Advertisement
_I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_
_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_
_Wattpad: missxoxo00_
_PG:27_
_BOOK:2_
Advertisements
*GIM. KHADEEJAH*
Kwance nake akan gado, Hawowata kenan daga kasa, Domin Ammi tace na dena zuryar zuwa sashen ta tunda yanzun bani kadai bace. Ajiyar zuciya na sauke fuskata na kumshe da murmushi, Kaunar da Salman da Ammi kemun yanzu ta kara nunkuwa, Wata irin tarairaya nake samu daga kowannen su. Gwaggo ta fada ma kullum cikin aikomin da tofi take, Addah Maryama ma kullum cikin zuwa ta duba ni take. Lamarin sai godiya ga Allah daya had’ani da miji nagari mai kaunata, Suruka ta gari da kuma yan uwan miji masu gatanta ni.
Yanzu babu abunda na nema na rasa a duniya sai rashin iyaye, Wanda su Kawu daddy su Ammi suna iyakar ko’karin su wajen maye gurbin su. Sai dai iyaye daban ne a duniya, Ni yanzu da za’a kwace komai nawa a dawomin dasu sai nafi farin ciki.
Kwakwar manja ta dake gefe na janyo na shiga ci hankali kwance ina lashe yatsu na. Cikin haka sai ga Salman ya shigo sanye cikin jallabiya hannun sa rik’e da flask din shayi da kofi da cokali. Tinda ya taho nake bin hannun sa da kallo domin ni yanzu banda bacci da ciye ciye ba abinda nake.
“Zawjatii.. Maman unborn. “
Advertisements
Zama yai a gefe na yana kallo na cike da tattali.
“Na’am Zawj.. Tea ne ko kunu?”
Daria ya kyalkyale da ita yana shafa gefen fuskata,
“Kunu ne… Ammi ta bayar akawo miki. Kunun gyada.”
Yunkurawa nai, Zan mike yai hanzarin tare ni.
“Yi hak’uri tawan. Idan kika tashe shi yana bacci fa? Ki dinga yi ahankali.”
Na kalli shamilallen cikin nawa ina dariya.
“O ni ‘yasu… Toh nide nide nide yunwa nake ji ai.”
Na fada ina turo baki gaba cike da shagwaba.
Zubamun kunun yai a kofi ya jinginar dani a k’irjin sa yana kafamun cup din akan baki na,
“Ungo asha lapia.”
Gani nai zai batamin lokaci na karb’e kofin na kafa kai na shanye, Sai danasha sau uku sannan naji ya isheni. Na wanko baki na. Na dawo kusa dashi na zauna.
“Allah sarki Ammi naa..”
“Ni Fa? Ni ba naki bane?”
Hannuwana biyu nasa tafukan na rufe fuskata. Kunya ta kamani.
“Ammin ce akwai kirki, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, Allah ya juyo da hankalin Yareemah Ibrahim agare ku ya waiwayo gida shima.”
“Aaamin Yaa Rabbi…”
Ahankali ya sumbaci tafin hannu na yana sake rike ni sosai tamkar Za’a kwace ni. Cikin rada ya shiga cemun,
“Na fad’a miki wani abun farin ciki…?”
Da sauri na gyad’a kai na ina kallon kwayar cikin idanun sa. Wadda nake samun nutsuwa sosai a duk sanda na kalle ta.
“Khal… Wato Yareemah Ibrahim ya farfad’o daga sihirin kafewar da akai masa a korea. And Alhamdulillah hankalin sa ya dawo jikin sa. Zancen da nake miki ma ya kusa shigowa kasar nan …”
Bansan sanda wasu zafafan hawaye suka shiga reto a fuska taba..
“Nooo….! Kuka? Subhanallah! Mena miki Zawjati? Na fa’di wani abun daya tayar miki da hankali?”
Ahankali na girgiza kai na, Nasa hannu na na riko nasa ina murmushi,
“Kukan farin ciki ne Zawj.. Kukan dadi ne kawai. Shin Ammi tanada masaniya kuwa?”
“Ah’ah tukunna dai… Akwai lokacin da muka gama tsara komai, Kinsan dawowar Khal masarautar nan akwai ruguntsumi fa. Saboda love kina ji?”
Gyada kai nayi alamun ina sauraron sa. Cikin nutsuwa ya cigaba da cewa,
“Saboda sun dauka har yanzu bansan matsayin Khal ba awaje na, Sun dauka har yanzu Khal na can yadda suka kafe shi, Kuma sun dauka har yanzu Ammi na cikin kangin rayuwa na rashin mu a kusa da ita… Kuma sun dauka dagaske bana haihuwa…”
Na dago da sauri ina kallon sa. Ya gyada kai cikin tabbatarwa.
“Ke haske ce acikin rayuwata Zawjatii, Na gaya miki kece mahadin rayuwar Salman ibn Aliy. Dake Allah yayi zamu samu KIBIYAR hallaka makiyan mu na masarautar nan. Domin kedin dashen Allah ce…”
“Yanzu idan suka nemi kashe ni fa..?”
“Karki damu da yardar Allah babu abunda zai faru dake da abun dake cikin cikin ki, Domin mun dogara da Allah shi din mubuwayi ne gagara misali.. Sai abu na biyu Dr. Fiddau zata dinga zuwa kullum tana duba lapiar jikin ki.. Sannan Za’a kawo amintattun hadimai da zasu dinga kula dake, Motsin ki, Baccin ki, shawagi, Abinci, anything dai daya dangance ki zasu tsaya akan ki. Kada ki manta kina da ni kuma ga Ammi… Ai zawjati ke yargata ce gaba da baya…”
Nayi murmushin da hakorana suka bayyana, Duk kuwa da kasan zucia ta a dankare yake da fargaba sosai. Na gudun kar a hallaka ni da abinda ke tare da ni, Hannu nasa akan marata ina shafa wajen ahankali. Wani irin sanyi naji yana ratsa ni. Cike da karfin gwiwa nace,
“Allah ya temake mu… Allah ya kara kare mu da kariyar sa. Mugun ji mugun gani Allah ya kiyaye..”
“Aamin Zawjati.. Allah ya miki albarka, Ya kara miki so na a zuciar ki, Tunda nide duk minti sonki nunkuwa yake acikin zucia ta. Ke kuwa har yau baki gayaman wasu kalamai da zan tabbata kin mallakamun zuciar ki ba. Inaga sai na kara zage damtse sosai na yak’i ragowar burbushin kaunar m…”
Ban bari ya karasa ba nai saurin hade bakunan mu waje d’aya, Ni kaina nayi mamakin hakan da nayi, Amma na tabbata hakan shine ka’dai zai iya bashi amsar tambayar sa. Sai da na tabbatar ya gamsu sannan na zare baki na ahankali. Ido cikin ido na kalle shi,
“Waya gaya maka bana kaunar…? Ka cire dik wani waswasi dake tasiri azuciar ka, Ni Khadija daga rana irin ta yau.. Na mallaka maka zucia ta da gangar jiki na sai yadda kayi dasu. Ina kaunar ka, Kauna marar gauraye. Tun ina durbun lokacin Ina cikin SIRADIN RAYUWA, Nayi ta addua Allah ya bani miji nagari wanda zai so ni ya kaunace ni, Na maka ta larabci MIN QALBi na nake kaunar ka tsakani da Allah, Da ace dan adam yasan ABINDA KE CIKIN ZUCIYA to da tabbas zaka son matsayin ka awajena ya wuce ‘kima. Kada ka damu da masu mana SARAN BOYE zawj.. Domin Insha Allah ni Khadija dashen Allah ce, Na tsallake tarko kala kala na rayuwa, Saboda haka da yardar Allah sai na zamowa makiyanmu KIBIYAR AJALI.. Kai de ka zuba idanu…”
Lumshe idanu Salman yai ya bude su akaina yana wani irin tsadadden murmushi,
“Na yadda my love… Na kuma tabbatar kafin wata dayan dana kiyasta tacika a game dinmu dake, To tabbas kaunar zata ninku fiye data yau…”
Murmushi nai nima na shagala da kallon kyakkyawar fuskarsa,
“Tabbas kuwa Zawj.. Insha Allah lokacin nasan kagama dani, Na gama dilmiyewa acikin kogin kaunar ka.. Kalli tin yanzu ma bare nan gaba.. koya kace?”
“Lalle na cancanci kyauta daga wajen gimbiya..”
“Tabbas kuwa ka cancanta.. Amma hak’uri zakayi kata shi ka shirya zuwa zaman fada..”
Hannuna ya kaiwa sumba me matukar ratsa jiki da bargo, Ya sake narkemun ajiki yana wasa da jelar gashi na,
“Ai gaba d’aya gimbiya kin maida Salman tamkar ba sarki ba, Ni fa gaba d’aya mantawa ma nake da wata sarauta idan har ina gaban ki. Barin ace yadda muke dinnan jikin ki na gogar nawa, Gashin ki mai matukar k’amshi yana busa kamshi,…Zawjatii! My unending love for you is my vision, my hope, my goal, and my soul. Ina kaunar ki sosai Zawjatii na. Please ki bari naji dumin jikin ki, Dan kadan zamu yi fa. “
Ya karashe maganar yana kokarin dage rigata, Daria nayi kawai na kamo hannun sa na sunbata a hankali,
“Zawj….”
“Zawjatii..!”
“Kayi hak’uri.. Ka tashi ka tafi dan Allah.. Kaji?”
“Zan sa waziri fa ya zauna, Zance banda lapia, Yanzu zansa ayimun iso dashi.”
“A’ah..! Ka tashi ka tafi.”
“Yanzu haka zan tafi ba abun da zan samu?”
Mikewa nai na riko hannun sa ya tashi tsaye shima,
“Muje na shirya ka katafi kaji..?”
Gyad’a kai yayi, Hannu cikin hannu muka koma dakin sa. Na shiga fito masa da duk abubuwan da zai saka. Na temaka masa ya kara yo wanka, Na shiga shirya shi ina masa kirari,
“Kaga dawisu sarkin ado nawan, Da kwalliyar ka ala hallice ka Zawj, Taka a hankali lu’u lu’u abun son kowacce mace! Amma fa sai dai suyi hak’uri domin wannan lu’u lu’un nawa ne ni kadai.. Ko shaheedah sai ta kama kanta.”
Murmushi naga yayi ya sake tallabo ni yana kissing kan hanci na. Na sunkuya ahankali ina faffesa masa turare ajikin kayan sa,
“Kaga katangar zinare majingin mace, An gayshe da sarkin sarakuna, Mai basannabas, Tsarin jikin ka da hankalin ka na shugaba mai shugabantar masu rauni. Takawar ka daidai ranka ya dade mai dogon zamani, Sun buga sun barka ya zasuyi dakai? Girman kane Allah ya baka, Ya zasuyi?.. Waya isa ya amsa balle har ya amshe? Kai ka iya kai zakayi ranka ya dade.. Kai ne gaba muna biye. Nawaje na.. Allah ya dawomin da kai lapia..”Cc:OD
Na k’arashe ina zura masa glasses dinsa cikin idanun sa, Lalle Salman anyi kyakkyawan sarki mai kyakkyawar halayya. Gaba salamun baya salamun. Wata iriyar runguma yayi mun, Ya saqalo hannuwan sa muna kallon kanmu tacikin mudubi ya d’aura kansa akan kafada ta. Nasa hannu d’aya ina shafa kwantaccen sajen sa…
“Zawjatii na… Na biya ki da kai na, Ruhi na da Qalbi na. Na biya ki da amanata da dik wani sirrina, kece kofar mabudin alkhairi na, Kuma kece katangar mahallakar makiyana. Hakika ke kika cika Salman ibn Aliy ya zama cikakken sarki mai cikakken Iko….”
Nai saurin riko hannunsa Na juya muna fuskantar juna,
“Kalaman ka sunyi tsau…..”
“Karki karasa rabin rai na…. Nan gaba kadan zaki tabbatar da hakan. Amma kafin sannan dole na baki ladan kirarin nan.”
Daukata yayi a hannu ya kaini dakin da nake dazu ya kwantar da ni, Ya janyo bargo ya lullube kafafuwana. Ya zauna a gefe hannun sa cikin nawa,
“Zawjatii naa.. Ina kaunar ki sosai. Zantafi fada sai na dawo, Amana addua”
Ya karasa yana rungumeni kamar Wadda Za’a dauke a gudu, Cikin muryar lallashi ina shafa gadon bayan sa nace,
“Allah ya kare mun kai, Ya dawo mun da kai lapia. Allah ya dora ka akan makiyan ka, Ya Kara maka madaukakiyar kasaita da kwarjini da nasara akan kowane lamuran ka.”
Dak’yar na iya yage shi a jiki na kamar wani cingom ya sauka ta sashen sa hannun sa rik’e da rawanin da Za’a nada masa…
*FADA***
Sai da Salman ya zauna dogaran sa suka kare shi sannan sannu ahankali yan zaman fadar sarki suma ‘d’aya bayan d’aya suka shiga shigowa ana fad’in sunayen su sai su zube su rissina su kwashi gaisuwa sannan su zazzauna gefe da gefe. Shi kuma Salman nadaga saman wata kasaitacciyar kujera yana hakimce. Kallon dukkanin su yake ta cikin bak’in gilashin dake idanun sa, Amman gangar jikin sa ce kawai a fada, Gaba d’aya zuciar sa da tunanin sa naga Khadija dake sashenta tana bacci.
Haka dai zaman na fada ya kasance, Wannan rukunun suzo su kawo koken su, Wasu suzo neman tallafi, Sai sabbin tsare tsare da masarauta zata kawo, Wanda zaman ya kasance daga sarki sai manyan yan majalisar sa. Cikin haka Yareemah Abdulqadeer ya shiga yanata bubbudawa. Sai kirari dogarai suke masa, Ya baza babbar riga da tulin rawani akan sa.
“Gayshe ka Yareemah Abdulqadeer, Gyara kintsi dakyau!!”
Cewar wasu dogarai daga bayan sa. Wambai ya murmusa yana nuna masa kusa dashi, Abdulqadeer ya zauna, Dogari na cigaba da masa kirari
“An gayda Yareemah Abdulqadeer, Dan sarki jikan sarki, Kaga hakimin waje, Mai girma makaman basannabas.”
Sallamar dogaran sarkin kofa yai, Akabar fada daga sarki sai manyan yan majalisar sa. Kowa yana kawo tasa matsalar har akazo kan Abdulqadeer, Fuskar nan tasa ba rahama, Sai dai duk kwarjinin sa SAS ya dame shi ya shanye. Cikin k’asaita da isa yafara magana,
“Ran sarki ya dade…. Sallah na dada ‘karatowa, Kuma dawakan yanki na duk sun jigata bazasuyi abun arziki ba wannan sallar, Shine nakeso asa ma’aji ya bada isassun kudi da za’a sayo wasu ba sai an dinga wahalar hayowa ba. Saboda wannan sallar na shirya gasar sukuwa da za’ayi da masarautar kudu… A ha’da da kudin abincin dawakan da kayan kwaliiyar su…”
Salman yai murmushi kawai ta cikin rawanin sa. Kowa ya tsaya jin abinda zai tofa, Samun kansa yai cikin karfi gwiwa yace,
“Kudin wajen waziri makudai nasa gaba d’aya a baka dasu Munaya kuyi hidimar biki, Wanda na tabbata har yanzu akwai sauran su awajen ka..”
Abdulqadeer ya girgiza Kai yana sake bade rigar sa,
“Wannan kudin kamar yadda ka umarta kudin biki ne kuma anfanin su ya kare, Tun tuni suka k’are, Ga ma’aji nan a gefe so nake ka bashi dama yanzu ya bada kudin.”
Waziri dake gefe yai shiru, Salman yai gyaran murya kafin ya sake cewa,
“Asusun masarauta yayi kasa Makama. Ka dada hak’uri zuwa shagalin sallar gaba. Zan sa a hayo dawakai masu inginci. Koya kace waziri?”
Waziri ya gyad’a kai kafin cikin gasgata abunda sarki yafad’a Yace.
“Hakane ranka ya dade, Sai a hayo dawakai masu kyau.”
Wani tsaki abdulqadeer yaja yana kallon waziri, Da alamun tsabar bacin rai yama manta a’inda yake,
“Kai dai babban munafuki ne waziri, A haka kake tunanin zan tafi tare dakai kana cin dunduniyata?”
Waziri ya kalli chiroma (shine mahaifin Mama Huwaila wato mahaifiyar AbdulQadeer.) Chiroma yai saurin riko kafadun abdulqadeer yana kokarin janye shi, Abdulqadeer kuwa sai surfa zagi yake yana karkadawa waziri hannu. Shi kuwa Salman farin ciki ne fal zuciar sa ganin dabarar da yai taci. Gashi nan kansu yafara rabuwa. Bayan fitar Yarima Abdulqadeer, Galadima ya muskuta sosai yana karkada k’afafuwa,
“Ran sarki ya jima har yaga ‘yayan kannen sa, Ko yaji sanyi anasa idanun…”
Salman dai yana zaune akan kujera yana duban su, So yake yaji kuma yau da me suka zo. Waziri dake gefe duk kuwa da ransa na susar abinda AbdulQadeer ya masa bai fasa tanka zancen galadima ba,
“Sarki na sauraron ka Galadima. Amma kalaman ka sunyi tsauri, Meke tafe daku kuma wannan zuwan?”
Chiroma ya amshe zancen da,
“Munzo ne akan maganar auren sa da mukace lalle yayi, A baya mun bashi wata d’aya zuwa biyu. Yanzu da yardar Allah mun soke wancen zancen. Nan da sati d’aya zuwa kwana ki goma mukeson ya bamu sunan wadda ya zaba acikin tsatson jinin masarauta.”
Waziri ya fusata kamar gaske yayi kan chiroma, SAS ya dakatar dashi ta hanyar gyaran murya, Cikin nutsuwa hankali kwance yace,
“Na amince…”
“Ranka ya dade ka amince fa kace.. Ka amince? Akan me zaka amince akan abunda ba dolen ka bane?” Cewar waziri cikeda damuwa.
SAS ya murmusa ta cikin rawani,
“Kada ka damu waziri, Na amince.. Nan dukan ku iyaye na, Nasan babu wanda zaimun zab’en tumin dare. Na karbi zancen chiroma da hannu dubu.”
Waziri ya shiga magiya yana rok’an SAS daya janye zancen sa kai kace gaske ne. Saboda yadda ya dinga bori tubaran kan lalle shi bai yadda da zancen dasu chiroma suka yanke ba. Shi kuwa SAS gyaran murya ya sake yi, Dogaran sa suka kare shi. Ya mike yai hanyar sashen sa ta baya. Ya barsu nan suna muhawarar yadda komai zai kasance. Ciki harda waziri dayafi kowanne zakalkalewa, Amman duk zancen da suke baya tanka duk abunda chiroma yake fa’da saboda abunda jikan sa Abdulqadeer ya masa dazu ba jimawa.
Jiki na ‘bari chiroma ya kara kaskantar da kansa yana bawa waziri hak’uri. Waziri ya girgiza kai yana yatsina fuska,
“Wato tun yanzu kenan yafara kirana da munafiki inaga idan mun dora shi ya zama sarki? “
“Allah ya baka hak’uri ranka ya dade. Haba wane Mutum, Shi ya isa ya fara ma bare yayin? Waya sa aka nadashi makaman idan ba kai ba waziri?”
“Atoh shi nagani nima…”
“Zanje na sami mahaifiyar sa yanzu ba sai anjima ba ranka ya dade, Ka Kara haku’ri, Kasan yaran zamani.”
Ficewa ciroma yai jikin sa na ‘bari. Fada ta zama sai galadima da waziri. Waziri yai ajiyar zuciya yana kallon galadima kafin yace dashi,
“Tun ba’aje ko’ina ba kaga abunda nasha gaya maka zai auku ko? To wannan kadan ne akan nan gaba. Shiysa nace maka muyi meyiwuwa mu san abinda zamu sa agaba, Domin idan muka kuskura muka dora abdulqadeer sarkin basannabas to ina tabbatar maka dacewa a rannan zai tube mana rawanin mu. Kaga dukkanin mu jikokin mu mata ne, Gwara Kai akwai Ilyasu.. Shima yaro ne wannan ba wanda zai dora shi akan mulki. Amman chiroma fa? Dukkanin jikokin sa mazan sun isa su gaji sarautar nan, Kuma kasan tabbas idan mulki ya koma hannun tsatson ismaila Rabo.. To akwai bahaguwar matsala.”
“Ranka ya dade duk abunda ka fada gaskia ne, To amma ina mafita?”
“Mafita d’aya ce… Wadda Idan na gama bincike akanta zuwa jibi zan sanar da kai..”
Haka dai suka cigaba da yan zantattukan su, Daga karshe sukai wa juna sallama Kowanne ya kama gaban sa. Salman dake dakin sirrin sa yana saurarar dik abunda suke cewa.. ahankali ya danna wani madanni dake dauke da tambarin ‘file saved…’
Mikewa yai ya fice zuwa sama, Ya le’ka dakin da Khadija take ta bacci kamar Kasa. Dakin sa ya koma yai wanka da alwala hade da d’akko Qur’ani ya bude ya fara Karantawa… Zuciar sa dauke da adduar Allah ya basu nasara akan wannan ruguntsumi da ke tunkaraso nan kusa………
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma’ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥.
GIPHY App Key not set. Please check settings