KIBIYAR AJALI 32

Advertisement

 _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B32_

*GIM SHAHEEDAH*

Advertisements

Tunda ta isa sashenta take kuka tana birgima, Kamar tababbiya, haka take duk sanda take a hautsine tahau farfasa sauran kayan dake dakinta wanda bata fasa ba. Tana yi tana cizgar gashin kanta. A haka mahaifiyar ta gimbiya Asmau ta kira ta,

“Hello fulani..”

“Na’am.. Hajjaju!”

Tak’arasa tana cigaba da rusgar kuka, Hankalin gimbiya asmau yai matukar tashi, 

“Fulani! Menene? Eh! Waya saki kuka? Menene kiyi magana mana.”

“Hajjaju! Ta tabbata cikin nan gaskiya ne, Wallahi tsabar tashin hankali ban kare masa kallo ba hajjaju, Baki gansa ba ya girma..”

Advertisements

“Kina nufin kice har ya nuna sosai kenan? Katarar ubancan.”

“Har Salman na matsa mata kafafu, kingan su atare kuwa hajjaju? Wallahi bansan sanda nai gajeriyar suma ba hajjaju. Ina cikin damuwa Hajjaju, Da alama zamana yazo kar..”

“Karki karasa, Uban uban su daga ita har shi Salman din, Banda mahaifin ku ya tsaya akan su, Ai da Aliyu Salman mahaifin sa ma bazai sarautar basannabas ba wallahi. Ciki tamkar yabi iska ne, Dan dole musan abinyi akansa yanzu yanzu kuwa.”

Shaheeda tasake barke wa da kuka tana jujjuya kanta kawai, Idanunta Salman da dije kawai suke tariyo mata, a yadda tagan su dazun nan Salman din na marairaicewa dije. 

“Fulani! Ko bakya jina ne?”

“Inaji hajjaju.. Yanzu hajjaju idan zancen ya fito fa? Kinfasan yadda mukai rufa rufar sa shekaru da yawa,.”

“Kassh! Banace ki dena damuwa ba? Yanzun kikasan abubuwa nawa zansa amiki!? Ciki harda binne maganar bazata taba fitowa ba. Ciki kuwa idan kwantar wa ne sai musa a kwantar yabi fatar cikinta.”

“Toh Hajjaju..”

“Yauwa fulani. Kwanta ki bacci da munshari kinji? Karma maganar can tasaki a mawuyacin hali.”

Sallama sukai takashe itama ta katse. SHAHEEDA kuwa Sabon shafin kuka ta bude taitayi tana bori. Can Salman ya kirata a waya, Dakyar ta iya dagawa tana share hawayenta.

“Hello shaheedah..”

“Na’am”

Ta amsa shi tana mai kokarin daidaita muryar ta.

“Ya jikin naki.? Na dawo na tarar bakya dakin, why?”

Shaheeda ta kunduma masa zagi  azuciarta tana share hawaye a fili,

“Na wartsake shi yasa..”

“Okay.. Zan zo anjima.”

Kit shaheeda ta katse kiran tana mai wulli da wayar. Tunanin yadda hajjajun su zata bullowa lamarin kawai take, Domin shaheeda irin mutanen nanne masu oya oya. Komai na ta so take ya zama babu matsala. Tana ta zaune, Dake period take, Sai dai ta tashi ta canza pad tadawo ta zauna. Har Salman ya shigo tana can tana tunani.

“Inata sallama kinyi shiru.”

“Banjiba. Barka da dare.”

“Barkan mu.. Ya jikin naki?”

Ya fada yana taba goshinta, Ta goce tana yamutsa fuska, Kunsan tabarmar kunya da hauka ake nadeta, Fashewa tai da kuka tana zubewa a jikin sa.

“Menene.. Jikin ne?”

“A’ahh..! Salman meyasa zaka ci amanata har haka?”

“Amana kuma? Wata amanar taki naci?”

“Yanzu fisabilillahi shekara da shekaru nayi hak’uri na zauna da kai duk tsawon lokacin nan, Nayi nayi muje Habeeb medical center dake Oman a samun cikin nan ka ki… Amman shine a asirce ka ka kai amaryar ka aka dasa mata.. No wonder kuke bobboyewa, Kwana biyu bata gidan ashe da walakin.”

Har tayi ta gama Salman kawai binta yake da kallo, courage dinta na matukar bashi mamaki. Murmushi kawai yayi, Ya kamo hannunta yana murzawa a hankali,

“Shaheedah.. Idan hankali ya ‘bata hankali ne ke nemo shi, Duk wani mumuni baya cire rai ga rahamar ubangiji, Babu wanda abu dake bamai yiwu wa ba fyace Allah ne ya kadarta haka kingane? Dan doctors sunce bazaiyiwu ba shikenan kuma kika dauka bazaiyiwun ba? Uhm? Ina karatun ki”

“Meka dauke ni Salman, Jahila?”

“No ni bance ba, Kawai naga a matsayin ki na mai zurfin ilimi sosai bai kamata kice haka ba.”

Fincike jikin ta tayi daga nasa ta mi’ke tsaye.

“Idan mutanen duniyar nan zaka tara bazan yadda ba, Saboda tsagwaran makirci ne. Ko dai zuwa kukai aka sa mata, Ko kuma zuwa tai ta sa meshi ta wata hanyar, Kai bazaka sani ba domin naga alama an wanke an baka ka kasha. Amman dai tabbas ka kwana da sanin wannan ciki ba naka bane..”

Mikewa yai shima yana kallon cikin idanunta, Ta janye da sauri saboda kwarjinin daya mata.

“Haka kikace ko?”

“Eh haka nace.”

“Shikenan! Mu kwana lapia..”

Ficewa yai batare daya kara bi takanta ba. Ita kuma ta zube awajen tana hawaye. Jakadiya Abu dake labe tana jinsu ta dora hannunta a kirji tana zare idanuwa. 

*SAS*

Yana koma sashen sa, Wanka ya shiga yayi a bandaki hade da alwala, Ya zura kayan bacci ya nufi sashen Khadija. Tana baje akan carpet tana cin gyada. 

“Zawjatii..”

“Honey bunny.. Ka dawo?”

“Eh na dawo..”

“Ya jikin nata?”

“Taji sauki.”

Gyada kai nayi kawai na cigaba da cin gyadata, Na daga kafafuna na dora akan cinyarsa daya zauna a kusa da ni, Ni kuma kai na yana daga can gefen gado na dora kai na akan tum-tum.

“Dan mammatsamun kafafuna.”

“Okay… Your highness.”

“Yauwa takawa na.. A matsa dakyau.”

Matsamin ya fara yi cikin kwarewa. Yana shafamun heat balm awajen,

“Meye labari..?”

“Hm babyn ka taita kicking dina, Naita cin abinci. Saura kadan fa dazu na rama naushin data mun.”

Zare idanu yai yana daria, Ya saki k’afar ya dawo santar kai na yana d’aga rigata sama, Hannun sa yasa yana shafa cikin, Hade da dora kansa akai 

“Little one! Ayi hak’uri a dena dukan Mami, Tace Zata fara ramawa.”

“Mami?”

Na tuntsire da daria, Na mike zaune , Na barshi yanataiwa cikin magana kamar da wani yake.

“Uhm.. Mami da dadi fa. Ko akwai wanda kikeso, Mama, Maama, Ammi, Oumma, Maa, Mommy, Ayii, Ummi.”

“Ai Kowanne yayi dadi har Mamin. Zamu zaba sai babyn tazo.”

“Mace zaki haifa mana love?”

Ya fada yana shafa gashin kai na. Na lura abubuwa mafi soyuwa a jiki na dayake muradin so akwai gashi a gaba gaba. Na dora kai na akan kafadar sa ina shafa kwantaccen sajen sa,

“Inason mace.. Saboda saka mata kaya pink, Da yi mata kitso.”

“Nima inason mace… Mai kama dake sosai. “

“Me kama da kai dai. Sai tafi kyau”

“Wa yagaya miki.. ?Tab! Me kama dake dai Insha Allah. I can’t wait. Allah dai ya saukeki lapia.”

“Aamin! Aamin.”

Dauka ta yai gaba d’aya ya dire akan gado, Yasa hannu ya kashe fitila. Yana mai janyo bargo ya rufe mu, Daga nan wasan ya canza aka shiga fagen daga sosai…. 

<><>>>>>>>>>>>>>>>.    <><><><><>>>>>>>>>

*SASHEN  JALEELAH*

Jakadiya Abu dakyar tayi bacci saboda maganganun Salman da shaheeda data jiyo akan cikin da dije ke dauke dashi, Gari na haske tatafi sashen Mama Jaleelah don sanar da ita labarin cikin. Tunda itace d’iyar waziri. 

Mama Jaleelah na hakimce akan kujera gama cin abincin ta kenan tana hutawa, Da alamun bacci ne yakeson d’aukar ta duba da yadda take lumshe idanu ahankali tana bud’e su. Jakadiya Abu tashiga bayan anmata Iso, Tana zama tafara haki saboda da tazara tsakanin sashen hadimai dana matan gidan. 

“Hakkin me kike Abu? Gudu kikayi ko kuwa wani ne ya biyo ki nan din.? Laifi ki kai ko menene? Kinzo sai numfarfashi kike, Tashi ki bani waje in babu abinda ya kawo ki.”

“Tuba nake ranki ya dade, Allah yakara miki lapia da nisan kwana. Wallahi daren jia ban runtsa ba shi yasa ka.”

“Bakida lapia ne?”

“Kalau nake ranki shi dad’e… Furgici ne kawai da tsantsar tashin hankali dana shiga.” 

“Ina ji..”

“Tun kwanakin baya nake wani bincike, Toh Allah da ikon sa sai daren jia sakamakon binciken ya fito..”

Mama Jaleelah ta mike daga kishingid’en da take ta zauna tana duban jakadiya. 

“Ke na fara sanarwa, Domin abunda ya shafe kine ya kum…”

“Jeki ga ainihin zancen.”

Jakadiya ta saki nannauyar ajiyar zucia kafin cikin tabbatarwa tace,

“Gimbiya Khadija.. Na dauke da juna biyu.. Har ya girma.”

Mama Jaleelah ta mike saboda jinta da ganinta daya dauke na yan Wasu dakikai. 

“Maimata abinda kika ce…”

“Gimbiya Khadija na dauke da juna biyu.”

Ai Jaleelah bata jira karashen zancen jakadiya ba tashige cikin dakin ta, Jikin ta sai kakkarwa yake. Waziri (mahaifinta) ta kira ta fada masa komai. Alokacin Waziri kuma ya gama shiryawa zashi fada. Da sauri ya koma ya shige cikin dakinsa ya rufe tare da tuge rawanin kansa ya yi cilli dashi, banda cije baki da bubbuga hannu a kanshi babu abinda yake yi. Uban gumin da yake tsatsowa daga jikinsa sai ka rantse da Allah daga wanka ya fito tsabar digar da gumin keyi. Zagaye kawai yake a cikin dakin zuciyar shi cike da matukar mamaki jin cewar amaryar sarki Salman tana dauke da juna biyu.

Ta ya ya mace zata samu ciki bayan an tabbatar da cewar mijin ba zai taba haihuwa ba? Karya ne wallahi dole akwai wata kullalliya da Salman ya shirya yi a cikin masarautar nan, shi yasa yaje ya auro wacce ba jinin sarauta ba. Yar talakawa da bata da arzikin komai sai bin gidajen yan uwa.

Karar wayarsa ce ta katse masa tunanin da yake yi, ya lalubi cikin aljihunsa ya ciro yana dubawa. ‘Mai martaba’ ya gani baro-baro ransa ya yi mugun baci ya mai da wayar cikin aljihunsa. Ba zai dauka ba domin yanzu jin tsanar Salman yake yi a fili ba wai a zuciyarsa kadai ba. Ya tsane shi tsana mafi muni da babu wani dan Adam da ya taba tsana kwatankwacin wannan.

“Sai na illataka Salmanu, sai na nuna maka baka da wayo bare kuma dabara. Bana sonka bana kaunarka, ko mahaifinka na zauna dashi ne kawai ba dan ina kaunarsa ba bare kuma kai da aka haifeka a gabana. Ni zaka munafinta ka nuna min cewa ni ne abokin sirrinka? Ni zaka mayar sauna wanda besan abinda yake yi ba Salmanu? Kayi kadan wallahi, ba a haifeka ba ballantana kace zaka fini dabaru. Muje zuwa zan nuna maka koni waye Salmanu, wannan cikin ba a isa a raina mana hankali akan shi ba, Sai kun fadi yadda akai kuka samo shi munafukan banza munafukan wofi.”

Cewar waziri da yama rasa abinda zai yi saboda tsabar damuwa da shiga tashin hankali. Domin rashin haihuwar sa da shi zasuyi amfani wajen tsige rawanin sa, Wani kiran ne ya kuma shigowa, cikin masifa da zage-zage ya ciro wayar da niyar kashewa ya yi zaton Salman d’in ne sai kuma ya kara ganin sunan Jaleela, ya dauka a fusace yana cewa.

“Menene kuma, Zaki bi ki dameni?” Cikin damuwa Jaleela tace.

“Abba ance fa cikin yafi wata hudu, kuma na gangaru da yake min aiki yanzu yace ya kasa gane meye a cikin mace ko namiji, shine na kira na ce ko z….” 

Bata karasa ba waziri ya yi hanzarin katse ta.

“Kinga Jaleela ki rabu dani, duk wannan fafutukar da nake yi so nake naga sarautar ta dawo hannun mu, Amman gashi nan abu yana neman hargitsewa. Tun farko nace miki muyi maganin su Abdulqadeer dasu Maheer, ya zamana duk yara mata gareku, amman shegen taurin kai irin naki kika ce, A’a ai kuna hade dasu Huwaila. Toh yanzu..Sai kije ku nemo mafita da kanku, su suna da maza Wanda ko babu jinin Salman a duniya zasu Iya karbar mulki, kuma tsab zasu Iya korarki daga cikin masarautar. Dan haka ki rabu dani naji da abinda yake damu na nima.”

Zata kuma yi masa gardama ya katse kiran tare da jan wani mugun tsaki dan a yanzu Kowa ma waziri haushinsa yake ji musamman a wannan lokacin da yake cikin zafin zuciya da bacin rai. Kaya ya sauya ta yadda ba zaka taba tunanin shi bane, ya fito ba tare da yabi takan iyalinsa ba yaje ya dauki Mota ya fice.

Gurin tsibbun sa ya nufa, yana zuwa ya tarar da shi yana ta dariya ba kakkautawa, tsayin lokaci bokan na dariya waziri be kula shi ba dan hatta shi din ma a wannan yanayin zai Iya yi masa rashin mutunci dan yana ganin kamar ma yana sane da cikin amman be sanar masa.

“Nasan dama zaka zo da kanka ba aike ba, nasan zaka shiga cikin wannan yanayin shi yasa tun farko nace maka Salman baya amfani da duk maganin da kake kai masa.”

“Ni yanzu so nake naji daga Ina matsalar take?”

“Hahahahahah aljanu su taimake ni na taimaki Waziri. Ai babbar matsalar tana tare da Salman, Gimbiya Khadija ita ce matsalar ku gabaki daya waziri. Wannan yarinyar da kuka raina, kuke ganinta kamar karamar alhaki, a yanzu itace zuciya da ruhin sarkin ku Salman.”

“Kana nufin kace min cikin da ake magana na Salman ne? Ta ya ya hakan ya tabbata bayan shi din juya ne bashi da wani tasirin yiwa mace ciki?”

Boka ya kalli waziri tare da cewa.

“Koma dai menene kuje ku tambayi matarsa ta farko, ita tasan menene gaskiyar lafiyar sarki Salman game da samun ciki.”

Waziri ya kuma kallon boka cike da takaici, Sannan ya kawar da kai yana furzar da iska daga cikin bakinsa yace.

“Ina son kayi min dalla-dallah da kanka, bana son naje na samu kuskuran magana, ka gaya min duk abinda yake faruwa.”

Sake bude idanuwa Bokan ya yi tare da daukar wani faifai mai dauke da kasa a ciki ya yi dangwale-dangwalensa, kuma kallon waziri ya yi yana wani irin abu da harshe kamar tsohon maye sannan yace dashi.

“Idan har kuka bari aka haife abin da ke cikin nan da rai, humm-hummm waziri.”

“Yanzu babu abinda zaka Iya taimaka min dashi?”

“Akwai magunguna waziri, kaga Ina da wanda za’a Iya kwantar da cikin ta shekara goma be tashi ba. Akwai Wanda zata Iya haifa amma babu rai. Akwai kuma wanda zamu bayar tayi barinsa Koda yakai watanni tara. Wanne kake so? Saboda ko wanne yana da sharrudan da za’a kiyaye.”

Waziri ya gyara zamansa cikin ransa yana jujuya wanda zai ce ayi, daga kashe dai yace da Boka.

“Ina son ka bani wanda za’a daure cikin ya zamana tamkar babu shi dan bana son ma ace tayi bari ko ta haihu ya mace, wannan duk zai sa Mutane su san cewa zata Iya kuma haihuwa nan gaba. Amman yanzu idan aka daure cikin kaga Sai ayi ta faman jira aji shiru har ma ace tayi karyar ciki dan ta cuci mai martaba.”

“Aljani d’an tsartu ya karbi bukatarka, yanzu haka zai kawo maganin da za’a baka.”

Boka na rufe baki kuwa sai ga wani kullin leda baka ta fado, Bokan ya dauka tare da mikawa waziri yana kuma yi masa karin bayani.

“Karbi wannan maganin, yanzu Aljani d’an tsartu ya karbo maka a can kasar faleru. Za’a zuba shi cikin abu mai ruwa wanda take sha, ko lemo, ko Shayi, ko kuma ruwan sha. Idan har ta sha sau uku yau daya gobe biyu jibi uku, Ina mai tabbatar maka da cewa rana ta hudu zata tashi taji batajin komai a cikin ta.”

Cike da murna waziri ya amsa yana jujjuyawa, muryar Bokan ce ta dawo dashi daga kawa zucin da ya tafi, inda yake cewa.

“Da akwai sharadi.”

“Toh Boka wane irin sharadi ne? Gaya min saboda indai akan wannan lamarin ne zan Iya yin koma menene.”

“Shikenan tunda kace a gaya maka. Sharadin shine idan har bata sha ba tsawon kwanaki uku. Zaka shiga cikin mawuya cin hali, wanda kai kanka Sai ka kyamaci kanka bama wani ba.”

“Toh Wai me yasa ba za’a kashe ta ba ne ita yarinyar?”

“Na Sha gaya maka ba zamu Iya halaka ta ba kai tsaye, kasan munsha gwada tura aljanu dan su kashe ta. Amman sai a kama mana su, wajan aljanu dari uku aka kama mana duk a sanadin yunkurin kashe yarinyar. Kayi hakuri da son kashe ta dan ba abu ne me yiyuwa ba.”

Ajiyar zuciya waziri ya sauke daga nan ya zaro uban kudi ya ajiyewa Boka, a cikin aljihu ya saka maganin daga nan ya mike ya tafi ba tare da ya yi masa sallama ba. Burinsa kawai yaje ya aiwatar da wannan aikin maganin, tare da daukar aniyar hana Dije da Salman kwanciyar hankali… 

…..Falaki na daga gefen farfajiyar fada da wayar sa a hannu yana duba tracking din Waziri, Tun daga tafiyar sa har zuwa dawowar sa fada. Saving yai ya turawa Salman. Ranar dai gaba ki d’aya Waziri bai shiga fada ba. Koda ya dawo ma da daddare suka hadu dasu wambai, Waziri ya sanar musu da cikin dije, Kowannen su ya shiga cikin madaukakiyar damuwa da tashin hankali. Gaba d’aya tracking d’insu waje d’aya ya nuna. Salman shi abunma daria yaso bashi , Suna daga zaune shi da dije suna kallon su, Suna kuma cin gugguru sai kace a cinema.. 

“Kada ki damu da makaman tsibbun su, Lapia zaki haife abinda ke cikin cikin ki.. Sannu ahankali zasu san wannan cikin KIBIYAR AJALI.. Zai zamar musu, Mai dauke da cikin kuma kainuwa ce, Domin ke din sulke baya tare ki sai kin gitta…”

Nayi dariya ina shafa sajen sa dake kyalli..

“Insha Allah honey bunny, Da Allah muka dogara, Yanacan a madakata. Oganniya yar baffana nake, Ko Gajiyalle hakura tayi ta sallama….”

Kafa yasa ya kwantar da kujerar da muke Kai tazama kamar gado. Yasa hannu d’aya yana zagaye labbana. 

“Mantar dani damuwar su zumaaa na.”

Murmushi nai kawai domin na gano me yake nufi, Na juya masa baya. Hakan ya bashi damar kashe fitila muka tunkari abunda ke gaban mu. Ina kaunar Salman, Domin a fagen soyayya anya yanada na d’aya kuwa?… Duk wata damuwata a daren nan sai dana nemeta na rasa, Sai ma samun kai na nayi da tallafe abuna muka gurji soyayyah..

*DURBUN*

*MAI GARI JAMILU*

“A hayye- A hayye, Ga jirgi ga jirgi! Ga mota ga mota, Yan birni-Yan birni…”

Haka wasu dandazon yara suka shiga zagaye kofar gidan mai gari jamilu suna ife ife, Sun taru rukuni rukuni suna kallon ba’kin da suka zo wajen mai gari jamilu, Jeep motoci guda biyu, Sai luxurious bus guda d’aya, Sai helicopter dake shawagi a saman kauyen, architect ne aciki yana zana yadda za’a yi makarantar, Da yadda za’a shimfidawa kauyen titi wanda zai kai kaika har kan titin birni. Bayan tafiyar yan birnin wanda nambobin jikin motocin su duk na gwamnati ne sai bus dince kawai me dauke da tambarin masarautar Basannabas. Mai gari jamilu ya sake tara dattijawan garin maza yana sheda musu yadda sukayi da mutanen da sukazo daga birni a takaice. 

“Ku zazzauna, Ku saurara. Labari ne mai dadi nazo muku dashi.”

Mudi da yaje wucewa jin mai gari na cewa labari mai dadi yazo dashi sai yaja ya tsaya yana cigaba da bantarar raken dake hannun sa.

“Mai gari jamilu muna saurara.”

Cewar na laraba, Mahaifin su uwande. 

Mai gari ya sake gyaran murya fuskar sa dauke da farin ciki,

“Kunsan muna cikin jimami na maganar da gwamna ya turo mana, Za’a bamu wajen zama a kauyen Landantsan dake gaban mu, A kuma biyamu kudin gonakin mu, Kusan dukkanin wani mazauni dake durbun kama babba, yaro, tsoho Kai har na goye yasan mu mutan durbun bamuyi marhaba lale da zancen nan ba, Amma ya zamuyi da gwamnati? Duk kuwa da marayar mu ce nan tun ta kaka da kakanni. Wasunmu har sun fara binciken matsugunin da zasu zauna a kauyen landantsan, Saboda makarantar kwana da za’ayi da sauran ma’aikatar aiyuka da za’ayi guda d’aya anan din,

“Toh albishirin ku mutanen durbun, So nake Kowanne daga cikin ku ya fadada murmushin fuskar sa har zuci, Ya kuma sanar da iyalai na gida yadda akai.”

“Kaga mai gari jamilu, Ni wannan dogon bayanin duk mun san shi, Menene alfanun maimaita shi Eh?”

Malam Garzali ya tambayi mai gari cikin kosawa.

“Kai kullum bakacin ribar zance Malam Garzali, Baka taba bari a karasa zance zaka hau ya akai?”

“Yo ai gaskia ne mai gari.. Dole mu tambaya, Nabar buhu na a daji ne kar awakai su cinye dan amfanin ciki.”

Mai gari ya gyada kai, Hade da mikewa tsaye sosai yadda na baya zasu gano shi. Sannan yafara magana da k’arfi yadda kowa zai juyo shi, Ciki harda mudikalle daya tsaida abasiya mai awara suna zance.

“Mutanen Durbun.!!! Mai girma gwamnan birni da mai martaba sarkin mu dake birni, sun ce a sheda muku, Maganan tashi mu koma kauyen landantsan na gaban mu an soke ta..”

Dattijawan wajen suka magana Kowanne cikin farin ciki, 

“Ku saurara bangama ba, Malam ilya, Malam Sabiu ya isa haka nan, Ku saurara jama’a. Wannan mutanen da sukazo daga birni wakilan gwamna ne dana sarki, Sunce a shaida muku an soke zancen tashin mu, Sai dai abu d’aya ne zasu yi amfani dashi, Gonakin mu na bayan gari dana gefen kan tudu wajen rafi, Dana gangaren bakin kasuwa… Zasuyi amfani dasu wajen ginin makarantar kwana babba wadda yan bautar Kasa zasu dinga kwana, Duk wanda gonar sa ta shafi wajen to sunce Za’a biya kudin gonakin baki d’aya harda karin wasu kudaden, Sannan matar mai martaba wadda ance zatazo nan gaba, Tasa a mana titi kyauta wanda zai kai har cikin birni… Yadda mukayi dasu, Saboda haka cikin satin nan Za’a fara aiki, Nasaka hannu na wakilce mu baki d’aya nida hakimi. Yanzu zamu zaga gonakin dan daukar sunayen duk manomin da gonar sa take wajen, Za’a aika da takardar birni, Zasu zo da kudaden kowa..”

Sai farin ciki, Gaba d’aya dattijawan mazan da mata dake leke ta saman zaure sai suka fara murna, Kowa fuskar sa dauke da farin ciki marar misaltuwa. Mudi ma tsabar farin ciki ko zancen basu gama ba da Abasiyya ya mike zai tafi, Abasiyya taja hannun rigar sa, Fuskar nan tata tasha dige digen jamfarce. Girar data zana ta hade da kunne. Ba sauk’i dai gaba d’aya. Ita nan ta kure karshen gayu. 

“Ina zaka bamu gama ba.”

“Sauri nake Bebi Abassy tawa. Zanzo zancen ai anjima.”

“Yasin ba zuwa zakai ba, Kawai dai kai tsoran ladiyo kake har yanzu..”

“Allah ya sawwake, Kede ku bari akawo kudin auren kiga. I lobiyu bebi ta.”

“I lobiyu nima nawan. Mezan samu?”

“Ungo wazobia, Kafin nazo anjiman.”

Sallama sukai ya tafi gida yana tuno yadda Abasiyya Zata zama matar sa. Yana shiga ya fara kwalawa su Gajiyalle kira,

“Gajiyalle, Gajiyalle.”

Fitowa tai daga bandaki tana dafe ciki,

“Mudikalle ina maganin zawon?”

Mudi ya dashare baki yana cizan yatsa, Hamsin din data bashi ya siyo mata maganin kenan ya bawa abasiya kudin tad’i.”

“Tab ki jika kwakin jiya kisha kawai, Gajiyalle an fasa tashin mu daga durbun, gonakin su ale hamza kawai Za’a yi amfani dasu ayi makarantar.”

Gajiyalle ta dankara masa harara tanemi gefen dutsin gurji ta zauna tana nishi,

“Bankadadden banza, Mokadadden wofi, Kana gani wazobiyar adama ce dakyar ta aramin saboda yadda naketa zaryar zawon nan shine zakaje ka kashe? Toh narantse da uban daya haifeni ko zaka siyar da kan rantalelen danka sai ka kawomin wazobiyar nan.”

Mudi zai magana ladiyo tafito tana gud’a da hanci,

“A hayye! TubarkAllah Masha Allah, Ga rantalelen kai nan a jikin ki..”

Mudikalle zai magana ladiyo ta dire tsallen albarka tana karkada masa hannu, 

“Ja tsaya karamin munafiki maci amana, Wa yagaya maka bansan Abasiyya kake nema ba zaka aura? Ko kaga anwa uwata kishiya da zakayo mun? Baka isa ba wallahi, Kaje can ku karaci sharholiyar ku da ita, Amman ba zaka auromun ita gidan nan ba. Gida nawa ne nan bana wata ba.”

Gajiyalle dake numfarfashin ciwo jin ana tunkaho da gidan ta saita mike tayo kan ladiyo,

“Wane gida ne naki? Nace uban wa ya baki nan gidan.”

“Badake nake ba tsohuwar kilaki kawai, Tsabar gulma da munafurci kin tako tinkis tinkis kina jan kafa. Maza kafin nasa k’afa na shure ki.”

Nan fa gajiyalle ta cire dankwalin dake kanta, Gashin ta ya zama furfura yayi dagaje dagaje, Ta daure dankwalin a kugu tana lailayo ashariya tana zundumawa ladiyo. 

“Ke sanyi nai, Ki tambayi kowa, Wacece Gajiyalle mai yar hakiya, Duk matan garin nan a baya ba wanda ya kai ni yawan kiwo da zabbi da kaji…”

“Ina ruwana dasu, Tunda ban shigo na gansu ba, Abinda nasani shine kin kuntatawa yar mijin ki kin zalunce ta, Kowa da yake ubanta ma ke kika kar shi.”

“Kinci malamar kan uban ki. Da uwannanniya mai yakuwa gyatumar ki zanyi ba dake ba.”

Cewar Gajiyalle cikin fushi, Ko mayafi bata saka ba ta fice fuuu Mudi na tsaye ya rasa yadda zai yi. Halipha ‘dan su sai jan rigar sa yake,

“Abba abinci. Abba abinci.”

“Zo nan halipha muje bakin kasuwa”

Cewar ladiyo. Mudikalle zai hanata fita, ladiyo ta dura masa ashar tana karkada masa hannuwa,

“Kai ka isa ka hanani fita, Babu zanci agidan naka? Bakin kasuwa anan ka auro ni, Don haka dole ka kyaleni tunda tun fil azan acan ka ganni. Idan gyatumar ka tadawo kuma ta tankade mana garin can, Matsa sullutu kawai.”

Tana gama magana ta sabe halipha a hannu tafice, Shi kuma Mudikalle ya rasa yadda zaiyi, Daga karshe ya yanke shawarar bin Gajiyalle, Acan ya tarar dasu da sirikar sa uwannanniya sunata dambatuwa da Gajiyalle, Sai kasa ce ke tashi. Duk yadda akai aso rabiyar fadan nan sai da aka kasa. Sai da suka daku lilis sannan wakilin mai unguwa ya tasa k’eyar su duka biyun zuwa gaban mai unguwa jamilu domin ayi shari’a……

_😂💔Haka dai zaman yake kasancewa a durbun: Ladiyon Mudikalle kenan a gidan Gajiyalle mai yar hakiya… 🧚🏻‍♂️_

Asha hutun weekends Lapia ❤️

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 21

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _KIBIYAR…

KIBIYAR AJALI 16

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 16…

KIBIYAR AJALI 10

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p PG: 10…

KIBIYAR AJALI 17

Advertisement  I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p NANA HAFSATU❤️…