Advertisement
*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 17*
___________________
Advertisements
*_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA’ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_*
_Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._
*_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma’abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._*
_To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_.
*_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka👇🏻😁_*
Advertisements
*Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY*
SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_*
Ummu Dufail @ Facebook
Ummu Dufail @ instagram
Phone no: 07067943479.
_Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin😉👍🏻_.
_____________________
*Page 17*
………..Tarba mai ban mamaki da tu’ajjibi Zinneerah ta samu daga hajiya iya, harma da wasu daga cikin jikokinta dake gida ta iske a sashen. Duk yanda taso ta takura kanta saboda baƙunta da rashin sabo sunƙi bata damar hakan. Dan sai faman jera mata tambayoyi suke tamkar ƴan jaridu.
Dolenta ta saki jiki dasu dan su biyun duk sa’anninta ne. Biyu mata, Bahijja da Meenal wadda taci sunan Hajiya Iya kenan. Sai ɗaya Namiji mai suna Jamal.
Harga ALLAH Zinneerah taji daɗin kasancewa dasu, dan ta fahimci sunada tarbiyya da sauƙin kai sosai, sannan son ɗan uwansu ko yaya yake wannan trianing da akai musu ne tun asali.
Cikin katsesu Hajiya Iya dake shafa man zafi a ƙafarta tace, “Niko kun isheni da subaɗi Bahijja. Kuma barni nai hira da Innon tawa kunbi kun hana. Sai ku tashi ku kaita wancan ɗakin kuɗan ƙara gyarawa duk da dai ko jiya Rahi ta gyarasa ta samu taɗan watsa ruwa ta huta dan shine zai zama ɗakinta”.
Wani irin waro idanu Jamal yayi tare da zabura. Haka Meenal da Bahijja ma duk sai da suka zaro idanunsu. Jamal yace, “Granny kina nufin ɗakin Yayanmu fa kenan?”.
Harara sosai Hajiya iya ta watso musu tana ƙyaɓe fuska. “Eh shi dinfa nake nufi ba waniba. Zuwa yake ƙasar ne da har za’a wani cigaba da faman barin ɗaki haka aljanu na dubulwa a cikinsa? Ubansama daya haifesa bai tuna inda yakeba shekara kusan uku balle ni da iyakata haihuwar uban nasa”.
Yanda ta ƙare maganar cikin ɗacin rai ya saka jikinsu duk yay sanyi. A sanyaye Meenal tace, “Kiyi haƙuri Granny, mu dama zaki yarda sai mu tafi da ita sashenmu, kinga saita zauna a ɗakinmu dan ALLAH”.
“Hakan zaifimin daɗi kuwa Amina. Sai dai kuyi haƙuri nafison zamanta kusa dani akoda yaushe. Koba komai zanga fuskar Innota naji sanyi”.
Kansu kawai suka iya kaɗa mata, dan tunda ta faɗi haka basu isa jayayya da ita ba. Ko min roƙon da zasu mata kuma bazata canja ra’ayintaba. Zinneerah dai najinsu kanta a ƙasa, sai dai babu abinda ta fahimta a zancen nasu kuma. Amma ganin yanda fara’ar fuskar Hajiya iyan ta ɓace tun daga maganar ne ya saka jikinta yin sanyi itama……
“Taso muje kiga ɗakinki Sister”. Bahijja ta katse tunanin Zinneerah tana kama hannunta cikin nata. Babu musu ta miƙe tabi bayanta, Meenal da Jamal ma suka mike suka biyosu.
Kallo Hajiya Iya ta bisu dashi idanunta na cika da ƙwalla. Dan maganar nan ta tado mata da wani babban miki dake zuciyarta tsahon shekaru, mikin daya shafi rayuwar ɗanta da jikanta, Saurin saka hannu tai ta sharesu tare da miƙewa ta nufi hanyar ɗakinta tana ɗan ɗingisa ƙafarta dake mata ciwo tinda safe.
“Sister Zinneerah lallai keɗin mai sa’a ce”. Meenal ta faɗa tana tura ƙofar ɗakin da suka iso a ɗan lungun corridor ɗin dake facing jikin ɗakin Hajiya Iya. Kafin Zinneerah ta iya cewa wani abu Jamal ya karɓe da cewa “Mai sa’a kuwa ta gasken gaske. Dan kece ta farko a tarihin gidannan kaf da zaki rayu a wannan ɗakin na Yayanmu bayan shi kaɗai dake rayuwa a cikin kayansa idan yazo ƙasar”.
Haka kawai gaban Zinneerah ya faɗi batare da tasan daliliba. Har suka shige ɗakin ita tama kasa motsawa balle ɗaga ƙafarta. Ganin hakan yasa Jamal dawowa da baya yaja hannunta suka shige ciki, duk da taso ƙoƙarin ƙwace hannun nata amma yaƙi bata dama sai da suka shigo tsakkiyar ƙaton ɗakin da batamasan yanda zata fasaltashi ba a fahimceta.
Sakin hannunta da Jamal yayi ya bata damar ɗago idanu tanabin ɗakin da kallo. Yayinda hancinta ke shaƙar mata wani irin mayataccen ƙamshi mai sanya zuciya salama. Wani irin saki gaɓɓanta sukai a lokaci ɗaya, ta zubama su Bahijja daketa yaye fararan ƙyallayen da aka lulluɓe komai na cikin ɗakin dasu saboda gudun ƙura ta hausu.
Sai da suka gama yaye komai ya bayyana Meenal ke faɗin, “Bara na ɗakko kayan shara mu tayaki ɗan ƙara gyarawan baƙunta. Kuma mufa kibar mana wannan ɗari-ɗarin Madam”.
Cikin tsokana Jamal yace, “Barta sotake mu kirata baƙauya maybe. Gwarama ki sake damu kafin su Yah Haneef su dawo gidannan gobe idan ALLAH ya kaimu, dan zasu cinyeki da bakine”.
“Kaji munafiki, saina faɗa musu yasin”. Bahijja dake hararsa ta faɗa.
Yanda Jamal yay da fuskane ya saka dariya kufcema Zinneerah batare data shiryaba. Hakan yay dai-dai da dawowar Meenal ɗauke da kayan shara ɗakin. “Oh ALLAH, kokefa ƴar uwa. Ni kuwa an taɓa faɗa miki keɗin ƙyaƙyƙyawa ce musamman idan kina dariya?”.
Kasa bata amsa Zinneerah tayi, sai dariyar tatace ta koma murmushi kawai. Hakan datai ya saka su Jamal kwashewa da dariya a tare. Bahijja tace, “Kinga kinsatama ta haɗiye abinta da wannan bakin naki da bai gani ya ƙyale”…….
“Wai nikan sharar zakuyi ko damuna da shegen surutu?”. Suka jiyo muryar Hajiya Iya dake tunkaro ɗakin.
A take kowa ya nutsu suka fara ƙoƙarin sharar. Shigowa tai har yanzu fuskarta a dagule da ɓacin ran ɗazun. Tabi ɗakin da kallo da ƙyau kamar mai nazari. A ƙarshe ta sauke idonta akan Zinneerah dake ƙoƙarin tayasu itama. Haka kawai kuma sai taji ɓacin ran nata ya sassauta, dan wani tunani ne yazo mata a rai yanzun nan. Ta sauke ajiyar zuciya da juyawa ta fice a ɗakin tana murmushi.
Tsaf suka gyara komai dan an horar dasu aiki tuni. Cikin kanƙanin lokaci ƙyawu da tsaruwar ɗakin ya ƙara bayyana a idon mai kallo. Musamman da suka cire labulayen ɗakin duk suka sake canja wasu fararen tas dan dama fararen suka cire. Kaso mafi yawa dake a ɗakin kalar blue and white ne. Sai wasu colors ɗin ɗai-ɗai da ba’a rasaba. Da yawansu kuma an ɓaɓɓoyesu ma.
Idanu ta lumshe a hankali tana maijin wani abu mai nauyi dake a ƙirjinta yana narkewa sannu-sannu zuwa cikinta. Nannauyar ajiyar zuciyar da bata shirya fitartaba ta kufce mata a karon farko. Kusan a tare Meenal, Bahijja, Jamal suka dubeta. Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, dan sun fahimci Zinneerah bata da sakewa da mutane, gata kuma da alama akwai miskilanci tattare da ita.
★★
Ƙarfe bakwai da wasu mintuna Alhaji Kabir ya iso katafaren family House ɗin nasu. Bayan samun wajen fakin da direba yayi ya tsaya aka buɗe masa ya fito riƙe da leda a hannunsa wadda kowa yasan mai ita. Dan babu fashi kullum sai ya shigo da irin wannan ledar domin mahaifiyarsa koda iyalansa basu samu hakanba. Sanin baya bama kowa dakon ɗaukarta, shi yasa babu wanda ya tunkaresa domin karɓa. Sai dai sauran kayansa da ɗallami driver ya kwasa zuwa sashensa shi da iyalansa. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya Iya kansa tsaye.
Ɗauke da cikkakkiyar sallama a bakinsa ya shigo falon duk da yasan a irin wannan lokacin Hajiya iya na ƙuryar ɗakinta. dan idan tai sallar magriba bata fitowa sai isha’i. Amma yanada tabbacin baza’a rasa wasu daga cikin ƴaƴansaba da basa rabo da sashen a koda yaushe.
Ilai kuwa yana shiga da fuskar Zinneerah da Meenal ya fara tozali dan sune ke facing ƙofa. A take falon yay tsit kowa ya ƙara nutsuwa. Sai Meenal ce datai saurin miƙewa ta nufesa domin amsar ledar hannun nasa. “Baffah sannu da zuwa?”.
“Yauwa uwata kune anan?”.
“Eh Baffah, munzo tarbar Sister Zinneerah ne tun ɗazun”.
Murmushi Alhaji Kabir yayi yana maida kallonsa ga Zinneerah data risinar da kanta ƙasa tun bayan amsa sallamarsa. Ya ƙaraso cikin falon sosai su Bahijja ma na masa barka da dawowa. A hankali Zinneerah ta zamo ƙasa tana faɗin, “Sannu da zuwa Baffah. Ina wuni”.
Murmushinsa ya sake faɗaɗawa da faɗin, “Yauwa ɗiyata. Welcome to Shira’s family”.
“Thanks you Baffah”. Ta faɗa a hankali cike dajin kunya.
Ya cigaba da faɗin, “Yaya kika barmin ƙanwata da ƙannanki da Abbanki?”.
“Lafiya lau Baffah, sunce suna gaisheka”.
“Ina amsawa. Alkairin ALLAH yakai garesu. Tashi ki zauna”.
Babu musu Zinneerah ta miƙe ta koma kusa da Meenal data kaima Hajiya Iya leda ta dawo ta zauna. Shikuma ya wuce bedroom ɗin Hajiya iyan domin gaisheta.
Tunda yay sallama a yanda ta amsa masa ya saka gabansa faɗuwa. Cikin ƴar ruɗewa ya ƙaraso ƙaton ɗakin nata itama da sassarfa. Gabanta ya zube jikinsa na rawa. “Innata mike faruwa naji muryarki tamkar baƙyajin daɗi?”.
Ɗago kyawawan idanunta da mafi yawan ƴaƴa da jikokin gidan suka gada a wajenta tai tana kallonsa. A take hawayen da taketa maƙalewa tun ɗazun suka silalo mata tare da murmushi a lokaci guda. Sake ruɗewa Alhaji Kabir yayi idanunsa shima na kawo ruwan hawaye.
Kanta ta girgiza masa a hankali tana share nata. “Hawayena basu zuba domin kai ba Kabir. Suna zubane a dalilin ɗan uwanka da ɗanka. Dan kai ɗa ne tamkar da dubu ga kowaɗanne irin iyaye. Sai dai dalilin rashin dace da matar farko ya zame maka tabo damu kanmu”.
Kansa ya duƙar zuciyarsa cike da ƙarajin kunyar mahaifiyarsa. Yace, “Kiyi haƙuri Innata. Nasan niɗin mai laifine a gareki, amma dan ALLAH ki yafemin, dan bazan gazaba wajen cigaba da neman afuwarki a dalilin auren Hindatu har randa zanbar duniya”.
“Karka damu komai ya wuce ai, ALLAH ya ƙaddara sai Moddibo da ƴar uwarsa sun fito ta tsatsontane. Yanzu babar matsalarmu shine dawo dasu cikinmu su da Ahmad. Kabir da gaske dai shima Ahmad matarsa ta ƙwacesa daga garemu. Yanzu ace Inno ta rasu amma Ahmad ya gagara takowa ƙasarnan yayimn ta’aziyya shida zuri’arsa. idanfa lissafina na tafiya dai-dai shekarun Ahmad kusan biyu kenan shima rabonsa da ƙasarnan. Garama Moddibo ai, tunda koba komai nane yake da mahaifiyarsa a can, kuma yana kiranka ku gaisa kai. Amma Ahmad fa, inaga ƴaƴansa ma ƙananu yanzu haka ba gama sanina sukaiba…”
Kuka ya ƙwace mata.
Sosai Baffa ya sake rikicewa. “Innata dan girman ALLAH ki daina kuka. Kiyi haƙuri dan ALLAH, addu’arki da tamu Ahmad yafi buƙata, shiko Adnan ki barni dashi, a wannan karon daga shi har Hindu bazan ɗaga musu ƙafaba. Kuma insha ALLAH namiki alƙawarin a wannan karon zanbi duk hanyar data dace domin maido ɗan uwana gida shima”.
“Kayya Kabir. A baya fa kayi irin wannan namijin ƙoƙarin amma kaga ta sake sabon shiri, harshi Moddibo ɗinma da ada bayabin ra’ayinta yanzu ta sake janyesa. A zatonmu kusancin da Khalipha ya samu da shi zai kawo wani canjin sai gashi ba hakaba. Ahmad kam shi tashi matar baƙin cikin ganinsa cikin ahalinsa kawai takeyi shiyyasa batason yazo garemu, hakama ƴaƴanta. Wannan shine illar da nake faɗa muku na aure a bariki tun a wancan karon, amma duk sai kuka gaza fahimtata. Gashi tun ba’aje ko inaba komai na daɗa lalacewa”.
“Kiyi haƙuri Inna”. Baffah ya faɗa zuciyarsa na ɗacin akan kuskurensu da bijire matan da sukai a wancan lokacin.
“Haƙuri kam ai dolene”.
Kasa sake cemata komai Baffa yayi shi dai sai ban haƙuri. Sai da yaga hankalinta ya kwanta sanann ya miƙe ya fice domin zuwa gabatar da sallar isha’i tunda ya cinye lokacin zuwa yay wankan anan.
Bai iske su Zinneerah a falonba yanzu. Da alama sun shige gabatar da sallar suma.
______________★
Duk yanda Alhaji Kabir yaso rintsawa a daren yau hakan ya gagara. Ba komai ke masa kai kawoba a rai sai tattanawarsa da Mahaifiyarsu akan ɗan uwansa da babban ɗansa.
Su uku kacal mahaifiyarsu Hajiya Iya ta haifa a duniya. Shine babba, sai ƙaninsa Ahmad, sai autarsu Bilkisu da ayanzu haka tana Lagos tana aure. Rana ɗaya aka ɗaura masa aure da ɗan uwansa Ahmad, wanda mafi yawan mutane sukafi sani da suna AA Shira. Shi da ɗan uwansa soyayya sukema juna mai tsanani tun ƙuruciya. Bayan sun kammala secondary tare suka wuce ƙasar London ƙaro karatu. Cikin amincin ALLAH suka haɗa digiri ɗinsu na farko dana biyu duk a tare. Tun suna farkon fara digiri na biyu Kabir ya haɗu da Hindatu. Asalin Hindatu ƴar ƙasan Nigeria ce. dan mahaifinta ɗan nanne. Sai dai mahaifiyarta ƴar asalin ƙasar Morocco ce. Amma suna zaune a ƙasar London tun tanada ƙuruciya, acan ta girma tamafi sanin can matsayin ƙasarta fiye da Nigeria dan sukan jima basuzoba. Ƙyaƙyƙyawa ce itaɗin sosai kasancewarta halfcast ce. Sai ALLAH ya bata wani irin usilin ƙyau mai ɗaukar hankalin mai kallonta.
Duk da yasan ba wannan ƙyawun nata bane ya ruɗesa ga sonta, amma shima ya taka rawar gani wajen jan hankalinsa gareta. Bayan sun kammala digirinsu na biyu suka dawo Nigeria kamar yanda mahaifinsu ya buƙata. Dan yana bukatar suzo suyi aure. A hanyar dawowar tasune shi kuma Ahmad ya haɗu da tasa a jirgi. Ita dai kowa nata na Nigeria, amma a Turkey take karatunta, a lokacinma tazo hutu ne. To zamu iya cewa soyayya ce irinta farat ɗayan nan ta shigesu su duka. Dan basu rabuba sai da kowa yasan adireshin ɗan uwansa.
Koda suka iso suka huta babu wani jan rai iyayensu suka gabatar musu da matan aure. Amma Kabir da Ahmad ƙiri-ƙiri sukace sufa duk sunada matan aure. Hajiya iya ce ta fara nuna rashin yardarta akan hakan amma duk suka nuna bamai rabasu da masoyansu. Gudun samun ɓaraka yasa Marigayi Alhaji Abdul-Mutallab zaunar da Hajiya Iya yaymata nasiha harta amince badan ranta yasoba.
A take aka hau shirin biki, cikin kanƙanin lokaci komai ya kammala dan ana zuwa nemawa Ahmad auren Sumayya babu wani ja’inja aka bashi. Haka shima Kabir aka bashi Hindatunsa. Ansha biki na nunawa sa’a lokacin, dan Alhaji Abdul-Mutallab ya tara musu. Bayan biki duk aka kai amare garin Bauchi.
Ƙyawawan halin Hindatu yasa Hajiya Iya ta fara sonta, sai kuma akazo dandanan ta samu ciki. Duk da Hindatu na karatu a jami’ar London bata taɓa nuna ƙorafinta nason komawa makarantaba. Tai shiru abinta har ALLAH ya sauketa lafiya ta haihu ɗanta namiji da yaci suna Abdul-Mutallab. Amma saboda alkunya suke masa laƙani da suna Adnan, Hajiya Iya kuma na kiransa Moddibo saboda sunan mijinta.
Hindatu bata taɓa nuna damuwa kosan sake komawa London cigaba da karatuntaba harta yaye Moddibo ta sake samun wani cikin. Sai da tana gab da haihuwa ne bayan rasuwar Alhaji Abdul-Mutallab da wattani biyu tace tanason komawa londan ta sake sabon ginin kartunta daya ɓalɓalce itama, dan matar Ahmad ta koma ita tuni. Shima kansa Ahmad ɗin yana can tare da ita wai zai cigaba da nasa karatun.
Tofa babbar magana. Dan ko Kabir yace bai aminceba, a yanzune zasu fara gina zuri’ar ahalinsu tayaya zata tsiro da hakan bayan tasan wannan itace matsalarsu akan Ahmad da matarsa da tunda suka tafi baya ko wiwayen gida sai an tuna masa. Inko har tace dole sai ta koma London karatu to shi zai ƙara aure. Dan dama wadda su hajiya iya sukace ya aura yaƙi tana nan batai aureba.
Wannan furucin ƙara aure shiya baƙanta ranta tace sai ya saketa. Shikuma babu wani dogon tunani ya saketan. Sai dai ya mata gargaɗin zama ta haihu, amma taƙi. Su Hajiya iya na batun sasantasu Hindatu ta ɗauke Adnan ta gudu London wajen iyayenta.
Kamar wasa tun daga wannan tafiyar Kabir keta kai kawon ganin ɗansa da jaririyar data haifa sun dawo hannunsa hakan ya gagara, dole ya ƙyaleta yay aurensa, har matar tazo tai haihuwa uku itama. Mata biyu da Namiji ɗaya. Khadija, Hafsat, Sai Abdul-Mutallab da suka sake sakawa ana kiransa shi kuma Khalipha. Sannu-sannu ƴaƴa suka fara yawaita a wannan family.
Cikin ikon ALLAH a tsakanin ALLAH yayma mahaifin Hindatu rasuwa. Inda a wannan zuwan nasu Nigeria ne Hajiya Iya ta amshe Moddibo cikin dabara daga hannun hindatu aka barta da ƙanwarsa.
Riƙon Adnan ya dawo hannun hajiya iya. Sai dai kuma yana kammala secondary daga tafiya karatu ƙasar London aka sake samun matsala, su Hindatu suka sake ƙwace abinsu. Sai dai Alhmdllh duk hutun duniya a Nigeria Moddibo keyinsa. Wannan ne ya ɗan sanyaya ran Hajiya Iya. Amma duk da haka basu daina yaƙin son maido ƙanwarsa da kawunsa Ahmad shima jikinsu ba. A dalilin Adnan da shima rashin zuwan ƙanin mahaifin nasa gida ke cin ransa suka sake dawo da hankalin Uncle Ahmad cikinsu a shekarun nan, sai dai kuma suna murna an samu waraka shima sai Adnan ɗin ya ɗauke tasa ƙafar gaba ɗaya a dalilin aure da Hajiya iya ta matsa masa saiya ƙarayi. Saboda matarsa ta farko da har yanzu bata haihuba ɗiyar ƙanwar hindatu ce. Tunda sukai aure da Adnan baifi sau uku ta yarda tazo Nigeria ba ma……
Nannauyan numfashi Baffah ya sauke mai haɗe da ajiyar zuciya saboda fahimtar da yay tunaninsa yayi zurfi. A yanzu haka kuma ba tunanin abinda ya shuɗe bane mai muhimmanci garesa, a’a abinda zaizo shi ya kamata yay tunanin gyarawa kodan farin cikin mahaifiyarsa ma dasu kansu shi da ƴar uwarsa da zuri’arsu. Dan haka ya sake zurfafa a wani dogon tunanin da bai dawo hayyacinsaba sai a wani tsahon lokaci daya samo mafitar da yaji har a cikin ransa ya gamsu da ita sannan…………..✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za’a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
GIPHY App Key not set. Please check settings