MAKAUNIYAR KADDARA 19

Advertisement

 *_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

*Page 19*

_________________________

Advertisements

*Assalamu alaikum warahmatullah,  shin kinaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what’s app kokuma ya ziyarci shafinmu  a instagram* @turare_by_awwaba mungode*

______________________

*Page 19*

………..Sosai zaman hutun nan yayama Zinneerah daɗi. Dan koba komai shaƙuwa sosai ta sake shiga tsakaninta da Little, dan yanzun taɗan rage yin kawaici akansa. Hakama ƙannenta koda yaushe suna nane da ita.

      A randa ta cika kwanaki goma sai ga su Jamal babu zato wajen sha ɗaya na safe. Lokacin suna shirin fita gidan sunan ƙanwar Maman Halima. Duk da taso taje gidan sunan sai zuwan nasu ya kauda son fitar, ta shiga murnar ganinsu. Su maman Halima kam dake goye da Little suka tafi bayan sun gaisa dasu Bahijja iyayen rawar kai.

    Sukam babu ruwansu da wata baƙunta. Dan sakin jikinsu sukai tamkar a gidansu. Sai hakan yayma maman sadiq daɗi sosai, dan koba komai hakan girmamawace suka nuna mata. Maman Sakina da yaranta kam sai suka shige ɗaki suna leƙensu ta Window da gulmar a ina su mmn sadiq ɗin suka samo yaran ƴan gayu haka?. Basu da mai basu amsa, dan haka suka cigaba da habaice-habaice da sukar mmn sadiq ɗin harma dasu Meenal da basusan da zamansu a gidanba. Harda cewa kodai a gidansu Zinneerah ke zaune aikin wanke-wanke yanzun?. Sai suka yarda a haka duk da suma sun san faɗane kawai danjin daɗi. Dan Zinneerah batai kama da wadda taje aikatauba.

Advertisements

       Su Jamal ma sun sami rabon nasu zagin sosai, dan koda sukazo suka iske Maman sakina a tsakar gida dasu Luba ko kallo basu ishesuba. Sai mmn halima data tarbesu da fara’a suka gaida cike da girmamawa. Hakanne ya sake baƙanta ran mmn sakina taja ƴaƴanta suka shige ɗaki.

      Wainar filawa Zinneerah tai musu kamar yanda sukace suna buƙata, sai da sukaci suka ƙoshi Abba ya dawo gidan bayan la’asar suka gaisa sanan driver yazo ya kwashesu harda Zinneerah da taso yin sallama da Little da sauran yaran, dan sanda maman halima ta wucene da shi yana barci, ko ganinsu su Bahijja ma bayi sukaiba. To da yakema ba sanin labarinsa sukaiba basu kawo komai a ransuba sun zatama ɗan mmn halima ɗinne duk da dai basuga fuskarsaba.

       Sosai Hajiya iya dasu Yah Moos’ab suka nuna farin cikinsu na dawowarta. Tare da faɗi mata sunyi kewarta kowa a gidan. Cikin ƴar dariyarta tace, “Nima nayi kewarku ai, wani lokacin har mafarkinku nakeyi”.

       Sunji daɗin maganarta har cikin ransu, dan itama suna mata kallone na ɗaya daga cikinsu bawai wadda tazo cin arziƙi gidansu ba. Moos’ab da bai cika yawan maganaba shi dama yaɗan ɗage gira yana gyara kishingiɗar da yay a kujera da faɗin, “Ni ba yarda nai dakeba fa yarinya”. 

     A hankali Zinneerah ta ɗago manyan idanunta farare tas ta zuba a kansa, irin kallon da yake matane ya sakata saurin maida nata ƙasa tsigar jikinta na tashi, ba yaune karan farko da Yah Moos’ab ɗin ke mata irin wannan kallonba, shiyyasa a mafi yawan lokuta bata wani cika sakewa da shiba sosai. Kasa bashi amsa tayi, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana faɗin, “Wataran dai zata fashe”.

       “Minene zai fashe?”. Cewar Haneef dake a kusa dashi yana latsa waya.

     Saifudden yace, “No jaridar mai tsadace, duk maiso ya tanaji kuɗi akwai ranar da zan saida muku”.

     Abidah ce tai dariya tanama Saifudden alamar jinjina. “Ai Yah Saif nima na daɗe da harbo jirgin, kasanfa idanuna sun iya gane-gane nima, duk randa suka tashi saya ka nemoni zan ƙara da nawa rahoton”.

     Tsam Zinneerah ta miƙe zata bar wajen, dan haka kawai ta tsargu da zancen nasu, tanaji a ranta kenan suma duk suna sane da Yah Moos’ab ɗin komi?.

      “A’a, auta ina zuwa?”. Cewar Safiyya da sauri.

      “Im ihm Aunty Safiyya zanje cikine nayi wanka”.

     Da sauri Ni’ima tace, “Wankafa? Ba shigowata Granny ke faɗin kina ciki kina wankaba Auta (Mafi yawan lokaci haka suke kiranta auta).

      Kasa magana tai, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana raira waƙa. Duka Moos’ab ya kai masa. Yay saurin wuntsilowa a kujerar yana cigaba da dariyarsa. Da sauri Zinneerah tabar wajen ranta fal tsoro. Ɗakin da har yanzu ta kasa sakin jiki da zamansa ta shige tare da faɗawa saman gadon a karo na farko. Tai ɗan murmushi dajan filo ta cusa kanta a ciki. A ranta kuwa rayawa take itakam karsu Yah Saifudden su jawo mata rigima. Ina ita ina soyayya da waninsu bayanma duk kallon yayu take musu itakam. Wannan zance ai da girma yake idan har yazo a yanda zuciyarta ke hankaltar da ita game da take-taken Yah Moos’ab ɗin. 

      Haka ta kasance cikin dogon tunanin da har barci mai nauyi yay awon gaba da ita batare data saniba. Harsuka gama hiratsu kowa ya miƙe zuwa makwancinsa basu sake ganintaba. Hajiya Iya kam dama ta kwanta tuni saboda maganin mura da tasha, kuma dama ita ba’a doguwar hira da ita, tanada saurin barci. Wani lokacinma sai jikokin nata suzo su ƙaraci shirmensu a sashen bata saniba. Dan kullum nanne wajen hiratsu sai dai idan yayansu na gari kam babu sakewa, duk da suna zuwa a hakan.

     

        Sosai Zinneerah taji daɗi barci akan wannan gado da yau ya zame mata na farko, dan ko fitsari bata farka yiba yau saboda daɗin barci. Sai kiran sallar farko na asuba ta buɗe idanunta da ƙyar tana karanto ɗaya daga cikin addu’ar tashi daga barci.

“الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور”

Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba’ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.

       Sai da ta bada ratar kusan mintuna uku bata motsaba dan idanunta su ƙara saki sosai sannan ta tashi zaune tare da zuro ƙafarta ta sauka a gadon. Tayi mamakin ganin an kashe mata wuta da lulluɓa mata bargo, sai dai tasan bazai wuce ɗaya daga cikin su Aunty Safiyya ba. Wanka ta farayi da ɗauro alwala ta fito. Bayan ta gabatar da nafila raka’a biyu ta ɗakko AL-QUR’ANI ta fara duba inda akai mata ƙari jiya a islamiyyasu data koma zuwa ta anguwar su mmn sadiq. 

    Tana zaune a wajen har akai salla. Bayan an idar tai Azkar kamar yanda Hajiya Iya ke maimaita mata muhimmancin yinta a kowacce safiya da maraicen duniya. Sai da ta kammala gari yay haske ta miƙe ta gyara ɗakin tsaf kamar yanda ta saba, ta saka kayan ƙamshi ta fice zuwa taya su baba Rahi aiki. Amma sai da ta fara shiga ta gaida Hajiya Iya da mura sannan.

        Sai da suka kammala komai tsaf suka shirya tebir sannan ta koma ɗakin domin yin wanka. 

       Sanin ba kowa ke shigowa ɗakinba sai Hajiya iya yasata fitowa kanta tsaye da towel. Sai ƙarami da take ƙoƙarin naɗe kanta data wanke a ciki. Wani irin mugun tsargawa zuciyarta tayi dai-dai lokacin da take fitowa daga ɗan lungun da toilet ɗin yake. Tsabar ruɗani da firgici batama san ta saki towel ɗin da take ƙoƙarin ɗaurawa kantaba a ƙasa….

     Ƙyaƙyƙyawan matashin dake zaune hakimce a bakin gadon ƙafa ɗaya kan ɗaya waya manne da kunnensa ya ɗago dara-daran idanunsa masu cikar gashi da haske yana kallonta da alamun tsantsar mamaki a cikinsu. Hannunsa yakai bisa kwantaccen sajen fuskarsa da babu yawan fara’a a kanta ya shafa ɗan guntun sakewar dake kanta na ƙoƙarin gushewa gaba ɗaya. Sauke hannun daya shafa fuskar yay yana gyara ɗayan dake riƙe da wayar da yakeyi har yanzun yana janye idanun nasa daga kanta yana furzar da wani irin huci daya saka Zinneerah dawowa hayyacinta ta ƙwalla ƙara dan duk zatonta aljanine kawai ya shigo mata, shiyyasa tai sumar wicin gadi.

      Gaba ɗaya ya saki wayar a ƙasa, yay saurin saka tattausan hannunsa ya toshe kunnuwansa yana runtse idanunsa da ƙarfi.

      

     Kusan rige-rigen shigowa ɗakin akai tsakanin Hajiya Iya da Baba Rahi.  Su duka kan Zinneerah sukayi dan babu wanda ma hankalinsa ya kai kansa. Hajiya Iya ta kamo Zinneerah da alamu suka nuna bata cikin hayyacinta jikinta. “Ya ALLAHU, Zinneerah! Zinneerah kinga buɗe idonki gani tare dake. Miya faru? Ko wani abune ya tsorataki?. Rahi kawo ruwa a bata dan ALLAH da sauri”. 

       Fita Baba Rahi tayi da sauri sai gata da ruwa ta dawo. Amsa Hajiya iya tai ta bama Zinneerah daketa faman ɓoye fuskarta a jikin Hajiya Iya nata jikin na rawa dan ta tsora sosai musamman data sake kallon fuskarsa yanzu hankalinta ya sake tashi. Kaɗan ta sha dan bata tare da nutsuwar shansa. Hannunta na karkarwa ta sake ƙanƙame Hajiya Iya  ta nuna inda yake zaune kunnensa toshe, hakama idanunsa a rufe har yanzu.

       “Aljani, wlhy Aljanine Granny”. Tana maganar hawaye na ziraro mata kamar an buɗe fanfo.

       Daga Hajiya iya har Baba Rahi turus sukayi suna kallonsa suma fuskokinsu ɗauke da mamaki musamman Baba Rahi da sam bataga shigowarsaba duk da tana kitchen tana wanke-wanke. Sai dai tabbas taji baƙon ƙamshin turare datai tunanin ko cikin samarin gidanne suka fara shigowa yin breakfast.

         Fuska hajiya iya ta haɗe da kamo hannun Zinneerah dake nunashi har yanzun ta riƙe, ta sake kwantar da ita a jikinta tana shafa mata baya da sauke ajiyar zuciya. “Kinga Zinneerah kwantar da hankalinki ba aljani bane mutumne”.

     “Wlhy ba mutum bane Granny, aljanine, dan aljanine kawai zai iya buɗe ɗakin dana rufe kuma na cire key ɗin kingansa acan na ajiye……”

       “Shiii, ya isa kiyi shiru, Yayankune ba aljaniba, yanada key a hannunsa shiyyasa ya shigo”.

       Kafin Zinneerah ta samu damar cewa wani abu Baffah ya shigo ɗakin saboda jiyo muryar Zinneerah ɗin dake magana tana kuka, sai kuma ya jiyo hajiya Iya itama.

      “Lafiya kuw….” ya kasa ƙarasawa saboda sauka da idanunsa sukayi akansa shima. A take fara’ar fuskar Baffah ta ɓace ɓat. Saurin duƙawa Baba Rahi tai tana gaishesa. Bai iya amsa mataba sai hannu kawai ya ɗaga mata. hakanne ya sakata tashi da ta fice a ɗakin.

           Hijjabin Zinneerah na salla hajiya iya ta jawo ta saka mata, batare da tace komaiba ta kama hannunta suka fice daga ɗakin. Bayansu Baffah yabi shima batare da yace uffanba.

        Kansa dake a duƙe tun haɗa ido da sukai da baffa ya ɗago a hankali yabisu da kallo har suka fice gaba ɗaya. Sake lumahe idanun yay da furzar da huci mai ƙarfi tare da kai hannunsa ya dafe kansa. 

      

        Tsaye cirko-cirko suka iske yaran gidan da suka fara shigowa sashen. Dan har sunji labarin zuwan Yayan nasu gidan a bakin Yaya Khalipha da sukazo tare.

      Wucesu Hajiya Iya tayi riƙe da hannun Zinneerah dake sharar hawaye ɗakinta. Baffah kuma ya nifi dining shima fuska a ɗaure.

     Baffa mutum ne mai barkwanci ga yaransa, amma idan ransa ya ɓaci dolene kowa ya shiga hankalinsa. Da sauri Safiyya ta taso inda yake ta fara ƙoƙarin haɗa masa abincin gabansa. Hakan yasa suma sauran yaran nufo dining ɗin duk suka zauna. Hajiya Iya ce ta fito daga ɗakinta tana ƙwalama Jamal kira. Dai-dai yana ƙoƙarin zama danshi shigowarsa ma kenan sashen baisan mike faruwa ba.

      “Na’am Granny ”. 

Ya amsa yana maida kujerar daya jawo tare da juyawa gareta. 

     “Ka shiga ɗakin can ka ɗakkoma Zinneerah Uniform ɗinta da jikkarta”.

      Cikin rashin damuwa da abinda tace ɗin, yace, “Okay maa”. 

     Yanda ya nufi ɗakin kansa tsayene ya saka sauran ƴan uwansa binsa da kallo. Bahijja ta saka hannun ta rufe bakinta jin dariya na neman kufce mata. Meenal kam ƙasa tai ƙarƙashin tebir tamkar zata gyara wani abu tayi tata.

       “Oh ni Jamal ni za’a saka na ɗakkoma ƙanwata abu. yau yarinyarnan zatasha ƙwanƙwashe a kai kuwa a class na rantse”. Yay maganar yana tura ƙofar ɗakin da shiga kansa tsaye. 

     Wani wawan birki yaja yana waro idanu waje ganin wanda baiyi zatoba tsaye yana ƙoƙarin zame rigar saman suit ɗinsa. Cikin rawar baki yace, “Bar… Ba.. Barka da zuwa Yayanmu. Kazo lafiya? An barosu lafiya? Ya hanya?”.

     Yanda ya jero gaisuwar kawai zaka fahimci a kiɗime yake. Shiko da ake gaidawar kallo ɗaya yay masa ya janye idanunsa batare daya amsa ko ɗayaba a ciki, dan gaba ɗaya ransa a dagule yake. Yasan shiɗin mai laifine ga mahaifinsa da kakarsa. Amma yayi zaton Baffa ya yafe masa kamar yanda ya roƙesa tun a waya kafin ya taho….

     Da sauri Jamal ya juya zai fice a ɗakin….

          “Mi kake buƙata?”.

   Nutsatstsiyar muryarsa mai kama data rowa ta bayyana cikin kunnuwan Jamal. Tamkar zai fasa kuka ya juyo garesa. “Yayanmu Granny tace nazo na ɗaukama Zinneerah Uniform ɗinta zamu wuce school”.

      Uffan baice da shi ba, sai ma towel daya ɗauka a akwatin da yazo dashi ya nufi toilet abinsa. Jamal na ganin ya shige ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da nufar Uniform ɗin Zinneerah dake ajiye a bakin gado ya ɗauka sauri-sauri tare da schoolbag ɗinta da takalma ya fita da gudu.

        Shikam koda ya shiga toilet ɗin kallon tsaf ya shiga masa, dan a rayuwa ya tsani ƙazanta. Jin ƙamshin toilet ɗin gaba ɗaya ya canja daga nashi ya sakashi cije baki a ransa yana raya hukunci da zaima yarinyar nan da har idonta yay tsaurin shigo masa ɗaki tai wanka. Gamsuwa da tsaftar bayin ya sakashi ƙoƙarin ajiye towel ɗin hannunsa a bazata idonsa ya sauka akan B&P ɗin Zinneerah data shanya. Kauda ido yay yana wani cizar baki da rinmtse idanu da ƙarfi, a fusace ya rataye towel ɗin ya fito yana ƙwala kiran sunan Jamal. 

       Wayam babu Jamal a ɗakin alamar ya gudu, ya riƙe ƙugunsa da hannaye duka biyu idanunsa na canja launi saboda haushi. Ƙofa ya nufa kamar zai fita sai kuma ya fasa ya dawo da baya yanayin ƙwafa. Haka ya haƙura ya gudanar da dukan uzirinsa, sai dai sau goma idonsa yakai ga kayan sai sun sami tsarabar harara talatin da tsaki. Sai wani faman yamutsa fuska yake tamkar yau ya fara ganin irinsu.

     Oho ita mai kayanma batasan yanayiba. Dan tanacan tayi shirin makaranta bisa umarnin Hajiya iya. Sai dai ranta cike yake da ruɗani. a kuma matuƙar kiɗime take da ganin wannan fuskar. Tasata gaba Hajiya Iya tai suka fito dining domin karyawa. Baffa ta fara gaidawa sannan su Haneef dasu Ni’ima. Ta bama Meenal da bahijja hannu sukai musabaha sannan ta zauna.

     Hajiya iya kam da suka fito tare abinci ta fara shiryawa. wanda kowa yasan na yayan nasune, shiyyasa duk suke addu’a a ransu kar mutum yazam shi za’a aika yakai masa.

    Ganin Hajiya iya ta zauna bayan tagama yasa kowa ke ƙoƙarin ganin ya gama ya fita, Jamal ne ya fara miƙewa yana kallonsu Zinneerah. Guys kutashi muje kunsan yau Sir Mansur ne damu a period ɗin farko”.

      Daga Meenal har Bahijja sun ramfo saurin nasa. Dan haka suka miƙe da hanzarinsu suna faɗin, “Hakanefa ka tuna mana”.

      Miƙewa Baffah yayi yana goge bakinsa da tissue. Ya ɗan kallesu ya kauda kansa. “Kumuje sai mu saukeku dan zan shiga makarantar taku ne”.

      Sosai daɗi ya kamasu. Duk suka washe bakuna suna kashema juna ido najin daɗi yau tare da Baffahnsu zasuje school. Duk da dama yakan musu haka lokaci zuwa lokaci dan kawai ya sakasu farin ciki.

       Zinneerah dai duk jikinta a sanyaye yake har yanzu. Babu abinda ke mata gizo a zuciya sai ƙyaƙyƙyawar fuskarsa mai cike da kwarjini da kamalar cikar haiba. Sallama sukaima Hajiya iya sukai waje suna ɗagama sauran yayyensu hannu.

             Cikin raɗa-raɗa Saifudden yake cema Moos’ab mumafa mu tashi mu fece dan yau gidanan akwai ƙura tsakanin Granny da Yayanmu. Wannan faɗan kuwa yafi ƙarfin ganinmu koda ta bayan katanga ne”.

    Miƙewar kuwa duk sukayi sunama Hajiya Iya dake kicin-kicin da rai sallama. A dai-dai wannan lokacin Khalipha ya shigo falon da sallama. Kansa ƴammatan sukai cike da ihun murna ƙasa-ƙasa dan gudun kar Yayansu yajiyosu. Fuskarsa washe da murmushi kuwa ya buɗe musu hannayensa. Sai dai harar da Hajiya iya ta balla masa ce ta sakashi maida hannun ya naɗe a ƙirjinsa yana dariya. Duk da haka sai da sukaje suka ɗan fabu da jikinsa suna jera masa kalaman kewarsa da sukayi. 

     Gudun samun matsala yasa sukai masa sallama suka fice su dukansu. Shi kuma ya ƙarasa ga Hajiya iya. Ɗan rungumeta yayi ta gefe yana faɗin, “Oh my sweetheart, i miss you so much”.

       “Oh ai nazata kaima ka koyo halin turawanne ka fara ƙyama da gudun danginka”.

       “Kai! Granny ni na isa. Babu wani ɗaukaka da ALLAH zai mana a duniya mu kyamaceku ai. Dan kune kuka nunamu ga duniyar harta san da zamanmu”.

     Cikin taɓe baki tace, “Kai kasan wannan ai. Banda wasu bauɗaɗɗu masu bahaguwar rayuwa”. Ta ƙare maganar da harar gefenta tana ƙara ɗaure fuska.

      Juyawa Khalipha yay da sauri saboda jin ƙamshinsa, ya kuma tabbatar da shi Hajiya iya ke wannan zancen. Ilai kuwa shine ke takowa inda suke, kuma komai da Hajiya Iyan ta faɗa ya shiga cikin kunnuwansa. Amma yay tamkar bai jiba sai ma kujerar daya ja ta dining ɗin ya zauna.

     Murmushi Khalipha yay yana dubansa. “Barka da fitowa Yayanmu. Yanzu nake batun zuwa na fiddoka kayi breakfast dan nasan kana jin yunwa sosai”.

       Wani ɗan murmushi yayma Khalipha ɗin yana lumshe idanunsa masu yalwar gashi da cikar gira. Khalipha yasan halin kayansa. Dan haka cike da rashin damuwa yace, “Mi za’a haɗa maka?”.

     Kafin ya bashi amsa Hajiya iya ta amshe da faɗin, “Ni ban girka abincina da shi ba. Sai yayi waya su ƴan can London ɗin ko Morocco su kawo masa yaci”.

       Ƙaramar dariya Khalipha yayi da kai hannu ya fara buɗe kwanikan dake shirye akan tray wanda ya tabbatar nasu ne. Shiko gogan hannayensa kawai ya harɗe a ƙirji yana kafe Hajiya iya da kallo.

      “Bar kallona malam karka cinyeni da waɗanan shu’uman idanun naka  lokacin mutuwata baiyiba”.

       A karo na biyu ya sake sakin lallausan murmushi yana kauda kansa gefe. Cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Bazata canjaba kullum”.

      “Anƙi canjawar dan ubanka”. Hajiya iya ta faɗa tana zabga masa harara da masa daƙuwa.

     Bakinsa yaɗan taɓe da ɗaukar wayarsa ya hau latsawa kamar bashine ya takalo rigimarba. Khalipha dai abinci yake haɗa masa yana dariya, dan inhar Yayansu na gidan nan irin wannan rigimar shi da kakar tasu ba sabon abu bane. Sai suyi sau goma a rana su shirya. Hakan kuma bazai hana gobe su ɗora daga inda suka tsayaba.

     Masifa Hajiya Iya ta cigaba dayi, inda take shiga ba nan take fitaba. Shi dai yay mata shiru yanata cin abincinsa hankali kwance. Danshi mutum ne da baya wasa da abinci. Cinsa yake bil haƙƙi da gaskiya a duk lokacin daya samesa. Musamman daya kasance mutum mai tsananin son abincin Nigeria ma.

       Hajiya iya dai batai shiruba sai da tayi mai isarta sanann ta mike tabar wajen. Dan Khalipha ne keta faman bata haƙuri, shiko yayi kamar babu shi a wajen sai cin abinsa yakeyi.  

    Bayanta yabi da kallo harta shige. Ya maido idonsa kan Khalipha, “Besty matarnan bazata taɓa canjawaba da wannan faɗan nata?”.

        Dariya Khalipha yake sosai. “Yayanmu kaimafa mai laifine, bai kamata kai mata shiruba, amma ka barni da bada haƙuri”.

      “Bazaka gane bane, itafa idan kana bata haƙuri kamar tunzurata kakeyi. Bakinta ko gajiya bayayi”.

       “Munafiki, ai inajinka”. Suka jiyo muryar Hajiya Iya da basuji fitowartaba a bayansu.

      Dariyace taso kufce masa. Dan haka ya miƙe da sauri yana goge bakinsa da tissue yabar falon gaba ɗaya. Da alama gaida matan gidan zaijeyi.

          Harya gama ficewa bai daina jiyo masifar Hajiya iya da dariyar Khalipha ba. Ya ɗan dafe kansa yana furzar da huci da faɗin, “Madam Problem”…………✍

       *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘

_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖

_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝

_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓

_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔

_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za’a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

      

       

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like