MAKAUNIYAR KADDARA 29

Advertisement

 *_TYPING📲_*

*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*

*Page 29*

Advertisements

_________________________

*MG’s SKIN CARE*

(With us, your skin is elegant..)

Are you guys  looking for where to buy ur skincare product @ mg’s skincare is the best plug for you🤗

Do you wish to have that flawless skin that’s free of all skin prblm 

Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉

Try mg’s product nd I assure you you’ll never use any other product except mg’s product✅

Mg’s will gv you the best out of all 

With mg’s product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃

Advertisements

We have herbal whitening black soap now nd beauty set available

Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗

Just gv it a try now nd see wonders✅

Chat:08062991549

Call:08064532391

Soap price:3k

set:11k

Follow us on 

Instagram@glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

Nd guess wht🦻

Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis  30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is  the time to glow🧖‍♀️

Pamper ur skin🦵

Shine like a bride 👰

be part of the glow team karkubari abaku lbr

Just chat 08062991549 to plc ur orders😘

Do not forget to follow us👆

Like nd comment pls dearies😘

Patronize us🙏

mg’s always serve you the best✅❤️

KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU, INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE.

_________________________

*Page 29*

………….Meenal da ke ƙarshensu ce ALLAH ya bata ikon hango Yah Khalipha. Cike da jin daɗi da zumuɗi tace, “Guys ga Yah Khalipha can”.

     Kusan duk a tare suka kalli inda ta nuna ɗin, hakan yayi dai-dai da ɗagowar Khalipha ɗin kuwa shima idanunsa suka hango masa su. A tare suka nufi juna cike da zumuɗi da farin ciki. Jamal ya shige jikinsa suma su Bahijja haka. Hannu ya miƙama Zinneerah alamar tazo itama sai ta noƙe kafaɗa tana murmushi. Sosai hakan da tai yay bala’in birgesa. Ya saki ƙannensa yana nufowa inda take fuska ɗauke da murmushi.

      “Uhm Gimbiyar mata ke ta dabance fa”.

     A bazata kalmar tazoma Zinneerah daga bakin nasa. Kamar yanda shima tazo masa a suɓutar baki. Ta ɗago manyan idanunta cikin nasa tana wani warosu irin alamar dai mamaki. Kansa ya girgiza mata shima yana waro nasa idanun dariyarsa na ƙara faɗaɗa. Babu shiri Zinneerah tai dariya da saka tafin hannunta ta rufe fuskarta dan taji kunya kuma.

        Su Jamal dake musu dariya suma suka shiga gaishesa. Da kulawa ya amsa musu har ita Zinneerah data samu ta gaishesa a ƙarshe. Daga haka suka nufi taxi suka shiga yana faɗin, “Kuyi haƙuri fa nan kunsan ajiye mota ga talaka sai yayi nishi, motar gidan Yayanmu ya fita wajen aiki da ita”.

          Cikin rashin damuwa da wannan suka shiga dariyar maganarsa. Sai ma suka koma tambayarsa Hajiya iya. A take ya fara basu labarin tana nan suna zuba tsiya da Aunty Farah. Yana basu labarin rikicin da akeyi a gidan suna kwasar dariya. Sai dai ko sau ɗaya Zinneerah bata saka baki a hirar tasuba. Murmushi kawai takeyi tana dai saurarensu da kallon hanya, zuciyarta na yaba ƙyawun ƙasar burtaniya da tsarinta. Tare da godiya ga UBANGIJI da ya bata damar ƙetare ƙasarta zuwa wata ƙasa batare da ko a mafarkinta hakan ya taɓa zuwa mata a cikin ranta ba.

        Sai da suka iso inda ya dace ta kawo numfashi, waje ne daya samu tsararrun gine-gine da burgewa ga mai kallo. Babu wani hayaniya a wajen dan saima ka ɗauka ba gidaje baneba wata ma’aikatace. Su kansu sai bayan shigarsu ainahin cikin estate ɗin suka fahimci nannefa inda gidan Yayan nasu yake kenan. Sun haɗu da mutane ɗai-ɗai dake kai kawo, kamar masu fita da masu shigowa. Duk da kasancewar ginin estate ɗin a dunƙule yake waje ɗaya idan ka shiga baka da alaƙa dana kowanne, abinda kawai zakai nufar hanyar da zata kaika ainahin number naka building ɗin. Abinda kuma zai birgeka a rayuwar wajen babu ruwan wani da wani. Iyakarka da kowa hello hii idan an gamu.

        Zinneerah daketa tunani a ranta taketa ayyana dolene turawannan su dinga ganinmu a banza. Dan duk wani jin daɗin duniya tamkar an tattarashine garesu. Basusan wani tashin hankalin rayuwaba sukam sam. A African kashe-kashen nan kawai ya ishi bawa da yunwa. Mu baga neman lahirarba duniyar da mukeso kuma kullum cikin wahal damu take. Gamu nan dai babu fasali ko wasu abubuwan birgewa duk mun fita a hayyacinmu…..

    Nannauyan numfashi ta sauke saboda taɓatan da Bahijja tayi, “Haba Baby ina kika tafi haka ne?”.

     Ɗan murmushi Zinneerah tayi da duƙar da kanta saboda kallon da Khalipha ya kafeta da shi. A hankali tajawo trolly ɗinta ta fito a cikin taxi ɗin tana gyara bag ɗinta. Jamal sarkin tsokana yace, “Ashe ni ƙauyancina ma kaɗanne ga wadda ta fini”.

     Harara ta zuba masa da kai masa duka ya goce yana dariya. Khalipha ya girgiza kansa yana nufar ƙofar da zata sadasu da gidan na yayansu yana faɗin, “Uhm kudai tuna a ina kuke yanzun, kokuma ku koma Nigeria ba’a yanda kuka zo Burtaniya ba”.

        Dukansu sun fahimci inda zancen nasa ya dosa. Dan haka duk sukai ƙaramar dariya kowa na faɗin albarkacin bakinsa. 

         Tunda suka shigo man kan kowa ya tsiyaye tas suka koma santin zuciya, sunaji a ransu dolene Aunty Farah da take hura musu hanci ashe tasan abinda ta taka. A ɗan corridor ɗin kafin ka shiga ainahin falon duk suka cire takalmansu suka saka cikin drawer dake a wajen alamar ba’a buƙatar ganinsu a waje. Sabbin Slippers na zaman gida Khalipha ya ciro daga cikin drawer ɗin ya miƙa musu. Kowa cira yay ya saka sannan suka shigo ainahin falon daya tsaru harya gaji. Sai ka rantse ma ba’a amfani dashi tsabar yanda yake fes. Tozali da Hajiya iya dake hakimce zaune ta ƙara ƙyau ya mantar dasu a ina suke da kuma santin. Tuni suka yadda bags suka nufeda da gudu cike da ihun farin ciki duk suka ɗaneta.

    Itama dai cike da farin cikin ta tarbesu tana dariya dajin ƙaunar ƴan jikokin nata da kewarsu. 

        Cikin ɓacin rai Farah ta fito daga wani lungu danjin hayaniya na neman halaka mata kunnuwa, sanye take cikin wando dogo da riga da sukai mata ƙyau ainun, taku take cike da isa da ƙasaita fuska a yatsine. Taja ta tsaya turus tana dubansu alamar batama san da zuwansuba, dan sosai mamakin ganin nasu ke bayyana mata kan fuska ƙuru-ƙuru. Gashi kuma babu damar magana saboda hajiya iya. Sai dai wani kallon tsantsar takaici takema Khalipha da shima kai tsaye ita ɗin yake duba. 

     Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta janye idanunta daga kansa ta maida kansu Meenal da sai a yanzu nasu idanun suka ganta. Duk da sunsan halinta na wulaƙanci sai sukai ƙoƙarin nuna murnar ganinta suna gaisheta cike da girmamawa kodan darajar wanda ya ajiyeta a gidan. A yatsine ta amsa musu ɓacin ranta na kasa ɓoyuwa, ta kafe Zinneerah da ko kallon inda take bataiba balle gaisheta da ido.

       Zinneerah da batasan tanaiba gaba ɗayama hankalinta nakan Hajiya iya batasan da zuwanta wajenba. Lura da kallon da Farah kema Zinneerah ɗinne yasa Khalipha kiran sunanta.

    Ta juyo fuskarta ɗauke da murmushin da takema Hajiya iya ta dubesa. batare da yayi maganaba ya nuna mata Farah. 

     Da iya gaskiyarta tace, “Ayyah Aunty kiyi haƙuri bansan kin fito bane. Mun sameku lafiya? Yaya jikin Granny”.

      (Buhun bura uban nan kayyasa) Farah ta ambata a zuciyarta tana kafe Zinneerah da wani shegen kallo, dan babu abinda ta hango a zancenta sai tsantsar rainin wayo a gareta. Batare data amsama Zinneerah ɗimba tabar wajen cike da takunta na ƙasaita da izza kai kace wata sarauniya ce.

     Gaba ɗayansu da kallo suka bita. Hajiya iya ta girgiza kanta kawai tana mai nema mata shiriyar UBANGIJI a ranta. Yayinda su Jamal duk jikinsu yayi sanyi. Zinneerah kam ko’a jikinta, dan itako a masu mugun hali taga waɗanda suka taka Farah suka shanye mizaisa na Farah ya dameta. A bazata dariya ta siɓicema Khalipha ya kauda kansa gefe yanayi. Dan haka kawai ta bashi dariyar. Ita dake takaicin zamansa shi kaɗai ga wasu huɗun nan an kuma kwaso mata bayan Hajiya Iya. Sai dai kuma shi duk zatonsa tasan da zuwan nasune tun farko, amma a yanda tayi yanzu kam ya tabbatar Yayansu ya ɓallo ruwa yau.

       Hajiya iya ce tai masa daƙƙuwa, ya ɗauke kansa yana haɗiye dariyar badan yaso ba. Itama maida hankalinta ta sakeyi gasu Bahijja dake gaisheta da tambayar lafiyarta, itama tana tambayarsu mutanen gida da hanya.  

       Sai da Khalipha yace, “Ashe ƙaryar gajiya kukeyi daman”.

        “Yah Khalipha ganin Granny yasa gajiyarma ta gudu ALLAH”. Bahijja ta faɗa tana dariya. Murmushi yayi da kallon Granny dake magana da Zinneerah fuskarta a washe itama alamar tana cikin farin ciki yau fiye da kullum, sai yaji daɗi a ransa. Koba komai sa huta da mitarta na a maidata gida ita ta gaji da zaman kurkuku.

      “Assalamu alaikum”.

   Suka tsinkayi muryar Yayansu dake ƙoƙarin shigowa a bazata. A take duk sukai tsit da maida dubansu ga ƙofar. Khalipha ya miƙe ya nufesa ganinsa ɗauke da ledoji a hannu. Suma ɗin duk tsaye suka miƙe domin bashi girmamawa. Ledojin ya miƙama Khaliphan yana faɗin, “Thanks besty” ba tare dasu sunji miya faɗa ɗinba. Sai motsawar laɓɓansa kawai suka hanga. 

      Cikin haɗa baki sukace “Barka da dawowa yayanmu;

      Sai yanzune ya kallesu fuskarsa da ɗan sakewa amma ba murmushi yakeba. Ya zame rigar sanyin saman suit ɗinsa yana hanging ɗinta a hanger ɗin dake gefensa, sannan ya ƙaraso cikin falon. Gaba ɗayansu gani sukai ya ƙara musu ƙyau da cikar haiba a idanu, kamar yanda Hajiya Iya da Yah Khalipha suka ƙara musu. Sai da yakai zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan yay magana.

    “Kun iso kenan?”.

     Nanma a tare sukace, “Eh Yayanmu”. 

       Batare daya kalli kowansuba ya jinjina kansa yana musu nuni dasu zauna. Babu musu suka zauna suna gaisheshi da tambayar jikin Granny.

       “Ta warke ai, tunda gashi tana mana boren sai kunzo”.

      Duk da ba cikin raha yay maganarba sai da sukai ƴan ƙananun dariya suna gumtse bakuna. banda Zinneerah da tun shigowarsa kanta ke a ƙasa murmushi yanzunma kawai tayi.

    Granny dake hararsa tace, “Ai ni ba irin wasu bane da basa son mutane. Na saba jina cikin hayaniya da karaɗin ƴan jikokina ina jin daɗi”.

     Karan farko ya saki lallausan murmushi yana miƙewa da ɗan taɓe baki, duban Khalipha daya kai ledojin abincin kitchen ya dawo yayi. “Besty ina zuwa”. Ya faɗa yana nufar hanyar da Farah ta fito ɗazun. 

       “A fito lafiya Yayanmu” Khalipha ya faɗa yana wata shaƙiyyar dariyar tsokana ƙasa-ƙasa da kaiwa zaune. Hajiya Iya data fahimci mi yakema dariyar tace, “Halan zargina ya zama gaskiya akan ƴar tutsun tasa? Tunda yanzu dai ba lokacin dawowarsa gida bane ba”.

        “Ai da alama itace tai kiransa a waya ko kuma ta kira Mammah ita kuma ta kirashi, dan a yanda ta nuna mamakin ganin su Jamal na tabbata bai sanar mata zuwan nasuba. Kinsan wannan jikan naki shine dai-dai dasu ai, ya manna musu rashin m ya noƙe da barinsu suyita masifa”. Khalipha ya bata amsa magana ƙasa-ƙasa kamar wani munafiki yana ɗan dariyar ƙeta.

       Dariya Hajiya iya tayi itama, “Kaɗanma ta gani indai nice Amina, ita Hindatun idan ta isa tazo gidan mana ta sameni ja’ira kawai. Nima nan saina saitasu a layi da ƙyau ai kafin nabar wannan garin da ba daɗin zamane da shiba”.

      Sudai su Zinneerah da ba sanin ina zancen ya dosaba saurarensu kawai sukeyi, ita babban burintama azo a basu masauki ta kwanta dan kanta ciwo yake mata.

       Shiko Khalipha dariyarsa ya cigaba da sha dan show ɗin na Granny na birgesa. Sosai a zaman nan nata take ƙara cusama Yayansu son ƴan uwansa a ransa da sanin muhimmancin su da girman zuminci. Shiko da alama yana haddace karatunta tsaf kuma yana aiki dashi. Dan rana ɗaya babu zato ya sanar masa ya kira cikinsu Haneef akan tahowarsu Meenal nan ɗin. Bashi ba hatta Granny tayi mamaki dan duk tsogumin da take masa nason zuwan su Zinneerah ɗin batai zaton zai saka suzo ɗinba. Aiko ranar yasha addu’a a wajenta da albarka.

    To yanzu dai gasu sunzo, shi dai yasan akwai ƙura akan wannan zuwa nasu gidan, musamman daya kasance uwargida gimbiya Farah batasan da maganar zuwan ba, amma bara su zuba ido suga yanda wasan zai kasance dai, tunda shima yayan nasu ba kanwar lasa baneba………….✍

       

*_Masha ALLAH Guys, ina fatan asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._*

*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘

_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖

_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝

_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓

_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔

_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za’a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

          

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like