KIBIYAR AJALI 29

Advertisement

 _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B29_ 

*SAS*

Advertisements

Yana kishingid’e akan d’aya daga cikin saitin kujerun dake dakin sa, Dake wani lokacin idan kambun mulkin suka motsa masa to ko dijen sai dai tazo da kanta wajen sa, Ya kan debi lokuta shi kadai yana dik wasu harkoki da suka shafe shi. Toh yanzun ma shi kadai ne, Ya tsurawa tv idanu can yayi tsaki ya kasheta gaba d’aya. Wayar sa ya janyo ya kira Yareemah Khal. Wanda ke Abuja har yanzu, Khal ya gayda shi cikin girmamawa,

“Kana lapia…?”

“Lapia qalau ranka ya dade, Ya wajen su Ammi?”

“Tananan qalau, Duk lapiar su lou Khal.”

“Ya gimbiyar mu, Ina fatan anata kulamin da little nephew/niece dina?”

Daria mai sauti SAS yayi, 

Advertisements

“Alhamdulillah uncle Khal… Ya Abj da Dr.?”

Khal a bangaren sa kuwa shafa k’eya yayi yana tuno shagwabar data gama masa yanzu a waya.

“Lapia Alhamdulillah Yaya.” 

Ajiyar zuciya Salman ya sauke yana jan kasan leben sa,

“Ka jini shiru kwana biyu ko?”

“Tuba nake ranka ya dade. Ai na kikkira baka d’auka, Sai na kira falaki yake cemin lapia qalau wani aiki ne ya sha maka gaba.”

“Wallahi kwana biyu inata yadda zan bullowa lamarin su waziri ne, Alhamdulillah dai plan A was successful. Zancen aure an soke shi, Ina jiran naga iya gudun ruwan sune kafin na saki babban bomb din ya tarwatsa su..”

“Allah sarki Yaya! Allah ya temaka ya bada sa’a da nasara akan abunda aka sa agaba…”

“Aamin Khal! Afuwan ka kara dakatawa dai nan gaba kadan zaka dawo..”

“Babu komai ranka ya dade, Allah ya kai mu lokacin ya dora mu akan makiyan mu, Aamin.”

“Aamin Khal…. Na Dr.”

Murmushi Khal yayi wanda har sai da SAS ya jiyo shi, Sallama sukai bayan sun taba hira kadan. Daganan SAS ya kira Abdullah a waya nanma suka gaysa. Yana kammala duk wayoyin da zaiyi ya jingina kansa sa da kujera yana lumshe idanu. So yake kawai ya had’u da Ammi ya ganta ido da ido, Duk video calls din da sukeyi yafuso yaganta a zahiri, Tun hawansa yana sarki bai kara sanyata a idanun saba (Zahiri) har rana i ta yau…

  ***••.    ***••.     ***••. 

  

Fitowa tai daga sashen ta sanye cikin kayan alfarma, Taci ado sai yauki take yi, Dogarai sai kirari suke mata,

“An gaishe da gimbiya matar mai martaba, Diyaga sarki Ibrahim hashimu na Bullo. Kun gaji sarauta tun zanin goyo. Gyara kintsi dakyau.”

Suna tafe itada Sadiya hadimarta zasuje sashen mai martaba, A hankali shaheedah kewa sadiya magana ba zaka taba cewa tana motsa baki ba,

“Kince har yanzu bata fitowa ko?”

“Eh ranki ya dade, Bata fitowa kwata kwata, Wasu na zargin kila bata cikin masarautar ne.”

Murmushin fuskar shaheeda ya fadada jin an ambaci kila dije bata gidan ne. Zata shiga bangaren Salman ta juya ta kalli bangaren dije ta zabga masa harara sai kace dijen tagani a Zahiri,

“Shegiya! Allah yasa kinbar masarautar gaba d’aya kenan.”

Shigewa ciki tayi kanta tsaye, Ta kwankwasa dakin Salman, Yana hakimce ya gaji ya kunna tv yana kallo. 

 “Yes.. Come in.”

Shiga shaheedah tayi tana rangwada, Salman ya d’ago yana kallon ta, Tayi kyau sosai tamkar saliha, Amma a zuci ba Allah a ranta. Tuno lokacin da aka fara hadasu aure yayi, Shiru shiru ga kyau ga iya kwalliya. Ashe ashe ba son tsakani da Allah take masa ba, Ta hada hannu da miyagun mutanen cikin masarauta dake nufar sa da sharri da mugun alkaba’i, Ya sake narke idanu yana kallon ta ta mika masa hannunta ya ri’ko yana danne bacin ransa. Zama tai agefen sa tana kallon sa. Ba gilashin data saba ganin sa dashi kullum, Karo na uku kenan da tadena ganin sa dashi a idanun sa. Shi kuwa Salman kallon ta dayake tambayoyi ne fal a kirjin sa akanta. Shin meyasa ta masa karyar shine baya haihuwa? Take cutar sa ta bayan fage? Ajiyar zuciya ya sauke jin tanata masa magana,

“Na’am! Shaheedah….”

“Darling…!”

“Ya kike?..”

“Lapia lou, Ina kewar ka sosai my king..”

Murmushi ya ‘kakaro yana duban ta ahankali,

“Nima haka…”

“Ina mamakin canzawar ka kwana biyu.. Ka dena using glasses dinka, Sannan yanayin ka ya canza sosai.”

“Ko? Bakyaso na dena?”

Ya samu kansa da tambayar ta haka yana satar kallon agogo gudun kar Dije ta shigo. 

“Nooo! Ya kara maka kyau hakan. Kawai dai ka dena saurin hannu kaji?”

“Insha Allah bazan kara ba.. Bakin ce kin yafemun ba ko?”

“Na yafe..”

Tafada tana dora kanta akan kafa’dar sa. 

“Inada meeting… Shaheedah.”

“Okay! your honor, Zan…”

“Zan zo later.”

Shaheeda ta fadada murmushin ta, Zancen dijen da zata kawo ma tsabar farin ciki sai ta mance, Ta futa da sauri bayan ta masa sallama ta koma bangaren ta. Yana ganin tatafi ya nufi dakin da Khadija ke bacci cikin rawar jiki…

*GIM. KHADEEJA*

Cikin bacci na jiyo tamkar anamun susa, Jin matse matsen yayi yawa hakan yasa na bude idanu na dake nauyin bacci, Salman na gani akaina yana murmushi, Ya lakuce mun kumatu da yatsan sa na dama yana goga hancin sa akan nawa,

“Ya Rouh! Rise and shine.”

“Oh no… Bacci nake ji fa, Ka kyaleni pls.”

“Awa nawa kenan kina baccin? Ai yayi yawa.”

“Uhm.. Uhm”

Na fada Ina turo baki gaba, Ya kai mun rantsattsiyar sumba a gefen kumatu na, Can ya dawo kan mara ta, Da tsakanin kirji na, Na shiga ture bakin nasa ina yatsina fuska, Santar kunnena ya zura bakin sa yana min magana mai kashemun jiki, 

“Dearest one… I keep telling you, I like adult only things…”

Juyawa nai gefe na bashi baya inason nayi wani baccin, Ya sake nanuke mun yana shafa jiki na, Ina mamakin yadda baya gajiya da nanikemun kamar gum, Dole na kyale shi muka yi baccin mai dalili gaba d’aya. Muna tashi na shirya shi ya futa Wai zai duba shaheedah, Kishi duk ya kamani. Rankwafo wa yayi yana daria ahankali,

“Meya faru wifey…?”

“Yanzu duk kwalliyan nan na shaheeda ne?”

“Laa Zawjati tafara kishi na..? Alhamdulillah Allah kaine abun godia.”

Na yatsina fuska, Ina tabe baki na,

“Wanda kakeso ai shi kakewa kishi…”

“Lalle nazama dan gata tunda baby na kishi na. Kibari na dawo kwalliyan da zan miki… Zakisha mamaki.”

Ficewa yai yana dariya, Na bishi da harara kafin na shige band’aki nasake watsa ruwa saboda yadda nakejin zafi dukda na’urar dake sanyayani. Ba jimawa sosai Salman ya dawo daga wajen shaheedah sallamar sa kawai naji, Ya sake nunakeni yana shinshina gashin kai na.. Nai Ajiyar zucia kawai ahankali nace ‘Allah ya hada ni da maqalalle…’ 

Shi kuwa Salman yana jikin Dije yana tariyo tambayarsa da shaheedah ke tayi akan jakadiya Abu. Meyasa zai cire ta daga wasu abubuwan nasa? Shi kuma Salman yasan a asirri sukai magana da jakadiya, Kuma hakan dayai yayi ne kawai saboda karta fuskanci dije nada juna biyu, Dole ne yaje yai bincike akan jakadiya Abu, Bai taba dauka makircin nata ya kai har haka ba. Wato dai gaba d’aya masarautar nan sai ahankali bakada sirri sai kayi takatsantsan. 

*WASHE—GARI*

Bayan fitar Salman fada abadan, Nayo wanka cikin wani lace d’inkin bubu, Ban daura d’ankwalin ba nade yafa mayafi karami akai na. Umma Hansatu na kitchen tana aiki, Da sauri tafuto muka gaysa, Na shiga tunanin abinda zan ci,

“Ranki ya dade me za’a dora miki..?An dai kammala abincin rana.”

“Sannun ku Umma Hansatu! ni ko wainar fulawa na samu ta manja data ji kayan hadi da yajin tafarnuwa Nagode.”

“Yanzu kuwa ranki ya dade…”

Ina tsaye tana soyawa inaci don zalama, Sai da naci sosai sannan nace ta toyamun sauran ta zuba a plate akaimin sama. Sama na koma na zauna a parlor ina kallon drama din da ake na turkish ‘forbidden love’ Ji nai sama sama tamkar ana magana a kasa . Na cigaba da cin wainata ina korawa da ruwan zam-zam me tofi. 

Hannu na na hagu rike yake da wayata. Tun dazu nake kiran wayar Ammi bata shiga, So nake mu gaysa dan duk yau banji muryar taba, Don kullum sai na kira na gaysa da ita, Tunda bana zuwa sashen ta yanzu. Na ajiye wayar a Gefe na kanannada wainar na doni yajin tafarnuwa nasa a baki na. 

Hadimata Nabawiyya ta kwankwasa kofa ta shigo cikin ladabi,

 “Allah ya kara miki lapia da nisan kwana.. Kinyi bak’uwa, Tana kasa.”

Ai da sauri na dire plate din hannu na, Na wanke hannuwa na , Nai sauri na shiga daki nayi brush na kurkure da mouthwash. Turaruka na sake faffesawa sannan na gyara d’aurin mayafin jiki na, Zaman kadaici ba dadi, Duk yadda akai wata dana sani ne tazo, Da sauri na sauka kasan ina harhada matattakalar bene.

 “Ahhhhhhhhh! Malama Mardiyyah naaaa! Wayyo Allah dad’i. Yau gani ga malama na. Malama shigo.”

Da sauri na rungumeta ina kamo hannunta, Domin har cikin bargon jiki na da jini na nake jin Malama Mardiyya. Babban parlorn kasa muka zauna, Malama sai kalle kallen ko’ina take. Aka kawo mata kulolin abinci aka cika gabanta dashi, Sai kallon ta nake. Tunda tanada tsafta sosai da kwalliya, Da tadan manyanta ma batadena ba, Daman karamun jiki ne da ita. 

 “Malama! Barka da rana…!”

Na fada ina tsugunnawa.

 “Ahh meye haka Khadija? Dan Allah tashi, Haba, Ai kin wuce gaisuwar tsugunno yanzu, Balle keda ke auren sarkin mu baki d’aya.. Ina zuwa wani awaje yace ayimin iso.”

 “Malama ya bayan saduwa? Ai nayi fushi sosai.. Dan ma dai.. I love and miss you so much. So na dai na fushin yanzu.”

 “Alhamdulillah! Kiyi hak’uri Khadija.. Abubuwane sukai yawa, Na canza layi na wanda nake da number ki, Tun sanda na kawo ki ki kai post-utme dinnan. Na bar kano.”

Tunda Malama mardiyya ta fara magana harta gama kallonta kawai nake ina murmushi, Ganinta nake tamkar yayata ta jini, 

 “Allah sarki Malama… Insha Allah khair! Kin koma lagos kenan?”

Malama mardiyya tai murmushi tana kurbar orange lemonade din hannun ta,

 “Eh mun koma, Canjin aiki akaiwa Abban su, Kai Masha Allah! Gidan ki yayi kyau Khadija.. Kinga ribar hak’uri ko? Ai nagaya miki akwai rana irinta yau da zaki bani labari.”

Nayi daria kawai nima ina bin parlorn da kallo,

 “Ai kuwa dai kin fada malama..”

Na dan bata labarin auren a takaice, Hararata Malama Mardiyya tai tana danna cinyar kaza abakinta,

 “Yimin shiru kafin na zane ki.. Da alama a makaranta na manta ban taba dukan ki ba, Kila sai yau. Yo ai babbar sokuwa se ke.”

 “Meyasa kikace haka Malama..?”

 “Saboda ba yadda za’ai dan ya tsaneki ne zai auro ki ya narka miki wannan gidan da uban dukiya duk ke kad’ai? Ahh sannu, nace sannu.”

 “Hmm! Malama bakisan wahalhalun rayuwar dana shiga bane.. Jini fa Malama, jini aka sakarmun naita shan wahala na dauka period ne. Ka tsorata, Da yawan jin wari gaba d’aya banajin k’amshi. Ga rashin bacci da faduwar gaba. Malama nasha wahala.. Amma dai Alhamdulillah komai ya wuce.”

 “To ai Alhamdulillah tinda yanzu komai ya shige. Insha Allah komai yazo karshe Khadija. Ai ke din *KIBIYAR AJALI* ce, Wadda sulke baya tare ta sai ta wuce.. Kiga tsallake tuggun Gajiyalle ma bare nasu? Yo me zasu miki? Kedin wacce iriyar gwagwarmayar rayuwa ce baki gani ba? Wanda da Allah ya kawo k’arar kwana ma da yanzu sai labari.. Amma gaki nan tamkar me ran k’arfe. An buga dake an barki ya zasuyi dake uhm? Sai kallo daga nesa yar kanwata.”

Nayi murmushi kawai.. Inata tuno sanda taketa wahalhalu da ni a Durbun.

 “Tunanin me kike Khadija..?”

 “Babu komai Malama.. Kawai na tuna baya ne.”

“Kai abincin nan yayi da’di… Yau gani a gidan Khadija na.. An cikamin gabana da kayan kwalam da makulashe na gidan yan gayu..”

Nayi daria kawai ina lankwasa hannaye na,

 “Ni kam ina Malam auwal?”

“Wai wai Wai.. Allah sarki Auwalu.. Wai.. Ai inaga rabona dashi wajen shekaru biyu kenan. Yace dani zai koma can shagamu dangin mahaifiyar sa zaiyi aure ya kuma fara kasuwanci, Saboda teaching dinnan ba inda zai kai shi..”

 “Allah sarki Malam Auwal.. My first love..”

Muka sheke da dariya..  Malama mardiyya tacigaba da cewa,

 “A’ina ya zama first love din naki? Mu da kika ‘kimu..? Kai Allah sarki shima auwal seda na ce masa karfa kiyayyar da kakewa Khadija ta juye ta koma soyayya yace aa wallahi.. Sai gashi yana roko na wai dan Allah naje gidan ku a bashi ke ya aura.. Nace wa? Badani ba wallahi..”

“Allah sarki Malam auwal..”

 “Ya durbun..? Kin koma kuwa?”

“Aa wallahi tun bayan tahowata ban koma ba.. Zan je, Amma sai nan gaba kadan.”

 “Allah ya kai mu. Allah ya dafa miki ya dora ki akan makiyan ki Khadija..”

 “Aamin Malama mardiyyah..”

“Ko sai kin sauka lapia ba Insha Allah..”

Na rufe fuska ta da tafin hannu wai ni kunya, Malama mardiyya tacigaba da cewa,

“Ai kinsan rannan sai bayan tafiyar ki naita dana sani nace ko number ki ban karba ba, Toh Ina can ina mamakin wayewar yar k’anwata.. Ubangiji Allah yasa mutu ka raba keda mai martaba Khadija, Aita haku’ri, Rayuwar aure gaba d’aya hak’uri ce.. Kinji?”

Hira muka shiga yi sosai da Malama tacigaba da bani shawarwari akan zamantakewar aure, Na Karu Sosai da bayanan ta, Kamar a makaranta haka tadinga mun bayanin komai dalla dalla, Mun jima muna hira sosai ta kakkawomun magungunan mata irin na yoruba dinnan, Da turarukan wuta kai harda na mopping da wanki da wanka na *yerwaincense&more..* Allah sarki bata masan inada wasu turarukan ba na yerwan. 

Nima na hau sama na hado mata shatara ta arziki domin Malama mardiyya idan ka cire kawunina da suke a raye da Salman da Ammi sai ita a wanda nake kauna gaskia. Zan iya cewa ma banda sama da ita ta wani fannin.

Har bakin gate na rakata, Kowannen mu fuskar sa dauke da hawaye haka muka rabu.. Domin jirgin safe zata bi ta koma birnin ikko. Amma tamun alkawarin zata sake dawowa Insha Allah, Nima nace mata idan na sake ziyarar lagos zanje wajenta tunda mun karbi lambobin juna….

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 33

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 16

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 16…

KIBIYAR AJALI 32

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…