KIBIYAR AJALI 34

Advertisement

 _INA MASOYA MA’ABOTA SON ‘KAAWATA KITCHENS DINSU DAMA DECORATION NA GIDAJEN SU? TOH KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA…_

_KAYA NE INGATTATU DA AKE KAWO MUKU SU TUN DAGA KASAR 🇩🇪 GERMANY..! KOWA YASAN GERMANY AKWAI KAYA MASU INGANCI, SEKA SHEKARA DA SHEKARU KANA AMFANI DA KAYAYYAKIN SU BASA LALACEWA. ANYI SU CIKIN TSANTSAR INGANCI DA KUMA RAHUSA… WADANNAN KAYA *MAAB LUXURY HOME* DAKE GERMANY TA KAWO MANA SU NIGERIA. RIGIJI GABJI FA KENAN.. BABU RUWAN KU DA WANI PRE-ORDER KO SHIPPING FEE, KAYAN *MAAB LUXURY HOME* SUNA NAN A KASAR MU NIGERIA, SAI DAI KAWAI KU HANZARTA KU GARZAYA KU BIYA KUDI KU KARBA…_

_MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME…_

_SUNE A KAN SAHUN GABA INDE WAJEN SIYAN KAYAN KITCHEN NE DA NA KAWATA GIDA, WATO A TURANCE KITCHEN UTENSIL’s& HOME DECOR…_

Advertisements

_INA UWARGIDA? AMARYA? YAMMATA DAKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI? ZAWARA MASU SHIGA DAGA CIKI? IYAYE MASU NEMAN INDA ZASU SAYAWA ‘YAYAN SU KAYAN GIDA? YAYYE MAZA, MIJIN MATAR SA😉? SAURAYI DAKE SON BURGE BUDURWAR SA WAJEN GWANGWAJE KYAUTA? TOH *MAAB LUXURY HOME* TA TANADAR MUKU DUKKANIN ABUBUWAN AMFANI NA KITCHEN, DANA KAWATA GIDA, YAITA WALWALI YANA HASKAKAWA.._

_AKWAI KAYAN KITCHEN MAI KAWATA KITCHEN, WANDA ZAI SA KISHIYA KWAFA, YASA DANGIN MIJI SU FARA HABA HABA DAKE, DUK INDA AKA SHIGO CIKIN GIDAN KI ASAN EH TABBAS KEMA KINA AMFANI DA KAYAN *MAAB LUXURY HOME*, KAYAN KAWAATA GIDAJE MASU HASKA KO’INA NA GIDAN KI, KAGA GIDA A NIGERIA AMMA TAMKAR A NAHIYAR ‘KETARE.._

_MAAB LUXURY HOME, TANA SAIDA KAYAYYAKI MASU INGANCI DA KYAWUN GASKE, AKWAI RAHUSA WANDA KOMAI KANKANTAR KUDI KANA IYA SIYAN WANI ABUN AWAJENTA, KAYANTA BA SAI MASU KUDI BA, KOWA YANA IYA GARZAYAWA YA SIYO NASA, ABUBUWAN DA YAWA, KAYAN DAGA CIKI AKWAI IRIN SU:_

_DINNER SETS, SERVING TRAYS, CUTLERY SETS, JUGS, FOOD FLAKS, THERMO FLASKS. DA SAURAN SU ABUBUWAN HOME DECOR._

_DOMIN NEMAN/TUNTUBAR KAYAYYAKIN *MAAB LUXURY HOME*, GA DETAILS DIN KAMAR HAKA: _

_INSTAGRAM: MaabLuxury home._

_WhatsApp number: +491521 4642007_

Advertisements

_Facebook: Maab Luxury Home_

_Adireshin su na yanar gizo: maabluxury.com_

_suna garin KANO. Amman suna tura kayayyakin su ko ina a fad’in nigeria. _

_KYAU, INGANCI, RAHUSA… SAI MAAB LUXURY HOME_

_MAAB LUXURY HOME: A NUMBER 1 PLUG FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS AND HOME DECOR._ 

_WHICHEVER WAY YOU WANT IT.. THEY’VE GOT YOU COVERED. #SUPER AFFORDABLE AND DURABLE. TELL A FRIEND TO TELL A FRIEND…. ABOUT MAAB LUXURY AND HOME. _

_100% TESTED AND TRUSTED: NATIONWIDE DELIVERIES_

_B34_

***Da asubar fari Salman ya temaka mun na shirya, Kayan da zan sassaka da duk sauran abubuwan bukata tuni tun daren jia falaki yamun gaba dasu. Ana idar da sallah kuwa, Yan dawowa daga masallaci kafin su faffara haramar tahowa, Salman yasa muka sauka, Ta waya mukai sallama da Ammi. Har cikin mota ya rakani yana rik’o hannu na,

“Allah ya miki albarka, Ya baki lapia, Allah ya karemun ke ya tsare ki daga idanun duk wani abun ‘ki.”

“Aamin Aamin Zawj.. Allah ya baka nasara a dukkanin lamuran ka.”

“Zanyi kewar ki sosai… Anya bazan biki ba?”

Nayi murmushi kawai ina rungumo shi, k’amshin turarukan jikin sa suka daki hanci na na lumshe idanu ina sake bude kofofin hancin, 

“Kada ka damu ai kullum zamu na yin video call, Da waya INSHA ALLAH!”

“Ba fa dad’ewa zaki ba, Ah to da komai ya fara dedeta zan sa a dawo dake.”

“Duk yadda kayi dai-dai ne zawj, Allah ya tsare min kai da tsarewar sa, Aamin.”

Kyakkyawar sumba yamun sannan ya sakar mun wata a goshi na, Yana sake kankame ni katamau.

“Ki kula mun da kan ki, Duk extra abunda kike bu’kata ki gayamun.” 

“Komai da ka bayar wadatacce ne, Allah ya saka maka da khairan.”

“Aamin Aamin… Zawjatii.”

Mun jima yana ta sakarmun shagwaba, Ganin Idan banyi da gaske ba zai bari mu tafi ba, Ahankali na zare jiki na daga nasa,

“Kar gari yayi haske..”

“Okay gimbiya tah! Allah ya kaiku lapia.”

“Aamin, Kai ma Allah ya baka sa’a.”

Sallama mukai ya koma ciki mu kuma muka ja mota muka tafi, Ni da Umma Hansatu. Su Gwaggo Ta Fada sunyi matukar farin cikin gani na, Suka rasa inda zasu saka kansu don dadi, Sai nan-nan akeyi da ni, Sunata tarairayata. Ruwa na watsa kawai nabi lapiar gado, Na shiga baccin daren jia da banyi ba. 

*MASARAUTAR BASANNABAS*

Duk wasu hanyoyi da zasu bi wajen ganin sun kashe abunda ke cikin dije sun kasa, Kwana biyu dijen ma gaba ki d’aya sun dena jin ta, Dan rahotan da ake binsu dashi an dena kawo musu, Dukka ninsu basuda masaniyar inda take bare su kai mata farmaki.

Ganin babu wata hanyar bullewa sai suka shirya makirci, Suka kira babban taro, Duk wani mai rawanin basannabas sun aika masa da sakon gayyata na taro da za’ayi. Lokacin SAS bayanan ma yaje ziyara masarautar gagarabadau. Falaki ya kira yake sanar dashi abunda yake faruwa kan taron gangamun da za’ayi. 

Da jin haka Salman sai ya sanarwa da gwamna abunda ake ciki, Ya kuma kira sauran masu mukamai na fad’a a ji. Duk wasu abubuwan da zasu zamo masa kariya na evidence ya bawa falaki, Ya kuma sanar dashi ta hanyar da zai kawo komai ana tsaka da yin taron.. Shaheeda ma anata b’angaren mahaifinta mai martaba da mahaifiyar ta gimbiya asmau duk sunzo tun ana sauran kwanaki 2 da taron. 

SAS..Gama wankan da yai kenan, Dama yana ta sak’e sak’e a ban’daki, Kawai ya mike ya shirya cikin kaya riga da wando na shadda ya dora hula akai, Ba karamun kyau yayi ba ya faffesa turaruka masu sanyin K’amshi. Kansa tsaye ya nufi sashen Ammi. Tana parlor da Khaleel sai Abdullah dake shirya kayan sa a akwati zai tafi karatu kasar waje nanda yan kwanaki. 

Yana shiga duk suka mike, Ciki harda Ammi data dububice cikin farin cikin ganin sa duk kuwa da tsahon lokacin da ya dawo hankalin sa basu taba had’uwa ba sai ta waya, 

“Yaya… Barka da dare.”

“Ranka ya dade!  barka da dare!”

Cewar Yareemah Khal da Abdullah, Salman ya amsa su kafin ya zube yana gayda Ammi,

“Ammi..! Barka da dare. Fatan na same ki lapia? Allah yaja kwanan ki.”

“Mai martaba…! Kai ne da kanka?”

“Ni ne Ammi.. Nace bara nazo mu gaysa”

Yana magana yana goge hawaye, Hakama Ammin dake goge hawayen farin ciki, Sosai suka kara gaisawa ya nemi waje daga kasanta ya zauna, Tayi tayi ya zauna akan kujera yak’i. Saboda girmamawa.

“Bara a kawo maka abinci.”

Mik’ewa tai tashiga kitchen da kanta ta kakkawo masa abincin ta ajiye agaban sa.

“Bismillah ga abinci nan.”

Saboda yasan idan shi kadai ne ba lalle ya ci da yawa ba kuma zata masa fada tunda tasan halin ‘kin cin abincin sa, Ya kallo Khaleel da Abdullah yana kakaro murmushi,

“Ku sakko muci mana.”

Ba yadda zasuyi haka suka sakko kowanne ya wanko hannu, Sukai bismillah suna ci, Ammi na ta kallon su cikin tsantsar k’auna, Yau ga dukkanin yayanta data mallaka a duniya, Wanda aka raba na tsahon lokaci , Yau sune agabanta kowanne cikin hankalin sa, Suna cin abincin kwarya daya. Suna ci suna hira har suka kammala, Lokacin an kira sallar ishai khaleel yajasu salla a parlorn ammi na daga bayansu gwanin ban sha’awa.. 

Bayan sun idar suka shiga wata hirar ta yaushe gamo, Don dadi Ammi tarasa ina Zata sa Kanta, Komai ta dakko saita ajiye agaban Salman har Khal da Abdullah suka fara su fa? Ai lalle tafison Salman. Agogon sa ya kalla dare yafara yi don haka ya rausayar da kai cikin girmamawa ya shiga yiwa Ammin bayanin taron da za’ai ya kar’kare da,

“Tabbas taron al-muhim dan a tozarta ni ne nasani, Domin sun jima suna tsara shi, Ban tab’a Kawo zasuyi hakan ba, Sai falaki ne yake sanar da ni tafiyar da nayi ta satin baya. Wallahi nayi matukar mamaki Ammi.”

“Kai ku tashi ku bamu waje.” Ammi ta juya tana kallon Khaleel da Abdullah. 

Salman yai saurin karkada kansa ,

“No ammi.. So nake na fada agaban su ai.”

“Toh Shikenan! Babu komai mai martaba, In sha Allahu! Za Kai galaba akan su da yardar mai duka. Kai da Allah ka dogara, Domin komai nisan dare gari zai Waye, Allah zai bayyana mai gaskia. Allah yasa hakane mafi alkhairi.”

Hawaye ne suka shiga zubo masa yai hanzarin gogewa yana dedeta muryar sa,

“Ammi ki gafarce ni da abunda zan fada dan ALLAH”

“Ina sauraron ka.”

“Ammi wani tunani na yanke ‘dazu a zuciata, Ammi sanda aka dakko ni a makaranta aka nad’ani sarki ba so nake ba, Har kwanan yau kuwa bana jin sarauta a raina Ammi, Domin gaba d’aya kambun mulkin ma a hannun su yake sai Yadda suka tsara, Kawai dai Allah ne ya kubutar dani daga gare su, Hankali na ya dawo na fara gano yadda shugabancin yake.”

“Duk na sani, Kuma Insha Allahu yadda komai yake kan warwarewa Allah zai cigaba da dafawa mulkin ka.”

Yanzun Kuka ne yaci karfin sa yayi mai isar sa yana mai sake matsawa daf da Ammin ya kamo kafafunta yana hawaye,

“So nake na bar musu sarautar Ammi… Hakan shine zaifi koda kuwa komai ya warware. Mu kanmu zamu fi zama cikin kwanciyar hankula da nutsuwa.”

Ammi ta girgiza kai itama tana goge nata hawayen,

“Karkace haka salmanu, Wannan sarautar taka burin mahaifin ka ne kai kanka kasani, Maganar sa Kullum bata wuce idan kaine da ragamar mulkin basannabas to tabbas Za’a samu adalci da zaman lapia, Domin tun kana ‘kankanin ka da kai, Ka keda kauda kai a abubuwa da dama, Kanada hak’uri da sanin yakamata, Dan Allah kar hak’urin ka yau ya gaza mana mai martaba, Kacigaba da hak’uri ka kara hak’uri karka bar musu gadon mulki, Makiya ai dariya za suyi, Gani zasuyi tamkar sun ci galaba akan ka ne…”

“Shikenan Ammi.. Dama amincewar ki nake nema, Na hakura.”

“Allah ya maka albarka, Yaci gaba da maka rik’o da lamuran ka.”

“Aamin Ammi..”

Nan su Khal suma suka shiga yi masa addu’a sosai, Salman dik farin ciki ya ishe sa, Yau Gashi wajen Ammi cikin sauran yan uwan sa sunata zumunci. Sai da dare yaja, Sannan ya mike zai tafi su Khaleel na masa rakiya, Har ya kai k’ofa ya dawo yana kallon Khal yana daria,

“Ammi.. Ya gaya miki kuwa?”

Ammi tayi murmushi tana kallon Khaleel din itama,

“Zancen Dr.?”

Salman yai daria yana rufe baki alamun mamaki,

“Yanzu Khal ka gayawa Ammi zancen Dr Bintuu? Baka ji kunya ba? “

Khal ya shiga sosa keya yana wasa da zoben azurfar hannun sa.

“Ai nace da komai ya daidaita sai aje ayi tambaya akai komai ko?”

Cewar Ammi tana daria, Salman ya gyada kai yana dafo kafad’ar Khal yana tsokanar sa,

“Oh dana dauka dana Abdullah Za’a hada, Idan ya kare karatu ya dawo.”

Duk suka tuntsire da dariya banda Khal dake wa Salman kallon ‘gaskia a’ah..’ Wasa da daria sosai suka yiyyi sannan yai musu sallama ya wuce sashen sa ta kofar baya, Kalaman Ammi na dad’a kara masa kwarin gwiwar cigaba da gudanar da mulkin Basannabas. 

*RANAR TARO….*

Tun daga babban gate da zai sada ka da cikin masarautar ta basannabas zaka fara hango motoci da suka amsa sunayen su, Kowanne mai nad’i da sarauta tsatson Basannabas yazo taron da bawanda yasan masaniyar me Za’a gudanar aciki. 

Duk girman masarautar Basannabas, Sai da wajen faka motoci yayi Kadan, Aka dinga faka motoci har awajen farfajiyar masarautar, Su kansu su waziri sunyi mamakin ganin yadda ake tuk’akowa rukuni rukuni harda su sarkin musulmai Prof Ibrahim Ibrahim, Su Limamin masallacin Basannabas, Su Tafida, Sarkin kasuwa da sauran su. A farfajiyar cikin masarautar aka saka kujeru da carpets carpets, Gefe d’aya majigi ne aka sashi babba, Wanda dik a’inda kake a tsaye ko zaune zaka hango duk abubuwan dake faruwa a wajen taron. 

Waziri ya dubi wambai  yana rufe hannun sa da bakin sa,

“Majigi kuma? Me za’ai da majigi? Waya sa akawo?”

Wambai ya karkada kai yana mamakin ganin majigin shima,

“Ranka ya dade wallahi bansani ba.” 

“Tambayo mana chiroma kaji, Allah yasa ba shine yayo wata kullalliyar ba.”

Tashi wambai yai ya koma wajen da chiroma da galadima suke, tambayar su yayi, Kowanne yace shima baida masaniya. Ya dawo ya sanarwa waziri, Duk da haka zuciar Waziri nata kokonto akai,

“Toh Waye yayi haka?”

“Kila cikin su Mama Huwaila ne ko?”

“Eh zai Iya yiwuwa.”

Suna tai da Zaune, Baki sai tudadowa suke Kowanne da rawani kunnuwa biyu, 

“Ni kai na ma ciwo yake yi, wambai! Kanada dan Panadol kuwa?”

“Wallahi ranka ya dade babu, Sai dai nasa a samo maka, Tashi yai ya nemo Panadol sachet d’aya ya bawa Waziri da ruwan roba, Yasha biyu yana dafe kan nasa dake sara masa sosai. Wuri ya cika ya batse zuwan mai martaba kawai ake yi. 

*SAS* 

Yana daga saman fadar sa yana hango komai, Yayi wata iriyar shiga kasaitacciya mai d’auke da wani irin ado mai haskakawa, Lalle Allah yayi halitta. Kayan ba kadan ba sun amshi tsarin halittar jikin sa. Sallah nafila ya idar ta neman samun nasara akan lamuran sa, Shine ya mike bayan yayi adduoi ya tsaya yana kallon al’ummar dake zazzaune. 

Cikin takun sa na kasaitaccen sarki mai jini a jika ya shiga sauka daga benen, Labbansa na motsawa na addu’oin da yake karantawa. Gaba d’aya duk inda ya wuce kamshin turare ne ke tashi, A k’asan parlorn sashen sa ya tarar dasu falaki da Alhassan,

“Takawar ka lapia dawisu sarkin ado, Ina gwanin wasu? ga nawa.. Allah yaja zamanin sarkin mu, Kayi musu fintinkau, Allah yakara maka daukaka, Nasara taka ce da ikon mai iko…”

Falaki ne ya shiga yi masa kirari yana rissina masa, Alhassan ma ya dauka yana cigaba da kara yi masa wani, Salman dai murmushi kawai yayi, Falaki ya leka ya kira dogaran sarki, Suka rufe shi gaba da baya, Haka suka wuce tare dashi har zuwa wajen taron, Ya zauna a babban wajen da aka tanada masa, Gefen sa daga kasa dogaran suka zauna, Ciki harda falaki da Alhassan. Sai daya zauna sannan sauran fadawan da suka kakkare shi da rigunan su suma suka zazzauna. 

Sannu ahankali kowanne dake wajen taron ya shiga zuwa ya rissina wajen Salman ya kwashi gaisuwa, Fadawa na amsa su bayan sun kira sunayen sarautar su. Ciki harda Waziri da yan tawagar su, Da Kowanne kansu a sunne kallo d’aya zaka musu kasan basuda gaskia, Waziri kuwa da kansa ke barazanar ‘ballowa daga gangar jikin sa saboda azabar ciwo riko gefen rigar wambai yai ya temaka masa suka mike. Panadol dinnan kuwa dik bayan minti yake ‘balla ya sha, Yana tafe yana runtse idanun sa,

“Kan nan nawa ya’ki lafawa.”

“Allah yakara maka lapia zai lafa da yardar Allah.” 

Wambai ya shiga karfafawa Waziri gwiwa. Salman dai yana hakimce akan kujerar sa, Sauran baki dake wajen kowa yana sauraron yaji abinda yasa aka tara su. Waziri ne ya tsaya a wajen da aka tanadar don magana ya kira wanda zai bude taro da addua. Bayan an bude taro da addua, Waziri ya sake koma wajen lasifa ya dauka ya shiga gaisuwar ban girma ga mai martaba da kuma bayanin lale maraba ga sauran yan majalisar sarki dama sauran baki dake wajen. 

Kowa yayi shiru yana sauraron Waziri, Ciki harda Salman dake son yaji ta inda zasu fara. Ya fara bada labarin tarihin masarautar Basannabas a takaice. Daga nan Waziri ya koma ya zauna, Wambai ya taso yafara bada nasa bayanin. 

“I naiwa dukkanin daukacin al’ummar wajen nan barka da zuwa, Musanman mai martaba sarkin mu Salman Aliyu Salmanu. Mai girma sarkin musulmi, Mai girma limamin basannabas, Mai girma san turaki, Tafida…. Yaita lissafo masu manyan mukamai, Sannan yai jam’u yanaiwa kowa barka da zuwa.”

Bayan yagama ya koma ya zauna. Galadima yataso yana tafiya dakyar saboda ciwon kafa. Ya gayshe gayshen sa, ya karkare da.

“Toh wannan gayyata da akaiwa duk wanda ya halarci wajen taron nan Za’a tattauna akan wasu abubuwa biyu ne zuwa 3. Wanda mu yan majalisar sarki muna cikin alhini, Abun yanata cin mu, Har ya zamto muna kokarin yanke hukunci, Waziri ya hana mu, Domin Waziri tamkar mahaifi yake awajen sarkin mu. Muka hakura abubuwa dai suka cigaba da gudana barkatai ba tsari. Daga karshe ganin shi kansa Waziri ya kasa ya nemi damu hada taro kowa ya halarta ya kuma ga sakamako don kada mu yanke hukunci da ka. Saboda idan mukace zamuyi shiru to lallai ragamar mulkin Basannabas na gab da tabarbarewa.”

Galadima ya fashe da kukan makirci yana goge hancin sa hankici. Cikin kuka ya shiga kiran chiroma . Dukkanin daukacin mutanen dake wajen suka fara surutu kowa yana tofa albarkacin bakin sa. Salman dake zaune sake gyara zaman sa yak yana kallon kalar makircin Kowannen su ta cikin gilashin sa, Chiroma ya karbu lasufika ya cigaba da magana,

“A gafarci galadima, Abubuwan ne ba dadin fada, bare saurara… Wato maganar dai ku gafarce ni baki d’aya ta shafi sarkin mu ne Salman, Wanda mu ba zamu iya yanke hukunci ba sai da izinin kowannen ku nan, Duk dai wasu sakamakon bincike mun tanada, Dukkanin ku da kun gansu zamu yi gaggawar yanke hukunci…”

Kowa yai shiru yana jiran chiroma ya k’arasa. Salman kuwa murmushi kawai yake yana mamakin su, Wannan ko gaskiya ne abunda suke fada, Wanne irin tozarci ne har haka? Har abada sun gama kunce masarautar Basannabas mai tarin sarauta, Ita sauran masarautu ke kwaikwaya a komai, Amma sai yau gashi rana d’aya, Yan Uwan sa, ko ace iyayen sama sune keson ganin bayan sa, Duk akan gadon mulki? Ajiyar zuciya ya sauke yana cigaba da addu’oin da yake yi. Chiroma ya sake gyaran murya yana yi da karfi sosai,

“Abu biyu ne ya masu matukar razana, Abune mai daure Kai da haddasa ciwo a zucia. Kowa yasani, Bamu kad’ai ba har mutanen gari, Ga sheda nan awaje na, Gimbiya shaheeda matar mai martaba ta farko ita ta bamu, Kowa yasan sarki Salman baya haihuwa, Bayada ishasshiyar lapia, likitoci na kasashe wajen biyar sun sanar a bincike da suka yi baya haihuwa, Shi kansa gashi nan mai martaban bai musa hakan ba duk tsawon shekarun nan. 

“Rana d’aya, Ya karo aure, Bamuda masaniyar zaiyin ma yayo bamu hana ba, Duk kuwa da ba haka tsarin yake ba, Amma yayi biris da zancen mu ya karo auren wata daban da bamu san wacece ba, Rana tsaka sai ga juna biyu, Ana yamadidin ai na matar sarki ne gimbiya Khadija.. Shin taya tasamu juna biyu  bayan hakan ba Zata taba faruwa ba? Duk tsawon shekarun da sukai da gimbiya shaheedah bata taba nuna gazawarta ba, Tayi hak’uri ta zauna dashi. Amma mai martaba yaci amanarta haka. Tambayar mu anan juna biyun wannene gimbiya Khadija ke dauke dashi?,

“Tunda ya auro ta ya dena jin maganar Waziri, Domin Waziri shine ke nuna masa yadda zai tafiyar da mulkin Basannabas. Duk kuwa dama bobboyewa ake yau ya kamata afito a fadi gaskia, Waziri shine ke mulkar Basannabas, Kowa yasan waziri bashida lokacin kansa, Kullum yana tare da sarki yana nuna masa abubuwan mulki, Gaba d’aya yadda Basannabas ke tserewa sauran masarautu akan mulki da adalci duk Waziri ne. Allah ya Kara muku Lapia baki d’ayan ku, Shigowar wannan mata ta mai martaba Basannabas ba alkhairi bane, Domin tundaga lokacin ya juya wa Waziri baya akan komi sai abunda tace. Duk kuwa da rabin rayuwar sa akan gado yake yinta kullum ba ishasshiyar lapia,

“Sai Waziri ne ke jagorantar masarautar, Mun sha tambayar sa ya gaya mana gaskiyar alamari akan juna biyun gimbiya Khadija yak’i fada. Daga karshe sai ya futar da ita daga cikin masarautar ma baki d’aya, Ga matar sa tafarko nan tun sanda ya karo aure baya kulata ya dena shiga harkarta ranku ya dade. Kwanaki har hannu ya daga ya sharara mata mari ya farfasa mata jiki agaban gimbiya Khadija, Wai akan ta shiga turakar sa ba iso, sai datai sati tana jinya, Ga mahaifinta nan sarkin bullo shima ya halarci taron,

Tari ya shiga yi yana matse matsen hawayen Karya, Kallo ya koma kan Salman dake bin chiroma da kallo yana jiran ya Karasa jin Sharrin da yake ta zayyanowa. Chiroma ya sharce majina yana cigaba,

“Wasu abubuwan ma dai ba zasu fad’u ba saboda sunyi tsauri ainun, Daga ciki akwai yadda asusun masarauta ya yashe, Babu abun arziki, Komai ya kare mana a masarautar nan. Munce ya je ya nemi lapiar sa yaki. Allah ya kara muku Lapia a duba zancen nan, Shi sarki ne a zahiri yadda yake zaune dinnan amma a badini sai Waziri ya temaka masa, Bashida Lapia ta k’wanyar kai da gangar jiki, Idan Karya labbana suke, Gashi a tambaye shi ko yasan yan uwan sa da suke ciki d’aya, Yareemah Khaleel da yareemah Abdullah! Allah ya Kara muku Lapia shi kansa Yareemah Khaleel din yana can K’asar waje yana masha’arsa, Yareemah Abdulqadeer da su Kai makaranta d’aya yayi yayi su dawo yaki.” 

Haka chiroma ya shiga hada karairaki yanata zayyanawa, Ya karkad’e da,

“Wadannan sune ka’dan daga cikin Matsalar dayasa muka hada wannan babban taro, Munason ku duba zancen mu, Ku kuma hada kai wajen tsaida hukunci d’aya, Ko dai a sauke mai martaba sarki Salmanu, Ko kuma yayi Murabus da kansa a yau yaje ya nemi lapiar kwakwalwar sa, Ya kuma kauda waswasin cewar ‘dan cikin gimbiya Khadija nasa ne…”

Sallama yayi ya koma wajen zaman sa ya zauna yana murmushi, Waziri sai bin sauran yan majalisar sarki yake da kallo yana ganin yanayin su. So yake alokacin su yanke hukunci. Salman yai dariya kawai yana mamakin shirmen su. Bai tab’a zata haka zasuyi abun ba tsari ba sai yanzu. Lalle ya raina kololuwar tunanin su ciki da waje. Sign yayiwa falaki, Falaki ya fita da sauri yana danna wayar hannun sa. Gyaran murya ya sake yi Alhassan ya gyada kai shima yabi ta baya ya koma can karshe da remote din majigi a hannun sa.

Cikin haka sai ga gwamna yazo, Waziri yayi matukar mamakin ganin gwamna, Amman duk da haka yaji dadi don gani yake gwamnan a bayan su yake. Saboda gwamna na da ikon cire sarki ya canza wani, Idan aka kama sarkin da babban laifi, Jikin Waziri na rawa saboda murna ya tashi ya yiwa gwamna lale maraba da yan tawagar sa. Ya kuma sake yin bayanin komai a takaice. Murmushi kawai Salman yai, Dogarin sa ya dakko wata hadaddiyar lasifika ta magana ya zura masa a jikin rawanin sa. A kasaice yana bin Kowanne su da kallo. Adduoi ya fara yi tamkar balarabe, Sannan ya kara da cewa,

“Assalamu Alaikum wa rahamatu Allah wa barakatouh, Ina yiwa d’aukacin mahalarta wannan taron barka da zuwa, Musanman mai girma gwamna da masu girma iyaye na masu albarka, Duk kuwa da bansan hakikanin abunda taron zai gudanar ba sai yanzu da akai magana akan sa, Naji dadi kwarai da gaske, Kuma dama ina fatan hakan tafaru, Ko ba jima ko ba dade dama yakamata kowannen ku yasan komai. Amma kafin sannan Za’a rarraba muku sheda ta farko ku gani a rubuce, Daganan sai sauran su biyo baya..”

Cikin haka sai ga wasu dogarai da takardu fal a hannun su, Suka shiga rarrabawa dukkanin masu rawani dake wajen, Hade da babbawa kowanne lasifika ko zaayi tambaya, Mai girma gwamna ma aka bashi, Kowa ya shiga dubawa. Ciki harda su waziri dake neman haukacewa, Tashi yai jiki na bari ya isa ga lasifika yana daga takaddun yana bayani,

“Wannan ai ba zasu bamu gamsasshiyar amsa ba, Domin Za’a iya zuwa ayi na bogi.”

Sai haske wal, Alhassan ya kunno majigin nan, Bayanin likitocin suka shiga yi daga wannan yagama na wannan asibitin yayi, A haka har asibiticin biyar suka gama magana suna bada hak’uri. Kallo ya koma kan Waziri, Mai martaba sarkin Bullo ya fusata matuka jin ana karyata shaheedah, Ya shiga karyata zancen Salman yana bubbuga k’afar sa, Ransa ya sosu sosai. Salman yai murmushi kawai,

“Masu girma Kunga dai zancen farko yadda sakamakon su ya kasance, Wallahi.. Lapia ta qalau, gimbiya shaheedah ita tahada makircin ta da likitocin suka bada results na bogi a lokacin.”

“Amma mai martaba ya akai duk kasashen nan da sanin ka kukaje amma amma har suka maka ‘kage haka?”

Cewar Tafida yana daga inda yake a zaune. Salman ya kada kai,

“Baba Tafida… Duk kasashen da mukaje alokacin bansan inda kai na yake ba, An jefe ni da sihiri, Ban isa na aikata abu da karan kai na ba sede a bani Iko, Kasashen da muka jajje asibiti dik mai martaba Ibrahim Hashimu ne ya dauki nauyi.. Na kuma yadda hakan ne ban musa ba, Sai bayan na karo aure komai ya warware a bangare na sena tafi wata ‘kasa a boye naje aka sake mun general checkup anan aka tabbatar mun da kalau nake. Ashe matsala badaga waje na bane daga wajen gimbiya shaheeda take.”

Guri ya dauka da maganar mutane, Sarki Ibrahim Hashimu duk kunya ta kamashi ganin yadda ake juyawa ana kallon sa. Waziri ya dafe kansa dake jujjuya masa yana kallon su wambai. Salman ya sake yin wani tattausan murmushin yana jan kasan leben sa,

“Toh dai bangaren banida Lapia bazan iya haihuwa ba duk zancen kanzon kurege ne, Wanda aka shirya shi cikin tsantsar makirci da tsibbu, Sannan juna biyu da gimbiya Khadija ke dashi, Nawa ne halak malak Dr. Fiddausi Mashi jikar sarkin cillire ita ta tabbatar mana mai daki na ta samu karuwa, Da banyi niyyar fadar komai ba, Amma Tunda abun Yazo da haka, Gwara na warware duk wani d’aurin goro. Na kara aure ne saboda ina da ra’ayin karawar, Babu ruwana da lalle sai diyar wane, Babu ruwana da nasabar ta, babu ruwana da ilimin ta, babu ruwana da abinda wani zai fada a kan ta. Ita nake so a hakan ta. Tarbiyyar ta ta isheni komai. Matsayin ta a gareni ya wuce mizani . 

“Inaso na nunama duniya wacece ita a gareni. inaso na shelantama masu mulki irina su san cewa ba sai mace tana da irin nasabarsu ko nagartarsu bane ta cancanci zama matarsu.  Na yi koyi da mahaifina Marigayi mai martaba Aliyu Salmanu. Dan shima ya auri mahaifiyata da irin matsayin da gimbiya Khadija ke dashi lokacin da yake matsayin sarki. Wannan shine tabbacin sanadin girmama kiyayyarta da tamu a cikin masarautar basannabas. Lalle tarihi ya sake maimaita kansa,  mabudin karya lagon kaifin duk wani jahilin dake tunanin yar mulki sai dan mulki? Talaka sai dan uwansa talaka. Daga rana irinta sanda na auri Khadija, Ni Salman sarkin Basannabas na biyu na soke duk wata kirkirarriyar al’ada ta cewa sarki sai ya auri tsatson sarauta. Kowa yana da damar auren burin ran sa. 

“Tunda na aurota ake jifanta da asiri kala kala, Wanda har sai da aka dauketa daga masarautar akai mata magani, Da temakon Allah da dagewar Khadija akai na na samu lapia daga sihirin da aka manna mun, Bayan tadawo masarauta kuma bata tsira ba, Ace mutim da matar sa amma babu damar suyi auratayya? Ranku ya dade…! Har cikin shukar sashe na gimbiya Shaheedah ta binne wani tsibbu duk dan kar na dau Khadija a matsayin matata..”

Wuri ya kacame da magana, Sarki Ibrahim Hashimu ya shiga karyatawa yana magana da karfi cikin izzar sarauta,

“Shaheeda ba zata taba aikata haka ba, Wannan shiryayyar magana ce kawai don wata manufa taka ta daban.”

Cikin haka sai ga falaki da bokan daya fassara ma’anar tsibbun da shaheedah ta binne,

“Ga sheda anan zai fadi komai… Amma kafin sannan bara ku kara ganin tabbacin magana ta.”

Alhassan ya saka Video din sanda shaheedah da batula ke binne kwadon nan a sashen sa acikin shuka, Wasu duk suka mimmike suna kallon ikon Allah, Sosai jikin sarki Ibrahim Hashimu ya fara rawa yaja kasan rawanin sa yana dartse harshen sa.

“Toh bayan anyi haka sai na saka falaki ya tone yaje ya nemo wanda zai iya sanar mana da musabbabbin binne wannan kwado.” 

Falaki ya fito da kwado da laya ya ajiye kowa yana gani, Bokan ya shiga fad’ar amfanin saka kwadon da yadda zai illata rayuwar Khadija. Guri ya dau magana kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa. Falaki ya sallami bokan ya tashi ya tafi. 

“Ina fatan masu girma kuna yadda da zance na ganin gashi nan a zahiri kuna gani.” 

“Allah ya kara maka lapia muna gani. Lalle makiya sun maka zobe.” Cewar san turakin Basannabas. 

“Yanzu kimiya da fasaha sun kara daukaka a duniya, Wannan fefen bidiyoyi kawai kerawa akai aka yisu, Don a soki gimbiya shaheedah, Fuskar ta Za’a cira a saka, Da sani akayi haka.” Waziri Yafada yana kallon Salman kur da idanu. 

Salman ya numfasa, Yana kambama kokarin Waziri,

“Yanzu duk wannan shedar duk basu kwanta maka ba Waziri?”

“Kwarai ranka ya dade, Basu kwanta ba. Ban yadda dasu ba.”

“Toh shikenan, Ina tunanin wadanda Za’a saka yanzu zaka gamsu da su.”

Alhassan ya danna duk wasu videos da na’urar cctv ta dinga recording, Gashinan komai anaji ana kuma gani tamkar alokacin akeyi, Kowane sashe na masarautar yana ciki, Banda na Ammi. Amma gaba d’aya sauran sashen kowa nasa yana nan. Kuma Kowanne anata nunawa, Waziri jikin sa ya fara rawa ganin komai da suke aikatawa shida matan gidan da su wambai gashi nan ana nunawa kamar alokacin, Har sanda shaheedah taje bangaren nasu da zancen da suka yiyyi. Duk wasu abubuwa da suka aikata duk ananata nunawa, A takaice dai babu abunda babu. Aka shiga kallon kallo kowa yana mamakin su waziri. Wurin yayi shiru, Yai tsit tamkar ruwa ya cinye, Da alama mamaki dukkanin su suke yi. 

“Ran sarki ya jima, Lalle kayi namijin kokari wajen gano komai. Shin ta yaya akai hakan batare da kowa yasani ba cikin su, Kenan dama kana hankalce da komai? Ko kuwa wani ne yake temaka maka?”

Majidadin Basannabas ya tambaya cikin tsantsar mamaki.

“Ai majidadi magana ce mai tsawo, Tunda Waziri yace bai aminta ba, Zan danyi y’ar takaitacciyar magana kafin a sake sakin wasu bidiyon. Kamar yadda Kowannen ku ya sani, An nadani sarki bayan mahaifi na ya rasu. Lokacin ina makaranta ma na gama ban dawo ba aka dakko ni ko result ban tsaya karba ba sai daga baya. Bayan dawowata da maganar alokacin yan majalisa na tsaka da shawarar ranar nad’i, Idan baku manta ba. An bada wasu kwanaki 5 kan kowa ya koma can kuryar tsohon ginin da da anan su Baffa suke kafin adanyi renovating nan din, Tunda kowanne sarki kafin ya hau sai anyi gyare gyaren masarauta ciki da waje, Toh a dan tsukukun nan nayi amfani da damar saka duk na’urar cctv recorder a sashen dake daukacin masarautar baki d’aya. banda na gimbiya shaheedah, Saboda alokacin itama tanada mugun nufi akai na. Ita sai bayan naje nayi checkup naga lapia nake, Sai na saka nata daga baya ina hankaltar motsin ta. Ni da Aminai na biyu muka zauna muka tsara komai, Domin tun a lokacin na fuskanci inada makiya na fili, Falaki da Alhassan babban bafade na dasu muka tsara komai, Duk kuwa da bayan an nad’ani sarauta sai aka juyar mun da hankali ya zamto na manta komai, Amman Alhamdulillahi da temakon su falaki bayan na dawo daidai sune suka tunasar dani sashen da na’urorin suke, Ashe daman a boye suna zuwa suyita adana komai…. A takaice da temakon wadannan bidiyoyi nasan masoyana da makiyana na fili dana boye.” 

Yana gama magana Alhassan ya saki sautin tracking din da akaiwa su waziri dasu wambai, Duk inda suka jajje da maganar da suke yi duk ana jiyo komai, Salman ya cigaba da cewa,

“Bantab’a sanin Waziri cin dunduniyata yake yi ba, Amma dama ance, Mugu bai da kama. Har wajen bokan da yake zuwa sai da mukai tracing muka aika yanzu haka yana nan Za’a kirawo shi.”

Ai Waziri bai karasa Jin Salman ba  ya yanke jiki ya fadi yana dafe kansa. Cikin haka sai ga bokan sa da yar tsintsiyar sa a hannu. Nan bokan ya zauna ya fadi komai na daga tsibbun da Waziri yake sa shi ya yiyyi. Waziri ya shiga kuka wiwi yana bori. 

“Nayi matukar razana da ganin tarkon da wazirin yake yimun, Ban taba dauka shine jagoran makiyana ba, Hakika na dauki Waziri tamkar mahaifi na, Domin haka na taso na gansu tare da mahaifi na. Ban taba dauka zaici amanar abotar su da mahaifi na ba data zumunci yarika nakasa mun rayuwata har haka ba. Nayi mamaki, Mamaki mai matukar razanawa.”

Salman ya cigaba da magana yana goge hawayen dake zuba a idanun sa,

“Wambai, Chiroma, Galadima, Da su Mama Huwaila da ‘yayansu gaba d’aya ba sona suke ba, Sun dauki karan tsana sun dora mana, Duk wani tuggu da sharri akai na da mahaifiya ta ake zuba shi, Wani abun tausayin harda matata shaheeda aka hada baki ana cutata itama kuma tana yin nata tsibbun na daban. Itada mahaifiyar ta kullum cikin asiri, Abun na matukar dauremun kai… Tun samun juna biyun gimbiya Khadija kuma sai suka kara daura damara gaba d’aya su da yayan su da ita kanta shaheedan da mahaifiyar ta kullum cikin farmakin juna biyun Khadija suke… Alhassan saki bidiyos dinnan na shaheeda.”

Alhassan ya saka, Tiryan tiryan aka dinga nuna dukkanin abubuwan da shaheeda keyi, Da sanda suke waya da mahaifiyar ta akan cikin. Cikin zafin nama sarki Ibrahim Hashimu ya shiga magana ,

“Wannan ai kana shiga hurumin daba naka ba, Sirrinta ne kaje kana shiga meyasa? Sam bai kamata ba.” 

“Ranka ya dade daka kara hak’uri ka cigaba da saurara, Shin wacece gimbiya Rahama?”

“Ya akayi? Itama zaka ce ta maka sihirin ne? Iye?”

“A’ah ranka ya dade, Ka cigaba da saurara dai.”

Nan aka cigaba da nuna sanda suke waya , Gimbiya Asmau na gayawa shaheeda ta kwantar da hankalin ta ko gimbiya Rahama ma iska ta turawa cikin ta haife katangare gashi nan sai tarihi. Ai bai karasa saurara ba sarki Ibrahim ya mike cikin zafin nama ya nufi sashen gimbiya shaheedah. Nan waje yacigaba da kacamewa da bidiyoyin al’ajabi da aketa saki. Daga wannan sai wannan, Wannan ya kare wannan ya shiga, Sannu ahankali har aka gama kallo da sauraron kowanne. 

“Sai magana ta biyu sunce inata barnatar da asusun masarauta, Sun manta da kambun mulki a hannun su yake, Sai yadda suka yanke. Bani da damar na musa sai sun sani a gaba, Musanman wambai dasu galadima..”

Ai Salman bai karasa ba su wambai suka shiga magana Kowanne Yana mai nuni da Waziri dake a yashe yana koke koken kansa zai ‘balle. Kuka yake wiwi yasan yau tasu ta Kare,

“Duk kutingwilar Waziri ne..”

Cewar Galadima, Cikin rawar jiki.

“Yallabai duk sanda zakaji muna shi ya aiko mu, Ko kuma muce daga sama, Yasin Waziri ne, Shine ummul aba’isin komai. Mu kanmu bamuda ra’ayin kanmu sai abunda ya zartar.” 

Wambai ya fada yana mai kwakwaso rantsuwa ya dire. 

“Tabbas ranka ya dade dik abunda suka fada haka yake, Waziri ne jagoran mu, Komai shi yake kitsa shi.” Cewar chiroma.

Salman yai daria yana girgiza kai, Sun bashi daria ainun, 

“Duk naji zancen ku Baba, Na kuma san shine shugaban ku, Amma kamar yadda Kowa yagani a bidiyo, kuma kowannen ku Yanada wani quduri na daban acikin zuciar sa, Kamar Kai chiroma so kake a sauke ni jikan ka ya gaji mulki,Wato  k’ani na dan Mama Huwaila, Makaman Basannabas, Wanda kukasa aka nada sarauta a satin daya dawo daga waje. Sai kai galadima so kake sarauta ta dawo hannun ku tsatson Masekiri Tajiri, Sai kai wambai Kai kuma jelar Waziri ne, Duk inda yai kana nan, So yake ya karb’u sarauta tinda baida jikoki maza sai mata, Idan ya zama sarki kai ne zaka zama wazirin sa…” 

Rantse rantse suka fara yi, Salman ya juyar da kansa kawai yana duban mutanen wajen baki d’aya 

“Makiya sunmun zobe gaba da baya koina ba madafa, Jakadiya ta ma itama ashe tasu ce, Hadimai na da wasu daga dogarai na duk yan leken asirin su Baba Waziri ne. Maganr yashe kudi da suke yi ga ma’aji nan ku tambaye shi sisi dan yin abun Kai na bana Karb’a duk suke wawure komai yadda sukaga dama. Da hankali na ya dawo ne nasa aka kwashe rabi da kwatan asusun masarauta na bawa ma’aji karami ajiya, Maganar ba kudi da suke fada suna da sheda, Amsar itace asusun masarauta na dauke shi daga hannun ma’aji babba ya koma hannun ma’aji k’arami. Sai magana ta gaba akan ai banda lapiar kwakwalwa? Shin Waziri wacce iriyar rashin lapia ce kwakwalwa tah ke dauke da ita?”

Waziri na kwance ya mike da azama yana karkade jikin sa jin an tabo masa inda yake masa kaikayi. 

“Ai ba Karya nayi ba, Garin shaye shayen ku da mugun abunda mahaifiyar ku keyi ne yasa kwakwalwar ku ta juya daga kai har su. Ai an tanbayeka dazu ma kayi shiru, shin wanene Yareemah Khaleel da Abdullah agare ka? Wacece Hajia Sa’adatu, Jama’a kowa ya saurara yanzu zaku tabbata yana da matsala a kwakwalwa..”

Salman yai murmushin gefen baki yana jan kasan leben sa. 

“Waziri idan bacci kake gwara ka farka, Waye yake shaye shaye? Wacece ke aikata mugun abu? Kada ka zarce iyakar magana, Ka daidaita bakin ka, Babu ruwana da kusancin mu na jini, Wannan magana da kai zata iya kaika ga halaka..”

“Nide tambaya nayi ai, Kowa yana sauraron ka. Ka basu amsa.”

“Ammi…. Gimbiya Sa’adatu Abdullah diyar marigayi sarkin kofa na da, Itace mahaifiya ta, Sannan Yareemah Abdullah da…”

Bai karasa ba Waziri ya dire tsalle sai gashi agaban gwamna,

“Ranka ya dade a duba kunnuwan sa, Na tabbata wani ne ke sanar masa.”

Salman yai daria mai sauti, Ya tashi dogaran sa suka rufe shi, Ahankali aka kammala sunce rawanin kansa, Kyakkyawar hular kansa ta bayyana. Ya cigaba da cewa,

“Ga sheda nan kaga ni ko? Babu komai a kunnuwana Waziri, Dan Allah ka sawa zuciar ka salama, Baka ganin yan uwanka yadda suka fadi gaskiar su? To Shikenan dai. Yareemah Abdullah wanda yaci sunan kakan mu, Mahaifin Ammi, shine dan autan mu, Yanzu haka shiri yake zai tafi kasar waje yin university, Sai Yareemah Ibrahim wanda akafi sani da Khal, Ko ince Dr. Ko? Domin ya zama cikakken likita da zai iya fede cikin ka Waziri ya juya maka kayan hanjin ka. A fefen bidiyon baya kun so yin fada da abdulqdeer kan kun kasa sanin inda yake bayan kun kafe shi acan ko? To Khal yana nan, Lapia cikin kwanciyar hankali.”

“Bamu yadda ba…”

“Karya kake, Karya kake Waziri, Waziri rissina ka bawa sarki hak’uri.”

Cewar falaki da kalaman Waziri suka wuce ‘k’ima. Waziri ya rissina gudun idanun mutane ya bawa Salman hak’uri, Salman ya cigaba da cewa,

“Noo ai bakai laifi ba Waziri, Aikin kune kun kafe shi da sihiri ya za’ai ya dawo ko? Toh lalle kun manta da Allah dake can a madakata? Yanzu haka dai Khal na nan a tare damu anan, Zan basu izini suzo dan kowannen ku ya soke waswasi daga zuciar sa. Dr. Khal, Abdullah kuzo.”

Yana rufe baki Yareemah Abdullah da Yareemah Khal suka fito, Ashe suna wani waje a boye, Khal sanye yake cikin kayan likitoci ya saqala stethoscope 🩺 a wuyan sa. Ba karamin kyau kayan suka amshi jikin sa ba, Hakama Abdullah daya baza wata shadda ya dora hula akai. Suna zuwa suka rissina suna gayda Salman, Sannan suka daga hannuwa suka gayda mutanen wajen baki d’aya, Habawa sai kallo ya koma kansu kuma baki d’aya. Masoyan su suka mike suna tafi. 

“To gashi nan dai Waziri, wambai, Chiroma, galadima, Kun gani ko? Mahaifiyar mu ma tana sashen ta hankali kwance, Sihirin dake kanmu baki d’aya ya warware, Muna kuma fatan Allah ya mai da ‘koko masaki…. Sani ne bakuyi ba, Gaba d’aya komai ya daidaita kansa, Matata kuma ta kuke neman kashe abunda ke cikin cikinta, Wannan cikin KIBIYAR AJALI  ne, Ku duba tarin harin da kuka kakkai masa amma ba abunda ya faru, Sai ma kawo karshen tuggun ku da yayi, Domin Idan kuka Auna a mizanin hankulan ku zakuga cewa tun samuwar sa zuwa yanzu komai naku yake dada tabarbarewa, Asirin ku yaketa tonuwa, Mai dauke da shi kuma kafin Allah ce. SULKE BAYA TARE TA SAI TA WUCE….”

Ya karasa fadar duk abunda bai fada ba a takaice, Yana gama magana, Dogarai suka rufe shi suka maida masa da rawanin sa. Kowa yanata Allah wadai da halinsu Waziri… Wata zungureriyar mota ce tashigo mai dauke da tambarin abinci, Abinci ne had’adde aka shiga bin kowa da ke zaune ana ajiye masa da ruwa da lemo.. Salman ne ya dauki nauyin komai, Shi da gwamna kuma suka koma cikin fada. Aka bar yan majalisa baki d’aya suna tattauna yadda sakamako zai kasance, Su Waziri sun koma gefe sunyi jigum jigum kowannen su jira yake ji matsayar da za’a yanke. 

Shi kuwa sarki Ibrahim Hashimu yana komawa sashen SHAHEEDA ransa a matukar b’ace ya shiga daddanna mata ashariya, Domin gadon zagi tayi, Sai da ya musu tatas daga ita har uwar tata Sannan ya zauna yana huci,

“Kin tozar tani fulani, Kin wulakanta ni.”

“Bappa me nayi? Wallahi sharri ake Min.”

“Uban ki kikai shaheedah, Koda yake awajen mahaifiyar ki kika gaji komai, Duk munga abunda ya faru bare ku karyata… Cikin jikin Hajia Rahama ashe Hajia ke kikai tsibbu ta haifi kadangare? Kikasa na korata gidan su ina tana tarayya da aljanu? Toh wallahi Allah ya tona asirin ku keda ita.. Babu ruwana da alkawarin auren ku da Salman, shaheedah daga yau na warware shi, Ya dauki kowane Irin mataki akan ki, Wallahi babu ruwana aciki. Kunyar da kikasa yau naji a cikin dubbannin mutane ba zan taba mantawa ba, Ke kuma Hajia na kyamaci kasancewar ki uwar yayana, Don ina kwadayin samun tsatso daga zuriar Basannabas sai ki Kawo sihiri aciki? Tunda Allah bai kawo haihuwar ba ba sai a hakura ba. Kika takura kan na bada jirgi na su zazzagaya asibiti a duba lapiar su ashe ashe sharri zaku hada? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un. Kaico, Kaico..” 

Mik’ewa yai ya fuce yabar su nan sunata bori, Kansa tsaye ya wuce wajen motar sa driver yaja shi, Bai dire koina ba sai airport, Ya koma masarautar sa, Yana ta tsara yadda zai tunkari gidan su hajja Rahama matarsa daya saka a baya ta dalilin gimbiya Asmau, Su Shaheedah kuwa sai bori suke suna farfasa kayan dakin , gimbiya Asmau na tayata, Sunayi suna kuka kamar tab’abb’u.  

     *ZAMAN MAJALISAR SARKI*

Bayan sun kammala cin abinci, Sunyi sallar azahar da aka kira a alokacin, Sake sabon zama suka yi na yanke hukuncin da za’a dauka akan karar da su Waziri suka gabatar, Da kuma sakamakon komai da Salman ya bayar shima. Gaba d’aya sun gama tattaunawa sun kuma tsaya a matsaya d’aya. Suka koma wajen gwamna, Salman ya basu waje suka sake ganawa dashi. Nan ma dai matsaya d’aya ce data baya gwamna ya bayar. Aka sake ranka yawa baki d’aya kowa ya koma wajen zaman su na waje suka zazzauna. 

San turakin Basannabas ya mike bayan ya karanto komai yai addua ya fara magana cikin nutsuwa ya k’ark’are da,

“Kusan dukkanin mu nan zuri’a d’aya ne, Tundaga kan zuriar marigayi sarki ilyasu Jirgau zuwa ga Masekiri Tajiri. Duk abu d’aya ne mu, Sai tsirari da aka bawa sarauta wanda suma baki d’aya an zama daya. Sune wakilan al’umma dake waje, Kusan duk sarautar kowa ta gado ce bata taka haye bace. Akoda yaushe masarautar muce agaba sauran na take mata baya. Kowa kwaikwayar mu yake a tsarin mulki da komai namu gwanin ban sha’awa. Munada tarbiyya, Adalci, Da sanin ya kamata. Nayi mamaki kwarai matuk’a da ire iren haka tafaru. Allah kuma yasa wannan shine karo na farko kuma na karshe, ba za’a sake samun karo na biyu ba. Mai martaba Allah ya kara maka lapia da nisan kwana mai amfani Aamin.”

“Aamin Abba.. Sai dai zan tari numfashin ka..”

“Tuba nake ranka ya dade, Allah yaja zamanin sarki Salmanu na biyu.”

“Idan har wannan hukunci da zaku yanke zai shiga tsakanin zumunci, Na rokeku da kuyi hak’uri, Ni zan sauka daga…”

“Allah yaja zamanin ka, Haba wane Mutum? Ai Kuma Idan ba’a dau mataki ba, Na bayan mu zasuyi abunda zaifi wannan, Kada ka manta tsarin mune kowane sarki sai an rubuta rayuwar da yai sanda yanakan mulki.”

Salman yai shiru yana sauraran san turakin Basannabas. San turaki yaita jawabin sa, Kafin ya kark’are da,

“Waziri da iyalan sa (Mama jaleelah), Chiroma da iyalan sa (Huwaila da zuriar ta) Galadima da iyalan sa, wambai da iyalan sa, Da sauran dukkanin mai hannu acikin abubuwan da suka aikata, Kama daga hadimai, Dogarai da matemaka da suka mara masu baya, Da matar mai Martaba ta farko gimbiya shaheedah diyar Ibrahim Hashimu, Kowanne an yanke masa hukunci, Bisaga yadda muka duba tsarin yadda doka ta shirya amatsayi na na attorney general, Da justice Umar jirgau (Tafida) Da Barr. Aliyu Aliyu Tajiri. Mun yanke dukkanin su kowa zai biya tarar kudi mai tsoka ko kuma zaman gidan yari bisaga cutar zamba cikin aminci, Sannan su matan, su Huwaila da yaran su zasu bar cikin masarautar nan don dama mai martaba ne yace su zauna lokacin da aka nadashi a ka’ida kamata yai kowa yakama gaban sa, Tunda an babbawa kowacce gado, Kowa ya gaji gida, Sai su kuma su waziri sakamakon hada kayuwa da kukai wajen tsibbu da neman halaka rayuka, Za’a ciccire ku daga sarautar ku daga rana irinta yau an cire kowannen ku daga rawanin sa, Sannan duk kanin jikokin ku su Abdulqadeer kenan suma an sauke su, Sannan ko nan gaba babu wanda zai yi sarauta acikin su. 

“Abu na biyu, Sai hak’uri da gaba d’aya ku da iyalan ku zakuje ku roka wajen mai babban daki Hajia Sa’adatu bisa cutar da ita da kuka yi itada yaranta, Kun shiga tsakanin uwa da ‘ya’ya, kun raba zumunci, Nan ma akwai cin tara sosai da zaku bibbiya, Sai maganar asusun masarauta nanma zaku biya ko a dauki kadarar ku a mayar da ita a bakacin barnar kudin da kuka yiyyi.. Sai gimbiya shaheedah wannan wuka da nama na hannun sarkin mu, Ya danganta da irin hukuncin da zai yanke a nasa bangaren. Amma bisaga hadin kai da tayi da ku da kuma nata makircin a boye za’a ci tarar ta sosai na son kisan juna biyun gimbiya Khadija dama raba tsakanin mai martaba da mahaifiyar sa. Sannan mun yanke alak’a da masarautar bullo daga rana irin ta yau…”

Haka dai yaita magana ya kasafta komai yadda zai kasance cikin nutsuwa. Daganan sarki musulmi da limaman masallacin Basannabas suka yiyyi wa’azi akan illar sihiri da tarin haramcin sa, Bayan sun kammala wa’azin san turaki ya kar’kare da,

“Toh wannan shine abunda yan majalisa suka yanke baki d’aya. Kowa yasan falaki, Falaki dan uwa ne domin jika ne agare mu, Kuma mun yaba da hankalin sa dama gudunmawar daya bawa sarkin mu, Don haka falaki zai zama wazirin sarki, Shi kuma Alhassan zamu bashi sarautar wambai. Sauran muk’aman kuma sai mun duba sosai zamu sake sabbin tsare tsare don nad’a wa’enda suka dace, Kar mu sake yin zab’en tumun dare.. Sai abu na gaba ko ciwon kai mai martaba da ahalin sa suka yi wanda ya wuce tunani to kowannen ku yakuka da kansa, Zamu mika ku ga hukuma tayi yadda takeso da ku.”

Ya karashe da addua kowa ya shafa, Aka tura dogarai suka garkamo su waziri dake tirje tirje, Waziri yanata hawaye, Kansa yayi zafi dau. Yanata bori da alamun yazama mahaukaci tuburan, Ya fara shukar abunda suka girba dubada yadda ya shiga kokarin cire kayan sa, Kankace me? Su Huwaila sun furfuto suna koke koke ganin an kame iyayen su. Basu san harda su za’a hada ba, Sannu ahankali aka shiga watsewa, Gwamna yaiwa Salman Sallama shima ya tafi, Kowa ya taya Salman murna dasu Abdullah. Masoyan su sai kukan farin ciki suke yi. Salman kuwa ya kasa rufe bakin sa sai murmushi yake yana gaggaysawa da jama’a don dama shi baya ‘kyamatar owa. Sai dai tsantsar kwarjini da yake dashi. 

*SAS*

Sai bayan isha’i sannan kowa ya watse, Sashen shaheedah yaje bayan yayi wanka ya tarar ba kowa harta kwashe kayanta ta gudu. Zungureriyar letter ya rubuta da shedar sakinta, Allah ya bata wani nagari, Da doriyar lalle seta biya wasu kudade kamar yadda hukuma ta kayyade. Alhassan ya tasa ya bawa takardar da kudin jirgi yace yaje ya kai mata kuma karya dawo sai da kudin da hukuma tace. 

Sashen Ammi ya nufa, Yana tafe yana waya da dije yana gaya mata duk abubuwan daya faru, Don farin ciki dije harda kukan dadi,

“Kinci abinci ko?”

“Naci Zawj..”

“Kin kusa dawowa ai mu rakarkashi soyayyar mu. Kunje immigration office da Addah maryam ko!”

“Eh munje… Anmun passport da thumbprint, Nagode Allah ya saka da alkhairi.”

“Aamin.. Se kita addua, Idan da rabo sai kije umra ko! Ko hajj kikeso?”

“Wayyo love! Kowanne ma. Allah ya tabbatar da alkhairi.”

“Kana waje ne naji alamun tafia..”

“Eh zanje sashen Ammi.. Yarinya acan zan kwana yau..”

“Wayyo kamun wayo, Kabari na dawo sai muje mu kwana”

“Lalle Zawjati, Nak’i wayon, Sanda kika gudu kika tare a sashenta ai baki gayyace ni ba..”

“Alokacin fa b….”

“Banida man kai ko..?”

“Ah ni ba abunda nake nufi ba kenan, Haba takawa, Ina nufin lokacin sihiri na kanka.”

“Hmm! Allah dai ya mana maganin su, ‘Yayan iska. Yauwa gobe falaki dasu Addah maryama zasu rakaki durbun da safe..”

Kasa boye murnarta tayi, Tashiga kwarara masa adduoi tana masa kirari. Murmushi fadade a fuskar Salman, Ya zauna a gefen shukar kofar parlorn Ammi sai da yagama wayar sa da dije tas sunata narke soyayya, Sannan ya tura kofa ya shiga. Tana zaune ita dasu Khal sunata hira. Salman ya shiga ya duka ya kwashi gaisuwa wajen Ammi. Taita tayashi murnar nasarar da sukai. 

“Tab ranka ya dade sai yanzu ka shigo?”

 Cewar Khal yana kunshe dariar sa.

“Eh ya akai?”

Salman ya tambaye shi yana jan kasan leben sa.

“Ah bakomai, Munata jiyo kane kana waya da alama aunty Khadija ce, Don munjiyo kuna I love you, I love you most….”

Takaici yasa Salman wawuro filo ya cillawa Khal.

“Kaji tsoron Allah, Ni ba wata waya da nake, Falaki ne.”

“Ohh… Falaki??? Allah sarki. Lalle kuna aminta sosai.”

Tashi yai ya  bishi cikin wasa, Don dama su biyun nan aminan juna ne sosai, Khal ya shige daki ya kullo, Ammi ta tsaya tana kallon su da dariya. A tare sukaci abincin dare baki dayan su, A babban faranti. Raba dare su kayi suna hira. Har Salman yake sanarwa Ammi tafiyar su wadda zasuyi tazo, Nan sukaita tsara yadda komai zai kasance. Ranar Salman a sashen Ammi ya kwana. A dakin kasa, Sukaita buga psp game shida su Abdullah, ajiye sarautar yai a agefe daren ranar, Sukaita warkaja mi da yan uwan sa.

     *GIM KHADIJA*

Tun asubah dana tashi ban koma ba, Dama jiyan ma bacci rabi da rabi nayi, Zucia ta kumshe take da farin cikin nasarar da Salman yayi, Sai kuma ziyara da zankai marayata ta Durbun. Da sassafe naci abinci nayi wanka, Wani hadadden lace na saka da laffaya, Gold dina na cikin lefe na d’auka d’aya na saka da warawaran sa da zobu na. Na zuba dauri na dora glass sai kamshi nake,

“Na gayda gimbiya, Uwargidah kuma amaryar sarki Salmanu na biyu.”

Addah maryama ta shiga zubamun kirari tana jinjina mun hannu,

“Godia nake Addah maryama ta ta mutunci. Allah ya karemun ke.”

“Gaba salamun baya salamun sarauniya. Idan kin kammala kintsawa sai muje ko.”

Daga kai nayi, Na dauki jakata, Gwaggo mukayi wa Sallama muka futo farfajiyar gidan, akori kura motoci na gani, Guda biyu babba da karama, D’aya kayan sawa ne da mata da maza sabbabbi (atamfofi da shaddodi) Dayar kuma kayan abinci ne a babbar motor a shak’e. Na juya na kalli Addah maryama kallon karin bayani,

“Inji mai martaba.. Yace a kara miki da wannan ki rarraba..”

Ta mikomin wata y’ar jaka bandir din kudi ne yan 200 fal aciki. Sababbi sai sheki suke. Idanuwana suka kawo ruwa, Na rasa wane irin so Salman kemun, Na kira bai d’auka ba kila bacci yake. Alokacin kuma yana gani,  godiar ce baya so tayi masa. Mota muka shiga, Falaki yaja mu, Motocin yan sanda har biyu na mana rakiya, D’aya a gaba d’aya a bayan mu. Umma Hansatu na gaban motar mu ta rike mun jaka ta, Ni da Addah maryama a baya. Ina owners corner, Idanuwana sanye cikin gilashi baki. Message na shiga zanawa Salman na godia,

“Dearest honey bunny.. Zawj! Eternal love of my soul. Habibi da’iman, Miftahul qalb dina… Assalamu alaika zumanaaa! Hasken idanu na, annurin rai na. Miji na, uban ‘ya’ya na INSHA ALLAH! Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa’a a duniya. Ina fatan dawowa ta gare ka Lapia, miji na abun alfahari na.! Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune cikin mota zamu durbun,  amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Nayi kewar ka. Ina son ka. Ka kula min da kanka. Honey bunny! The impact of your love is undeniable. It has made me realize how much I adore you. My life with you has transformed my dreams into realities. I love and miss you soo much., #Kisses and hugs❤️❤️”

Ina gama rubutawa na tura masa, Addah maryama sai tsokana ta take yi, Nayi daria wani lokacin na tanka, Na juya inata kallon yadda muke wuce dajin Allah, Ga duwatsu nan da bishiyu, Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u…. Addua ce dauke a baki na naketa yi kan Allah ya kai mu lapia yasa mu dawo lapia, Ina tunano yadda zanga su Uwande ko yayanta nawa yanzu?..

Cikin tunanin da nake Salman yamun reply.

“Zawjatii Maman unborn na. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tunanin ki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Wannan k’amshin naki na tafiya da ni, Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zaki dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina kaunar ki sosai.. Zawjatii na! You always guided me through darkness, You are the force behind my success, A special thanks on this special day for being a wonderful human being, and a great wife! Journey mercy life partner, I love and miss you most..🥰❤️”

Ina gama karantawa na rungume wayar ina murmushi, Banbi takan Addah maryama dake cigaba da tsokanata ba. Jefi jefi muke hira, Umma Hansatu nata munsharin bacci. Ba dadewa muka isa marayata.. Dandazon yaran dake bin motocin mu a guje ne yasa nayi daria ina tuno baya. Durbun kafin Allah, Marayata tushe na.. Allah sarki baffa da umma ta.. Na sauke idanuna akan sabon shagon danaga an bude a bakin kasuwa, ‘Na ‘Dahare furobishon sutor an fons an keken haya..’

Na danyi daria ina sake bin yadda aka rubuta, Allah sarki Ilimi da dadi yake. Mamaki na shiga yi wane na adaman kenan? Ba dai mijin ‘dahare me tafasa ba? Idan kuwa itace gaskia na tayasu murna. 

  ******DURBUN*****

Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more

ZAFAFA BIYAR

NA KUDI NE::: 

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma’ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 18

Advertisement   _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 19

Advertisement  _ I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS…

KIBIYAR AJALI 30

Advertisement  _I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p_ _BOOKS DIN…