Advertisement
*JH0023* Dafe kansa yayi a fili yace “oh God ciwon kai Meenah naji tashi muje kiji fah ni bama abinda kike tunani bane” daqyar ya samu ya lallabata suka shiga ciki ta qofar baya suka shiga quarters din Yana riqe da hannunta suka shiga ciki ya rufe qofar ya saki hannunta ta fada kujera ta kwanta yayi murmushi yace “Meenah kishinki yayi yawa bansan meye kike kishin ba kullum cikin tuhumata kike meye yasa kike zargina ne?” Lumshe idonta tayi taba banza ajiyarsa yasan tunda tayi haka bazai samu arziqin mgn ba dole ya haye sama ya cire kayansa ya watsa ruwa ya dawo ya dauketa cak suka haura saman har yanzu a sama take dashi bata bashi fuska ba Ganin hakan yasashi shima ya qyaleta da asuba kuwa Yana shafawa yaji Babu ita ya bude idonsa yaganta saman sallaya ya miqe yayi miqa yayo alwala yazo ya tada sallah.
Kitchen ta shiga ta dora tea yanzun bata jure yunwa jikinta har rawa yakeyi ta dafa Indomie ta fito.
Jerawa tayi a dinning ta zauna tanacin Indomien ya sauko sanye da doguwar riga bata dagoba balle yasaran zata kallesa yaji babu dadi sosai hakanan ya zauna ya zubanta ido sun hada ido yakai sau biyar sannan tace masa morning” zuciya yaja yace “kin tashi lfy” bata bashi Amsa ba ta hada tea dinta ta fara Sha ta miqe zatabar gurin ya riqota ta juyo ta zuba masa manyan idanunta baisan sanda ya saketa ba tabar gurin.
Duk jikinsa yayi sanyi baison ganinta cikin damuwa miqewa yayi yabi bayanta tana tsaye a tsakiyar dakin sai kaiwa da kawowa takeyi ya jingina jikin qofar ya kira sunanta ta tsaya Amma bata juyo ba takowa yayi ya tsaya a bayanta suna kallon juna ta madubi ya shafa gemunsa ya nemi guri ya zauna yace “bawai fushinki ne yake damuna ba not akan abinda kike fushin shine yake damuna nifa ba abin da kike tunani ne yasa…..” Dagansa hannu tayi tace “na tsani qarya a rayuwata wlh bazan iya hanaka ba domin bani na dora maka ba kaine ka dorawa kanka kawai abinda nakeso ka fitarni a lissafinka ka qyaleni nayi rayuwata kayi taka.
Da sauri ya dubeta kamar zaiyi mgn sai Kuma ya miqe yace “ok” daga haka wata kalma bata kuma shiga tsakaninsu ba har ya gama shirinsa ta hada masa kayansa ya dauki jakarsa yace “zan tafi” batare da wani basa muhimmaci ba tace “Allah ya tsare ya taimaka” kudi ya zaro ya aje mata ya juya Yana tafe Yana cewa banida isassun kudi a hannuna ki riqe wadannan ba dadewa zanyi ba kafin bikin su Ya’isha zan dawo” Yana fadin haka ya fice da sauri saboda karyar masa da zuciya take neman yi itama jikinta yayi sanyi sosai tabisa da kallo tana hangensa har ya fice daga quarters din ta zauna tana saqawa da warwarewa can dai taga bazai kaita ba ta shiga daki ta kwanta.
Advertisements
Kasancewar ita kadai ce bata tashi a bacci ba sai yamma tayi wanka ta tafasa taliyarta da bushasshen kifi taci ta kora da lemo ta miqe ta lalubo wayarta zaro ido tayi 7 missed nasa tana Shirin kiransa ya sake Kira ta Kara a kunnenta yace “kina bacci ko?” Murmushi tayi tace “eh na tashi naga missed naka Ina fatan ka sauka lfy” Amsa mata yayi sukayi shiru na dogon lkc can yace “fushinki gareni Yana azabtar dani Meenah kiyi hqr don Allah” a kasalance tace “yafa wucce Baffa’am kawai dai Raina baya dadi ne idan na tuna kana raba Mana Abu mafi daraja da wasu wadanda basu cancanta ba.
Yaji dadi sosai sukaci gaba da hirarsu har zuwa wani lkc sannan sukayi sallama cike da kewar juna tana kashe wayar wayar Amrah ta shigo ta daga shigo ta dauka daga yanayin yanda suke gaisawar tasan da wani saqo a zuciyarta Amma ta maze taja numfashi tace “burinki ya cika hankalinki ya kwanta kin yaudareshi kin Sanya masa ciwon zuciya kawai saboda wani quduri naki Meenah Ya Kareem bai cancanci wannan sakayyar daga gareki ba yasoki lkcn da bakisan komai ba shine yanzu dan kin zama komai kika gujeshi……”
Dakatar da ita tayi da cewa “kina mgn da yaen da bana ganewa Amrah meye ma laifina ne cikin zarginki nima kamar yanda kowa yaji sama taka hakanan naji bansan wani abu bayan abinda kuka sani ba nidai na wayi gari naganni matsayin matar Baffa’am dina Kuma na yarda da abinda Allah ya tsara na karbeshi to meyece tawa a ciki?” Wata dariya Amrah tayi tace “bawai inayi miki mgn don kaina bane domin ni da eh dinki da aarki babu abinda zata qaramin Amma dai ki sani baki auri mijin daya dace dake ba domin kuwa ya rainanki hankali ne kawai saboda sha’awa ya aureki Kuma bazai taba canza hali saboda ke ba ke mufa a qarshe ma godiya mukayiwa Allah da Allah baisa mun dauko Kara da kiyashi ba maita ai bala’i ce a qarshe dai Ina Mai farin cikin sanar dake Ya Kareem zaiyi aure zai auri wacce tafiki asali nasaba da nagarta kinsan dama rayuwar duniya qwarya tabi qwarya akeyi”
Dukkannin kalaman Amrah babu Wanda ya daki zuciyar Juhud kamar Wanda tace Allah ne ya taimakesu Basu dauki Kara da kiyashi ba maita ai bala’i ce…..” Kashe wayar tayi cikin dimuwa tayi tagumi itadai tana ganin jarabawa Wai ya akayi ta zama mayya ne? Tana tsaka da tunanin nan Kiran Mom ya shigo ta daga a sanyaye cikin rawar murya tace “Mom…. Momy Ina yini” zuciya Mom taja tace “me Amrah tace miki?” Saita muryarta tayi cikin kuka tace “babu komai Mom” shiru Mom tayi sannan ta kashe wayarta ta miqe ta shige daki ta fada gado ta rushe da kuka yau ce Rana ta farko data fara jin shauqi da tunanin Ina zata Sami wani dazai zame mata abokin shawara dazai bata mafita cikin matsalarta maita? Maita?
Advertisements
Ta maimata yakai sau goma sannan ta iya miqewa ta shiga bathroom tayi wanka tayi magrib ta dauki qur’ani tana karantawa har akayi Isha tayi ta haye gado zazzabin dare ya aurenta ga kadaici hakanan tayita juyi da missing din Baffa’am dinta bacci ya fara daukarta taji wayarsa ta dauko ta gyara kwanciyarta ta Kara wayar a kunnenta tace “tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci zuciya biyu makusantan juna” numfashi ya sauke yace “Same to ur my Meenah meye ya hanaki bacci 11:40pm” kasa tayi da muryanta tace “kewa da tunanin mijina gami da missing lallausar fatarsa” dariya abin yabashi yace.
“Au haba dama kina jina a zuciyarki haka”
Murmushi tayi ta shafa saman kanta tace “komai na duniya hawa yake Yana sauka nikam sonka baitaba sauka a zuciyata ba Baffa’am tunda ya riga ya hauhawa don Allah ka riqemin amanar kanka kaji” qaramar ajiyar zuciya yayi yace “bakida matsala matata am dama mom ce tace tanason ki koma Daura a fara shirye shiryen biki dake Wai harda bikinmu zaa hada ayi” abinne ya bata dariya tace “biki Kuma Baffa’am nikam na yafe nawa su Bari su hada dana suna….” Duk da baa gabanta yakeba Saida ya zabura ya miqe yace “suna Meenah mun samu qaruwa be?” Jikinta ne yayi sanyi tace “hakane Baffa’am kwana hudu da lkcn period dina ya wucce……” Wani ihu ya saki Hadi da kabbara yace “wayyoh dadi Meenah shine baki fadamin ba na fara tanadi me zaki haifamin mace me kama dake ko?” Rufe idonta tayi tana share hawaye me hade da murmushi yace “amma kamar murnarki batakai ba my Meenah meye damuwar ne ko har yanzu fushinne?”
Girgiza kai tayi yace “talk me Mana” aa tace tare da cewa “bacci nakeji Baffa’am” da murnarsa yace “aikuwa zan fadawa Mom tabarki kada hayaniya ta damarmin ke ki huta kinji rayuwata” qit ya kashe wayar baa dauki 10 minutes ba saiga Kiran Mom tace mata “yayimin kwatancen gidanku gobe zanzo na daukoki gara ki dawo nan gidan ki zauna a bangarensa da zamanki anan Babu kowa bakisan kowa ba ga lalurar ciki Allah ya inganta ya rabaku lfy kinji me sunan yaya” a kunyace ta amsa suka Dan taba hira suka aje layin tana ajewa Kiran Ya’isha ya shigo tace mata “ke wlh banza ce daga zubar da wancan sai kika bude abu kika Kuma karbar wani nifa wlh banyi miki sha’awar haihuwa yanzu” shiru tayiwa Ya’isha jin hakan yasa ta gane yan iskan na kusa bazata kulata ba ta gimtse wayarta washegari kuwa 12:00pm a KD tayiwa mom da Muntaz tunda suka shigo yake binta da kallo yana hadiyar yawu a ransa yace “wow! Manyan kaya wannan guy chege ne yasan takan dadi dubi yanda wannan babyn take qara hauhawa abin kamar…..” Mom ce ta katse masa tunanin da cewa ai saika tashi ka Debi kayan mu tafi salmanu”
Zungi² ya miqe yabisu Mom na gaba Juhud na binta shikuma Yana qarewa halittar bayan Juhud kallo har suka isa mota ita da mom ne a baya shike driving har Daura suna tsayawa motar Mai Martaba tana tsayawa ya fito Mom ce tace da Juhud “kije ki gaisheshi” da faduwar gaba ta nufeshi ta rusuna ta kwashi gaisuwa Babu wata alama ta bacin rai ko damuwa ya Amsa mata tare da cewa “Meenah kawai saiji mukayi kinbi Wanda ya kawoki” da sauri tayi qasa da kanta saboda fitowar Kareem a part dinsa da yanda ya zubanta ido.
Tsayawa yayi cak Yana kallonta ta miqe tabi bayan Mom data nufi part din Rasheed tana cewa “wlh sakarcin Rasheed yawa gareshi Mai Martaba yabarta ita kadai a gda ga kadaici ga laulayi shine nace gara a dawo da ita nan kada dukan yayi mata yawa” tana tafe take mgnr suka gifta Kareem dake tsaye kamar dashe cikin sanyin yanayi tace “sannu Ya Kareem ya jikinka?” Wani yawu ya hadiye me daci ya juya yabar gurin gabadaya sai taji Babu dadi hakanan dai tabi Mom suka shiga abin mamaki bayine keta gyaran ɓarrayin fita mom tayi tace “bari na turo miki yan uwanki su tayaki shirya kayan”
Gdy tayi ta nufi ƙofar shiga dakin shima kamar falon an canza komai taja numfashi ta kulle qofar ta fada wanka ta fito daidai lkcn taji muryar Ya’isha ta bude mata suka rungume juna tace “wayyoh aure dadi gsky Big Cele Yana ban ruwa ke Kinga yanda kike wani glowing hajiyata fadamin meye sirrin 2 months kacal kamar kin shekara ana miki bayin ruwa” harararta tayi tace “kefa yar iskace meye Kuma bayin ruwa ana zamne qalau an fada miki Kuma kowa ma dan iskanne irinku ni zikiri kawai muke da karatun qur’ani da shaikh Baffa’am dina tunda ya saceni” dariya suka sheqe da ita Ya’isha tace “shegiya aifa dama Mana shiyasa naganki da sabon ciki ashe a ruwa ya baki kika kurba” gumtse dariya tayi tana cewa “hmmm yarinya kina wasa da mazan fama komansu na baiwa ne wato idan My Baff na bada darasi ji nakeyi kamar babu wani sauran gwani a duniya ke Bari fah kiji Allah Baffana akwai iya tsinko fure nakusa nayiwa kaina asar…..”
Shigowar jakadiya ne yasasu gimtsewa ta rusuna cikin ladabi tace “Allah ya taimakeki Mai Martaba ne yake kiran taron gaggawa a gidannan yace maza kizo kema tunda Allah ya dawo dake” Saida taji wata faduwar gaba ta dai dake tace “ok muna tafe” kallon Ya’isha tayi tace “meye ya janyo taron?” Miqewa Ya’isha tayi tace “akwai matsala ne kinsan fah Mai Martaba yasa Yaya Salman da Yaya Arman duk sun dawo da matansu gdannan wannan dalilin yasa Mom ta matsa kema ki dawo to tunda ya sauko ya amincewa dawowarki aketa tuka rigima da wadannan matan biyu Hajiya Bilki mahaifiyar su Aunty Zulaihat tana zugasu ita da Addah wai karsu yarda a kawo musu mayya tazo duk ta lashe musu kurwar yara a banza da mazan Basu daukar abinda muhimmaci Amma suma naga yanzu kamar maganganun sun fara tasiri ke harfa cewa sukayi wai kece kika lashe su Zulaihat da Ado driver saboda qudurinki na auren Big Cele”
Jikin Juhud Bari yakeyi dajin wannan sabon bala’in data fara karo dashi a wannan sabuwar rayuwa tata bata gama yanke abinyi ba Amrah ta shigo bakinta dauke da “la’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin” Saida ta tofa kusurwa hudu sannan tace “saqo daga Mai Martaba yace ku kadai ake jira” badon Juhud taso ba ta sanya hijjab dinta suka fito Ya’isha na qarfafa mata gwiwa suka Isa meeting hall din gdan kowa ya zubawa Juhud idanu harda Kareem ta sunkuyar da kanta tana neman gurin zama Mom ta riqo hannunta ta zaunar da ita kusa da Aliya matar ya Arman aikuwa tayi zunbur ta miqe tana qunquni itadai Juhud zama tayi Mai Martaba yayi gyaran murya ya fara bude taron da addu’a yace.
“Banso Kiran taro a daidai wannan lkcn ba so wata yar jumurda ce tasa dole na kiraku musamman akanki Aminatuh alal haqiqa a baya an zauna zaman gsky da rashin sani so yanzu abubuwa sun fasu Wanda mukayi qoqarin ganin mun kare zuri’a daga darsa zargi ko kokwanto Amma abin ya faskara wannan dalilin yasa na yanke shawarar kiranku nidai nasan iyakar zamanmu dake na shekara uku baki taba cutar da kowa ba duk da cewa akwai maganganun da naji suna yawo a bakin mata bamu daukesu seriously ba wannan tasa na Kira domin roqonki domin shi wannan abu a boye yake idan har da gaske hakanne mu bazamu qiki ba tunda mijinki yanasonki Amma kiyiwa Allah kici gaba da riqe kanki kada ki gwada Mana wannan mugum abu idan Kuma sharri ne to Allah ya saka miki sannan mgn ta qarshe banason qyara ko tsangwama a tsakanin ahlina wannan abu itama ba ita ta dorawa kanta ba gadar mata dashi akayi sannan alamu sun nuna batama da qarfi a jikinta Ina fatan kowa ya fahimta…..”
Tunda Mai Martaba ya fara mgnr ta rushe da wani kuka me gigita zuciyar me sauraro tana girgiza kai bakinta Yana rawa Mom ta riqota da sauri jikinta tana shafa bayanta cikin kuka tace “Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un Allahumma ajirni fih musibati wlh tallahi billahil lazi la’ilaha illahuwa niba mayya bace sharrine kawai ku yarda dani nikam meye nayiwa rayuwa ne me nayiwa su Baffa Ribado suke bina har gidan aurena da wannan mugum sharrin meyesa kakata ta mutu da baqin cikin sharrin maita Innatu ta harta mutu tana maimata min basuda wata alaqa da maita kyaune yaja musu da hassada ake kiransu mayu nima Kuma saita tsallako kaina wayyoh Allah Baffa wayyoh Innatu wayyoh mijina don Allah ka dawo ka fada musu niba mayyah bace…..”
*littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*
*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*
*_Oum Hairan_*
GIPHY App Key not set. Please check settings