KIBIYAR AJALI 33

Advertisement

 _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_

_BOOKS DIN KUDI NE, KI NEMI NUMBOBIN MU DAKE KASAN SHAFUKAN MU, DON MALLAKAR NAKU, KI GUJI SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA. DAMA MASU RUBUTAWAR.. KODA KIN SIYA DAN ALLAH KARKI MANA SHARING.. 🤲🏻_

_B33_

****Zaune nake a cikin daki duk nabi na gaji sai kace wacce tayi aikin wahala, gaba daya zaman dakin ne ya ishe ni, ina son sauka kasa na dinga ganin gilmawar mutane amman babu hali Salman ya hanani a cewar sa za’a Iya hada baki da masu shigowa sashen nawa su barbad’a wani abin, tsautsayi yasa na bi takai su illatani ko su illata baby.

Advertisements

Sallamar d’aya daga cikin hadimai a kofar daki na yasa nai saurin waigawa Ina amsawa, na bata umarni ta shigo bayan na zura hijabi a jikina. Hannunta dauke da jug garai garai wanda hakan yasa ni hango ko menene a ciki wato damammiyar fura da nono an sanya kankara a ciki gwanin ban sha’awa, 

“Ranki ya dade mai babban daki tace a kawo miki ko kina da bukata, Umma Hansatu bata kusa shi yasa ta bayar a kawo miki.”

Tunda na hango furar nan babyn ciki na ya/ta dinga harbi na kamar za’a huda min ciki. Na karba jiki na kyarma tare da yin godiya ta juya ta fita, na karasa wajan table na ajiye tare da dakko kofin da nake shan shayi na zuba, ni kai na yadda furar tayi shar ga kamshin ayaba dake tashi a ciki yasa na kagu na ji ta cikin baki na. Karar da wayata keyi ne ya dinga rabamun hankali saboda ringing d’in Salman ne, na dauki kofin tare da karasawa gurin wayar ina shirin dauka naji ta tsinke dai dai sannan kuma naji an shigo cikin dakin da gudu, kafin na tabbatar da waye naji an buge kofin tallatsin furar ya sauka saman fuskata.

Salman ne yana tsaye sai faman haki yake da alama gudu ya yi da zai taho. Ya dafe kai tare da rintsa idanuwa, ni kuma na yi kicin-kicin da fuska rai na a bace dan na shirya kaiwa baki na ya yi min wannan abin. Kusa dani ya matso tare da rungume ni, kai na dake kirjinsa yasa kunnuwa na jiyo min yadda bugun zuciyarsa ya tsananta. Murya na rawa yana shafar bayana ya fara magana.

“Karki sha furar nan Zawjatii… Kar ki sha. Karya ne ba daga gurin Ammi aka aiko dashi ba, daga gurin Jaleelah ne waziri ya zuba maganin da ya karbo gurin wani tsibbun nasu shi dasu wambai shine suka kawo miki.”

“Innallilahi wa’inna’ilaihir raji’un… Na shiga uku ni Dije, me yasa banyi wannan tunanin ba? Karo na ba adadi kenan, Koda yake sunyi amfani da Ammi kuma daman Umma Hansatu ta tafi gurinta karbo min kilishi, shi yasa nayi tunanin da gaske ne, kai ya akai ka sani?”

Advertisements

Sai da ya dan dago fuskata ya kalleni ya sake maida kai na kirjin nasa yace.

“Ina ciki Ina wani bincike nagani, bayan sun bawa waziri maganin , Shi kuma ya zuba maganin sai suka bawa jakadiya Abu tasa a hijabi ta nufi bangaran Ammi, to daga can ne ta bawa yar aikin Ammi tace ta kawo, ita kuma da tazo ta bawa daya daga cikin ma’aikatanki tare da yi miki bayanin da tayi miki cewar inji Ammi. Na kiraki tun farkon da naga kin karbi kofin amman baki daga ba, ganin kin tashi yasa ni fitowa da gudu karki je kisha kija min asarori.”

“Kai wannan masifa da me tayi kama?”

“Shi yasa nake son mu kuma yin taka tsantsan dan gabaki daya mutanan nan sun shirya lalata min cikin dake jikin ki. Takun da Zaki canza yanzu shine ki dinga zama da hijabi yadda zasu dena ganin girman cikin nan bare su kawo masa hari.”

“Na shiga uku a dakin nawa na sai na saka hijabi?”

“Eh! Dan Allah kiyi min wannan alfarmar dan Allah my love.”

Na rausayar da kai, ni kai na ina jin yanzu na fishi kaunar cikin nan saboda yadda nake jin kaunar abinda yake ciki. Salman ya dago ni tare da karasawa dani wajan gado muka zauna, kafin ya yi magana na riga shi.

“Insha Allahu zan kiyaye, yanzun ma matsalar da aka samu shine babyn na ganin furar aka fara nuna min ana cewa za’a sha. Kuma fa ban jima da cin abinci ba, amman kaga hadama.”

“Babu komai indai fura da nono ne bari nasa Falaki ya kawo miki mai rai da lafiya.”

Nayi murmushi tare da kwanciya kan kafadar shi Ina tuna wani labari da nake karantawa, yadda mijin yake wulakanta matarsa saboda kawai tayi ciki shi kuma be shirya haihuwa da wuri ba. Sabanin Salman dubi yadda yake tarairayata yana bani kulawa ninkin wacce yake bani kafin cikin. Sallamar Umma Hansatu ne yasa shi saurin dago min da kai, nuni ya yi min da zai gudu yana cewa.

“Bana son asan da kofar nan shi yasa.”

Na gyada kai Ina masa dariya ganin yadda yake sand’a tamkar marar gaskiya. Sai da na tabbatar ya shiga ya rufe sannan na tashi Ina amsa sallamar da take yi.

“Umma ki shigo mana.”

“Au to ai naji ba a bani izini bane shi yasa Gimbiyar mu.”

“Ai kuwa tunda kikai ta farko nake ta amsawa Ina shigowa bakiji bane.” Na fada cikin son dauke mata hankali da wani hasashen a kai na.

“Kinga barna nayi shine nake kokarin gyara gurin.”

“Asha ai da kin bari nazo nayi, yanzu ma tunda Allah ya kawo ni, Sai kije ki zauna na gyara ranki ya dade. Ga kilishin kuma tace duk Abdullah ne ya kwashe bata kula ba sai gani tayi yana ci.”

“Allah sarki Ammi na, shi kuma Abdullah yaci rabon shi.” 

Muka sanya dariya saboda yanayin yadda na karasa maganar cikin wasa. Ita kuma ta gyara gurin tas ina gefe ina cin kilishi na. Bayan ta kammala ne da na tashi zan shiga toilet na tafi da ragowar furar na zubar tare da wanke kofin Ina dad’a yiwa Allah godiya da ya kubutar dani wannan tuggun. Ina fitowa na kuma hayewa gado na zauna Umma Hansatu tana bani labarurruka na ban dariya, ashe duk Salman yana ganin mu sai text message d’in shi na gani yana cewa.

“Masha Allahu love.. kina da cute smiling face, idan kika yi dariya kuwa ina kasa controlling kai na, I love you so much.”

Ban san lokacin da na kuma sakin dariyar ba Ina rufe fuska dan nasan kallo na yake yi a inda yake, Umma Hansatu kuwa tayi tunanin duk cikin labarin ta ne yasa nake kuma jin nishadi. Ta kuma gyara zama tana rattattako wasu labaran…

<>>€><>

Gaba d’aya zancen cikin dije ya gama karade masarauta da abunda ke cikin ta, Kowanne bangare maganar cikin suke yi, An sawa dije da cikin ta idanu. Sihiri, Makirci da tsantsar bakin ciki. Gaba d’aya ahalin masarautar suna cikin dimauce, Farautar ran dije suke da dan cikin nata mararan. 

**** Waziri kuwa gaba d’aya ya zama tabbabbe a zuci, A Zahiri kuma ya zama wani birkicacce. Ya dena zuwa fada saboda bakar mugunta yace bai da lapia ne. Nan kuwa kullum cikin tsara surkullen yadda cikin dije zai zube yake yi. Shida su Chiroma basu hakura ba suka sami wani garin maganin awajen yar mai ganye. Ya samu wani amintaccen hadimin sa ya kai maganin cikin sashen Khadija, Aka faki ido aka barbada a miyar da Umma Hansatu keyi. Ba masaniyar abincin bana dije bane na Umma hansatun ne. Kwanan Umma Hansatu 3 tana ciwon ciki dakyar ta farfad’o, Tun daga lokacin kuwa SAS ya hana dije cin abincin masarauta baki d’aya, Saboda a kayan abincin ma Za’a iya hada baki da wani ya zuba maganin cutarwa. Shiysa kullum sai dai ayi mata takeaway a boye taci.

Waziri kuwa an sanar masa tabbas Dije taci abincin nan, Sai jira yake yaji ana koke koken ta margaya, Yanzu abinda suka sa a gaba shine gaggauta cire Salman daga karagar mulki. Da daddare bayan sallar ishai suka taru a bangaren Mama Huwaila, Waziri ya tattauna abunda ya kawo su, Kafin ya cigaba da cewa,

“Sai kuma matar sa ta farko, Gimbiya shaheedah, Duk itace ta kawo mana cikas, Kan ai Salman baya haihuwa. Bashida ishasshiyar lapia. Nace a mana iso da ita nan ta mana bayani don mu ba mutanen banza bane. Domin gaba d’aya na tattara dik hujjojin da muka tsara nayi su a rubuce zamu aikawa gwamna ya tsige shi daga kujerar sa..”

Yana rufe baki, Parlorn ya d’auki magana baki daya, Dukkanin su sun hallara anata tsara yadda za’a tuge Salman a kujerar sa. A babban parlorn mama Jaleelah sukai zaman. Ba jimawa shaheedah ta shigo kanta a kasa tana raba idanuwa. A tsorace take ainun, Sai dai dake tana ji da kambun mulki ba zaka gane ba saboda yadda take yauk’i. 

“Barka da zuwa sarauniya.. Takawar ki lapia.”

Kowanne ya shiga mata kirari, Su wambai, Waziri, chiroma, Galadima, Makama da sauran yan parlorn. 

“Barkan mu.. Waziri ga ni! Ina fatan lapia?”

Ta karasa fada tana duba agogon hannun ta. 

Waziri yai murmushin gefen baki yana sakkowa daga kujerar daya ke zaune,

“Allah shi taimaki gimbiya.. Wani abune muka ji, Daya sanya zukatan mu a rudani, Mun ‘karyata a baya, Amman da muka tsananta bincike sai aka tabbatar mana da gaske ne. Shine mukeso muji gaskiya ta bakin ki..”

“Ban fahimce ka ba Waziri! Sanar mun abinda ya jefa zukatan ku a rudani..”

Waziri ya sake rissinawa yana dan daga murya,

“Maganar… Juna biyu da Khadija ke dauke dashi mana.”

Da sauri shaheeda ta mike tana dafe kirji,

“Juna biyu? Wacce khadijan? Wake dauke da shi? Bangane ba.”

“Au.. Ina nufin gimbiya khadija mai dakin mai martaba Salmanu na biyu.”

“Waziri!! Shin abunda kunnuwana suke jiye muni dagske ne ko kuwa? Don wane Salman din? Inde mijina kake nufi na yanzu to gaskia wannan zancen kanzon kurege ne, Domin salman baya haihuwa, Baida ishashshiyar lapiar da har wata acikin mu zata dau cikin sa. Sai dai idan awaje ta samo shi.”

Waziri ya juya yana duban sauran yan parlorn dake bin shaheedan da kallo kamar wata gaula, Domin hajjajun su tace komai rintsi ta tubure kan lallai batasan da zancen cikin Khadijan ba. Waziri ya numfasa,

“Kina nufin kice mun bakida masaniya akan juna biyun da take dauke dashi na mai martaba?”

“Zan maka Karya ne waziri?”

“Tuba nake ran ki ya dad’e, Lamarin ne da mamaki. Amman tunda ke kanki kince baki da masaniya inaga mu kuma.”

Shaheeda ta dafe hannuwanta da goshi , Irin tana cikin jimamin nan, 

“Idan ma dashi din… Toh lalle bana Salman bane, Tunda kunga zahiri a yawon asibitoci da mukayi na duniya.”

Waziri ya gyada kai yana kallon galadima. Galadima ya amshe zancen da,

“Toh wacce gudunmawa zaki bamu?”

“Wacce iri kuke nufi galadima?”

“Gudunmawa dai wadda zata temaka wajen kamo bakin zare, Wadda zamuyi amfani da ita wajen tarwatsa ita … Abokiyar zaman naki.”

Da jin haka sai ta zauna, Kasa kasa tashiga magana.

“Zan bada…Akwai general checkup results gaba d’aya wanda muka jajje da Salman, doctors ba adadi sunyi binciken su akan mu, An kuma gano shine mai matsalar.”

Chiroma ya sake matsawa tsakiyar parlorn yana rissana mata, Kamar yadda Waziri ya tsara musu su tattambaye ta. 

“Allah yaja zamanin ki, A yaya sakamakon ya kasance? Takaddu ne ko kuwa?”

Shaheedah ta dan yamutsa fuska tana taune kasan leben ta. 

“Duk abinda zai bada cikakkiyar gamsasshiyar amsa, Zai bayar, Domin akwai papers dake dauke da rubutun likitocin, Akwai fefan bidiyo dake dauke da bayanin komai, Sannan akwai sautin muryar likitocin wanda duk suna adane..”

“Alhamdulillahi ranka ya dade kana ji ko?”

Waziri ya gyada wa Chiroma Kai fuskar sa dauke da murmushi,

“Lalle gimbiya kin biyamu, Mungode kwarai. Wannan results din da zaki bamu dasu kadai zamu iya tsige yarinyar can daga zuciar Salman dama masarauta baki d’aya, Idan ta kama ma mu rabata da iska.”

SHAHEEDA dadi ya shiga ratsa ta tamkar ta tashi ta taka rawa don farin cikin jin Za’a fitar da Khadija daga gidan koma akashe ta baki d’aya. Waziri ya sake jinjina mata yana kakaro murmushi,

“Mungode kwarai matuk’a sarauniyar mu. Allah yaja zamanin ki. Sai ki bayar akawo mana.”

Mikewa shaheeda tai bayan ta daga kanta alamun Toh, Ficewa tai hadiman dake jiran ta awaje suka rufa mata baya. Tana futa su waziri suka tasa fefanta suna yi da ita baki dayan yan parlorn. 

“Rabu da ita, Itace babbar munafukar data fara ‘bata mana wasa, Na karairakin shine baya haihuwa ba ita ba, Ina sane na sako zancen futar da Khadija kadai ba tare danace tuge Salman gaba d’aya ba..”

“Kwarai kuwa Waziri, Nima da fari nayi mamakin fad’ar hakan da kayi, Sai daga baya nagano lob’a ta kayi.”

Cewar wambai dake gefe yana cin tufa. Haka dai sukaita tofa albakacin bakin su, Lokaci zuwa lokaci su Mama Huwaila kansa baki. Ana cikin tsara yadda komai zai kasance yareemah abdulqadeer ya fita da waya a kunnen sa, Can ya dawo fuskar sa babu walwala.

“Baba Waziri..”

“Na’am Makama.”

“Wata magana ce maras dadi aka sanar dani yanzu.”

Waziri ya zare idanu yana bin yareemah abdulqadeer da kallon karin bayani,

“Meya faru kuma?”

Bakin sa na rawa ya shiga gaya musu komai,

“Khal… Khaleel dake Korea, Wanda na dora akan motsin sa yau yake sanar mun wai kwana biyu bayajin dadi….”

Ai bai gama fada ba Waziri ya katse shi,

“Khaleel dinne ba lapia?”

“Noo! Shi wanda na saka ya dinga dakko mana rahotan Khaleel dinne wai baida lapia, Sai da ya kwanta a asibiti, Bayan an sallamo shi yaje gidan da Khaleel din yake..wai baya nan, Yaje asibitin sunce yayi resigning tun tuni, Yabi diddigi ance ya bar k’asar.”

“Zancen banza, Zancen wofi. Wambai, Galadima kuna ji ko? Wannan wani renin hankali ne na daban da za’a kawo mana kuma, Khaleel din da aka kafe shi shekara da shekaru ta ina har ya iya barin K’asar duk bamu da masaniya Sai yanzu? Toh yana Ina? Nace yana ina?

A hasale Waziri yake magana yana kallon abdulqadeer, Mikewar shima yayi yana tada jijiyoyin wuyan sa, Dama shi kunya bata isheshi ba,

“Okay zan maka Karya ne? Gani kake duk hadin zance ne? Zan hada kai da Khal ne na cuce ka? Lalle kabani mamaki, Amma banyi wani mamaki can ba gaskia domin na lura bakada yad-da. Zanyi maganin ka nan kusa.”

“Kai Yareemah meye hakan! Bashi hak’uri”

Mama Huwaila ta umarce shi tana zare idanu, Chiroma ma yashiga tsakani yana bada hak’uri.

“Kiyi hak’uri amma bazan bayar ba, Mena masa? Mtsss”

Yaja tsaki kawai ya fuce waje yana bugo musu kofar, Nan kowa ya kidime aka shiga baiwa Waziri hak’uri, Murmushin yake kawai yake yana amsa ‘bakomi ya wuce..’ Ransa a bace yaita danne zuciar sa har shaheedah ta aiko sadiya da wata brief case baka mai dauke da sakamakon komai, Karba kawai waziri yayi ya fice su wambai na biye dashi a baya suna faman ban hakuri.. 

*SAS*

Yana zaune shi da falaki suna kallon komai, Wani suyi daria wani suyi Allah wadai. Salman ya sauke ajiyar zuciya kafin yace, 

 “Mutanen nan sunfi shedan rashin imani, Allah ya kyauta… shin ka gama tura masa komai tuntuni ko?”

“Ai sun kai kusan sati ma a wajen sa, Har videos da komai na cctv duk na tattara komai na kai masa, Har cikin babban parlorn sa aka kaini. Gaskiya gwamna na da kirki wallahi.”

Salman ya numfasa yana murmushi,

“Ai adalin shugaba ne, Yanzu abinda ya rage kawai tattara komai a watsa shi agaban manyan yan majalisa. Jiran su nake su tunkaro mu kawai sai mu saki babban bomb din. Ka dai samu masu tsibbun nasu ko?”

“Allah ya Kara maka lapia da nisan kwana, Duk munyi magana dasu, Sun amince, Nace Za’a dakkosu a duk sanda muka nemi ganin su, Ai bokan Waziri shi yafi ban dariya, Yana ganin kudaden nan, Da mukullin sabon gidan nan daka bayar wallahi ya kunce komai ya shiga magana caaa. Wani lokacin wai har kulla toka yake ya bashi yace ya barbad’a a abinci.”

Salman yai murmushi kawai yana bubbuga mouse pad din hannun sa,

“Ai kamar doctors dinnan ne, Ina ce musu zan kai karar asibitocin su kotu, Suka shiga ban hakuri, Acikin awa d’aya gaba d’aya asibitocin da muka jajje duk kusan a tare kowanne ya turomin original results din, Harda karin signatures na board of directors. Gobe alhassan zai karb’o a airport, Kowanne a rana d’aya zai zo.” 

“Kai Alhamdulillah..! Allah yakara maka lapia da nisan kwana.. Lalle akwai kallo agaba. Ranka ya dade kayi matukar kokari wallahi, kayi bincike sosai a matsayin ka na lawyer.”

“Ai mun dogara da Allah, Hmm! Kaga na’urar kimiyya tagama mana komai na bankado sirrikan su, So Inde ka san yadda zaka tafiyar da technology a yanzu to sannu ahankali zaka gano komai.”

“Allah yaja zamanin sarki, Ya cigaba da dora ka akan makiyan ka Aamin.” 

“Aamin Yaa Rabbi… IN SHAA ALLAH! Cikin satin gaba zaka raka zawjati garin su.”

Salman ba kunya ko kadan agaban kowa baya iya boye soyayyar Khadija, Shiysa duk wani mai kusanci dashi yasan sunan Zawjatii na dije ne. 

“Toh ranka ya dade. Allah ya yarda.”

“Aamin, Anjima idan gari yayi duhu sosai sai ka dakko Khaleel, Sashen Ammi zai je kansa tsaye. Ku raba hanya tun a zauren bayi. “

Mikewa falaki yai yana rissina masa, Cikin girmamawa ya shiga yi masa sallama,

“Toh ranka ya dade.. Insha Allah kuwa hakan zaayi, Ka huta lapia.”

Ficewa yai yana sake rissina masa, Shi kuma Salman ya maida duban sa ga Waziri, dake dakin sa ya ciro takarddun da shaheedah ta kawo na sakamakon karyar ciwon Salman da akai yana duddubawa. Girgiza kai kawai Salman yayi ya mike ya haye sama abinsa, Bayan ya danna recording akan bidiyon bangaren waziri..

Falaki na dakko Khaleel dayai badda kama ba zaka taba kawowa shidin bane saboda shigar dogarai yayi, Tun a zauren bayi suka rabu. Ya shige sashen Ammi kansa tsaye, Dama tasan da zuwan sa, Tai masa iso suka haye parlorn sama, Acan ya rungume Ammi yana kuka mai tsuma zuciya, Na shekara da shekarun da bai sanyata ba cikin idanun sa………

*SAS****

Jikin sa sai rawa yake yana wanka a sashen sa, So yake ya gama kawai ya ji shi ajikin khadijan sa, Kwana biyu yanata aiki ba dare ba rana a dakin sirrin sa, Sai da ya tabbatar komai na shedar sa ya kammala tukun sannan ya danji sassauci a ran sa. Fitowar sa daga bandaki keda wuya yana shafa madaran turare a kayan baccin sa, Wayar sa tafara kara, Dauka yai cikin hanzari ganin Ammi ce, A ransa yana adduar Allah yasa lapia, Domin bata taba kiran sa. Gaishe ta yai cikin biyayya,

“Barka da dare Ammi….”

“Barka mai babban suna. Kaga na kira ka yanzu ko?”

“Ahh haba bakomai Ammi, Ni kinganni ma inata kokarin harhada abubuwan shedun nan.”

“Masha Allah! Allah ya temaka ya bada nasara.”

“Aamin Ammi.”

“Dama zancen Khadija ne.”

Zama yai akan gado yana taje sumar kansa, Yana kallon kansa ta mudubi.

“Ina sauraron ki Ammi..”

“Eh.. Wani tunani naketa yi, Har na kira gwaggon ma itama tace hakan zai fi”

“Koma menene Ammi na baki wuk’a da nama.”

“Ah’ah sai da amincewar ka, Dama maganar komar Khadija gidan Gwaggo ne. Idan komai ya dan lafa saita dawo d’akinta, Amma Kaga yanzu dai dubi yadda kowa idanun sa akan ta, Duk wata mugunta so ake a jefa mata.”

Nannauyar ajiyar zucia ya sauke yana kallon karamin frame din hotan Khadija dake gefen gadon sa, Ahankali ya janyo shi yana shafa dai dai wajen fuskar ta,

“Hakane, Na amince Ammi. Ni kaina sai nafi samun nutsuwa.”

“Yauwa…. Idan ka saka rana sai ka sa akaita.”

“Ko gobe ma Ammi.. Gwara ayi awuce wajen.”

“Babu takura ko?”

“Babu Ammi.. Nagode Allah ya saka da alkhairi ya dora ku akan makiyan ku. Aamin.” 

Sallama sukai, Ya mike jikin sa a sanyaye, Sam dai dai da second d’aga bayason dije tai nesa dashi. Ajiyar zucia ya sauke ya nufi d’akinta jikin sa duk ba kwari.

*G. KHADIJA*

Ina kwance ina aikin shan mangoro Salman ya shigo, Sanye nake cikin shigar half vest da zani, Kai na ba dankwali na bararraje ina shan mangoro, zama yai a gefe na yana janyo ni jikin sa,

“Zawjatii na…”

“Uhm.. Honey bunny naaa. Ya aiki?”

“Alhamdulillah ya ciye ciye? Ya baby na?”

“Gashinan munata fama. Mangoro na hudu kenan.”

“Ai kuwa ya isa haka nan, Zo mu wanke hannun da bakin.”

Daga kai nayi, Yana tayani mikewa, Ya zare hular kansa marar nauyi ya dora mun muka shiga bandaki, Ya temakamun nai brush, Na watsa ruwa muka fito. Har kan gado ya temaka ya kwantar dani sannan ya koma gefe na yana gyaramun kwanciya,

“Sannu zawjati..”

“Yawwa my love.. Amma meya faru naganka ba walwala?”

Murmushi yayi ya kamo hannuna yana sumbatar cikin sa,

“Bakomai fa Zawjatii.. Gajia ce kawai.”

Na yunkura dakyar na zauna ina tallabo fuskar sa, 

“Noo! Meya faru please?”

Hannun sa yasa akan cikina yana shafawa, A hankali murya a raunane yake gayamun,

“Bakomi wallahi, Kawai Ammi ce ta kira ni ba da’dewa, Itada Gwaggo sun tsara… Zaki koma gidan Gwaggo da zama na dan wani lokaci. Nace na amince gobe zaki tafi ma.”

Ni kaina sai naji wani rass, To amma ya zanyi? Kila hakanne mafi alkhairi, Kuma tinda yace Ammi da Gwaggo ta fada ai zance ya kare. Hannuna nasa nima cikin nasa ina murzawa a hankali,

“Na amince nima zawj.. Allah yasa hakane yafi alkhairi.”

“Insha Allah kuwa, Ammi tace kodan saboda yadda ake farautar ku keda babyn mu.”

Na numfasa ina kallon ciki na daya girma ba lefi. Nasa dayan hannun na dora shi akan na Salman muka shiga shafa cikin atare. Zafafan hawaye ne na hango suna reto a kyakkyawar fuskar Salman,

“Zawjati zanyi kewar ku sosai, Gaskia ba zaki dade ba zan dakko abata…”

“Ka rufamana asiri zawj, Kaga fa su Ammi ne suka yanke shawarar. Ni kam na amince da hannu dubu.”

“Ai dama haka kikeso..”

Ya fada yana turo baki gaba. Lakuce bakin nayi ina daria,

“Ba haka bane, Kasan manya da hangen nesa… Mu dai fatan mu Kayi nasara a wannan yakin dake tunkaro ka.”

“Hmm Aamin dai baby…”

Kamo hannun sa nayi na shjga zagaye su a duk wasu sassa danaga yanaso a jiki na, Hakan da nayi ba a karamun dadi Salman yaji ba, Domin nagani a yanayin sa, Kwantar dani yai akan pillow yana shafa gashin kai na,

“Banda raki dai… Yau zamu gurji kauna a daren nan, Duba kiga har anfara ruwan sama mai dadad’a daren masoya, Zan baki tukwici, Tukwicin kuwa shine zakije… Durbun idan kin koma gidan Gwaggo Addah maryama seta raka ki….”

Bansan sanda na finciko shi ya fado kan hannunaba saboda murnar jin zanje durbun,

“Godia nake zawj dina… Zumana mai dadad’a rayuwata, zaki kake, Ga isa ga ‘kasaita..”

Wata iriyar rantsattsiyar sumba mai tafiyar da duk wani damuwa sas ya shiga yiwa dije, Don dadi sai da takusa shidewa tana kara kankame shi. A haka ya dinga nuna mata kauna wadda takasa tantance gardinta da first night d’insu. Sumbatu masu daraja da kima ya shiga yi mata tana kara makalkale shi, Kowannen su hawayen dadi da farin ciki yakeyi, Wanda Salman ya shiga lashe na idanun dije cikin salon kauna, Yana kuma gaya mata kalamai masu dadi,

“Kece burin rai na, Rayuwata, Qalbi na da gangar jiki na baki d’aya, Zawjatii! A koda yaushe ina fatan ki kasance cikin farin ciki a rayuwar ki, Kasancwar farin cikin ki shine abu mafi tsada da daraja a wuri na.. Your kiss mends my heart, your touch lights up my soul, and your presence makes a difference to my world. Deejah na.. Although I may not have the right words to express you how I feel about you and how blessed I am that you came into my life. I just want to let you know that I love you with everything I’ve got and can’t imagine a life without you…”

Daga nan bansake sauraron duk wasu kalamai nasa ba saboda wata duniyar dadi daya jefa ni, Ranar na kara tabbatarwa zucia ta, Tabbas wata iriyar K’auna Salman kemun marar gauraye. Hawayen farin ciki ne suka shiga reto a fuska ta…. Duk kanin kofofin jikina sai suka shiga maraba lale da zafafan sakonnin dayake aika musu, Harta Kai na zama ni ke shugabanta shi ke daukan darasin daren ranar…….

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…

KIBIYAR AJALI 32

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…