KIBIYAR AJALI 31

Advertisement

 _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B31_

Advertisements

*GIM. KHADEEJAH*

Hidimar bikin su Ya shukrah muka shiga, Duk da dai ba zuwa nake yawon kasuwa da suke ba, Ina gidah abuna. Biki saura kwanaki biyu na koma gidan Kawu daddy, Na shiga cikin dangi akaita warkajamin biki da ni, Biki yayi kyau kwarai matuka, Kwanaki 3 akai anayi, Addah maryama sunzo dasu Umma Hansatu suma. Salman ma yabawa Kawu daddy tasa gudunmuwar duk kuwa da dakyar Kawu daddyn ya k’arba don shima dai dai gwargwado yanada nasa rufin asirin, Ni kuma tawa gudunmuwar Mami na bawa. 

Anci biki an darje, Amare kowacce an kaita gidan ta, Kai Ya hameeda ne banje ba can jos, Kawu daddy yace naje mata ziyara amman bayanzu ba, Ya shukrah kuma gidan ta ma ba nisa dana Kawu daddy domin unguwa d’aya ne, Sai dai layi ne ya banbambata. Wayyo yan uwa da dadi suke, Gaba da baya dik inda na juya sune, Anyi zumunci, Munsha hotuna sosai, Biki ya kare Kowanne ya koma inda ya fito, Anaiwa amare da angwaye fatan zama lapia da zuriya ta gari. 

Shaheeda kuwa sau wajen biyar tana zuwa sashen Salman amman bata haduwa da Khadija, Dik iya zurfin bincikenta bata gano hakikanin inda dijen take ba. Salman kuwa wani lokacin har guduwa yake ya barta saboda yadda take manne masa domin shi tsoro take bashi musanman ranar daya gama kallon cctv recording din bangarenta baki d’aya. 

 ***** A hankali ta karasa ta murda kofar parloun cikin shiga wacce take fatan wanda ta yiwa ya karba ya yaba da hannu dubu ba biyu ba. Ko babu komai tasan ita d’in mai aji ce, ban da zuwan Dije cikin rayuwar su shi kansa salman yasan Shaheedah akwai isa da takama har a kan kin kansa. Kicibus suka yi da Dr Fiddau zata fito, ganinta yasa Shaheedah zaro ido dan tasan ba lafiya ba indai aga ganta ansan wani ne babu lafiya tazo dubawa.

Baya tayi tana umartar Dr. da ta fito, bayan ta fito ne tace ta rufe kofar ta rufe duk bata kawo komai ba cikin zuciyarta sai da taji Shaheedah na tambayar.

Advertisements

“Ya akai Dr. na ganki anan?” 

Cikin dakiya Dr Fiddau tace.

“Lafiya lau Gimbiyar mu, mai martaba ne ya kira ni.”

“Jikin nashi ne ya motsa ko me?”

“Allah ya taimaki Gimbiyar mu ya kara mata hakuri da juriya, daman yace idan na fito nace a sanar dake yana son ganinki.”

Dr ta samu kanta da kwakuso karya, Saboda babu irin gargadin da Salman be yi mata ba akan karta sake ta gayawa kowa cewa Dije na da juna biyu, idan har yaji maganar ta fito kuma daga bakin ta ne to ya yi alkawarin sai ya koreta a jihar shi gaba daya. Yanzu Babban tashin hankalinta shine, Salman ta baro shi tare da Dije a daki, kuma tasan dole ne Shaheedah ta gansu, gashi yar kamar t-shirt ce a jikin Dijen ana ganin bullowar cikin jikin ta.

“Alright! Daman ina son nazo na duba shi bari na shiga thank you Dr.”

Gabaki daya rasa yadda Dr za tayi akan ta tsayar da Shaheedah daga shiga cikin dakin tayi. Tasan bata isa ba kuma Shaheedah mutum ce wacce bawanta be isa ya sata tayi abu ba indai na kashin kanta ne. Tayi saurin dakko waya tana kiran Salman amman be dauka ba saboda Dije na can na yi masa raki, daga tace bayanta sai tace hannu ko kafa haka yake bin duk inda ta fada yana matsa mata, yana jin kiran wayar a kan bedside amman ya kasa zuwa ya dauka saboda da ya dan tsaya zata ce ‘wash Allah’.

Babu ko sallama a haka Shaheedah ta murda kofar bedroom d’in tana lumshe ido jiyo kamshin turaransa da tayi. Sai dai kuma me, hango Salman tayi durkushe a gaban gado yana yiwa Dije tausa. Da yake baya ya bawa kofar sai ya zamana be san waye ba duk a tunaninsa ma Dr ce ta dawo, amman yadda yaga Dije tayi wata irin zabura ta juyo shine yasa shi saurin mikewa yana kallon kofar. Shi kansa Salman din da yaga Shaheedah a wannan lokacin sai da kirjinsa ya buga, saboda itace mutum ta farko a duniyar nan da baya son tasan Dije na da ciki saboda yadda yagani a na’urar dake dakko masa sirri dan yasan ba zata taba yadda ba duk kuwa da duk wata qullaliyar rashin haihuwar sa daga gare ta ne.

Baki bude take kallon su, Dije na kokarin janyo blanket ta rufe jikinta, sai dai abinda suke gudu shine ya kasan ce wato ganin cikin. Shaheedah ta dago kafa a hankali tare da rufe kofar ta jingina bayanta a jiki saboda yadda kirjinta yake bugawa da karfin gaske. Fatan ta da burin ta yasa ba abinda take zargi bane a idanunta. Salman ya kirkiro murmushi wanda iyakarsa saman lebansa yana tahowa gurin Shaheedar.

“Gimbiya irin wannan shigowa babu excuse?”

Ya yi maganar yana kokarin dafo kafadar ta, Ya ma manta when last ya kirata da gimbiya. tayi saurin dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, bugun zuciyarta yana daduwa tasa hannu ta dafe goshi tare da cewa.

“Salman amanata kake ci? Salman kai ne tare da wannan banzar matar akan gadon mu na mulki? Wait! Wannan toliyar ta cikin ta na meye?”

Komawa ya yi ya zama Salman d’in shi jin ta ambato cikin Dijen wacce ta rufe jiki da blanket ta tsaya tana kallon su. Shi kuma Salman ya tsuke fuska yana cewa.

“Ke baki da toliyar a cikin ki Shaheedah?”

“Kai kanka kasan cewa bani da tunbi, kuma itama ba shine da ita ba ballantana kace min shine.”

Haushi ya fara ciki Salman dan yaga alamar so take ta kaishi makura, gashi yama rasa abinda zai ce mata sai faman cizon lips da yake yi. Ni kuwa sakkowa nayi daga kan gadon har blanket d’in ban kallesu ba na nufi hanyar fita ta kuma danne kofar da bayanta, gashi bana son nace zan bi ta dayar kofar saboda babu wanda yasan da ita sai ni da Salman kadai.

Cikin Bazata kawai muka ga ta finciko blanket d’in ta tsaya tana kare min kallo cikin rawar jiki. Ta tabbata cikin ne da Khadija? Shin k’oshi ne ko kuwa? Idanunta ne? Kallonta ta mayar kan Salman baki na kyarma ta ce.

“Salman!!! CIKI?”

Haushi da takaicin ta suka taso min, dama ni ba hakuri ba bare nace in an min zan kyale, na ja tsaki tare da cewa.

“Eh ciki ne haramun ne dan nayi shi a yanzu? Ko kuwa kin dauka cewa dan kin kasa dauka uban Kowa ma ba zai dauka ba? Kinyi kuskure da kike tunanin cewa ni gunki ce ba zan Iya bukatar namiji a kusa dani ba. Namijin ma kuma tsadadden mijinki wanda yasan takan soyayya irin Salman…”

Jiri ne ya shiga kwasar shaheedah, Daman anata kawo mata tabbacin cikin ne, Bata taba yarda ba sai yau data ganewa idanun ta. Ta runtse idanunta dakyar ta budesu cikin tsantsar bakin ciki, Domin tuni wani abu ya taso ya tokare mata a wuya. Duk da son tayi borin karya hakan yaci tura, Domin wani ‘daci ne taji yana taso mata tundaga cikin ta zuwa wuyan ta, Sulalewa tayi ta fadi…

Yadda zuciya ta ke tafarfasa ne yasa banji tausayin ta na faduwar da ta yi ba, sai ma barin gurin nayi na tafi sashe na da sauri Ina faman masifa duk kuwa da kirjina a dankare yake da fargaba, Muguwa ce ta ajin karshe, Don basumin da dadi ba tun farkon zuwana masarautar. Har ga Allah banso taganni da cikin nan ba. Amma na dake zuciata kawai na koma sashe na. 

Shi kuwa Salman kwakwalwarsa ce ta tsaya cak saboda rashin sanin abin yi, ga Shaheedah a sume, sannan ga a yanayin yadda yaga Dije ta tafi yana tsoran karta yi wani abin da zai samu cikin ta. Dr fiddau ya kira awaya yace tazo dakin sa ta duba shaheedah. Shi kuma ya koma wajen Khadija, Zuwa tai cikin barin jiki dik a rude take ganin yanayin shaheedan, Ta fara ciro kayan gwaje-gwaje ta nufo wajan Shaheedah da nufin duba BP d’in ta, cikin hasala Shaheedah ta buge ta tare da hankadata tayi baya tare da bugar kofar bathroom. Sakkowa tayi daga kan gadon tamkar zararriya ta nufi Dr Fiddau wacce ke kokarin tashi, ta shako mata wuya tanai mata kallon tsana tace.

“Munafuka algunguma makiri kawai, ashe daman munafinta ta kikai kinsan komai? Fiddausi ni zaki yiwa munafinci dan babanki dan kaza-kazan uban can? Toh yau naga komai da kuke boye min munafuka kawai, tashi ki bar nan kafin nasa ayi miki jina-jina yar matsiyata.”

Ko samun damar kwashe kayan Dr ba ta yi ba haka ta fice daga dakin tana dafe goshi dan ba karamin buguwa ta yi ba da kofar. Shaheedah kuma ta fito, kamar taje sashen Dije amman ta fasa saboda hango su Falaki da tayi tasan kome tace ba zasu barta ta shiga ba tunda ta san Salman ya na ciki. Ta nufi sashenta cike da tashin hankali da hargitsin wannan al’amarin.

    **SAS kuwa yana zuwa sashen Khadija ya tarar da ita zaune bakin gado tana cin ayaba, mamaki ya yi mugun kamashi amman dai hankalinsa ya kwanta ganin ba cikin damuwa take ba. Ina jin motsi ni kuma na dago kai na kalli bakin kofar, ganin shine yasa ni maida kai na Ina ci gaba da cin ayabata wacce na biya ta kitchen na dakko na hawo sama abuna. Karasowa ya yi shima ya zauna a bakin gadon nayi saurin juyawa daya bangaran, ta haka ya gane cewa fushi nake dashi.

Tashi ya yi ya matso sosai kusa dani tare da janyo ni jikinsa, duk da cewa naji dadin hakan da ya yi min, amman sai naki nunawa, Sai ma kakkaucewa da nake yi ni a dole bana son ya rike ni kuma karya nake Ina so. Murya a raunane yana leko fuskata yace.

“Na yiwa Zawjatii na oum unborn laifi, amman ina neman afuwa a yafe min dan Allah bana son fushin nan wallahi.”

Na ajiye bawon ayabar cikin plate tare da juyowa na kalle shi Ina cewa.

“Gaskiya waccan matar taka tana da matsala. Shikenan dan ita ba ta yi ciki ba, Sai ya zamana duk wacce zaka aura itama ba zata yi ba? Na yadda makira ce wallahi, tafa san cewa itace ba ta haihuwa amman dubi yace take mamakin na samu ciki da kai… Yaa Rabbi! Allah kai mana maganin masu binmu da mugun abu.”

Cikin karyar da kai Salman ya kamo hannunta yana jan kasan lips dinsa, Cikin kasa kasa da murya in husky voice ya dube ni, 

“Shi yasa nake son kici gaba da kular min da kanki da baby na, nasan yanzu idanun mutane zai dawo kan cikin nan. Zawjatii wannan addu’o’in naki da bakya gajiya da yin su, kici gaba da yi, idan da wasu ma ki kara akai. Ina sonki Zawjatii da abinda yake cikin ki. Bana son ki kuma fita ko nan da can ne, hatta sashe na ki dena zuwa ni zanzo ko kuma duk Sanda kike bukata ta ki kirani. Ina sonku Dijangala na, ki rokar min Allah ya barmu tare please.”

Ya karasa maganar yana kwantowa saman kafadata da hawayensa masu dumi suka sakko min saman kirji na. Tausayinsa ya kamani, nasa hannu Ina shafa fuskarsa cikin sigar lallashi da tausayawa. Dan na karfafa masa gwiwa yasa na hadiye kukan da yake taso min, ina dan murmushi nace.

“Insha Allahu zanci gaba da yi maka addu’a mijina, babu abinda zai same mu..Sai abinda Allah ya kaddara mana. Bamu da kowa sai Allah da shi kuma muka dogara, nayi maka alkawarin kula da babyn ka dani kai na. Allah ya shige mana gaba a cikin dukkan aiyukan mu na alkairi, ya kare mu daga sharrin masu sharri. Kasa a ranka babu Wanda ya isa ya yi mana abinda Allah be so ba.”

Sosai kalaman suka yi tasiri a zuciyarsa, ya sake rungume ni a jikinsa yana shafar ciki na da hannunsa na dama. Saboda da ma na kawar masa da duk wani tunani marar kyau, sai na kwanta tare da janyo shi ya fado jiki na, cikin sauri ya sassauta nauyinsa yana zaro ido yace.

“Sai kinje na fasa miki cikin? Uhmm! Love?”

Ina dariya nace 

“Toh ai kai jarumi ne..Sai ka kuma saka wani.”

“Noooo my love! Wannan d’in ma wace irin siyasa ce ban yi ba kafin na samu ya shiga. Gwara dai na lallaba a sauke min shi cikin koshin lafiya.”

Kuma janyo shi nayi ina marairaice ido cikin nuna masa tsantsar bukatar sa dan so nake ya manta da duk wani tashin hankali da yake cikin zuciyar shi. Ai kuwa kamar jira yake nayi masa tayi, ya janyo ni jikinsa yana kai min sumba ta ko’ina ni kuma Ina karbar sakonnin nashi ta nuna masa jin dadin abin da yake min. Na tabbatar yanzu babu tunanin wata Shaheedah a ransa sai ni kadai kwallin kwal, na biye mishi kuwa har sai da ya samu nutsuwa sannan muka yi wanka.

Yana makale dani yana faman shafar ciki na yace min.

“Baby na wallahi yanzu kin fini yawan bukata meye sirrin.?”

Ina turo baki cikin shagwaba dan kuwa ba karya ya yi ba, ni kaina wani lokacin idan na kalleshe ko kuma tunaninsa ya ishe ni sai naji kawai Ina son kasancewa dashi, na rasa dalilin wannan al’amari. Sai da ina karanta wani posting a WhatsApp naji ana cewa wasu ciki yana..Sanya su yawan bukata. Amman ban gaya masa hakan ba Sai cewa nayi.

“Toh ba kai ne ba..”

“Ni kuma da nai mene?” 

Yayi maganar yana kama habarsa.

“Kai ne idan na kalleka sai naji kawai ni Ina so.”

Wani irin hugging ya yi min, da alama dadi da farin cikin kalamai na ne suka sa shi yi ba tare da ya sani ba, na saki yar kara ya sassauta tare da sumbatar wuya na yana fadin.

“Kice nima d’in dai ba baya ba? Na dauka maza ne kawai suke bukatar mata sometimes?”

“Ni ban sani ba, naka kawai na sani ko kallona kayi sai naji wani yarrrrrrr….”

Wayyo Allah farin ciki duk ya mamaye shi naji dadi ganin yadda yake nishadi. (lallai dole Ace wasu matan ba da bokaye suke kwace miji ba lol) Sai da ya tabbatar na shirya ya kwantar dani bayan ya matso min da tea flask dina da kofin shayin ya sumbace ni tare da ce min zai je dakin sirri ya duba dan yasan tabbas akwai maganganu bama magana ba. Muka yi sallama kamar bama so dani ni kaina ban so zai tafi ba saboda wata irin sassanyar soyayyarsa da take kuma ratsani….

SAS

Haka kawai Salman ya tsinci kansa da danna cctv din sashen Mama Huwaila. Ai kuwa nan ya tarar da ilahirin matan babansa banda Ammi, Rankatakaf su da ‘yayan su idan ka cire su Munaya. Zooming d’insu yayi ya shiga kallon mutanen parlorn baki d’aya.. Har zai tashi ya jiyo Mama Huwaila na magana,

“Kamar yadda Waziri ya sanar da dukkanin mu nan, Yanzu abu d’aya ne zamu sa agaba. Wato yadda za’a yak’i salman a saukar dashi daga gadon mulkin basannabas. Magana dayan biyu ce Idan yan majalisa sun nemi dalili, Baida ishasshiyar lapia, Mulkin ma Waziri ne ke jagoranta, Sai na biyu barnatar da asusun masarauta ba gaira babu dadi. An bugo statement of account, Wa’innan dalilai kwarara biyu yan majalisa zasu tattauna akai asa yayi murabus..”

Gaba d’aya yan parlorn suka sa shewa, Salman dake tsaye sai ya zauna, Ya janyo wayar sa dake gefe ya kira falaki.

“Ya.. Ka aiwatar?”

“Allah ya kara maka lapia, Na saka masa tracking device din da recorder, Na bi duk sauran tasu wambai duk na sassaka a duk inda ya dace. Toh yallabai a huta lapia.”

“Aamin! Allah ya bamu sa’a…. “

Ahankali ya jinginar da kansa akan teburin dake dauke da computers din, Wasu zafafan hawaye ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskar sa. Tissue ya janyo ya goge hawayen, Ya mike ya fice zuwa dakin sa……

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 29

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 27

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 16

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 16…

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…