Advertisement
*Page 41*
_________________________
*MG’S SKINCARE*
Hi my peole🙋♀️
Are you tired of using different skincare product that won’t work on ur skin no matter what❓then trust me @mg’s skincare is the right plug for you💯
Advertisements
Are you guys battling with pimples,dark spot, sunburn, acne, stretch mark,knuckle,dark armpit,damaged/bleached skin
Have you getting dark due to childbirth or sun exposure🥺worry no more@mg’s skincare gat you covered✅
Want ur skin to glow buh you don’t like using cream/lotion try *mg’s herbal whitening black soap* nd you’ll achieve that free/shiny skin🧚🏻♀️
For those that wanna achieve that milky flawless skin that turns head wherever you go🧚🏻♀️ try mg’s *beauty kit* that’s the secret to beautiful skin😎you’ll
get an amazing magic result😘 you can also buy the soap nd combine it with any of our product to get more result😀
Glow gang
What are you waiting for
Shop urs now before we get sold out again😍
Advertisements
Mg’s product is 1in town😃if you know you know kawai😜
Nd mg’s products are organic they dnt bleach they are made with natural ingredients that will make ur skin lk brighter nd tone ur skin😘 it just bring out
that hidden beauty in you😘we HV everything available now so is time to glow dearies
Pamper ur skin🧖♀️
Shine like a bride💯
Make ur skin brighter🤗
Glow🦵
Soap price:3k
Beauty kit:11k
Chat 08062991549
Call 08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
DNT forget to follow us😇like/comment😍
Team glow🤝
_________________________
*Page 41*
…………Tun farkon fara ƙulla auren da yaji sunansa a ciki yay mutuwar zaune, bai dawo hayyasa ba sai da sanƙira ya ƙara tabbatarwa da babbar murya. A
hankali AK ya lumshe idanunsa dake ɗauke da nauye-nauye kala-kala a cikinsu yana sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya.
Haɗa ido sukai da Baffah dake masa kallon nazari, kansa ya maida ƙasa yana ƙoƙarin danne ɓoyayyan al’amarin dake neman bayyana kansa a saman fuskarsa.
Shima Baffa sai kawai ya ɗauke kansa zuciyarsa na masa wasiwasi.
Koda aka mimmƙe domin fita a masallacin da ƙyar Saifudden ya iya kama Moos’ab da yay suman zaune, dan tun farkon fara ƙulla auren da yaji an ambaci
Yayan nasu sai da gabansa ya faɗi, jin zancen sanƙira kuwa tamkar saukar guduma ne a bisa tsakkiyar kansa. Gefe Saifudden ya maida shi tare bashi ruwa dan
yasha. Babu musu Moos’ab dake hawaye kamar wani mace ya amsa ya sha ruwan yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
“Wannan shine abinda na gudar maka tun farko Moos’ab, shiyyasa nace ka bayyanama Zinneerah kana sonta, ka kuma sanarma Baffah da Granny amma kaƙi wai
saita gama secondary school, gashi nan to shi Yayanmu yayi wuff da ita”.
Murmushi mai ciwo Moos’ab yayi, cikin raunin murya yace, “Saifudden ALLAH ya ƙaddara dama shine mijinta, kuma ni wlhy na haƙura na bar masa har abada.
Yayanmu yanada daraja da mutuncin da zamu iya sadaukar masa da komai, komai muhimmancin abinnan kuwa. Dan shima yayi mana abubuwa masu ɗunbin yawa da bazasu
ƙirguba. Sannan nasan Zinneerah zata samu dukan farin ciki daga garesa insha ALLAH. Kuma anyi maganin wannan mahaukaciyar matar tasa da kishi ya maida
zararriya, wlhy kodan kiran dataimin jiya da dare wai saina faɗa mata uwar little yasa naji daɗin ƙulla wannan auren, tunda tana kukan targaɗe ga karayanan
ta samu, sai tai zaman jinya kuma”.
Rungumesa Saifudden yayi yana share ƙwalla shima. Ya ɗagosa yana share masa hawaye da faɗin, “Naji daɗin kalamanka Moos’ab, hakan kuma ya tabbatar min
yaƙin da Granny da Baffa keyi akan sanin darajar zumincinmu ba abanza sukeyiba. Tabbas Yayanmu ya cancanci sadaukarwar da tafi haka ma, inaji a jikina kuma
maganar shekaran jiyace ta kawo wannan ƙulla auren, amma tabbas sun dace wlhy”.
“Tabbas na yarda da zancenka Saifu. Da alama hauka tai musu na haƙiƙa shiyyasa Yayanmu da Baffah suka yanke wannan hukuncin, na taya Yayanmu murnar
samun nutsatstsiyar yarinya mai kunya da tarbiyya ga haƙuri, sannan itama na tayata murnar samun gwarzon namiji mai haƙuri da mutunci, uwa uba ya tara
qualities masu yawa da duk mace take buƙata ga mijin aure, duk da nasan akwai ta inda shima yake da rauni kodan kasancewarsa ɗan adam kamar kowa. ALLAH ya
basu zaman lafiya, yasa ta zama sanadin farin cikinsa da kwaranyewar hawayensa akan rashin haihuwa”.
“Amin ya rabbi” Saifudden ya faɗa yana sake rungumesa.
A hankali AK dake a bayansu basu saniba ya ɗanja da baya yana lumshe idanu, tun sanda Saifudden ya kamo Moos’ab suka fito ya biyosu, dan ya jima yana
zargin akwai wani abu tsakanin Moos’ab da yarinyar, ashe kuwa da gaskene. Hannu yakai bisa sajensa ya ɗan shafa, kafin ya bar wajen batare da ya bari sun
gansaba.
Moos’ab ne ya farga da ƙamshin turarensa. Yaɗan janye Saifudden yana faɗin, “Bro ƙamshin turaren Yayanmu fa kamar nakeji”.
Saurin ja baya Saifudden yayi shima yana waige-waige, sai dai basuga kowaba a wajen, “Inaga hancin kane kawai, kaga zomuje karma a nememu”.
Koda AK yabar wajensu nufar inda su Dr Mahmud suke yayi, inda ya samu wani maroƙi yanata zabgama masa kirari duk zatonsa shine angon. Yana ganin AK ya
iso ko yay saurin kamo hannunsa da nuna musu shi, “Yauwa to ga angon nan bayin ALLAH”. Ya faɗa yana ciro kuɗi ya miƙa musu yana tura AK gabansu yana dariya.
Idanu sosai AK ya waro waje ganin sun zagayesa suna masa ihu akai, ai gudun hayaniyar tasu ya sashi babu shiri ciro kuɗi ya miƙa musu yana harar Dr
Mahmud daya koma gefe yana kwasar dariyar mugunta, su Mas’ood na tayashi ƙasa-ƙasa.
Jama’ar gari kuwa ganin ango yasa suketa sake tofa albarkacin bakinsu. Wasu suce ita cikin shege ya mata riba, wasu suce koma shine abokin tsiyar
tata, wasu su tayata murna, wasu suce sakkayar ALLAH ce ga zalincin da Inna tai mata, wasu suce baisan ta taɓa yin cikiba ƙila data bar garin ta zubar ne.
Wasu ko hassadace kawai, kasancewar sunso zinneerah ɗin basu samuba. Magana dai iri-iri. Har takai wani ya samu AK gefe yana masa gulmar wai kuwa yasan waya
aura?.
AK dake jingine jikin mota yana latsa waya ya ɗago ya dubi mutumin ƴar walwalar fuskarsa na ɓacewa ɓat. Amma duk da haka mutumin nan sai yay ƙasa da
kai yana wani soshe-soshe. “Ayi haƙuri Alhaji, ganinka mutum mai tarin kamala da mutunci yasa naji bara na faɗa maka gaskiya, dan na tabbatar an rufekane
akan yarinyarnan. Duk da kafin faruwar komai kowa yasan yarinyar kirki ce a garin nan dan har kwatance akema yara akanta. Amma daga ƙarshe ta ɓata rawarta
da taalle. Dan kuwa cikin shege tayi, Katsina tabi saurayi sukayo kusan mako biyar sannan suka dawo, a dalilin cikinne ma ta gudu a ƙauyen nan babu wanda ya
sake jin labarinta sai yau da kukazo wai aurenta. Nifa k……..”
Wani shegen kallo da AK ya dasa masa dai-dai ya ɗago ya sashi saurin haɗiye sauran zancen yana zazzare ido. AK ya gyara tsaiwarsa idanunsa na canja
launin ɓacin rai, cikin nutsuwarsa da rashin sakewa yace, “To dakazo kana faɗamin idan kuma nine nayi cikin fa?”.
A razane mutumin ya waro idanu waje. Sai kuma yay saurin yin ƙasa da kansa yana girgizawa. “Haba-haba Alhaji ni nasan hakanma bazata faruba. Ai daga
ganinka anga mutum mai mutunci da kamun kai, kawai dai an rufekane, amma dan ALLAH karka bari so ya rufe maka ido ka ɗaukama ƴaƴanka uwar banza”.
“Ai kaine banzan sha-sha-sha” AK ya faɗa a fusace, cikin kaushin murya yace, “Mutumin banza kawai, saboda tsabar rashin mutunci ko kunya bakajiba kai
kazo kana aibantamin mata? To bara na sanar maka kaima kaje ka sanar tunda naga shine aikinka. Shi wannan cikin da kuka ganta dashi nawane. Nine nai mata
kuma ta haifamin, daɗin hakannema yasa na aureta yanzu stupid ɓacemin anan”.
Da sauri mutum yabar wajen kuwa tamkar zai kifa, AK ya rakashi da wani irin kallon tsana da takaici, tsabar takaici dole ya buɗe motar da yake a
jingine ya shiga batare daya rufe murfinba ƙafafunsa a waje. Sosai launin idanunsa suka sake canjawa, badan kar ace yayi ƙarantaba da lallai saiya nunama
shegen mutumin nan kuskurensa yau wlhy. Tsaki yaja da dafe kansa dahar ya fara masa ciwo ƙasa-ƙasa zuciyarsa na masa zugi. Tabbas yanada buƙatar dawowa
ƙauyen nan domin wanke yarinyarnan duk da har yanzu baisan yaya ya samar da Abdul-Mutallab ba…..
“Yayanmu!” Moos’ab ya sake kiran sunansa a karo na uku.
Sai yanzu kunnensa ya ji, ɗago idanunsa yay ya dubesa, Moos’ab yay ƙasa da kansa cikin girmamawa yace, “Baffah ke kiranka”.
Komai baicema Moos’ab ɗinba ya fito a motar ya nufi cikin zauren maigari inda su Baffah suke tattaunawa da Baba akan abinda suka sani game da ƙaddarar
data afkama Zinneerah da har yau basusan mafarintaba.
Waje ya samu ya zauna yana ƙoƙarin ɓoye ɓacin rai da takaicin da mutumin can ya cusa masa. Cikin girmamawa ya sake gaida su Baba dan yanzu dai a
matsayin suruki yake. Sosai baba yaji daɗin wannan girmamawa. yakumaji a ransa AK ya kwanta masa, yana taya ƴarsa murna dajin insha ALLAH ta samu mijin
marainiya.
A nutse baba ya sake maimaita masa bayanin da yayma su Baffah game da Zinneerah, sannan a ƙarshe ya roƙesa alfarmar dawowar Zinneerah danya domin
shirya mata biki nanda wata ɗaya.
Ɗan murmushi AK yayi kansa a sunkuye yace, “Baba karka damu, duk yanda kukaso muyi mu masu biyayyane a gareku, sai dai kayi haƙuri a yanzu bata ƙasar
tana can London, insha ALLAH nan da sati biyu zata dawo”.
Cikin ɗan waro ido Kawu Rabilu yace, “Landan kuma? Ita Zinni ɗin?”.
Sosai yanda Kawu Rabilu yayi ya basu Saifudden dariya. duk sukai ƙasa dakai suna gumtse bakuna. Baffah ne ya amsama kawu Rabilu da cewar, “Eh suna can
gidansa tare da mahaifiyata da taje ganin likita. Amma kamar yanda ya faɗa insha ALLAH nanda sati biyu zasu dawo, kuma insha ALLAH suna dawowa zata dawo nan
ɗin itama a ɗauketa kamar kowace ƴa a kaita gidan aurenta”.
Jinjina kawuna suka shigayi na gamsuwa. Yayinda bakin Baba da nasu Kawu ya kasa rufuwa. Kasancewar yamma tayi sukai haramar tafiya. Naman zabi da
basuciba haka maigari yasa aka saka musu a mota hardasu tsarabar mangwaro, gwaba, kashu da nono da ƙwan zabbi. dan su Baba suma sai gasu da nasu tsarabar
harda Gwaggo Laritu da labari ya kaima ta bakin ƴaƴanta.
Lokacin da zasu wuce haka jama’a suka zagaye motocinsu anata ɗaga musu hannu. Sosai su Baffah sukaji daɗin wannan karamci, dan haka suka tafi zukatansu
fes kowa na ALLAH ya sanya alkairi.
★★★
Tun kafin Baba ya shigo gida labari ya samu su Inna. Zaune ta tashi dangangan kamar ba itace kwance kashirɓan tana kukan ciwo da ɗan nishi ba. Cikin
masifa take cema mai kawo labarin, “Kukam dai annamimanci bai muku kaɗan abaki Sahware. In banda shegen munahinci yaushe kikaga wata Zinni da har za’a
ɗaurama aure. Dalla hice mani agida kahin nai miki bankaɗa wlhy”.
Baki Safare ta taɓe tana faɗin, “To oho ni dai Asabe. Koki yarda ko karki yarda yanzu na wuto ana ɗaura auren Zinni a masallacin juma’a. Banga
dalilin da zaisa nazo na hiɗi abinda bashike nanba”.
“Kai kedai Sahwar ALLAH ya tsine maki albarka bankaɗaɗɗiyar mata watsatstsiya. Ki hitamin a gida wlhy kona nafka maki shegen duka naga mai ƙwatarki”.
Fita Safare tayi tana wata shegiyar dariya. Ana haka kuwa sai ga Tinene ta shigo gidan a guje tana hakki.
“Ke kuma lahiya kika shigoma mutane kamar wata korarra?”.
Yaya Gajeje ta faɗa dan shigowarta kenan gidan ko zancen Safare batajiba.
Cikin hakki Tinene ta dafe kanta dake mata ciwo dan dama sayan paracetamol ta fita yi, tace, “Inafa lahiya Yaya Gajeje. wlhy wani labari najiyo yanzun.
ga baba can a babban massallaci an ɗaura auren Zinni da wasu mutane manyan ƴan gayu al-qur’an”.
Tsit gidan yayi na wucin gadi, sai da Sa’a tace, “Inna anya kuwa maganarnan bada gaske bane? Bara dai na hita nima na jiyo mana”.
Yaya gajeje da sai yanzu taji abinda ke faruwa cike da zumuɗi tace, “Jeki jeki maza Sa’a. Kai ALLAH ya tabbatar da wannan zance da nayi hwarin ciki
mara misali wlhy”.
Amaryar Baba da duk ke saurarensu tun ɗazun bata tsoma bakiba ta kalli Yaya Gajeje da cewa, “Wacece wai ita Zinni ɗin?”.
Kai tsaye Yaya Gajeje dake murmushi tace, “Ƙanwarmuce itama mama……..”
A fusace Inna ta zaburo tana watsama Yaya Gajeje harara, “Ƙanwarku a gidan ubanwa. Gajeje ki kiyayeni. Ke kuma munahika da kike tambaya bara a faɗa
miki, itana ƴar kishiyace da zaman gidan nan ya gagareta kamar yanda kema zai gagareki. Dan wlhy na ɗau alwashin yanda na watseta kema saina watseki a gidan
nan dama garin nan baki ɗaya”.
Murmushi amarya tayi tana ɗauke kanta batare datacema Inna komai ba. Hakan kuwa ba ƙaramin harzuƙa zuciyar Inna yayiba. Ta miƙe dingangan kamar ba ita
ke ciwo ba tahau zazzaga bala’i tana zagin amarya da mmn sadiq da Zinneerah. A wannan bala’in baba ya shigo shi dasu kawu da yara ɗauke da kayan sweets dasu
biscuits da huhunan goro cikin gidan. Suna shigowa Gwaggo Laritu ma na shigowa………
★★★★
A ɓangaren su Baffah kam tunda suka bar Danya kowa ke tattauna karamcin da akai musu da abokin tafiyarsa. Motar su AK ce kawai ta kasance shiru dan
tunda suka tafi ya jingina kansa da kujera ya lumshe idanu yana tariyo maganar mutumin nan ma ɗazu daki-daki cikin ransa. Lokaci-lokaci Dr Mahmud kan
kallesa yayi murmushi. Sai da suka kusa shiga cikin kano ne ya ɗan sake dubansa da tsokana, “Haba ango duk daɗine ya saka zama kurman ƙarfi da yaji?”.
Shiru AK bai motsaba, sai da ya mula dan kansa ya ɗan buɗe ido ya harari Dr Mahmud ɗin, cikin rashin sakewarsa yace, “Dama haka kake da sa ido?”.
Dariya sosai ta kama Dr Mahmud har yana dukan sitiyari. Hakan ya saka AK ɗan sakin murmushi ya maida kansa ya sake kwantarwa da lumshe idanu. daga
nan bai ƙara tankawa Dr Mahmud ɗinba daya cigaba da tsokanarsa har suka isa gida.
Sun iso suka iske hajiya Bilkisu da suke kira da Mommy ta iso tare da babban ɗanta Huzaifa. Huzaifa kusan sa’an AK ne, sai dai AK ya girmesa da kusan
shekara biyu, amma ayanzu abokaine, dan saima suna tsokanar junane zaka iya sanin AK ɗin ya girmi Huzaifa.
Dr Mahmud na ajiyesa bai shigaba ya juya gida danya huta shima. Hakan yasa AK nufar sashen Hajiya Iya shi kaɗai, su Haneef kuwa duk sashen iyayensu
sukai kai rahoton ɗaurin aure. Hakama Baffah ɗokin jin zuwan ƴar uwarsa yasashi nufar sashen nasa kai tsaye dan tanacan, tunda bada yara tazo ba duka bazata
sauka a nata sashen ba.
Tunda AK ya shigo yaga Huzaifa zaune a falon Hajiya iya yanacin abinci sai ya ɓata rai cikin ɗan wasan da suka saba yace, “Oh oh yaushe wannan bawan
yazo mana gida” ya faɗa yana harar Huzaifa.
Dariya Huzaifa ya fashe da ita, saida yayi mai isarsa ya haɗe fuska yana harar AK ɗin shima. “Eh lallai ka nunamin kayi aure na biyu, ninema Bawan naka?
Yaro jeka bincika ni dakai wanene bawa?”.
Hannu AK yasa ya tallare ƙeyar Huzaifan. Yay gaba da sauri yana faɗin, “Magananne jeka bincika kaidai”. Ya faɗa yana shigewa ɗakinsa murmushi ɗauke
akan fuskarsa. Dan inhar yana tare da Huzaifa kobaiyi niyyar fara’a ba sai ya sakashi yinta dole saboda shi mutumne mai barkwanci dason wasa.
Cikin ihu Huzaifa yace, “Jeka fito ka sameni mijin mata biyu, indai maganace kuwa ka haɗu da ita yau ko barci bazan barka kayiba”.
AK na jiyosa daga ɗakin, dan haka ya girgiza kansa kawai yana murmushi. Kayan jikinsa ya cire ya nufi toilet dan watsa ruwa a gaggauce lokacin sallar
magrib karya ƙure masa.
★★
Abba kam koda ya isa gida da albishir ɗin ɗaura auren Zinneerah da AK ga Mmn sadiq sai kawai ta fashe da kuka dan farin ciki, Abba dake mata dariya
ya rungumeta yana lallashi.
“Tabbas mutanen nan sun cancanci yabo Hauwa’u. Dan halayyarsu na mana nuni da cewar har yanzu akwai mutanen ƙwari masu mutunci da sanin yakamata a
cikin masu arziƙi bakamar yanda mu mutane muke zargiba. Inda ace ana samu mutane irinsu Alhaji Kabeer Shira koda a talakawanma wlhy da duniya ta zauna
lafiya. Amma yanzu zakiga kowa ɗansa kawai da mutuncinsa yake karewa. Babu ruwansa dabin gaskiya koda ace yana ganinta ƙuru-ƙuru kuwa. Sau da yawa akan ɓata
tarbiyyar yarinya amma kiji iyayen yaron na amabaton ɗansu bazai auri lalatacciya ba. Bayan kuma bata lalaceba sai da taimakon ɗan nasu. Tare suka aikatafa,
amma sai a nuna tsangwamar macen fiye dashi namijin dan son zuciya. Bayan kuma shi namijin yafi macen hankali, ko ya girmeta, maybe ma shine yay amfani da
wayonmu na maza ya lalata mata rayuwar tata. Hakan zaluncine dason zukata muke aikatawa wajen ƙasƙantar da mace akan zunubi koda kuwa tare ta aikatashi da
abokin halittarta namiji.”
Hawaye mmn sadiq ta share tana duban mijin nata, “Yaya ai mutanen duniya haka suke tun na ƙarnin farko, suna amfani da raunin ɗiya mace akoda
yaushe wajen sake raunanata, sun mance a ɓangaren zunubi da hukunci duk iri ɗaya UBANGIJI zai mana ga duk wanda ya saɓa masa. Wlhy bammasan yanda zan
musalta maka daraja da kima ta mutanen nanba a zuciya ta, sukam waɗanne irin mutanene haka masu tarin adalci da sanin darajar ɗan adam?”.
Cikin dariyar farin ciki Abba yace, “Tabbas sun cika ƴan baiwa, dan samun irinsu a cikin al’ummarmu sai an tona. Amma akwaisufa. Yawaitar masu son
zuciyarne ya lulluɓe irinsu saboda ƙarancinsu a cikin mutane. ALLAH ya bamu ikon koyi dasu”.
“Amin” mmn sadiq ta faɗa wani irin sanyi da nutsuwa na saukar mata lokaci guda.
Abba yace, “Yauwa inaga ki shirya Abdul-Mutallab zasu aiko a ɗaukesa daga can gidan wai ƙanwar Alhaji Kabeer ɗince zatazo daga Lagos yau, itama za’a
kaimata shi ta gansa”.
Kai mmn sadiq ta jinjina masa tana faɗin, “To bara ka gani naje na tadashi a barci can kuwa sai nai masa wanka basai sunzo sunyi zaman jiraba”.
Cikin gamsuwa da bayaninta ya kaɗa mata kai……….✍
_Kuyi manage da wannan an mana rasuwane ban samu zaman nustuwar typing ba😊🙏🏻_.
*_A page na ƙarshe na ranar Friday akwai inda nai kuskure, hakan ta farune dalilin rashin yin editin ranar, nayi typing na gaji. Inda nasa AK yayi limancin
sallar zuhur nayi maganar yayi karatun salla har mutane na ambaton anyi baƙon balaraben limami. Please amin afuwa. Wannan ajizancine na ɗan adam sai daga
baya na farga dalilin maganar da wata tayi na sake komawa na duba page ɗin. Ina ƙara bada haƙuri Please, mantuwa ce da rashin editin kamar yanda na faɗa tun
farko😊🙏🏻_*
*Barkanmu da dawowa hutun weekend😍😍😘😘😘💃🏻*
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
GIPHY App Key not set. Please check settings