Advertisement
_I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_
_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_
_B30_
Advertisements
*GIM. SHAHEEDAH…*
Abubuwa ne suka taru sukai mata yawa. Ta kasa gane kan Salman, Duk sanda zata sa amata iso sashen sa sai ace sarki ya hana kowa shiga yana wani uzuri, Sai daga baya kuma yazo da kansa, Idan yazo kuma babu wani abu dake shiga tsakanin su sai dai ya tsiri dakko ipad dinsa yace wani aiki yake yi, Daga karshe tatashi tashige daki idan tafi to kuma baya nan ya tafi.
“Salman me kake boyemin ne?”
Ta tambayi kanta tana nazarin duk lokutan da suka ha’du uzurorin da yake bata duk d’aya ne, Gashi tamkar an sauya masa halaye. Babu wannan yawan ciwukan da yake. Kuma kullum kamar ransa a bace yake yana kokarin danne wasu abubuwan.
“Salman me yake faruwa ne…?”
Ta sake jefo wata tambayar tamkar shidin ne agaban ta. Mikewa tai tsaye tana kiran sadiya hadimarta,
Advertisements
“Ga ni ranki ya dade…”
“Sadiya… Kin bincika abunda na sa ki?”
“Nayi uwar daki na. Tabbas ance gimbiya kh…”
“Karki kuskura ki karasa sunan gimbiya kaza, Wacece gimbiya? Ta ina tazama gimbiya? Sama taka? Kodan an dosanata a ta biyu? Mata ba jinin sarauta ba komai ba, Yar kauyen kayau. Kizo gabana kina kiranta da gimbiya? Karna kara jin labban ki sunyi gigin kiran Khadija da gimbiya.. Kina ji ai ko?”
“Na fahimta gimbiya, Akasin labbana ne, Tuba nake ranki ya dade, Allah ya huci zuciar ki…”
“Sanar dani abunda kika jiyo.”
“Ranki ya dade…. A binciken danayo na kuma harhada da wanda akawo mun an tabbatar mun kh.. Khadija na nan cikin gidanta babu inda taje, Domin ance Umma Hansatu hadimar mai babban d’aki itace ke zaune da ita acikin gidan. Wasu sunce tayi wata bakuwa kwanakin baya harta rakota ma izuwa gate din sashen na su… Kuma ance takara murjewa tayi b’ul b…”
“Ya isa! Jeki.”
Sadiya ta mike ta fice, Shaheeda tai zaman yan bori tana jujjuya kai,
“Takara murjewa tayi ‘bul ‘bul… ?Hakan nada nasaba da Salman kenan? Shysa muke wasan ‘yar buya da shi? Nooo it can’t be.”
Waya ta janyo har zata kira hajian su sai kuma ta fasa, Tatafi wajen su Mama Huwaila ko zata jiyo wani labarin awajen su.
*GIM. KHADEEJAH.*
Ina zaune bayan nagama karatun alqur’ani, Waya na janyo na dan fara karanta hausa novels na online, Can na ajiye na koma parlor na zauna jira nake Umma Hansatu ta dawo daga gaisar da Ammi data je. Ba jimawa kuwa ta dawo, Sai dai yanayin fuskar ta gaba d’aya ya canza.
“Umma Hansatu lapia?”
“Lapia qalau ranki ya dade, Da akwai abunda kikeso ne yanzu na tashi nayi?”
“A’ah babu komai, Ya Ammin? Kince ina gaishe ta sosai ko?”
“Kwarai na fada Allah ya kara miki lapia, Tana amsawa sosai tace tanai miki ya jiki. Tayi miki adduoi sosai..”
“Masha Allah, Ina godia kwarai da gaske, Duk kalau suke ko? Kwana biyu inata kiran wayar ta bata shiga.”
Umma Hansatu tayi jim tana jujjuya kai,
“Menene Umma Hansatu?”
“Babu komai ranki ya dade.. Tace dai karna fada amma bazan iya kin fada miki ba, Uwar dakin nawa na kwance itama ba lapia.”
“Ammin..?”
Na tambayeta a matukar dimauce, Gyada Kai tayi cikin tabbatarwa.
“Zazzabi ne, Tashi wai taifol ne (typhoid).”
Mikewa nai na shige da’ki, Na kasa samun nutsuwa na kikkira Abdullah wayar sa off. Dan haka na kira Salman bai daga ba. Wunin ranar haka na wuni duk banjin dadi. Dakyar bacci barawo ya dauke ni ban farka ba sai tashi nai naji ana kiraye kirayen sallar magriba. Bandaki na shiga nayo wanka da alwala. Nayi sallah na Idar ina zaune akan dadduma Salman ya shigo,
“Barka da dawowa…”
“Barkan mu Zawjati.. Ya jikin naki? Ai na shigo naga kina bacci na koma.”
“Eh wallahi banmasan ya dauke ni ba, Da ina kasa tare da Umma Hansatu..”
“Okay! Kinci abinci? Me kikeson kici uhm?”
“Babu komai.. wai Ammi ba lapia? Ko bakasani ba kai ma?”
“Kai wannan Umma hansatun ta aminta dake, Ammi fa ta gargadeni kada na gaya miki, Ashe Sai da Umma Hansatu ta gaya miki?”
“Meyasa Za’a boyemun rashin lapian Ammi? Why?”
“Bakomai… Ammin ce tace dan karki tada hankalin ki ne, Wajen kwanaki uku kenan tana zazzabi a tsaitsaye typhoid ne da malaria.”
“Allah yabata lapia yasa kaffarane.”
“Kinason kije kiga jikin tane?”
Da sauri na gyada kai ina komawa kusa dashi, Ya janyo kafadata yana rungumeni,
“Idan aka idar da sallar ishai sai kuje da Umma hansatun, Tunda naga kin damu da yawa. Kinsan wani abu kuwa?”
Na girgiza kai ina kallon sa,
“Yau birthday din Ammi, Yau ne ranar da aka haifeta bazan taba mantawa ba, Mai martaba da kansa yake tsara celebrating birthday dinta duk shekara…”
“Allah sarki, Allah ya gafarta masa. Mezan bata as present?”
“Karki damu na riga na shirya komai nasa an kai inji ki, Nine tawa kyautar sai kunje zakiga wata iri zan bata.”
“Dan gayamun mana.. Haba Zawj..wayo?”
“Khal.. Khal zansa ya kirata su gaysa. Kinga dai shine wannan babbar kyauta duk duniya da Ammi zata fiso.”
“Gaskia kam, Kai Allah sarki Ammi..”
“Tohm ki shirya, Bara naje daki na kira shi.”
“Okay love…”
Harya fita ya dawo yana sosa idonsa d’aya nasan wani wayon zeyi mun.
“Zaki biyani kayan gift din danasa aka kaiwa Ammi nace inji ki.”
Nayi rau rau da idanu ina cuno baki gaba,
“Ni.. Ni mezan baka? Ai bance ka bayar ba wannan duk salon wayo ne, Daka barni ai da nayi da kai na.”
“Noo.. Ai aikin gama ya gama, Idan kuma kinason na kirata nace bake kika aiko ba to…”
“Ahh… Yanzu nawa zan biya?”
“Habawa Yarinya, Waya gaya miki kudi nake so?”
Na shiga raba idanu, Ina harhade hannuwa,
“Toh me kakeso…?”
“Ke nake so…”
“Na’am..? Bangane ba”
“Nace ke nakeso kawai… Ina kaunar ki sosai Zawjatii, Na kan ware lokaci nayi ta tunanin ki haka kawai, Ga ki dai na aure ki ke mallaki nace, Amma kullum kaunar ki kara ninkuwa take cikin zucia ta.”
Yak’arasa fada yana sakar mun kiss agefen wuya na,
“Kamshin ki…”
“Dariar ki…”
Nanma ya dawo kan baki na.
“Idanun ki….”
Ya fada yana sumbatar idanu na, Wanda na rufe su ruf ina shakar kamshin turaren sa.
“Komai naki… Komai naki yana tafiya da ni Deejah na! I love you with every fiber of my being.”
Ya karashe zancen yana rungumeni tsam a jikin sa, Nasa hannuwana biyu na riko bayan sa nima. Ina mai kwantar da kai na akan kafadar sa.
“Nima Ina kaunar ka sosai zawj… Ina maka kaunar kauna marar gauraye. Honey bunny! I love you as high as I can reach, as far as I can see, to infinity and beyond…”
“Nagode k’warai zawjati… Kin biyani da kalamai saura daya aikin ladan kai gaskia kin cika yar albarka.”
Na matsa ina daria, Shi kuma ya mike.
“Bara na kira Khal. Sai kuje idan anyi sallah. A gayshe ta sosai. Nayi baki a fada suna jira.”
D’aga masa kai nayi ina murmushi,
“Okay honey bunny, Allah yabada nasara, Ya dawomin da kai lapia.”
Ficewa yai yana dagamun hannu, Ni kuma na shige bandaki don tsarkake jiki na. Canza kaya nayi jikin doguwar riga abaya baka. Na yane kaina da mayafin rigar. Kiran sallah akayi. Nayi sallah hade da adduoi na, Na shasshafa turaruka, Na murza yar powder da da man lebe. Jiki na har rawa yake saboda son ganin Ammi. A kasa na tarar da Umma Hansatu itama ta idar da sallah,
“Muje wajen Ammi Umma Hansatu.”
“Toh ranki ya dade. Allah yaja zamanin ki..”
*Shi kuwa Salman yana shiga dakin sa ya kira Khal da hannu d’aya, D’aya hannun kuma yana dudduba closet dan saka kaya marar nauyi,
“Wa’alykm Salam Khal..”
“Yaya.. Barka da dare.”
“Barkan mu. Kaga na kira ka da daddare ko?”
“Ah tuba nake ranka ya dade, Ai dare beyi ba, Da fatan komai lapia?”
“Lapia qalau.. Ka tuno yau wacce muhimmiyar rana ce?”
Khal ana bangaren ya shiga jujjuya kai yana son tuno ranar amman ya kasa.
“Allah yakara maka lapia, Tuba nake na kasa tuna wacce rana ce.”
“Yau birthday d…”
“Birthday din Ammi… Afuwan ranka ya dade, Sai yanzu na tuna wallahi.”
“Masha Allah! To yau birthday din Ammi Khal, So babbar gudunmuwar da zamu bata d’aya ce.. Kasan menene?”
“Tuba nake ranka ya dade, Bansani ba.”
“Kiranta zakai a waya, zakaga na turo maka wata number ta message, Itace number Ammi, Zan hado dana Abdullah ma ka kira shi daga baya ku gaysa, Saboda yanata processing harkar admission dinsa inaga Manchester zai tafi yayo wannan civil engineering dayake mayatar so.”
Jin shirun Khal, Salman sai ya rude ya shiga jin ko lapia? Cikin shesshekar kuka Khal yace,
“Bakomai! Kawai na samu kai na cikin overly emotional.. Nagode sosai Yaya, Zan kira insha Allah yanzu kuwa. Nagode nagode.”
“Sai ka mata ya jiki daga nan..”
“Batada lapia?”
Khal ya tambaya SAS cikin kidimewa,
“Eh kwana biyu tanata fama da zazzabi, Amma da sauki ai Alhamdulillah!”
“Tohm Masha Allah! Allah ya Kara mata lapia da nisan kwana mai amfani, Aamin.”
“Aamin”
Sallama sukai wa juna, Salman ya shige toilet Shi kuma Khal ya shiga kokarin kiran layin Ammi.
*MAI BABBAN DAKI….*
Kishingid’e muka samu Ammi tana lazimi, Sanye cikin laffaya, Ta amshi kyakkyawar fuskar ta, Har tadan fada tubarkAllah, Saboda rashin lapiar manyan idanun ta sun kara futowa, Tana hango ni ta zauna tana murmushi,
“Oh ni ‘yasu, Sai da suka sa kikazo? Bayan jan kunnen da nayi, Nasan duk yadda akai mai martaba ne.”
Zubewa nai nashiga gaysheta, Ta amsa cikin fara’a, Umma Hansatu ma ta rissina ta gaysheta tana daria,
“Tuba nake ranki ya dade, Ni ce na sanar da ita, Saboda tashiga damuwa sosai da rashin samun ki awaya.”
“Ayyah… Zo ki zauna Khadija anan, Nan sanyin tiles. Kashe wayar nai sai dare yawanci nake kunnata, Sai dazu nema na kunnata gaba d’aya.”
Komawa nai inda tace din na zauna cikin ladabi,
“Ya jikin Ammi? Allah yakara afuwa yasa kaffarane.”
“Aamin Khadija. Aamin! Ya naki jikin? Allah ya raba lapia, Ya inganta.”
A zuciata na amsa da ‘Aamin’ ina maida kai na tv cikin kunya.
“Harda wahala Khadija? Ashe mai martaba ya sanar miki? Naga abubuwa da yawa, Da baki tashi kanki tsaye ba ai Khadija, Ni wallahi har na mance da ranar, Dake babansu sukaga yanayi shine suka ara suka yaba.”
“Babu komai Ammi, Allah yaja kwana ya karo wasu shekarun masu albarka Aamin”
“Aamin.. Akwai abinci a kitchen Hansatu hado mata, Khadija me zaki ci?”
“A koshe ma nake Ammi, Amman a zuba min kadan”
Tashi Umma Hansatu tayi ta kawomin, Ta kuma bamu waje, Parlor ya zama mu biyu kawai. Ahankali na bude flask din jollof rice da plantain, Se kuma soup din kifi a gefe. Cikin haka wayar Ammi tashiga ‘kara, Ta daga tana kallon screen din ta ajiye,
“Banason d’aukar number da bansan taba. Maybe wrong number ne.”
“Ammi da dai kin dauka..”
Nace ina kokarin cusa lomar shinkafa a baki na,
“Toh ai naga sabon layi ne fa babu wanda yasan number..”
Kiran ya yanke aka sake kira tukun sannan ta dauka,
“Assalamu Alaikum..!”
“Wa’alaykm Salam… Ammi.”
Ina daga zaune ina kallon ikon Allah, Ta cire wayar a kunnenta tasake maidawa kana iya jiyo komai rad’au,
“Ammi…! Ammi Barka da dare.”
Hannu d’aya tasa tana dafe kirji, hade da mikewa tsaye,
“Barkan mu dai…”
“Ammi baki gane me magana ba?”
Shiru tayi bata bada amsa ba saboda yadda hawaye suka shiga reto a fuskarta lokaci d’aya, Cikin kuka tashiga tambayar sa,
“Khaleel? Khaleel! Khaleel kai ne?”
“Nine Ammi… Nine Ibrahim, Khal ne Ammi. Ashe zaki gane ni Ammi.”
Shiru tayi tana kuka sosai, Can tad’aga wayar ta mayar kunnenta,
“Kana lapia Khaleel? Ya karatu?”
“Ammi ai na kammala, ‘Dan naki ya zama babban surgeon Ammi..”
“Ma.. Masha Allah Khaleel, Allah yayi albarka.”
“Aamin Ammi.. Happy birthday first love! Many, many happy returns.”
Ai wannan karon gaba d’aya rushewa tai da kukan farin ciki, Ta rungume wayar a kirjinta, Shima anasa bangaren kuka yake marar sauti.
“Ammi R u there.. kina ji? Kina jina Ammi?”
“Ina jinka Khaleel.. Ina jinka, Nagode Khaleel.”
“Toh ya jikin naki? Fatan da sauki sosai ko?”
“Naji sauk’i Khaleel, Na warke kamar banyi ba.”
“Allah yakara miki lapia da nisan kwana mai amfani Ammin mu. Nayi kewar ki sosai. Da Abdullah.”
“Muma haka Khaleel.. Muma.”
Tashi nai zan bata waje tamun alama da hannu danayi zamana, Inason strong bond dinnan, Uwa da ‘da suyi reuniting.. so captivating! Hawaye tashiga gogewa da laffayar ta na mika mata gidan tissue dake gabanta, Ai kuwa har mura ta kamata.
“Ammi… Kina jina?”
“Ina sauraron ka Khaleel.”
“Ki gafarce ni Ammi.. Duk tsawon shekarunnan dana dauka bana neman ku, Bana waiwayon gida, Bama nasan ayimun zancen gida. Ki gafarta mun Ammi ki yafe ni..”
“Bakamin komai ba Khaleel! Nasani ba yin kanku bane baki dayan ku, Kadena ma tunanin daga kai ne kaji? Duk cikin ku babu wanda yataba mun babban lefi Khaleel, Tun girman ku har kwanan yau. Allah ya yi muku albarka, Ya dora ku akan makiyan ku.”
“Aamin Ammi.. Anata fama dasu kam, Insha Allah nima Yaya yace nan kusa zai sa na dawo masarautar.”
“Ka dawo ne.?”
“Na dawo Ammi.. Ina Abuja, Ban wani dade can da dawowa ba.”
Ya karasa gaya mata yadda Salman yaje har can korea, Da yadda komai ya kasance a takaice. Ammi tayi murmushi faffada, Cikin farin ciki tace,
“Ai kuwa naji dadi Khaleel, Nagode muku dukan ku, Allah ya kara hada kawunan ku. Aamin. Sharrin mutum dana aljan, Sharrin karfe, Tsautsayi da asara, Baki d’aya Allah ya nesanta mu duka dasu.”
“Aamin Ammin mu… I love and miss you so much.”
“Nima haka Khaleel, Kar a manta da addua kaji? Nagode! Nagode. Allah ya saka da alkhairi. Okay to sai na jika, Sai da safe.”
Katse kiran tayi, Tana ajiye wayar ta dubi gabas tayi sujjada, Tajima kafin ta dago tana murmushi,
“Khaleel ne.. Yareemah Ibrahim kanin mai martaba, Shine mai bi masa, Sai auta Abdullah.”
“Okay! Na korea dinnan ko Ammi?”
“Shi fa.. Ya dawo yana Abuja, Kinji Wai mai martaba ne yace surprising dina zasuyi ranar birthday, Yau kenan. Wai shine babban present dinsa.”
“Allah sarki, Allah ya Kara hade kawunan su, Ya kawo karshen duk wani mai mugun nufi.”
“Aamin Ya Allah.. Aamin.”
Hira muke jefi jefi wadda rabi duk ta Khaleel dince, Har na wanko baki na dawo muka cigaba, Na jima sosai sannan na mata sallama nida Umma Hansatu, Muka koma bangare na.
****SHAHEEDA dake tsaye ta baranda tana kallon su, Tun wucewar su ta farko sadiya ta sanar mata, Shiysa ta tsaya har dijen suka fito, Kallon k’urilla ta shiga yi mata dik kuwa da dare ne, Akwai fitulu masu haskaka farfajiyar ciki da wajen masarautar baki d’aya. Kamar rana, Tun daga yatsanta tafara kallon ta, Dake abaya ce ajikin dijen ba kadan ba ta sake fitowa da murmurewar da tayi, Jikinnan tamkar ka tsaga jini ya futo, Saboda fresh din da tayi. Takara kyau sosai,
Tsabar kallon ta, Shaheeda har bigewa tai da kofa, Tasa dan yatsa a baka tana ciza… Gaba d’aya saita samu nutsuwa ta kasa, Ta shiga kiran Salman baya dauka shi kuma alokacin yana fada wayar na hannun falaki.
“Na shiga uku ni shaheedah.. Ba dai? Nooo”
Shigewa tai cikin gida aguje ta shiga kiran wayar mahaifiyar ta, Ta gaya mata komai ,
“Kwantar da hankalin ki shaheeda ki dena kuka dan ALLAH.. Ba dai ciki kike tsammani ba? To bazashi ko Ina ba, Yana sa akaiwa Gimbiya Rahama matar baban ku ehe?”
Cikin kuka shaheedah tace,
“Iska kika sa aka turawa cikin.”
“Ta haife me? Fadi da k’arfi..”
“Ta haifi katangare.”
“Toh Karki wani damu, Yadda zancen cikin rahama yazama sai tarihi haka na waccen shegiyar ma zai zama, Ba zama zamuyi ba, Ki tabbatar da tudin sa, Watan sa, Nauyin sa idan zai yiwu, Ta hakane zansa a cinna wa shegiya katangare dai dai girman cikin ta.”
Jin haka shaheedah ta fa’da’da murmushin ta,
“Sai Hajjaju..”
“Toro babba nake, Gimbiyar sarki Ibrahim Hashimu, Fadawa duniya kice kwarai mahaifiyar ki ce.”
“Allah yabar mun ke hajjaju..”
“Kedai bar kuka kawai Kinji? Sai komai ya lafa zamu koma K’asar nan a dasa miki cikin kuma dole ki haife dan uban uban Salman din, Bai isa ya kawo gaddama ba. Amma kafin sannan ki shiru da bakin ki, Kada ki bari kowa yaji kinji.. Kinsan babu wanda yasan hakikanin gaskiyar komai.. Kije sashen Salman din ko natan kan ki tsaye.. Ki gano mun dagaske cikin ne ko kuwa? Kinsan fa yan kauye Idan suka samu birni ta murjesu wallahi baka gane su.”
“Gaskia kam hajjaju.. Toh zan duba da kai na kuwa zanje har sashen nasa.”
“Yauwa, Kiyi suman karya, Kiyi bori ki nuna yaci amanar ki, Sai dai idan dasa mata kai. Kita bori a sashen nasa kinji?”
“Toh hajjaju.. Zan gaya miki yadda akai..”
“Yauwa.. Sai da safe, mai martaba na mun iso.”
Sallama sukayi, Shaheedah ta malale akan gado tana kyalkyala dariyar farin ciki.. Ranta fes. Gani take tunda hajian su ta tsaya mata batada wani sauran shakku…..
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma’ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
GIPHY App Key not set. Please check settings