Advertisement
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 74
…………“Dabarata ta jingina ciki ga Nu’aymah, da kawo hotonta ita da Yoohan shine burina Sooraj yay fushi yace sai Yoohan ya auri Nu’aymah. Ta hakanne kawai aurenta da Abdallah ko Naseer zai gagara. Duk da bana zargin Nasir da komai, amma inhar shi Nu’aymah zata aura tsugunne bata ƙareba kenan. Amma indai ta auri Yoohan inada yaƙinin zai bata kariya. Saboda alwashinsa na ranar da aka kirashi akan wannan batun ya birgeni. Ko bayan babu raina ina fatan ya zama garkuwa ga ahalin Firdausi. Sannan Nu’aymah ma zata samu lafiya ta dalilinsa tunda shine likitan da dama aka basu Number sa muka sace ni da Lurwan. Alhmdllh naci nasara, dan kuwa da bakinsa ya furta son auren Nu’aymah, duk da Sooraj bai bashi goyon bayaba a lokacin saboda jin nauyin ƴan uwansa akan su Abdallah na tabbatar yanason bashi. Lurwan ya shiga ruɗanin ganin zai rasa dama ta biyu, hakan ne ya sakashi sake dawowa gareni mu haɗa kai a wannan karonma. Ya kuma bani haƙuri da tabbacin zaisa Abdallah ya maida aurensa da Adawiya da zarar anyi aurensa da Nu’aymah. Na nuna masa na amince dan na samu a gama maganar auren Nu’aymah da Yahya cikin kwanciyar hankali. Daga haka na cigaba da gayama ALLAH dan agareshi kawai nake hangen samuwar nasarar kubutar da Nu’aymah daga tarkon Lurwan. Hidimar aurar da ƴaƴa ka
Advertisements
GIPHY App Key not set. Please check settings