Advertisement
_*KIBIYAR AJALI…..!!!!*_
_(Sulke baya tare ta sai ta wuce)_
🏹👑👩❤️👨💝
_*MALLAKAR:- NANA HAFSAT_*
_(MS XOXO)🧕🏼_
Advertisements
_®️ZAFAFA 5: 2021*_
_(PAID NOVELS//LITTATTAFAN KUDI NE)_
_*LITTAFI NA:2_*
_*BABI NA: KARSHE_*
_pls follow @Maabluxuryhome… on Instagram. Su na da kayyayakin kitchen dana decorating gidajen ku. Number wayar su ta WhatsApp: +491521 4642007…! Suna kano, Kuma suna tura kayyayakin koi’ina a fa’din Nigeria. Kayan *MAAB LUXURY HOME* tafiyayyu ne tun daga kasar Germany.! Kyau, inganci, Rahusa sai *MAAB LUXURY HOME*, Idan anje siya ace daga zafafa 5 ne Za’a zamu saukin kudi IN SHAA ALLAH! Siyan na gari mai da kudi gida sai kayan *MAAB LUXURY HOME*_
_*BOOK 2: PAGE 35_*
_*(END)_*
Advertisements
****DURBUN****
Kalle-kallen marayata na shiga yi, Babu laifi an samu cigaba na wasu sabbin abubuwan, Bayaga haka tana nan yadda na taho na bar ta, Dattijawan dana taho na bari alokacin baya yanzu sun sake tsufa sosai, Allah sarki rayuwa, Idan babu mutuwa akwai tsufa. Sai jiniya motocin yan sandan da mukazo suke yi, Duk inda muka wurga dandazon yara na biye damu. A haka har muka karasa kofar gidan mai gari jamilu.
Ganin yana tare da mutane a kofar gidan sa hakan yasa na shige cikin gidan kaina tsaye, Su Addah Maryama na biye da ni a baya. Allah sarki mai gari tun baisan nice dije ba har an cika gaban mu da ruwan pure water da lemon kwalba, Sai abinci a languna kamshin man kuli sai tashi yake.
“Sannun ku da zuwa ranki ya dade, Lale marhaban, Ai munata zuba idanu ance matar sarki zata zo, Sai jia da dare mai gari yace yau zaku iso.”
Ummita matar mai gari ta karasa fada tana janyo langunan abincin gaba na.
Mamaki nake kawai yanda ta’kara manyanta, Na numfasa ina tunanin zasu gane nima kuwa? Sai ga mai gari jamilu ya shigo da sauri. Gaisawa mukai, Yanata ban girma, Duk kunya ta isheni, Inda sabo na saba yadda akemun a masarauta, Amma acikin marayata dinnan duk sai naji ba dadi, Gashi sun manta ni. Ni kuwa dukkanin su ina kallon su na ke ganewa, Musanman mai gari jamilu aminun baffah na ne,
“Mai gari baka gane ni ba?”
Ya girgiza kai yana kallon ummita matar sa,
“Ranki ya dade na sheda ki mana, Duk kuwa da bamu taba haduwa ba, Amman an sanar mana cewa zakizo, Munga aikin alkhairi, Allah biya miki bukatun ki, Ya jik’an mahaifa, Idan suna raye Allah yaja kwanan su.”
Murmushi kawai nayi, Naja langar gaba na. Addah maryama ta bubbude mana, Shinkafa da wake ne sai man kulli da yaji. Gefe d’aya kuma soyayyun yan shila ne sunata kamshin kayan kamshi. Mai gari ya mike ya bamu waje, Ummita ma ta shiga cikin daki, Naci sosai ba lefi, Ummah Hansatu da Addah maryama ma sunci suma. Abincin yayi dadi sosai. Dama tunda idan Ummita tayi girki kana jiyo kamshin har wajen gangaren bishiyar dirimi…
Sai damuka kammala ci muka kintsa, Sannan Ummita ta futa ta kirawo mai gari, Sannu ahankali dattawan yan zaman majalisar mai gari suka shiga shigowa suna gaisar da ni.
“Ranki ya dade.. Matan karkarar mu na bayan gidan nan dake yafi inuwa….. Akwai yalwacacciyar bishiyar dirimi awajen, Inuwa ta wadatu da….”
Bai karasa ba idi na albasu ya shigo gidan yana lailayo ashariya yana saukewa akan sunan Gajiyalle.
“Mai gari kaji wani zance, A bakin kasuwa mukai caca na ciyo gidan da Mudin gaji yasa ka, Gida ya zama na wa, Nace na basu sati su tashi daga gida na, Sati ya zagayo zan karb’u abuna, Naje tsohuwar gyatumar sa fito kan lalle gida bai ciyu ba ai nata ne. Tana ta kwararo rantsuwa, Saura kadan na take kanta Allah mai gari.”
Ya karasa fada yana mai busa sigarin dake hannun sa.
“Kayi hak’uri idi, Wannan gida dama karanbanin Mudi ne, Amman ba nasa bane na Gajiyalle ne.”
“A hayye gani… Mai gari kaji wata sabuwar damfara Wai Mudi ne yasa gida na a caca… Har idi ya lakwume gidan yana ikirarin nasa ne, Yazo kofar gidan yana bushe bushen sigari, Wai mu fito wa’adin daya baya mu ya cika.. Shine nace gida bai badu ba ai nawa ne ba mallakin Mudi ba.”
Tunda Gajiyalle ta shigo tana magana na saki baki ina kallon ta, Mai hali baya fasa halin sa, Ta manyanta ainun a jiki da fuska, Domin dakyar naga tashigo gidan tana jan kafa. Amma masifar ta tananan kamar ma dad’uwa tayi. Zani daban, riga daban dankwali daban duk sun sha jiki. Ta yafa wani zanin kamar mayafi. Daman duk sanda take cikin masifa to fa bata kintsuwa a koyaya take haka zata fito daga gida. K’afarta ko takalmi babu, Tayi bu’dun budun da k’ura. Mai gari ya dafe Kai da hannu yana tsawatar musu,
“Naziru baida amfani da jiran kofar dana bashi, Wai shin bakuga baki mukayi bane?”
Idi ya zube yana gaishe mu, Hade da sosa keyar sa yana murje tabar hannun sa da kasan takalmin dake kafar sa.
“Tuba nake ranku ya dade, Kai nane a chake. Kunzo lapia?”
Su Addah maryama suka amsa, ni kuwa inacan wajen k’arewa Gajiyalle kallo. Itama tana nufin bata gane niba kenan? Zubewa tai tana rankwashin kanta,
“Sannun ku.. Kai kudub’us ko dan ‘kundun uba tun daren jia yake azabtar ni. Ina wunin ku, Anzo kalau? Ranku ya dade.”
Cewar Gajiyalle ta zube tana gaishe mu itama. Murmushi kawai nayi ina ajiyar zucia, Na dubi mai gari jamilu dake cewa su tashi su tafi,
“Ca-ca babu kyau, Mai gari ya kamata ka tsawatar musu, Yanzu dai kai idi zan bawa mai gari ya baka kudi me tsoka kaja jari kaji? Ita kuma kabar mata gidan ta.”
Duk suka zare idanu suna bina da kallo, Gajiyalle cikin kidimewa ta zube tana sharara godia,
“Insha Allah zan hane su, Basa ji ne can bayan gari suke zuwa suyi ta yi…”Cewar mai gari jamilu
“Nagode ranki ya dade, Gaskia kina adalci, Kin can-canci zama matar sarki. Allah ya kara budi.”
Idi ya fada yana mai cigaba da godia.
“Allah ya saka miki da alkhairi ranki ya dade, Nagode nagode, Dama gidan gadar sa nayi na miji na, Shine yaro na yaje yasa shi a ca-ca bamuda halin cin yau dana gobe, Ga yaro da mata da yake dasu, Ni ce n…”
“Tashi ki tafi gaji, Ya isa haka. Duk sanda za’a yi bakin kunya sai kun dizga mutane wallahi, An sanar daku ba sau d’aya ba ba biyu ba, Wannan matar sarki ce dake birni. Zaki tashi ko sai yan sandan waje sun rarumo ki.?”
Mik’ewa tai tana sake godiya tana kuma rankwashin kanta saboda kaikayin kudubus. Mai gari zai fita nasa Umma Hansatu ta kirawo shi, Sanin akwai mai karanta masa rubutu idan an aiko sak’o daga birni yasa na mika masa list din sunayen k’awaye na dama sauran mutane da nakeson mu hadu dasu.
“Ranki ya dade na menene wannan?”
“Mai gari kace baka gane niba, Nasan idan aka karanto maka sunayen wadannan mutanen dake jiki zaka gane, So nake a nemomun su…”
Zubewa mai gari yayi yana yanata godia, Ya fita, Ba jimawa ya dawo da tsumma a fuskar sa yana gogewa,
“Ranki ya dade da jin sunayen da kika bayar na tabbatar kin hada jini da marayan nan, Allah ya kara miki lapia, Sai dai ban waye ki ba. Tuba nake…”
“Mai gari jamilu… Sunana Khadija basheer.. Y’ar marigayi Malam bashari Inuwa na alkali.”
Rufe baki mai gari yayi, Hawaye na wanke fuskar sa, Cikin rawar jiki da baki ya shiga kiran Ummita, Tafito a rude itama tana tambayar sa menene?
“Ummita… Kema baki wanye taba ko? Matar mai martaba ce.”
“Nasani ranka ya dade. Nasan mai dakin sarki ce.”
“A’ahh! Ina nufin Dije fa. Dijangala diyar marigayi Malam Bashari amini na..”
Ummita ta mike tana kallo na, Na jijjiga kai ina daria, Su Addah maryama suka tsaya suna kallon mu.
“Nayi mamakin yadda baku gane niba, Gashi ina ganin ku na sheda ku.”
Kuka mai gari yake sosai, Ummita na hawaye itama. Sai kuma aka dawo hirar yaushe gamo? Mai gari yace tabbas sunji zancen tambayar aurena da akai a wajen Baba Ladingo da auren da za’a yi amman basusan sarki na aura ba, Wai gaba d’aya na canza kamanni,
“Yasin kamar an wanko ki a injin bature sai sheki kike. Binne ta karb’e ki ranki ya dade”
Cewar Ummita, Murmushi kawai nayi. Mai gari ya sakemin godiar gidan dana siyawa Gajiyalle,
“Allah ya saka da alkhairi, Tabbas badan kin bawa idi kudin nan ba, Toh da Sai dai su nemi matsugunin kwana dan kuwa bazai taba yarda ba. Shi kuma Mudi ya cika rigima ya rakito nan ya jajibo can. Rannan har shad’aya saura kwata suna wajen nan shida ladiyo matar sa.”
“Mudi yayi aure?”
“Yayi harda albarkacin da namiji ma, Yana auren ladiyo yar uwannanniya mai yakuwa..”
Na gyada kai ina tunano ladiyo babba ce fa ta kusa girme masa, Ina k’arama bana mantawa a bakin kasuwa take zama tareda maza har dare. Lalle ya ebo ruwan dafa kansa.
“Allah sarki rayuwa.”
“Dan fitina ma wai aure yakeso ya karo, Bansani ba ko zakisan Abasiyya mai awara?” Ummita ta tambaye ni tana murmushi,
“Kamar naso na tuno ta, Nasan dai sunan tabbas.”
Haka haka dai muka shiga hira, Lawwali ya lek’o yana sanarwa mai gari sunayen wadanda akace a kirawo wasun su sun hallara.
“Nagode mai gari, Akwai kaya na maza shaddodi, Na cikin wani buhu kai da sauran abokanan baffah na dake raye zaka babbawa, Sai sauran shaddodin a baiwa matasa da duk wadanda ya dace. Duk dai yadda ka tsara. Da kayan abincin duk a rarrabawa mabukata, atamfofin kuma ka daukawa Ummita d’aya, Zan raba wa su Balki sauran.”
Godia suka shiga yimun Ummita harda gud’a. Bayan tashin su daga wajen na juya ina fa’dawa Addah maryama komai a takaice,
“Wadda tafitan itace Gajiyalle matar babana da nake sanar miki. Mudin kuma ‘dan ta ne.”
“Lalle gimbiya kin iya saka alkhairi ga mai sharri, Allah dai ya cigaba da dafa mki Aamin.”
Ummita ta shiga daki ta dakko hijabi Zata mana rakiya gangaren dirimi.
“Aamin…Muje gangaren dirimin ko? Na rubuta baba ladingo an sanar mata zanje kuwa?”
Nan take shedamun ai Baba ladingo tarasu. Nasha kuka domin ita kadai ce kanwar kakana data rage, Shikenan gaba da baya yan uwan mahaifina sun kare? Na goge hawaye na hade da wanko fuska ta,
“Ku tashi muje..”
“Toh ranki yadade…”
Muka fice, Yan sandan na take mana baya har muka karasa wajen cincirindon matan karkarar mu. Suka zubamin idanu suna kallo na, Allah sarki rayuwa, Nima da haka nake yi ni dasu uwande idan yan birni sunzo. Idanuwana suka sauka akan Balkin haladu dake bina da kallo, Allah sarki auren wuri a kauye tamkar ta haife ni, Saboda ita ko karatu batayi ba sukai aure da haladu. Kamar na rungumo su baki d’aya, Sai dai nace bara na tuna musu wacece ni tukunna, Na rasa meyasa suka gaza gane ni, Gashi ni ba canza kama nayi ba sai dai ko yanayin jiki dana kara da haske. Na sauke ajiyar zucia, Ina amsa gaishe gaishen su. Wani natashi ne ya shiga kaude kaude, Kujerar gidan sa ya dakko da rawar jiki ya ajiye mana , Da alama shine sabon kansilan su, Saboda haka naji ana kiransa duk inda ya wulga. Ko ina Nafisan kansila yanzu? Ina daga zaune ina sake kalle kowannen su, Gajiyalle na layin tsofaffi a zaune ta zubamun idanu kamar zata hadiye ni.
“Assalamu Alaikum matan karkarar durbun..”
“Wa’alykm Salam ranki ya dade.. Anzo kalau?”
“Lapia lou.. Na same ku lapia? Iyalan duk kalau? Kaji, Zabbi da sauran kiwo hade da amfanin gona.”
Daria sukayi suna amsa ni, Kila mamakin yadda na juya harshe ina magana irin ta karkarar shiya basu dariya. Murmushi kawai nayi. Kafin na cigaba da cewa,
“Yanzu duk cikin ku nan babu wanda ya sheda ni?”
Suka shiga kallon kallo suna dashe baki, Wata yar budurwa dake zaune akan tabarma ta sosa kanta tana murmushi,
“Ranki ya dade mun wanye ki mana. Kece mai dakin sarkin mu dake birni.”
Na kada kai ina dariya,
“Shikenan?”
Nanma duk sukayi shiru na zare gilashin idanu na, Ina maida kallona sosai gare su,
“Sunana khadija Bashir Inuwa, Nasan baza ku taba mancewa da Dijengala ba, Ta mai-gari, Dije, Oganniya, Ta Gajiyalle mai ‘yar hakiya..”
Ai gaba d’aya sai waje ya kacame da magana, Wasu suka mimmike suna dafe kirji ciki harda Gajiyalle data lula duniyar tunanin k’arshen furucin da dije tayi a lokacin da zata baro ‘Durbun.
‘Shin wannan bai isheki ishara ba? Kisani kwakwalwar yaro bata manta duk abubuwan da aka yi mata na dadi ko akasinta. Ni Nana Khadija na zamar miki kainuwa dashen Allah, Duk da yadda ba taso na rashin uwa ba kyakkyawar tarbiyya hakan bai sa na lalace ba, Ni Khadija na zamar miki murucin kan dutse ban fito ba sai dana shirya, Nan gani nan bari wallahi Gajiyalle, Na zama dakalin majina dole a hau ni a zame, Ni Khadija na zamar miki *KIBIYAR AJALI* wadda (sulke baya tare ta sai ta wuce) Daukaka yanzu na fara ta. Duk abubuwan da ki kai min na bar ki da mahaliccin mu, Zai mana sakayya ranar sakamako, Kudi kuma da kuka sata kun dauki kudin cizo, Kina ganin keda dan ki kunci bulus? Allah ya kara miki tsahon rai, Ki dade kiyi ‘karko kamar bishiyar dabino, Ki saurari dawowata Durbun, Zaki madaukakin mamaki mai wuyar fassarawa. ‘
Mik’ewa tai hartana tuntube tayi baya da baya ta gudu gida ina kallonta, Murmushi kawai nayi na cigaba da yi musu bayani, Suka rufo kaina suka karemun kallo, Sojoji zasu dakatar dasu na hana ina dariya, Balkin haladu ta buga zani tana sosa kai.
“Qundin ubancan kayya kai, Yasin Dije ce, Ga kamana nan, Dije rai kanga rai? Kin wanye ni.?”
Na janyo hannunta ina dariya,
“Balkin haladu… Ya za’ai na mance ki? Nice na lissafo sunayen kuma nace a nemo mun ku, Inasu Uwande, Siyama, Nafisan kansila, Nana, Tsahare dasu furairatuwa?”
“Duk sunanan qalau, Nafisa ai tana binni itama tayi dace mijinta baki ga samb’alelen mahin din daya siya ba, Ya dankara mata gida a binni daku na biyu da wajen girki, Motoci biyu muka hayo mutan garin nan mukaje mata murna. Ai Nafisa ta dace. Siyama kuma tana auren dan mai garin landantsan, Uwande kuma itama ta hadu da kaddara mijin ya shikata tana birni tana aikatau, Nana kuma tana gangaren hayi acan tayi aure, Tsahare na can layin baya zan kirawo miki ita yanzu. Fureratuwa kuwa rai yayi halin sa.”
Tunda tafara magana nake kallonta kawai, Allah sarki rayuwa, Amman naji da’din ganin ta sosai na kuma ji dadin yadda ta saki jiki dani tana bani labarai, Dandazon sauran matan kuma sunyi jere su Umma Hansatu na rarraba musu atamfofin.
“Allah sarki fureratuwa Allah ya jikan tah, Kice su Nafisa ana fantamawa, Toh kuma Allah yasa ku dace, Ina haladun ki kuwa Balki?”
“Dan bankadaddiya zaki ce, Ai ya sau ni, Dama shika d’aya ne ya rage. Mun rabu ya dan’karo aure karamar yarinya yar rugar su Baffa lamido fulanin nan, Baki ganta ba jazir da ita. Ai kuwa ingaya miki na bar masa yaran nace ka kahe su inka ga dama.”
“Haladun?”
“Iyyi ai mayatar son ‘karin aure ce a ransa, Rance ma iyo ya dada auren ya sau ni.”
“Kudi yayi haka kome?”
“Ba wani kudi, Rigima ce kawai irinta sa, Jiran hyagon sama’ila yake fa, Sama’ilan Daudu? Ai ya bude hyagon waya yana chaji. To hine ike masa jira.”
“Toh Allah ya sawwake, Allah zai baki wanda yafi shi da yardar Allah.”
“Toh Aamin! Amman yanzu ranki ya dade ai na hige aure, Ke fa yayana 8, Wasu kan wasu rab’e rab’e, Ai kuwa can wajen hi na bar masa su.”
“Tab…! Allah ya kawo miki mafita Balki. Muje kimin rakiya gidan Gajiyalle.”
Jiki na azama ta mike tana gyara daurin zaninta, Duk ya jeme. Na tuno sanda ina durbun nima kayana duk a ‘bele suke, Sun kode.
“Addah maryama kuci gaba da rabawa banaje na dawo..”
“Toh gimbiya, Allah ya kare mana ke.”
Muna tafe Balki na zubamun surutu kamar gidan rediyo, A haka muka karasa gidan mu, Ko nace gidan da Gajiyalle ta gada. Tun daga zaure muke jiyo cacar bakin su, Na sake bude kunnuwa ina jiyo su,
“Gajiyalle ce da surukar ta ladiyo, Kullum sai anyi rabiyar fadan su.”
Cewar Balki, Na girgiza kai kawai cike da takaici, Muka karasa shiga bakin mu da sallama,
“Yauwa Alhamdulillah! Sannu da zuwa gimbiya dije, Ashe kece mai dakin sarki, Tun dazu nake son fitowa wannan algungumar makirar ta cire tsumman da nake kulle kyauren daki na dashi idan zan fita, Tazo tanata kumfar baki wai kin bawa Idi himilin kudi da Mudi ya saka gidan nan. Au inata zubar zance.. Ran ki ya dade sunana Ladiyo nice matar mudi.”
“Nagode sosai ladiyo. Ya mutan gida?”
“Sunanan qalau gimbiya. Kin sheda ni kuwa? Duk da dai ni ba tsarar shekara muke ba.”
“Na sheda ki ladiyo.”
Gidan na shiga k’arewa kallo, Inata tariyo sanda muna tare da baffana yana kira na da Ummin sa. Na goge hawayen daya zubomin, Gidan ya sake lalacewa katangar gefe ta rushe kana hango gangaren rafi. Rayuwa kenan dik babu kiwon da Gajiyalle ke tunkaho dasu. Na juya ina kallon Gajiyallen datai tsuru tsuru tamkar zata gudu. Gaba d’aya a tsorace take. Na kalli agogo na har yanzu goma batayi ba na safe, Dake da wur wuri muka taho,
“Ina kwana Gajiyalle..? Mu dada gaisawa, Awajen taro sai kuma na neme ki na rasa ashe gida kika dawo? Ko tanadin kayan kwalam ake tanadar mun ne?”
Gajiyalle jikin ta ya shiga kakkarwa tana harhada hannuwa,
“Ranki ya dade.. Ji nai kunnuwana na mun waswasi wai ke dije ce.”
“Ah ba waswasi bane, Ni ce nan dije taki ko kin manta kirari na Oganniya yar baffan tah, Ta Gajiyalle mai yar hakiya?”
Ai sosai Gajiyalle ta sake kidemewa, Gaba d’aya jikinta kakkarwa yake,
“Dan Allah kiyi hak’uri dije. Au ranki ya dade, ki gafarce ni, Dan Allah.”
Mik’ewa nai ina lalleka koina na gidan,
“Yafiya kuma? Me kikamin? Kin manta dama nace Insha Allah zanyi aure agidan bulo da siminti? Irin nasu Nafisan kansila? Nace zaki s…”
“Allah ya huci zuciar ki dik na tuna, Kince na tsumayi dawowar ki durbun, Zanyi mamaki kwarai da gaske, Ai kuwa nayin, Ina kanyi ma dije. Au ranki ya dade.”
“Kash! Dan Allah ki kira ni dije na, Nafi jin dadi domin haka nasani tuno baya.”
“Gwara ki dena tunawar ranki ya dade, Abar dai kaza cikin gashin ta.”
Turmi na janyo na zauna akai ina mai jefa chingom cikin baki na,
“Gajiyalle nafa zama yar jaridar dana ke ta addua Ina son na zama. Wallahi kinga alfanun karatu ko? Na zama babbar yar jaridan wani gidan rediyo na dokin karfe24. Ni kuwa ina Mudikalle?”
“Allah sarki! Allah yakara daukaka. Mu.. Mud.. Mudikalle yana..”
“Iya layin karbar kayan da kika zo dasu ranki ya dade. Kai halipha dan kan uwar baban ka tashi kaje ka kira baban ka a dandazon layin kar’bar kaya.”
Sai a sannan na dubi yaron da ladiyo ke magana dashi, Lalle ‘dan mudi ne kamar su d’aya kamar yayi kaki ya tofar.
“Kan uwar ki dai, Gyatumar ki uwannanniya mai yakuwa.”
Nan suka shiga fada, Ni da Balki muka zuba musu na mujiya muna binsu da kallo. Cikin haka Mudi ya shigo har yana cin tuntub’e, Saura kadan ya fado kan Balki, Ba Sallama bare gaisuwa sai ma kure ni da yai da idanu yana tafa hannaye,
“Wa billahil lazi dije ce! Ke dije, Gajiyalle kinga dije.”
“Kundin buhun ubanka, matar sarki ce ka zube ka debi gaisuwa.”
Cewar Gajiyalle da suka gama tular kokawa da ladiyo sai haki take.
“Ina kwana dije, An zo kalau, Dije kinga yadda kika sauya?”
“TubarkAllah! Mudikallen Gajiyalle kana nan dai da halin ka, Ashe kayi aure?”
Shafa kansa ya shiga yi, Gajiyalle taja tsaki tana tsurtar da miyau hade da sosa diddigaggen gashin ta me dauke da ‘kudubus.
“Sunyi masha’ar su dai an kakaba masa ita garin jajibe jajiben sa. Wannan dan me rantalelan kai na gefen sa na sane a yadda suka ce”
“A hayye ai barewa batayi gudu ‘danta yai rarrafe ba, Atoh munsan shafe shafe munsan hoda, Shima a haka kika same shi.”
“Kinci malafar kan uban ki, Uwar ki uwannanniya mai yakuwa itace tayi shegen ta haife ki.”
Ganin zasu sake wani fadan a karo na 3 sai na mike ina gyara laffayar jiki na,
“Ni zan dan shisshiga gidaje gaji, Ga wannan kwa dinka keda ladiyo. Wannan kuma ayi cefane, A nemi sanaa ayi abar zaman kashe wando, Kaji Mudi.”
Ina gama mikawa ladiyo ta wawure tana dauke tata atamfar da bindir din kudi guda 1 acikin yan dari bibiyun dana ajiye. Zubewa Gajiyalle tai da Mudi sunata godia, Gajiyalle ta kamo kasan laffaya ta tana kuka wiwi, Tana neman yafiya tah itada Mudi.
“Kash! Babu komai Gajiyalle..”
“Ba kice kin yafe ba.. Dan Allah kiyi hak’uri Dije, Wallahi ina ta ganin sakamakon gallazawar dana miki.”
“Kina kan gani ma.” Cewar ladiyo.
Cikin kuka Gajiyalle ta juya tana dankara mata harara hade da face majina,
“Kinci malafar kan uban ki ladiyo. Kuma aure ne dole Mudi ya kara.”
Zage zage suka fara, Ita Gajiyalle ta tsufa amma ba zata dena halin taba. Naja tsaki ahankali cike da takaici.
“Dije baki ce komai ba.”
“Nifa na mance da rayuwar ku baki d’aya gaji, Bakiga tunda na koma ban dawo ba? Toh wanda ya hada mu zaman taren ya tafi, Na yafe, Allah ya yafe mu baki d’aya..”
Ina gama magana na mike nai gaba abuna, Balki na biye da ni, Balki ta rarraka ni gidajen su Bara’atu me dinki, Da dara’ifa, Duk basanan ashe suna wajen da ake raba atamfofin dana kawo, Kayan abincin nasa mai gari ya ware kashi d’aya aka kaiwa Gajiyalle, Sauran kuma aka rarrabawa mutane, Sai zuwa suke muna gaisawa gaba d’aya mai gari ya shelan ta musu ni ce Dije. Ai kuwa nasha adduoi daga bakunan su masu albarka, Kudaden nanma haka na baiwa mai gari nace a rarrabawa mata suyi sana’a, Mazan kuma suje jari. Nabi yan yara na daddanka musu alewa da biskit da naira dari bi-biyu. Kowanne sai murna yake.
Na jima munata zumunci da hirar yaushe gamo, Ai kuwa suka ransa inda zasu sa kansu don dadi, Suka cikata gaba na da kayan kauye, Munsha tsaraba. Addah maryama sai daukan hotuna da bidyo take wai zata nunawa su mai martaba. Sai yamma tikis sannan muka dau hanyar komawa birni, Nace idan na haihu zan aiko da motoci matan suzo suna, Balki kuma nace ta tattaro kayanta ta dawo waje na ta zauna, Idan ta samu miji tayi aure, Mazan kuma ko yaushe suke so suzo su gaysa da mai martaba… Muka dau hanyar gida kowanne cikin yan rakiyata yaji dadin zuwan mu durbun.. Muna tafe Ina yiwa marayata kallon sai na sake dawowa da yardar mai sama…..
*****•••••. •••••*****. •••••.****
Anata kiraye kirayen sallar ishai muka koma gidah, A gajiye nake tikis, Don haka muna komawa nayi sallah naci abinci na malale sai bacci. Washegari bayan mun gama waya da Salman yace zai aiko a dauke ni da daddare, Addah maryama ta shigo dakin da nake da mai gyaran jiki aka fara yimin dilke da halwa, Bayan an kammala tamun jan ‘kunshi, aka gyaramun kai na, Sai turara mun jiki akeyi.
Wata sabuwar doguwar riga Addah maryama ta dakkomin, Abayace jawur da ita da mayafinta,
“Godia nake Addah maryama.”
“Ki godewa mijin ki shi ya aiko da komai.”
Muka tuntsire da dariya muna hira, Ta shirya ni sosai harda su kwalliya, Can sai ga wayar Salman wai na fito anzo dauka ta a waje. Nayiwa gwaggo Sallama , Addah Maryamah tamun rakiya har mota. Ina budewa naga Salman shirye cikin kananun kaya kansa da pcap.
“Ahh’ ranka ya dade. Da kai akazo dauka ta?”
“Ai dole nazo d’aukar gimbiya.”
Sallama mukaiwa Addah maryama daketa dariyar dana rasa silar ta. Muna tafe yana zubamin hira,
“Kinji kamshin da kike kuwa?”
Ya kamo hannu na yana murzawa a hankali,
“Wow! Fatarki sai sheki take da laushi.”
Bacci nake ji don haka na ky’ale shi yanata dibar zance, Kwantar da kai na nayi akan cinyar sa na daga kafafuna na mike su a kujera, Bacci yai awun gaba dani. Ban farka ba sai gani na nayi acikin wani hadadden Private jet, Salman na gefe na yana murmushi,
“Ko mafarki nake? Takawa Ina ne nan?”
“Hmm sace ki nayi baby…”
“wayyo zawj! inasu Ammi..?”
“Su Ammi ma sunyi tafiya itada su Abdullah, Zasu raka shi school, Su kuma zasu wuce dubai hado lefen Khal, Kinsan aure zeyi.”
Matsawa nai daf dashi har muna iya jiyo numfashin juna,
“Mu kuma fa Zawj?”
“Mu zamu saudiyyah ne, Kin tuno na gaya miki awaya? Zamuyi ibada ne daga nan kuma mu sayo kayan babies d’inmu.”
Wata runguma nakai masa saboda farin cikin dana samu kai na aciki, Wai ni dije ni ce zanje kasa mai tsarki? Allah buwayi gagari misali, Mai ‘daga wanda yaso asan da yaso. Wani fannin shafin soyayya muka bude a cikin jirgin, Bacci ya kwashe mu daga baya sai farkawa nai naji Salman na radamun,
“Baby tashi….. Mun iso Jedda…”
Wayyo Allah farin ciki, A wani hotel muka sauka, Muka tsarkake jikinmu, Wata shigar muka sauya a ranar muka dau hanya sai kasa mai tsarki.
*KINGDOM OF SAUDI ARABIA (MECCAH)*
*Raffles Makkah Palace*
Wani had’adden 5 star hotel muka sauka, Sai kalle kalle nake, Na dawo yar kauye ta tubiran, Muka je masallaci muka dawo, Salman ya zazzagaya da ni wurare, Bayan yayi ‘badda kama ba zaka gane shi bane. Sai dare can muka koma hotel d’inmu a gajiye.
“Zo muje muyi wanka..”
Ban musa ba na mike dak’yar saboda ciki na ya tsufa ba lefi. Wankan muka yo ya nadoni a bathrobe kamar wata jaririya. Har kan gado ya ajiye ni yana mammatsa mun kafafu..
“Sannu baby.. Kafafun ki har sun fara kumbura.”
“Yauwa zawj.. Zo kaji.”
Matsowa yai daf da ni muna musayar numfashi, Na janyo shi ina shafa kwantaccen gashin kansa, Hawaye ne kawai na farin ciki naji suna zuba a idanu na,
“Menene Zawjatii.. Me ke miki ciwo? Waya tabamun ke? Uhm? Me kikeso? Anything?”
Girgiza masa kai nayi ina shafa kwantaccen sajen sa,
“Banida kalaman da zasu fasalta maka yadda nake jin ka a rai na Zawj, Hakika duk wasu kalamai da zanyi amfani dasu ba zasu taba kai yadda kake a zucia ta ba. Ina kaunar ka sosai. Yadda kake sharemun hawaye na kake sani farin ciki kullum Allah ya biya ka da mafificin alkhairin sa. Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira….”
“Zawjati babu godia a tsakanin mu.. Duk abunda na miki ban fadi ba, Domin kece mabud’in duk wata kyakkyawar rayuwa dana tsinci kai na, Tabbas zaman ki mata gare ni shine babbar kyautar da Allah yayi mun bayan yayoni musulmi, Da iyaye ga yan uwa na, Sai kuma ke Zawjati. Kullum cikin yiwa Allah godia nake, Na gama dacewa da matar kwarai. Ai tunda na kyallara idanu na fara ganin ki, Nace tab Salman yanzu ne zakai aure.”
Hannu nasa ina dariya, Ya gyaramana kwanciya, Ta hanyar maida kai na kan dantsen hannun sa, Ya zamto hannun sa d’aya yamun pillow dayan kuma yana yawo dashi cikin ciki na da sauran sassan jiki na.
“Kace love at first sight ne…! Wato daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak’i? Har ka hango ka aure ni kenan”
“Kwarai kuwa Zawjatii habibty…. Ai idan ina kaunar abu dagewa nake da addua da istikhara sai na mallake shi.”
“Lalle nayi dace, Na kuma yiwa sauran mata zarra.”
Daria muka kyal’kyale da ita, A hankali ya shiga yimun tafiyar tsutsa a jiki na, Na shiga ture hannun ina mintsilin sa.
“Mintsini? Tab ai kuwa dole na rama…”
“Wayyo baby bani bace little unborn ne yasa.”
“Toh sai maman sa ta biya. Ko dai ki biya ni yanzu da zafafan abubuwa ko kuma na rama.”
“Ka yafemun mana… Banida abunda zan biya.”
“Tab! Ai kuwa kece me abubuwan biya. Bara kiga ni.”
Kashe fitar dakin yayi, Yaja bargo ya rufe mu, A hankali ya shiga fagen dagar sosai, Na biye masa har nafi me kora shafawa..
•••••
Bazan taba mantawa da rayuwar da mukai a birnin makkah ba, Satin mu biyu acan mun gurji soyayya kamar cin kwan makauniya, Mun yi siyayya sosai ta baby, Duk kuwa da naki ayimun scan bansan abunda zan haifa ba, Duk unisex muka siya wato wanda za’a iya sawa mace ko namiji. Daganan muka daga zuwa birnin Dubai wajen su Ammi. Ashe Sunanan itada Khal suna siyayyar auren sa.
Hotel dinmu d’aya dasu Ammi, Daki ne dai kowa da nasa, Mu muna kasa su suna sama. Awajen su Ammi na bararraje akan kujera ina bacci. Salman yana ta zaune yana jira na tashi mu tafi. Na bude idanu kenan naga bai tafi ba yana nan. Ai kuwa na maida kai na na kwanta sai sign yakemun da ido na mutashi mu tafi. Ni kuwa bazan iya wannan abun kunyar agaban Ammi ba.
Mik’ewa yai yana danna waya,
“Ammi sai da safe..”
“Toh mai martaba sai da safe….”
Har ya kai kofa ya sake juyowa yana magana,
“Ammi na tafi..”
“Toh mai babban suna, Allah ya tashemu lapia..”
“Aamin Ammin mu.. Bara na tafi. Sai da safe”
Khal dake gefe ya sheke da dariya yana cigaba da danna wayar sa,
“Ammi Aunt. Khadija fa yake jira.”
“Wa yagaya maka? Saboda me batana da ka’fa ba?”
Cewar Salman cikin borin kunya, Na danne dariya ta ina munsharin karya.
“Ai shine, Kai Khaleel ka cika tsokana..”
Cewar Ammi. Har Salman ya fuce sai ya dawo kuma yana sosa keya,
“Ga keys Idan ta tashi, ni zan dan shiga gari.”
“Toh Allah ya tashe mu lapia”
Khaleel sai dariya yake harda bubbuga kafa, Ni kuwa sai dana dau lokaci sosai sannan na mike ina salati,
“Kin tashi Khadija?”
“Na tashi Ammi.”
“Ya jikin naki?”
“Ah jiki da sauki…”
“Allah ya raba lapia.”
Ban amsa ba sai a zuciata, Nayi murmushi kawai ina kallon tv da keyi,
“Aunt ki tashi ki tafi ba, Yau mai martaba yacewa Ammi sai da safe yafu sau 10.”
“Khaleel handa shari .”
“Allah kuwa Aunt. Kay. Gashi nan dai yabar miki keys, Wai yaje zaga gari.”
Kunya duk ta kamani, Na mike na shiga bandaki na wanko baki na, Hade da watsa ruwa. Mun dan jima muna hira sannan na musu sallama na tafi. A bakin kofa na same shi yana muzurai, Daria abun yabani na shiga yi,
“A kace ka shiga gari.”
Ya dankaramun hararar wasa yana janyo hannu na muka shiga ciki.
“Daga yanzu har mu koma gida minti 20 kawai zaki dinga yi a tare dasu Ammi, Kin je kin saki baki da hanci sai bacci kike kin barni kamar me gadi. Wancen yaron sai tsokanata yake, Bayan wallahi naga sanda kika farka.”
“Takawa ni ina kunyar Ammi.”
“Ai kunyar ce tasa na kyaleki nima, Da ba Ammi bace wallahi sunkuto ki zanyi mu taho kinsan hali na dai.”
Na gyada kai ina rissina masa,
“Toh ayimun afuwa ranka ya dade.. Me kakeso a maka yanzu?”
Janyo ni yayi na fada kan cinyar sa, Ya zagayo da hanayen sa ta ciki na, Ta kunnena ya shiga radamun,
“Abubuwa da yawa nakeso, wanka tare da ruwan dumi, Kamshin nan na cikin kanki me tafiya da ni, Sai zafafan kisses dinnan naki… Kafin muje ga babban ladan.”
“A sau’kak’amun mana saboda baby..”
Na fada, Ina rausayar da kai na. Ya lakuce min kumatu yana sunbatar gefen kunne na,
“Ina kaunar ki Khadija na, Komai naki dabanne, Idanun ki na matukar tafiya dani. Dan karamin bakin nan naki.. Idan yasha strawberry lip stick dinnan.. Gashin ki.. Da nan da nan..”
Ya karasa fada yana nuna kirji na. Kamo hannuwan sa nayi muka shiga bandaki, wankan mukayo muka fito sai sake gayamun yana sona yake. Na riko tafukan hannayensa ina dora su akan fuska ta. Ina shafa su ahankali cikin kalaman dake nuna tsantsar kauna ga abunda ake kaunar na shiga ce masa,
“Nima ina kaunar ka sosai mai martaba, Zaki kake, ga isa ga kasaita. Lu’u lu’u sarkin d’aukar idanu. Dawisu sarkin ado, Zuma naa mai gardi da dad’i a baki.. Hmm kana rikita ni da kalar kaunar ka.”
“Kece sinadarin komai ai Zawjatii. Kada ki manta ke kika maida Salman ibn Aliy ya zama cikakken sarki mai iko ga al’umar sa… Ya kuma fatattaki makiyan sa a zabure. Nagode miki mata tah! Godia mai dimbin fatan alkhairi…”
Zanyi magana kenan ya katse ni ta hanyar zagaye hannun sa a jikin labbana cikin wani salo na kauna. Gaba d’aya ya hana ni magana saboda zafafan kisses din daya shiga yi mun a ilahirin jiki na, Tuni na bada kai bori ya hau..
<>. <>. <>. <>. <>. <>. <>. <>.
Kwanakin mu biyar a dubai muka koma kasar mu Nigeria da kaya nik’i nik’i. Siyayyan kalan lefen Yareemah Khal na amaryar da zai yi Dr. Bintu wadda mun gaggaysa a waya da ita, Har na matsu tashigo cikin masarautar mu kara kulla zumunci, Domin tanada son mutane, Kuma ma’abociyar kallon kdrama ce itama . Kusan kullum muna chatting a WhatsApp sai na tanbayeta ta mun recommending masu da’di. Nayo siyayyar kayan babies, Ammi ma ta kara mana wasu na maza daban dana mata kuma. Naji dadi sosai hakika ALLAH yabani uwar miji ta gari, Mijin kwarai, Ga yan uwansa masu kauna ta. Gwaggo Ta Fada har tayo mun yajin haihuwa. Suma kuwa Salman ya biya musu Hajj itada Addah Maryama da malamin daya temaka mana da addu’oin karya sihiri, Na masa godia sosai a ranar da ya gayamun. Domin nayi matuk’ar farin ciki…
*MASARAUTAR BASANNABAS*
A kwana a tashi ba wuya awajen ALLAH, safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Ranakun mu nata shud’ewa a haka. Tsaye nake sai faman tsuke fuska nake yi, Ina zaro doguwar riga wacce ba zata takura min ba daga closet, na zura ina ta dacin rai kai daka ganni kasan cewar bana cikin walwala. Bedroom silifas dina na zura Dr Fiddau dake tsaye tana jira na ta karaso tare da riko ni, hannu na ta sagalo zuwa kafadarta muka fara takawa tana cewa.
“Yauwa ranki ya dade daure ki taka, sannu Allah ya rabaku lafiya.”
Na daga kafa a hankali kamar ina tsoran karsu fashe saboda yadda naga sun kumbura, ina cizon lips na kasa nace.
“Amman dai Dr. kece kika bashi wannan gurguwar shawarar na cewa in dinga zagaye dakin nan ko?”
“Allah ya kara miki lafiya, ai tunda kika zo wannan stage d’in, dole wannan hanyar itace mafi sauki a gurinki da kuma babyn cikin ki. Sannu… Yauwa tako a hankali… Yauwa Gimbiya daure dai.”
Haka Dr ta dinga karfafa min gwiwa, Ina ta takawa da taimakonta, sai da muka zagaye cikin bedroom d’in sau hamsin sannan Dr tace na zauna na hutu. Nikam gaba daya kasa zama nayi sai kwanciya ina sauke numfashi da sauri da sauri. Da yake babu inda nake zuwa daga bathroom sai sallah sai kwanciya, hakan yasa na kuma murjewa nayi kiba hankali na a kwance babu abinda yake damu na, sai kumburin kafa da nake fama dashi kwana biyu.
“Ranki ya dade an jima ma ki daure kiyi wankan, Sai ki kwanta, insha Allahu zakiji dadin jikin ki.”
Kasa amsa mata nayi sai faman nishi nake yi saboda gajiya, tace min bari ta sauka kasa ta nemi wani abun taci yunwa take ji, kai kawai na daga mata, Ina lumshe ido tare da addu’ar zuwan bacci idanuwa na. Cikin hukuncin Allah sai bacci ya dauke ni mai dadi kamar kada a tashe ni. Wani irin mugun fitsari ne ya farkar dani wanda yasa ni tashi da sauri na shiga bandaki, gashi nayi sa’a kafar ta saki bana jin ko wane irin ciwo a jiki na.
Ina shiga na tsugunna nayi fitsarin Sai naga yaki tsayawa, sannan kuma yanayin yadda yake fitowa ba kamar da farko da Ina yi ba, ganin yaki tsayawa yasa nai tsarki na tashi. Ina kokarin fitowa Dr Fiddau ta shigo tana kallo na tace
“Sannu da farkawa Gimbiya, na leko ai naga kina ta bacci.”
Murmushi nayi tare da karasa fitowa, Ina cewa.
“Fitsari ne ya tayar dani, kuma nayi amman still naji abu yana bina kamar dai ruwa.”
Da sauri ta karaso ta rike ni muka karasa bakin gado na zauna. Ina zama kuma naji bahaya yana son kamani, nayi saurin rike Dr ina cizon lips yadda naji yana son fitowa babu shiri.
“Dr zan shiga toilet bakiji yadda yake son fitowa ba.”
“Gimbiya haihuwa zaki, haihuwa ce ta taho gashi nan faya ta fashe.”
Ai tana gaya min haka naji kirjina ya buga da karfi. Na zaro ido tare da kallon Dr fiddau kamar zanyi kuka, gani nake yi tamkar mutuwa zanyi idan haihuwar nan ta tabbata saboda tsabar fargaba. Hawaye suna bin fuskata ita kuma tana ta kokarin shirya gurin da zan haihu nace.
“Innallilahi wa’inna’ilaihir raji’un…. Dr mutuwa zanyi, kira min Honey bunny please.”
“Kiyi hakuri Gimbiya insha Allahu lafiya kalau zaki haihu kici gaba da addu’a bakin ki tsarkakakke ne a wannan lokacin.”
Cewar Dr Fiddau bayan ta gama yi min shimfadar ta kamo ni ta kwantar dani. Gabaki daya a rude nake banda addu’a babu abinda nake yi idanuwana banda Salman da irin rayuwar da muke yi mai cike da soyayya babu abinda yake hasko min, Sai naji kuka ya kuma kwace min. Wani uban nishi da nayi ne wanda ban san daga Ina ya fito a jiki na ba, naji Dr na cewa.
“Yauwa Gimbiya kin kusa.”
Ai ban san lokacin da nayi wanda ya fi na farkon ba, sai ji nayi baby na tsala kuka. Ni dai tunda na lafke guri daya ko motsi bana yi saboda jikin duk ya saki. Ko takan babyn ban bi ba sai wayata da nake son dakkowa wacce nake hange akan gado, buri na kawai naji muryar Salman ko zan samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Dr Fiddau taki miko min tana ta bani hakuri, ta nado babyn cikin towel tare da dora min shi akan kirji na tace nayi masa addua.
Lumshe idanuna nayi ina jin wani irin farin ciki marar misaltuwa, Wai yau ni Dije ni ce dauke da baby halak malak. Ban ma san abin da na haifa ba, kuma na kasa tambayar Dr gashi ita kuma bata sanar min ba. Tunanin da na shiga ne yasa na manta banyi adduar da tace nayi ba har tazo ta dauke shi tayi masa wanka tas sannan ta saka mishi kaya nima ta gyara ni tsab ba zaka taba cewa ni ce na haihu yanzu ba. Tana Murmushi tace.
“Toh Gimbiya kinga yanzu sai a sanar cewa kin sauka. Bari a fara sanarwa da Ammi.”
“A’a bani wallahi Honey bunny zan fara gayawa idan yaso sai Kowa yaji. Me Allah ya bamu a cikin jinsin mu?”
“Ranki ya dade prince ne.”
“Namiji kenan?”
Na fada da sauri Ina daukar waya ta. Fitowarsa kenan daga fada yana son yaje ya watsa ruwa yaji kiran nawa, kasan cewar sautin kiran ta na musamman ne yasa yana ji ya yi saurin dauka babu wani jira bare yanga. Cikin sassanyar muryar shi ya yi min sallama Ina ta faman murmushi.
“Baby kana ina yanzu?”
“Gani nan na fito daga fada, ya jikin naki?”
“Toh kawai ka biyo ta nan baby.”
“As you wish Gimbiyar zuciya ta, gani nan zuwa.”
Murmushi nayi ina kallon babyn dake ta faman yin bacci, Dr ta shirya shi fuskarsa kawai ake Iya gani a waje. Dr na kitchen Salman ya shigo, na kalleshi muka yi four eyes sai dariya nake yi. Shi kuma cak ya tsaya daga bakin kofar ya bude baki irin na tsantsar mamakin nan, kwayar idanunsa tana ta juyawa akan babyn da kuma kai na ya rasa wane irin al’ajabi ne wananan.
“Haba jarumin jarumai ya ka tsaya a nan.”
Maganar da nayi ce ta sanya shi karsashi ya yi saurin karasowa guri na yana taba min ciki yana kuma kallon babyn. Baki na rawa cike da son jin karin bayani yace.
“Baby me nake gani haka yi min karin bayani. Wannan babyn fa?”
Sai da na janyo shi jikina muka rungume sannan na nufi wajan kunnansa Ina cewa.
“Honey bunny har yanzu ka kasa ganewa? Toh na haihu kuma wannan babyn ka ne. Dr tace karna kira ka har sai komai ya lafa.”
Yaa Rabb! Wata irin runguma da ya yi min kai kace yau ne karan farko da muka taba haduwa dashi. Ya dinga kai min sumbata a sassan jiki na, kafin ya sake ni ya yi wajan jaririn, kallansa kawai ya yi Salman ya fashe da kuka yana daukar shi yana dorawa a kan kafadarsa. Ni kai na sai da ya sani yin kukan saboda yadda naga yana yi. Gashi kamar su d’aya, Tamkar yayi kayi ya tofar. Ashe da gaske ne zai ga gudan jininsa a duniya? Duk da yasan da cikin beyi zaton zai dauki babyn da hannunsa ba, sai gashi yau ya gani harma gashi a kirjinsa.
“Alhamdullah ya Allah kai ne abin godiya a duk wani lamari. Allah na gode maka.”
Yasa bayan hannunsa tare da goge hawayen ya sanya bakinsa a cikin kunnan babyn yana yi masa khuduba, Hade da tauna dabino yayi addua sosai ya diga masa ruwan a bakin sa.
“Sannu da kokari baby na, dole nayi miki babban tukwici ta hanyar sanyawa yaron nan suna Muhammad Basheer. Allah ya raya mana shi yasa ya yi halin mai sunan.”
Koda wasa ban taba kawowa zai sanya sunan mahaifina ba saboda nasan shima nashi ya mutu kuma yana san ya sakawa. Sai gashi ya bar nashi saboda farin ciki na yasa nawa. Salman dan halak ne akwai halacci akan koma waye. Rungume mu yayi nida babyn koda Dr Fiddau ta dawo ta hange mu komawa tayi tana dariya abin yana burgeta yadda Salman yake kula da matarsa da nuna kulawa da soyayya.
Waya ya ciro ya sanarwa da Ammi ya kira Gwaggo ta Fada ya sanar mata, Dasu Kawu daddy, daga nan zance ya karade masarautar Basannabas cewar Allah ya sauki Gimbiya Khadija lafiya. Su Umma Hansatu suka garzayo suna zuwa suka ganmu fes kamar ba mu ba nan Salman ya gaya musu shima sai da aka gama komai sannan suka kira shi.
Kafin kace menene dakin ya cika da mutane yan ganin baby, duk da cewar Umma Hansatu tace Ammi ta bada sanarwa kar wanda ya dauki babyn a hannu duk mai san ganinsa ya ganshi daga kwance Kar a dauke shi. Tayi hakan ne saboda tsaro kar aje ko akwai ragowar mahassada a cikin masarautar ba a sani ba.
Nima bayan an dan lafa na kira malama Mardiya na gaya mata haihuwar, cike da farin ciki ta yi min barka tace min kuma zata zo suna. Mami ma da kawu daddy sun zo tun a ranar suka yi mana barka Mami tace dani zata tafi gida nayi wanka a can, aka tambayi Salman ya shafawa idanunsa kwalli yace sam be yadda a kaini ko ina ba idan wanka ne shima zai Iya ba sai an kira wata ba. (Ba man kai😂🤦🏼♀️)Maimakon shi da ya yi maganar yaji kunya, A’a sune suka ji kawu daddy ya dinga dariya suka koma gida.
Da daddare Ammi tazo taga ‘Da, tace Umma Hansatu ta yi min wankan jegon, na bugawa Salman waya nan ma yace ba yadda ba shi wallahi babu wanda zai gane masa mata. Duk yar kunya da nauyin da yake tsakaninsa da Ammi batun wankan nan ya kekeshe ya hana, shi ya tayani nayi baya nuna min kyankyami ko kadan, dan da kanshi yake cire pad ya saka min wata cike da tsantsar nuna kulawa da soyayya gare ni. Gaba daya Salman ya dena zuwa fada sai waziri (Falaki) shine yake gudanar da komai, shi kuma muna tare muna jego kamar wata mace. 🤣
Cikin kwanaki biyu duk social media ta dauka da cewar sarkin Basannabas ya samu karuwar ‘Da namiji, ana ta yi masa fatan alkairi da karuwar samun wasu nan gaba. Yan uwa da abokan arzuka suka dinga zuwa suna bada tasu gudun mawar. Kawu daddy ma har kayan barka ya yi min irin wanda iyayen mace suke yi. Salman kuwa ba’a magana domin tashin adda Maryama ya yi ita da Alhassan suka dakko masu decoration suka zo aka shirya dakin baby tamkar a kasar turawa.
Ana gobe suna yasa aka kirawo masu tsara gurin events suka zo harabar masarautar suka kawatashi kai kace daman anyi gurin ne tun fil azal. Ya tsaru Iya tsaruwa harda toilet a guraran irin wanda ake kafawa aguri idan an gama a dauke aje a zubar.
Ranar suna yan uwana duk sun zo, kuma nasa aka dakko matan Durbun aka kawo su, daman nasa an ware musu inda za’a sauke su dan kar su zo suyi ta kauyanci ana zagin su suji babu dadi. Aka shirya ni tsab nayi masifar yin kyau irin wanda ko ranar bikin mu banyi ba. Baby ma da yaci sunan mahaifi na wato Basheer.. Yareemah Abdullah yace a dinga kiransa da suna *Hammad*, an shirya shi ya yi kyau shima kamar irin yaran larabawan nan. Shima Salman ya shirya Shiri irin wanda be taba yi ba, ya fito a cikakken matashin sa kai ba zaka taba cewa ya auri mata har biyu ba bare kace ya yi aure gashi har ya samu ‘Da ba.
Ya kalleni na kalle shi kowannan mu kishi ne cacim a zucin zuciya saboda dukkan mu munyi kyau kamar wasu amarya da ango ranar Dinner. Muka karasa rumfar da aka tanadar mana ta musamman, Addah Maryamah na bayan mu dauke da Hammad a cikin baby bag yana ta baccinsa hankali kwance. Muna zama aka fara daukar mu hotona ji kake Wal… Wal… Kyaras… Kyas.. Kyas.🔥
Daga nan Mc ya fara gabatar da abinda ya tara mu a gurin, Salman sai nan nan yake dani, yan durbun kuwa kasa rufe baki suka yi dan mamakin yadda baya jin shakkar rike ni a gaban mutane, sai rufe ido suke kamar akan su abin ya faru. Ni kuwa ko a jiki na, Sai ma dadi da nake ji ganin yadda duniya ta shaida soyayyar mu nida miji, na. Anci ansha an zubar da naira musamman ma Salman da yake ganin komai ya yi be kai geji ba saboda muhimmancin da muke dashi a zuciyarsa. Ko gurin mutane baya bari naje sai dai su sukaraso mu gaisa suyi min Allah ya raya, babu yadda banyi ba ya barni naje amman funfurus yaki.
Tun kafin a watse ya kama hannu na kota kan jaririn bebi ba muka koma sashe na, ya zaunar dani ya shiga bathroom ya tara ruwa sannan ya dawo ya zauna kusa dani.
“Taro ya tashi lafiya kizo kiyi wanka ki gasa jikin ki sosai, dan Dr Fiddau ta gaya min muhimmanci wannan wankan jegon.”
Na rike haba ta Ina kallansa da mamaki nace.
“Me tace maka?”
Yana zuge min riga ta yace.
“Cewa tayi idan baki sosai ba ba zaki kwari ba, kuma wai da wuri zaki takwarkwashe. Ni kuma gaskiya bana son ki riga ni tsufa Zawjati.”
“Nifa a gajiye nake yanzu, ba zan Iya yin wani wanka ba, Sai na huta.”
Be ce dani komai ba ya zare min rigar tare da daura min towel, ji nayi kawai an daga ni ya nufi bathroom d’in yana cewa.
“Wankan shi ne zai sa kiji dadin jikin ki, kuma ma ai ni na tattagoki daga filin sallamar ku da malama Mardiyar nan taki karewa. Ni wallahi har na fara kishi da ita saboda yadda kike bata kulawa ta musamman.”
“Na shiga uku honey bunny ka rufa min asiri na mutu maza su kai ni ba mata ba. Babu komai tsakanina da malama Mardiya sai mutunci tsantsar sa. Ka sani cewa babu wani abu a duniya bayan soyayyar annabi Muhammad SAW da ya zarce ka a zuciya ta. Karkai kishi da ita please honey bunny, kaunar ka ta musamman ce Allah ya dasa min ita a zuciya da gangar jiki na. Ina sonka fiye da yadda baki zai furta, ido ya kalla gangar jiki ta nuna. I love you so much Abie Hammad, yi min wankan ko zuciya ta zata samu nutsuwa da irin salon ka Zawj, My paradise.”
Rungume ni ya yi tsam a jikinsa yana zare min towel d’in jiki na a hankali har ya zame kasa. Kallo na ya tsaya yana yi tun daga sama har zuwa kasa kafin ya sakar mana shower a jikin mu. Yana shafa min ruwan a sassan jiki na yana magana mai cike da yabo tattare da kauna da soyayya tun daga karkashin zuciyarsa yana cewa.
“Allah ya yi halitta a nan gurin my love, komai naki special ne aka yi miki. Ni nasan ina daya daga cikin mazan da Allah ya yalwata da ni’ima na samun mace abar alfahari. Zawjatii babu inda ba zan iya nuna ki a duniyar nan ba, kin yi min ta ko’ina, Ina son duk wani abu da yake jikin ki musamman ma nan…”
Ya fada yana nuna fitilun kirji na, wanda yanzu haihuwa tasa sun kuma cika sun tsaya kyam babu rankwafawa.
“Anya zan barki kiyi breastfeeding kuwa? Madara za’a siyo masa a dinga bashi gaskiya saboda bana son su lalace.”
Ya yi magana still hannunsa yana gurin sai wasa yake yi dasu. Na kwantar da kai na saman kirjinsa ina shafo kansa nace.
“Honey bunny shima fa shayarwar yana da advantage a gurin yaro dama lafiyar abubuwan. Karka damu zan kula maka dasu yadda ya kamata, amman ka barni na shayar dashi hankali na zaifi kwanciya.”
“Haka ne my love kin tunatar dani kema, Allah ya raya mana shi bisa tafarkin addinin musullunci.”
“Amin habibi da’iman.”
Ya kashe shower din ya dauke ni sai cikin bathtub, muka dinga yar watsa ruwa tare da kwanciya jikin juna kafin daga bisani muyi wankan mu fito cikin nishadi da farin ciki. Daman tun muna bathroom muka jiyo wayoyin mu suna ta ringing, ya duba tashi yaga ten missed calls na Ammi, four missed calls na Abdullah da yazo mana hutu, seven missed calls na Alhassan da ragowar mutane . Nima na duba nawa naga duk wadanda suka kira shi nima sun kira ni wato Ammie da Abdullah sai adda Maryama dasu Ya Shukrah.
“Ba zasu barmu mu huta ba.”
“Banda abinka takawa yaufa suna dole a neme mu, kai kuma ka kawo mu daki nasan ana can ana gulmar mu, Allah ya sa ma…Kowa yasan Ina cikin rashin tsarki da fassarar da za’a yi mana sai Allah.”
Yana saka kaya yana cewa.
“Suyi su tafi ma kowa ya watse su barmu mu huta mu da dan mu.”
“Uhmmm lallai takawa babu alkunya?”
Kamo ni ya yi tare da zare towel d’in jiki na yana cewa.
“Wa zanji kunya ke ko ni.”
Ina dariya nace dashi.
“Zan rama ni ma.”
“Taho to.”
“Ai ba yanzu ba sai lokacin da kake nec….”
Na kasa karasawa ganin yadda ya bude baki yana zaro ido jin abinda zan furta.
“Kina karasawa zan kira Ammi na gaya mata.”
Jikinsa na fada Ina ta dariya dan ba karamin dariya yake sani ba a wannan lokacin, soyayyarsa tana kuma karuwa a rai na. Tsab ya taya ni na shirya nima dagwas sannan ya bude dayar kofar ya gudu sakamakon muryar Ammin da ya jiyo tana cewa.
“Wato ba zaka barta ba yau ma ko?”
Ina daura dankwali naje na bude suka shigo, ganin ni kadai ne yasa sukai ta mamaki.
“Ina Salman din yake.”
“Ammi ai da muka taho ya taho Sai ya wuce bangaran sa, nemansa kike?”
“A’a daman mutane ne ke ta nemanki, kuma naga shi ya dauke ki daga gurin. Shikenan to idan kin gama da wadannan sai ki zo ki sallami na waje.”
Cike da girmamawa na dan durkusa Ina amsa mata. Su Ya Shukrah ne suka shigo dakin ban bi ta kansu ba na wuce inda ake sunan na karasa sallamar da mutane sannan suma muka yi sallama suka tafi. Cikin kwanciyar hankali muka ci gaba da kula da yaron mu Hammad yaro mai farin jini tun a zanin goyo. Ranar da mukai arba’in tamkar lissafi Salman yake yi, sai gashi cikin shirinsa na kwanciya, ni a lokacin ma har mun kwanta na dora Hammad a jikina naji an karbe shi.
Kallon shi nayi ina kifta idanuwa tare da turo baki duk da cewar nima fa nayi missing d’in shi amman naki nuna masa kai tsaye.
“Ya haka?”
“Mai gurin ne yazo kinga ai dole mai tabarma ya nade.”
“Kai jaririn kake cewa ya bar nan.?”
“Ah to Baban jariri yazo ba dole ba.”
Sauka ya yi ya kai shi cikin gadon sa da yake bashi da rigima bacci yake ta yi, shi kuma ya dawo guri na bayan na rufe jikina da blanket, ya janye shi tare da kamo ni yana cewa.
“Baby ki shirya karbar kanin Hammad dan ni na fi son na gansu yan dagwai-dagwai a cikin gidan nan.”
Kafin nayi magana ya rufe min baki da tattausan labbansa, dama jira nake saboda uban gyaran da nasha sai faman tsunkuli na yake yana neman inda za’a bashi tallafi. Daga nan fa muka lula duniyar ma’aurata mai wahalar fassarawa…..
••••
Haka rayuwar aurena ta cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali, Duk kuwa da mu kan haura muyi fada da Salman lokuta da dama, Domin rayuwar aure gaba d’aya hak’uri ce, Sai yanzu nake tabbatar da zancen Addah Maryamah, Sai mun danyi fad’an mu sai kuma mu dawo mu shirya dashi kamar bamu yi ba.
Cikin yan shekaru kalilan na tara yara uku,Basheer wanda yaci sunan mahaifi na, Muna ce dashi ‘Hammad’, Sai Aliyu wanda yaci sunan mahaifin Salman muna kiran sa da (Aaleem) sai auta ta mai sunan Umma na jamila (Nour) wadda yau kwanaki 40 kenan cif da haihuwar tah, Alhamdulillah! Allah shine abun godia don kuwa dik inda na juya gaba da baya inada masoya, Ga yalwar albarkar ‘yaya dana samu, Ina business na shigo da kayayyakin kayan sawa dana gida daga Turkey da makka, Nace Zan koma aiki na Salman yace a wane garin gab’a gab’an naga matar sarki na fita zuwa aiki? Aikin kuma na jarida? Nan yamun toshiyar baki na kamfanin ruwan roba da pure water sai shagon kayayyakin da nake sarowa aka bude akan titin state road.
Dukkanin dangi na muna zumunci dasu, Ciki harda mutanen durbun, Dana ware musu sashen baki inda shaheedah ta tashi, Anan suke zuwa suyi hutun su su murje su koma, Balkin haladu yanzu itace babbar hadimata takara kyau, Zawarawa sai zuwa neman auren ta suke tace a’ah sai ta sake hutawa.
Gajiyalle ma takan zo, Wani lokacin Mudi da ladiyo ma suna zuwa, Wata tahowar kuma yazo da Abasiyya mai awara wadda ya aura ya ajiye a kauyen landantsan.
Inacan ina tunano cigaban dana samu a rayuwata sai jiyo kamshin turaren Salman nayi yana dukan hanci na, Na kauda kai na gefe ina cuno baki na gaba. Don dazun muka yi fada akan ba wata ziyarar arbain da zani. Sanye nake cikin atamfa samfurin doguwar riga, Nayi ture kaga tsiya da kallabin kai na, Na sake kyau sosai saboda gyaran jikin da aka mun. Zama yai a gefe na neman kamo hannu na na zame na koma can kusa da gadon baby Nour.
“_Soyayyah na baki yammata…Ki temaka ki amsa waka ta…! K’auna ne na baki yar gatah, Ki temaka ki amsa wak’a ta…. Don ni dai gaskiya kina burge ni, In kin sako kallabi kina tafi da hankali.. Don.. Ni dai… Gaskiya….Kina burge ni, In kin sako kallabi kina tafi da hankali… Ki tausaya dan Allah ga ni.. Soyayya nake nema komai kince zanyi… To ki taimaka dan Allah ga ni.. Soyayyah nake nema komai kince zanyi…_”
Waka ya kunna ahankali yana bin sautin ta yana shafa kallabin (dankwalin) dake kai na. Na cuno baki gaba ina daure fuska ni alalle fushi nake dashi, A raunane ya fara magana kasa kasa,
“Dan Allah kiyi hak’uri… Naji naji zaki je gidan Kawu daddy, Idan nai fixing lokaci ma zaki je har su Lagos, Pls ki dena fushi dani, Tsakanin dazu da yanzu dubi har na rame, Na kasa sukuni a fada…”
“Ni dai ka kyale ni….”
“Naki’ na kyale kin. Yi hak’uri ki tashi muje na gaya miki wani labari…”
“Kaga fa Nour ita kadai..”
“Nasa a kira Balki yanzu zata zo..”
Yana rufe baki sai ga Balki tashigo,
“Allah ya kara muku Lapia, Ranki ya dade ga ni.”
“Nour zaki dauka.. Zan taya Abien su aiki.”
“Toh Allah yakara miki lapia.”
Tura gadon da Nour take akai tayi, Suka koma dayan dakin, Shi kuma ya kinkime ni sai cikin daki yana ta nanataa.”
“Khadeejah yar jaridah.. Dijengala ta mai gari yar baffanta, Ta Gajiyalle mai yar hakiya, Oganniyar Salman sai yadda kikai dashi.. Na jinjinawa KIBIYAR AJALI.. kaga wadda aka buga aka barta, Sulke baya tare ta sai ta gittah.. Zuma naa, Zak’i ne dake mai ratsa bargo, Kasaita taki ce. Kyakkyawa mai kyawun hali… Ina kaunar ki, Kaunar kauna yar asali, Allah ya miki albarka.”
Jinsa kawai nake, A haka muka shiga ban’daki, Jikin sa har rawa yake. Ya dakko soso yana tatsa mouthwash akai. Na tuntsure da dariya ina riko hannun sa,
“Zawj bafa shower gel ka dakko ba mouthwash ne.”
“Au.. SubhanAllah! Ke dince duk kin rud’ani da wani fitinannan kamshi wannan *yerwaincense&more dai kice ta baki account details zan tura mata jari ta kara..”
“Godia muke takawa. Zan karb’o Insha Allah… Ina kaunar ka sosai…. Ka iya tafiyar da ruhin mace da magudanar jinin ta.. Ina kaunar ka nima sosai.. Miji na uban ‘yaya na. Na gaishe da sarkin Basannabas, Abien su Nour, Yayan Abdullah…..”
Da wannan muka lula wata duniya ta daban. Kowanne yana kokarin faranta wa dan uwan sa rai……
<>••••• <>•••
_Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Duka duka anan ni Nana Hafsatu na kawo karshen littafi na mai suna KIBIYAR AJALI..! Ina fatan dan fadakarwar dake ciki Allah yasa mu amfana da ita, Ya kuma bamu ladan fadakarwar, Kurakuren dake ciki rabbana ya yafe mana baki d’aya. Dan tsekon da aka samu ko akasin posting da wuri ina rokon yafiyar dukkanin ku, Dama duk wanda na batawa rai farawar book dinnan zuwa kammalawar sa…Ina neman yafiya👏🏻_
_Allah ya cigaba da riko da hannayen mu yasa mu dinga rubuta dai-dai. Zafafa biyar yan biyar (marubuta) na gaisheku duka, Dama makaranta zafafa biyar din gaba ki d’aya.❤️_
_Nagode k’warai da siyan kayan turare na da wasun ku suka yiyyi, Twas really beyond my wildest expectations, Heartfelt ❤️❤️Allah ya kara arziki mai amfani, Masu tambayan hotunan kayan kamshin zaku iya dubani a instagram: @yerwaincense_and_more. Ko Facebook page dina: yerwa collections. Domin tuntubata za’a iya nema na ta wannan number da ake siyan book din🥰._
_Wanda ya karanta book dinnan bai siya ba yai gaggawar biyana akan nera 350, Domin gudun shiga hakkin mallaka. 08095215215 ta Wannan number👈🏼Idan duka biyar din akeso naira 1,500 gaba d’aya completed documents d’insu, Sai a tuntub’e mu ta payment details d’inmu dake jikin shafukan books din mu, Sannan…Duk wanda ya dora mun book a youtube bada yarjewata ba Allah ya bi mun hakk’i na👏🏻_
_Masu tambayan books dina na baya: suna wattpad:missxoxo00_
_Sai haduwa ta gaba idan mai duka ya kai mu….🥂🔥🥰_
Show some love: follow/like and refer my scented products to ur beloved ones❤️ IG:yerwaincense_and_more
DAN ALLAH A DANNA MANA FOLLOW, A KUMA DINGA LIKING DUK ABUBUWAN DA MUKA DORA. LOVE Y’LL FISABILILLAHI!!❤️❤️
ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma’ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
_IDAN DUKA DOCUMENTS DINSU KUKESO ZAKU SAME SU AKAN NAIRA 1,500 KACAL. _
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
GIPHY App Key not set. Please check settings