya saqale wata jaka a jikin hannun akwatin. Waya ce a hannun sa da alama magana yake da wani mai matuk’ar muhimmanci saboda yadda yake sakin tattausan murmushi. Sanye yake cikin kananun kaya riga da wando ya d’aura overcoat akai, Samun waje yayi ya zauna akan kujera, Ya kira lambar da yai saving da (Yeobo-Bintu naah)🌷’
“Bintuunaahhh….! Lapia lou ina airport! Uhm…? Ki tayani da addua my love! Fushi kuma?”
Mikewa yai da sauri tamkar tana wajen, Domin kana iya jiyo zazzakar muryar budurwar dake magana ta cikin wayar. Shafa kwantaccen gashin kansa yai yana jan kasan leben sa, Kallo d’aya zakai masa kasan sun hada jini da SAS. Ha’kuri ya shiga bata yana sake rage sautin muryar sa.
“I’m sooo sorry yeobo (honey) Bansan fushin me ake dani ba, But kiyi hak’uri zan karb’i kowane punishment banda na rashin ki… Ina kaunar ki Dr. matar Dr. IN SHA ALLAH! Saranghaeyo ( I love you in Korean) .. An hak’ura? Masha Allah! Godia nake, Take kia love.”
Katse kiran yai yana murmushi ahankali yace,
“Kai.. mata.. sai a slow. Dole naje na bada hak’uri.”
Wani kiran ne ya sake shigowa, Jikin sa na rawa ya dauka sahibar ce sai kuma yaga SAS ne. Dauka yayi da sauri ya gayda shi cikin girmamawa, Salman din ma na bashi amsa cikin kulawa,
“Yasu Ammi da Abdullah…?”
“Kowa lapia lou! Ka taho kuwa?”
“Eh saura mintina kadan ina airport..”
“Ai na kira naji busy.. Kanata waya.”
Shafa sajen sa yayi yana daria,
“Da wani ne…”
“Ko dai da Dr. dinnan danaga itace wallpaper dinka ba.”
Daria Khal yayi. Ya shiga shafa keya kunya duk ta kama shi,
“Ayi hak’uri yallabai, Tuba nake.”
“Ahh bakomai.. Allah yasanya alkhairi, Idan ka dawo komai ya daidaita sai ayi bikin a huta ko.”
Da’di ya kama Khal da har sai da ya kasa boye murnar sa yayiwa SAS godia.
“Yanzu aina zaka sauka kenan?”
“Zan sauka Abuja yallabai…”
“Wajen Dr….?”
Nanma Khal yayi shiru yana daria ahankali, kafin yace.
“No zanyi submitting wasu takaddu ma. “
“Toh Allah ya dawo da kai lapia Khal.. Allah ya bamu nasara, Ya dora mu akan makiyan mu.”
Sallama sukai, Khal yayi hanyar departure…..! Zuciar sa dauke da adduar Allah yasa ya koma a sa’a…
_Afuwan zafafa fans.. Ba zaku samu kibiyar ajali ba na yan wasu kwanaki. Saboda wani uzuri daya taso🤲🏻Dana kammala zan cigaba da posting IN SHAA ALLAH!_
_Yar uwa kinason karanta zafafa amma documents? To zafafa na harhada kayan su. Da an kammala Za’a yi documents dinsu duka akan Naira dubu d’aya da…….._
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more
Asha hutun *Sunday* Lapia zafafa fans❤️❤️
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma’ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
GIPHY App Key not set. Please check settings