KIBIYAR AJALI 28

Advertisement

 _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B28_.

Advertisements

*GIM. KHADEEJA!!*

   ***Sosai nake samun kulawa ta kowane bangare, Sai dai fa Salman kulle yake mun yanzu, Karshen fita unguwa ta kuwa daga kasa sai bakin gate shima don saboda exercise, Ranar asabar da yamma Kawu daddy ya kira ni da kansa yake sanarmun za’a kawo kudin su Ya Shukrah da kayan lefe bayan sati biyu kuma ayi shagalin biki, 

“Allah yasanya alkhairi Kawu Daddy, Zan shigo In Shaa Allahu!..”

“Ah keda bakya jin dadi? Ba sai kinzo ba Khadija, An hutasshe ki, Ya jikin naki?”

Shiru nayi, Mamaki duk ya cika ni, Kenan Salman barbada zancen cikin nan yake tayi? Kunya duk ta dabaibaye ni, Dakyar na iya amsa masa ina sunne kai tamkar yana gaba na,

“Da sauki Kawu daddy…”

Advertisements

“Toh Allah ya raba lapia…. Hajia ma zan sanar mata zata kira ki.”

“Toh Kawu….”

“Ya sanarmun ma idan an kwana biyu zaki ziyarci durbun…”

“Eh Kawu”

Na bashi amsa duk kuwa da bansan yaushene Salman din zai barni naje ba. 

“Toh Allah ya kaimu.. Ki kula sosai Khadija, addu’oi na neman tsari, Nima zansa anan ayi ta saukar qur’ani, Allah ya kauda idanun makiya akan ki da abunda zaki haifa.”

“Insha Allah Kawu… Nagode Allah ya kara arziki ya bada nisan kwana mai amfani..”

Sallama mukai wa juna na kashe wayar, Ina kambaba rashin kunyar Salman akan cikin nan duk ya barbadawa dangi. Daga samun sa. Na kalli cikin nawa ina mamakin yadda yake a shamile haka amma ina dauke da ciki? Gama waya da Kawu keda wuya kenan sai ga shigowar call din Salman, Na dauka a hankali ina mai gyara zaman dankwalin kai na,

“Zawjatiii…”

“Na’am Baby! Ya kake?”

“Ba dadi….”

“Meyasa?”

“Saboda bakya tare da ni..”

“Dazu fa muka rabu da kai..”

“Duk sanda nake tare da ke, Banason mu rabu ko na second d’aya! Ina kaunar ki love.”

Shiru nayi ina murmushi kawai, Kalaman sa na dada ratsa bargon jiki na,

“Love… Kina jina kuwa?”

“Uhm! Ina ji.”

“Nayi lefi ne, Naji anyi shiru?”

“Eh mana kayi..”

“Ki shirya yanzu… Zanzo zance. Zanzo ban haku’ri.”

Kit ya katse kiran, Nabi wayar da kallo, Goma na dare saura kwata. Yana iya? Mikewa nai na shiga band’aki nayo wanka, Badan inason kamshin turaren jikin sa ba Allah ba wani zance da zan bari yazo, Wasu riga da wando nasa na English wears nayi packing gashin kai na. Ba dadewa sai ga kiran sa ya shigo,

“Ki sakko ina k’asa…”

Sai dana mula na huta tukun sannan na mike na sauka kasan, Ina hango shi akan kujera ya bada baya yana danna waya, Tun kafin na karasa ya taro ni yana riko hannu na,

“TubarkAllah! My queen.. Kinyi kyau sosai. Komai nake me mekyau ne, Sahibar zucia ta.”

Janyo ni yayi zuwa jikin sa yana shafa gadon baya na, Duk kuwa da fushin da nake dashi, Hakan be hanani lafewa a jikin saba, Na cusa fuska ta a k’irjin sa ina shakar daddadan kamshin dake fita daga jikin sa,

“Ina fatan za’ayimun afuwa akan kowane lefi ne da nayi? Duk kuwa da bansan laifin da nayi ba.”

Hannu nasa ina duddukan kirjin sa,

“Shine.. Shine.. Shine.. Ka fad’awa Kawu daddy zancen cikin nan.. Meyasa?”

Dariya yayi yana shafa gashin kai na,

“Ayimin afuwa my love, Na kira shine na gayda shi yake tambayar ki? Nace bakida lapia… To kinsan manya da gano duk wata kwana da kayi, Har yake sanarmun za’a kawo kudi da kayan sisters dinki…”

“Ya gayamun wai basai naje ba, Ni gaskia inason zuwa.”

“Kiyi hak’uri! Zakije bikin da yardar Allah, Amma ganin kayan ne dai ki hakura kya gani daga baya, Kinsan hayaniyar mutane, Dr. ta hanaki, Kinji? Sai me kuma nayi na kara bada wani hakurin?”

“Shikenan ya wuce…”

Sumbatar gefen kunne na yayi, Ya koma kan fuskata daga nan ya dawo tafin hannu, Nai saurin riko bakin ina murmushi, Shima murmushin yayi ya cigaba da cewa,

“Wata dayan dana deba mana akan game dinmu ta cika, Kuma naga nasarori sosai ta bangaren ki sai dai abu d’aya kacal ne da har yau banji daga bakin ki ba”

“Me?”

“Yadda nake nuna miki kulawa.”

Ya fada yana tabarbare fuska kamar zaiyi kuka.dariya na shiga yi, Mikewa yai ya dakko wata leda acan kasan kujera,

“Na manta nazo da toshiyar baki….”

Karba nai da sauri jiki na bari na zazzage ledar, 1 liter bucket ne na mint Ice cream da kuma sausage shawarma guda 5 da zafin su, Sai tarin chocolates. Habawa bararrajewa nai zan fara ci ya ri’ko hannu na,

“Bara mu kira Ammi dai muji ko? Ko zaki iya cin komai.”

“Na hakura da fushin da nake yi fa, Dan Allah ka kyaleni naci… Wallahi bakaji yadda babyn ka yakeso yaci ba.”

“Toh i sauri ci.”

Ya fada yana cire takardar jikin shawarman, Nayi murmushi kawai, Ya samun a baki, Na k’arba gaba d’aya na faraci ina gyada kai saboda dadi. Sai da nacinye har guda 3 nasha ice cream din sosai sannan naji na koshi, Banyi aune ba naji harshen Salman kan lebe na yana lashe gefen bakina, Daganan lamarin nasa ya zarce zuwa ga kiss din mai gaba d’aya, Ture shi nai dakyar ,

“Abu ne awajen shine na cire.”

“Daga cire abu kuma sai ka…”

“Sai me??? Dan kadan nayi fa love. Tuba nake to. Sai albishir na biyu amma gaskia bazan fada ba sai kin bani tukwici.”

“Me kakeso?”

“Kalamai daga zuciar ki… Wanka tare, Sai dan kisses and hugs haka masu zafi kafin miyi bacci.”

Wannan Salman din A ne wajen wayo ne,

“Na yadda..”

“Na samu gwamna da kai na ba’ai keba, Munyi magana sosai ta fahimta dashi akan yayi hak’uri da batin tashin yan yankin gaba d’aya, Illa dai gonakin dake gefen yankin, Za’a biya manoman ayi babbar makaranta awajen ta kwana. Hakan yayi miki ko?.”

Bansan sanda na wawuro shiba na rungume abuna tsam ina hawayen farin ciki,

“Nagode, Nagode, Nagode… Allah ya biya ka da alkhairi, Ya baka abinda kake nema dunia da lahira. Ina fatan gwamna yaji da’din shawarar taka?”

Handkerchief ya janyo a aljihun sa ya shiga gogemin hawayen cikin wani salo,

“Bar kuka My love.. Ai nima garin mu ne, Hakki na ne nayi abunda ya dace kinji? Kuma ya gamsu da shawarata dari bisa dari. Nasa a musu titi kyauta daga gare ki. So muje a wanke ni tas.”

Zanyi magana ya dauke ni a kafadar sa muka hau saman tare, Bai direniba sai akan gado,

“Baby kin kara nauyi tubarkAllah.. Oya ciremin kayan ki wanke ni ki sabe ni.”

Sai na samu kai na da ce masa,

“Wani lokacin sai nayita mamakin haka kakeda magana? Mutane bazasu taba yadda ba.”

“Ke ka’dai nake iya sakewa nayita magana sosai, Ni kaina Ina mamaki, Kuma sai bayan na auroki bakina ya bud’e haka, So kaunar kice sila my love.”

“Lalle na ciri tuta, Godia nake takawa… Takawarka lapia sarkin sarakunan nigeria baki d’aya, Nagode kwarai da duk kanin alkhairin ka gare ni, Hakika mutanen durbun zasu ji da’din wannan titi, Allah ya biya ka da mafificin alkhairin sa. Da sauran sarakuna zasuyi koyi da kai, Hakika da ansamu ci gaba sosai a kasar nan. Lalle Ka musu zarra nawan. Muje band’akin kafin na canza ra’ayi.”

Da sauro ya mike, Hannu cikin hannu muka shjga band’akin, Anan ma sai da muka bata lokacin yin wata soyayyar kafin mu fito mu shirya cikin kayan bacci. 

“Saura kalaman da sauran aiyukan ladan.”

Daria nayi jin wani wayo na daban. Kwanciya mukai akan pillow d’aya muna kallon juna, Hannun Salman na cikin jiki na yana yawo dashi. Cikin lumshe idanu nasa hannu ina shafa kwantacciyar girar sa,

“Miji na sinadarin rayuwata, Tauraro mai qawata rayuwata, Zuma naaa, A Ido da kyawun kallo a baki dadi mai dad’ad’awa, Salman ibn Aliy bin Salmanu dina nawa ni kadai, Zaki kake ga isa ga kasaita….”

Na karasa fada ina rufe bakunan mu waje d’aya, Nayi saurin jan zanin gado na rufe mu gaba d’aya, A ranar duk wani abu da Salman keso biye masa nayi, Na kuma yi amfani da karatun hazikar nan *BillynAbdul* marubuciyar da nake bin books dinta wajen ganin na faranta masa nima daren ranar Salman kuwa..Harda hawayen farin ciki, Ya shi mun albarka fiye da tunanin mai tunani, Tare da zayyano abubuwan alkhairi kan sune kyautata,Ni dai biye masa nayi kawai muka gurji lobayya tamkar cin kwan makauniya…

*MAI BABBAN DAKI…*

Fitowa tai daga kitchen, Hannun ta dauke da food flasks da flask na shayi, Sai wani tray daya sha kayan alatu akai, Umma Hansatu (Amintacciyar hadimar ta) Na gefen ta tana shirya kayan abincin acikin wani tsaftaccen kwando. 

“Ranki ya dade dole gimbiya da mai martaba suji dadin abincin nan, Tun daga k’ofar bayi ake jin kamshin sa fa, Dad’in ‘dadawa kuma da hannun ki kika sarrafa komai.”

Ammi tayi murmushi kawai tana gyaggyara gyalen da aka rufe kwandon dashi. 

“Hansatu kenan, Allah yasa yadda yayi dadi a  hanci a baka ma yafi haka dad’adawa..”

“Aamin ranki ya dade. Ai dole nema yayi dadi. Ina dawowa daga aiken nan zan kwashi nawa ganimar dad’in. Allah dai ya kara karya asirin da akai na shiga tsakanin ki da yaran ki, Ya waiwayo da hankalin Yareemah Khaleelullahi gare ki…”

Ammi ta fad’ad’a murmushin ta, Kafin ta dan sake matsawa daf da Umma Hansatun. Murya kasa kasa ta shiga ce mata,

“Ai Hansatu wata muhimmiyar magana nake son sanar dake, Amman bansan koda wasa wani yasan da ita, Kin san dai yadda masarautar nan take ko?”

“Insha Allahu ranki ya dade babu matsala, Allah dai ya kara miki lapia da nisan kwana mai amfani.”

“Aamin Yaa Rabbi! Tare da ke..”

“Ina sauraron ki ranki ya dade, Allah yasa alkhairi ne kunnuwana zasu jiye mani, Kuma Allah ya bani ikon rufawa wannan amana asiri.”

“Aamin! Zancen shine, Kinga dai kusan ko yaushe a dan tsukukun nan, Ina tura ki sashen gimbiya Khadija ki bawa falaki abincin ya karba ko? Bakida masaniyar abincin wanene acikin su ko?”

“Allah yaja zamanin ki, Wannan haka shike.”

“Toh abincin gimbiya Khadija ne, Harda shi mai martaban, Amma dai da abunda yasa akeyin sa hususan saboda Khadija ne… Ki tayasu da addua, Uwar dakin naki Allah ya albarkance su da…”

Zubewa Mama Hansatu tayi tai sujjada tana godewa Allah,

“Allah mungode maka, Allah abun godia, Allah Alhamdulillah! Masha Allah! Ubangiji Allah ya bata lapiar sauke shi lapia, Ya yiwa abunda za’a haife albarka. Allah ya kauda idanun makiya akai ya inganta.. Kai Alhamdulillah!”

Mikewa tai tashiga taka rawa, Ammi na dariya ahankali Itama farin ciki fadade akan fuskarta. 

“Aamin Hansatu! Aamin. Yanzu sai ki hanzarta ki kai musu, Kuma idan da hali ma so nake kije ki zauna da ita, Kinga shi shi kullum yana fada, Gashi sauran hadiman nata ba wasu manya bane.”

“Zuwa kai ran ki ya dade, Me zai hana? Da yardar Allah zan koma da gari yai duhu.”

“Masha Allah! Toh Allah ya yi albarka.”

Gyaggyara mata komai tayi, Umma Hansatu ta dauka ta nufi sashen Dije, Tana zuwa yau har ciki akai mata iso tashiga. Dije tayi murnar ganin kuloli shake da abinci, Zaman dabaro tayi tashiga ci hannu baka hannu kwarya. Ta kora da kunun tana shiwa Ammi hamdalah. 

“Nagode Umma Hansatu, Allah ya saka da alkhairi.”

Umma Hansatu taita mun addua kafin ta mike ta sauka ta wanko komai, Ta dawo tana mammatsa kafata dakemun ciwo sosai,

“Ai uwar gijiya tace na dawo na zauna dake idan babu damuwa, Nace babu zan dawo idan gari yayi duhu. Hakan ya miki??”

“Kwarai ma kuwa sosai Umma Hansatu, Allah sarki Ammi ina godia sosai. Allah ya saka da alkhairi.. Yanzu ma kiyi zaman ki ba sai anjima ba dan Allah.”

“Tuba nake ranki ya dade, Wai da so nake na dan d’akko abubuwan da zan bukata.”

“Eh da haka! Toh Allah ya kaimu.”

Mun dan jima muna hira sama sama, Kafin Umma Hansatu tayimun sallama tatafi. Ni kuma na bararraje awajen raina cike da dadi, Inata sakawa Ammi da alhairi bisa ga dawainiyar da take yi da ni.

*GIM. SHAHEEDAH!*

Tana tsaye tana kallon bango da alamun wani tunanin take, Can taja tsaki, Ba jimawa suka gama waya da hajian su, Ta Kara bata haku’ri da sake dorata akan yadda zata b’ullowa lamarin, Ajiyar zuciya ta sauke tanata mita kamar zararriya, Harda hawaye, Tana mai jujjuya kanta gwanin ban tausayi,

“Wayyo Allah na, Salman kaci amanata, Ta tabbata kai da yarinyar nan kunyi auratayya. Shikenan ni shaheedah dole na sauya taku. Wayyo Allah na. Mena rage maka da har zaka karo aure? Kodan ba ganina Kayi kace kana so na ba Eh? Kodan auren had’i ne? Salman why? Why? Why?”

Tashiga ball da flower vase din da aka Kawata su a parlorn, Cikin haka jakadiya Abu tashiga kanta a kasa,

“Ranki ya dade gani.”

“Jakadiya kin munafurce ni, Shin nawa aka biya ki akan uban kudaden dana baki da har kika dena kawomun zancen mai martaba Eh? Shigar sa futar sa komai nasa da duk abunda ya aikata nace ko a rubuce ne ki gwajajjala ki kawomun. Ba magana nake miki ba?”

“Tuba nake ranki shi dade. Babu wanda nake kawowa rahotan sashen mai martaba sai ke, Amma Idan k’arya nake a abunda zan fada kisa sarkin yan lufdi ya zanemun duwaiwai. Mai martaba da kansa ba ai keba ya jaddadamun karna kara shiga sashen sa, Iyakata harkar fada da yiwa al’ummah iso bayan haka yace komai ya sahalemun na de nayi na daga ayyukan dana keyi a baya.”

“Ya isa, Salman dinne zai ce ki dena zuwa sashen sa? Salman din ne zaice ya cire ki a al’amuran sashen sa bayaga ison fada kawai? Toh waya dora akai? Idan kikai mun Karya to tabbas zansa amiki jina jina tare da zaman gidan yari na lokaci mai tsawo.”

“Allah yaja da ran gimbiya, Abunda labbana suka furta gaba d’aya babu karya jikin sa. Falaki da Alhassan babban bafade, Su mai martaba ya dora akan komai nasa da yankin kofar kudu baki d’aya..”

Hannu kawai shaheeda tai mata alama data tashi taje, Jakadiya na fita shaheedah ta rafka tagumi tana jijjiga kai,

“Lallai Salman… Cin amanar har ya kai haka? Wacce irin soyayya kuke  haka da har cire jakadun ka daga bakin aiki.?”

Kwalawa hadimarta kira tayi tazo jikin ta na rawa, Ta shiga umartar ta kan leken asirin da zatai mata akan shige da ficen Salman,

“Sadiya sunan ki ko?”

“Eh ranki ya dade.”

“Yauwa ki kula sosai da duk abubuwan dana gaya miki, Karki batamin aiki kin daiji labarin abunda nayiwa Batula data batamun aiki ko?”

“Eh ranki ya dade, Insha Allahu zaki same ni me cikar aminci da gaskiya.”

“To tashi kije.”

Fita tai, Ita kuma shaheedah ta shige cikin dakin ta tana kokarin sake kiran ta hajiarta a waya.

*F A D A *

GABA d’aya an hallara anata fadanci, Wani zancen Salman ya tanka wani yai shiru, A haka har aka kammala. Manyan yan majalisa suka zauna. Don sake zantawa da sarki zama na biyu. 

“Sarki na sauraron ku. Ayi a gaggauce saboda yaje ya huta.”

Chiroma ya matsa gaba yana rissinawa,

“Allah yakara maka Lapia jibi ne daurin auren nan dakace ka amince.”

Nan Kowanne ya dauka wambai nayi, Galadima na karasawa. Salman dai duk yana sauraron su har suka kammala. Yai gyaran murya yana cewa,

“Toh dik naji batun ku.. Kuma… Na amince da fari sanda kukai min zancen ban tubure ba nace na yadda a auramun su, To bayan munyi haka, Sai naji sha’awarar karanta rayuwar sarakuna na baya na yankin basannabas, Na karu kuma na ilmantu sosai. Waziri ka karanta ko?”

Waziri ya kad’a kai cikin tabbartawa, kamar gaske. SAS ya cigaba da cewa,

“Na kwadaitu sosai da yanayin tsarin mulkin su, Musanman tsatson Masekiri Tajiri, Suna mulki ne bisa tsari da bin doka, Kuma dokar ta hau kan kowa komai girman rawanin mutum , Kai Allah ya jikan magabatan mu…”

“Aamin. “

Suka amsa baki d’aya, Kowannen su ya gaza fahimtar inda zancen SAS ya dosa. Murmushi yayi kafin ya cigaba da cewa,

“Batin na karo aure babu.. Bank’i ba nan gaba Idan ni na canza ra’ayi, Wanda gaba d’aya yanzu dai ni Salman ‘Da ga Aliyu jikan Salmanu babban Da ga Ibrahim… “

Bai karasa ba galadima ya mike har yana tuge rawanin sa,

“Akan wane dalili? kai ka isa ka ki amsar abinda muka yanke…?”

“Na isa Baba.. Duk wani hukunci da za’a yanke inde akwai cutarwa aciki magabata sun rawaita cewa Kayi fatali dashi.”

“Bangane ba ranka ya dade… Shin wanene zai cuce ka mai martaba? Waya isa balle har ya isar?”

Cewar waziri yana kallon su galadima ta wutsiyar idanu. SAS ya daga kai yana dan sake daga muryar sa sama,

“Inaga ba kuma lura da yanda aka sauya tsarin kayan cikin fada ba…”

Yana rufe baki Kowanne ya shiga duddubawa, Sosai gashinan an caccanza yanayin zaman wasu abubuwan, Duk kuwa da dai kayan ciki ne dai, Salman ya cigaba da,

“Shekaran jia ne nasa dogarai su canza yanayin tsarin saboda karbar bakuncin matemakin shugaban kasa, Badan ya fa’di zuwan nasa a kurarren lokaci bama da sabbi za’a zuba komai. Toh Allah cikin ikon sa, Dogarai na caccanza tsarin ciki ne sai sukayi gamo da wani bakin tsibbu.”

“Ba’kin tsibbu ranka ya dade?”

“Kwarai waziri.. Gaba d’aya duk kusurwoyin ma’ajiyar abu an dasa tsibbu a kasanta, Wani abun tsoratarwar ma shine har kasan kujerar da nake zama sai da aka hak’o wata kwalba mai dauke da layoyi wadda gaba d’aya nasa an bincikamun duk dan a cire ni ne daga karagar mulki, A cutar dani a kuma lahantamun rayuwa… Waziri dakai ka’dai na yadda shin a ganin ka zan yadda da zancen su wambai na cuci kai na na ki kuma koyi da yadda sarakunan magabata su ka zartar da tsarin mulkin su?”

Jikin waziri sai ya nemi fara rawa yai azama ya dawo gaban SAS yana rissina masa,

“Allah yaja zamanin ka.. Ban fahimce ka ba, Ace ina cikin masarautar nan aka aikata wannan danyen aikin? Toh Allah ya Kara maka Lapia shin anga sunayen wanda suka binne tsibbun?”

SAS ya girgiza kai yana murmushi,

“Waziri.. Kwantar da hankalin ka, Lapia lou nake, Kuma na tabbata babu sunan ka acikin wanda suka yi, Koma dai suwa nene yan majalisar sarki ne. Bazan kira suna ba, Ko suwaye sunsan kansu, A takaice dai nasa an kona duk abubuwan da aka tono…  Saboda haka maganar karo aure bazan yi ba gaskia.”

Wambai ya sake mikewa yana kumfar baki,

“Toh kai kanada yakinin an binna ne don a cuce ka? Kuma ni banyadda ba gaskia wannan zance ne irin naka don ka kawo yadda Za’a fasa auren ka. Ko kuwa?”

Su Galadima suka fara tofa albarkacin bakin su, Waziri yai musu alama da suyi shiru. 

“Ranka ya dade ka gafarce ni, Gaba da baya kanada makiya a masarautar nan, Baka gani wasu ne daban suka so suga bayan ka..?”

“Waziri!”

“Allah ya ja zamanin adalin sarkin mu.. Tuba nake.”

“Bakai lefi ba Waziri… Da kai d’aya tak na yadda kaf masarautar nan. Kuma nasan ba zaka hada kai da wasu ba don acuce ni, Saboda haka ka kara sanarwa su wambai nace bazan karo aure ba, Wannan magana an fasata, Domin Za’a iya auramun wa’enda za’a hada baki dasu, zasu shigo su kashe ni, Allah basshi nan gaba idan nayi ra’ayi don karan kai na na karo auren.”

Gyaran muryar da yai ne, Dogaran sa suka yayyabe shi ya mike ya fice hankalin sa kwance yabar su waziri suna tattaunawa akan zancen, Kowanne tamkar zai amayo wuta dan bakin ciki. 

“Sannu ahankali kunata batamun shiri, Agaskiya nayi dana sanin hade kai na da ku..”

Cewar Waziri cikin tsantsar bakin ciki, Su wambai suka shiga bashi hak’uri, Waziri ya tuge rawani ya shiga fiffita dashi yana sharce gumi duk kuwa da na’urar dake sanyaya fadar. 

“Ranka ya dade.. Ni Ina ganin hargagiya ce kawai don kada a aura masa su… “

Waziri ya watsawa wambai dayai maganar harara yana sake sharce gumin fuskar sa,

“Kai dai wani lokacin idan kayi magana sai na rasa tayaya kake bari tafito saboda rashin amfanin ta. Hargagiya? Bakasan ire iren abubuwan nan zasu zama yadena yadda dani ba? Idan ba yarda a tsakanin mu kuma kuma taku batayi kyau ba kuwa.”

“Tuba nake ranka ya dade… Ni sai nake gani kamar yaron nan tunanin sa ya fara dawowa, Du bada yadda yake magana cikin izza.” Cewar chiroma.

“Anya kuwa? Banaji gaskia, Domin da hankalin sa ya dawo dole zai waiwayi mahaifiyar sa….. Yan uwan sa, Dama karbar ragamar mulki gaba d’aya batare da bata lokaci ba. Gigin auren sa da yarinyar canne yake dibar sa.”

Waziri ya bashi amsa cikin tabbatarwa, Duk suka aminta da zancen sa, Kowanne ya shiga tofa albarkacin bakin sa. 

“Yallabai ya za’ai kenan yanzu? Ina mafita?”

Wambai ya dukar da kai kasa yana tambayar Waziri cikin girmamawa. 

“Maganar ‘karin auren sa a soketa gaba d’aya kawai, Kowa yaje yai tunanin wani abun da zamu yi amfani dashi wajen yakarsa har ya hakura ya sauka ko mu hada kai da sauran yan majalisa a sauke shi..”

Da haka duk suka tsaida magana d’aya, Maganr karin auren SAS an fasa, Sai sun bullo masa ta wani wajen da bai Zata ba.

Duk abunnan da suke SAS na saurarar su yana kuma ganin su ta na’urar computer. Murmushi yai irin na gefen bakin nan kafin ya sake danna madannin nan dake adana masa dukkanin bidiyon sirrin sa…..

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 31

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 21

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR…

KIBIYAR AJALI 27

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 18

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…